Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Habiba Adamu, Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Malaman Kano sun sasanta Abba Kabir da Sheikh Daurawa

    Gamayyar malaman addinin Musulunci ta jihar Kano ta ce ta sasanta gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf da Kwamandan Hisbah na jihar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa bayan rashin jituwar da ta kai ga ajiye aikin shugaban na Hisbah.

    Bayan wata ganawa da ta gudana a daren ranar Litinin a gidan gwamnatin jihar ta Kano, sakataren Gamayyar malaman, Dakta Sa'id Ahmed Dukawa, ya bayyana cewa sun shiga tsakani ne sanadiyyar kiraye-kiraye daga ciki da wajen jihar na ganin an warware matsalar.

    A cewarsa, matsayar da aka cimma na nufin cewa a yanzu babu batun murabus din Sheikh Daurawa daga shugabancin Hisbah.

    Dukawa ya ce: "Ya (Daurawa) dawo aiki, zai ci gaba da aikinsa".

    A ranar Juma'ar makon da ya gabata ne Sheikh Aminu Daurawa ya sanar da saukar sa daga kan muƙamin na shugaban Hisbah.

    Daurawa ya ce ya yi hakan ne bayan kalamai na kashe ƙwarin gwiwa daga gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf.

    Kwana ɗaya kafin nan, gwamna Abba Kabir ya bayyana rashin gamsuwa game da salon wasu ayyukan hukumar ta Hisbah, inda ya kushe matakin da jami'an hukumar ke ɗauka na tursasa wa waɗanda ake zargi da ayyukan 'rashin ɗa'a' shiga motar sintiri.

    Lamarin ya janyo zazzafar muhawara a ciki da wajen jihar, inda wasu ke ganin cewa kalaman gwamnan tamkar watsa wa kwamandan Hisban ƙasa a ido ne.

    Sai dai makusantan gwamnan sun kare shi, tare da cewa an yi wa kalaman nasa mummunar fassara.

    Wannan ne karo na biyu da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa zai sake komawa kan kujerar ta shugabancin Hisbah bayan yin murabus don ƙashin kansa.

    Malamin ya taɓa yin murabus a lokacin tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje bayan saɓanin da ya samo asali daga bambancin ra'ayi mai nasaba da siyasa.

    Sai kuma wannan karo inda ya sauka sanadiyyar rashin jin daɗi da gwamnan jihar ya nuna kan wasu matakan da yake ɗauka wurin yaƙi da ayyukan matasa waɗanda ke yaɗa ɗabi'u da suka saɓa wa addinin Musulunci a fili da kuma a shafin tiktok.

    • Abun da ya sa na ajiye shugabancin Hisbah
    • Yadda masu kuɗi ke lalata ƴaƴan talakawa a Kano – Daurawa
  2. Asuba ta gari

    Nan muka zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Nabeela Mukhtar Uba da Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  3. Yara na mutuwa saboda yunwa a arewacin Gaza - WHO

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus , ya ce yara na mutuwa saboda yunwa a arewacin Gaza.

    Tedros Ghebreyesus ya ce ziyarar da hukumar ta kai a karshen mako a asibitocin Al-Awda da Kamal Adwan ita ce ta farko tun farkon watan Oktoba.

    A wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta, ya yi magana kan mummunan yanayi da ake ciki a Gaza.

    Rashin abinci ya yi sanadin mutuwar yara 10, yayin da aka lalata gine-ginen asibitoci, in ji shi.

    Ma'aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta bayar da rahoto a ranar Lahadi cewa aƙalla yara 15 ne suka mutu sakamakon rashin abinci mai gina jiki da kuma rashin ruwa a asibitin Kamal Adwan.

    Wani yaro na 16 ya mutu a ranar Lahadi a wani asibiti da ke kudancin birnin Rafah, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Falasɗnu Wafa ya ruwaito a yau Litinin.

    Dr Tedros ya bayar da rahoton cewa akwai mummunan yanayin rashin abinci, yara na mutuwa saboda yunwa, matsanancin ƙarancin man fetur, babu abinci da magunguna, sannan an kuma lalata gine-ginen asibitoci a arewacin Gaza.

    An kiyasta cewa mutane 300,000 ke rayuwa da matsalar ƙarancin abinci ko tsaftataccen ruwa.

  4. Sakatariyar harkokin wajen Colorado ta nuna rashin jin daɗinta ga hukuncin Kotu a kan Trump

    Sakatariyar harkokin wajen jihar Colorado, Jena Griswold ta fitar da wata sanarwa a shafukan sada zumunta inda ta nuna rashin jin daɗinta ga matakin kotun ƙoli cewa Colorado ba ta da hurumin soke Trump daga zaɓen fitar da gwani.

    Griswold ta ce matakin ya janye wa jihar ikonta na ƙaƙaba sashe na 3 na dokar da aka yi wa gyaran fuska.

    Ta ce ya kamata Colorado ta iya hana masu karya rantsuwar zaɓe tsayawa takara," in ji ta.

    Griswold ta kare tsarin shari'a a Colorado da ya ce Trump bai cancanci tsayawa takara ba amma ta bayyana ra'ayin kanta game da batun.

  5. Za a ci gaba da shari'ar jagoran ƙungiyar ƴan tawayen Uganda – ICC

    Alƙalai a kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ta yanke cewa masu gabatar da ƙara na iya gabatar da ƙara kan tuhume-tuhumen da ake yi wa jagoran yaƙi a Uganda duk da cewa ba ya nan.

    Joseph Kony ne jagoran ƙungiyar ƴan tawaye ta LRA wadda ta sace dubban yara domin mayar da su sojoji ko cin zarafinsu.

    An tsara sauraron ƙarar ranar 15 ga watan Oktoba.

    Ana zarginsa da aikata laifukan yaƙi 33 da laifuka kan bil adama.

    Joseph Kony ya kafa ƙungiyar LRA a Uganda shekaru ashirin da suka gabata inda ya yi iƙirarin yana yaƙi ne domin kafa gwamnati bisa dokoki 10 na Littafin Injila.

    An gabatar da takardar izinin kama Mista Kony a 2005 sai dai ya tsere.

    A n taɓa samun lokacin da sojojin Uganda da Amurka suka bibiye shi amma suka yanke ƙauna a 2017 inda suka bayyana cewa raguwar da magoya bayansa suka yi na nuna cewa ba shi da sauran tasiri.

    Ana kuma zarginsa da azabtar da farar hula a arewacin Uganda ta hanyar kisa da sacewa da kuma lalata dukiya.

    A makon da ya gabata ne, ICC ya biya dala miliyan hamsin da shida ga mutanen da kwamandan LRA Dominic Ongwen ya ci zarafinsu.

  6. Kano Pillars ta yi rashin nasara a hannun Abia Warriors

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta yi tuntuɓe a babbar gasar tamaula ta Najeriya bayan ta yi rashin nasara da ci 1-0 mai ban haushi a hannun Abia United a wasan da aka buga a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

    Wannan sakamako na nufin cewa Pillars za ta ci gaba da kasancewa a mataki na 6 a teburi inda ta ke da maki talatin da shida.

    Ƙungiyar ta sai masu gida dai za ta buga wasanta na gaba ne a ranar Asabar 9 ga watan maris inda za ta ziyarci Rivers United.

  7. Faransa ta sa ƴancin zubar da ciki cikin kundin tsarin mulkinta

    Faransa ta zama ƙasa ta farko a duniya da ta sa ƴancin zubar da ciki cikin kundin tsarin mulkinta.

    Ƴan majalisar sun kaɗa ƙuri'ar a sake nazarin kundin tsarin mulkin ƙasar na 1958 domin tabbatar da ƴancin mata na zubar da ciki.

    Ƴan majalisa 780 sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da ƙudurin yayin da 72 suka nuna ja. Ƴan majalisar sun miƙe tsaye a harabar zauren a lokacin da aka sanar da sakamakon ƙuri'ar.

    Shugaba Emmanuel Macron ya bayyana matakin a matsayin abin alfahari ga Faransa wanda kuma ya aike saƙo ga duniya.

    Ƴancin zubar da ciki na cikin doka tun 1975 sai dai ƙuri'a ta nuna kusan kashi 85 cikin 100 na al'umma sun amince da gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin domin kare ƴancin zubar da ciki.

    Shi ne gyara na 25 da aka yi wa kundin tsarin mulkin na Faransa, kuma na farko tun 2008.

    Kafin jefa kuri'ar, Firaiminista Gabriel Attal ya shaida wa majalisar cewa ikon zubar da ciki na ci gaba da fuskantar barazana kuma batu ne da ke hannun masu ruwa da tsaki".

  8. Za a fara sabon tsarin Champions League daga kakar wasa ta 2024/2025

  9. Ƴan bindiga sun buƙaci Firaministan Haiti ya yi murabus bayan fasa gidan yari

    Gwamnatin Haiti ta kafa dokar ta-ɓaci ta sa'o'i 72 a ranar Lahadi bayan wasu gungun 'yan bindiga ɗauke da makamai sun fasa wani babban gidan yari.

    Aƙalla mutum 12 ne aka kashe sannan wasu fursunoni 3,700 suka tsere daga gidan yarin.

    Gungun ƴan bindigar sun buƙaci Firaminista Ariel Henry ya yi murabus, wanda ba a san inda yake ba tun bayan da ya yi bulaguro zuwa Kenya.

    Ƴan bindigar dai na iko da kusan kashi 80 na Port-au-Prince, babban birnin ƙasar.

    Haiti ta shafe tsawon shekaru tana fama da rikicin ƙungiyoyin ƴan bindiga.

    Sanarwar da gwamnatin ƙasar ta fitar ta ce, a ƙarshen mako ne aka afka wa gidajen yari guda biyu - ɗaya a Port-au-Prince da kuma wani na kusa da Croix des Bouquets.

    Ta kwatanta ayyukan ƴan bindigar a matsayin barazana ga tsaron ƙasa kuma ta ce ta kafa dokar hana fita ta dare a matsayin mayar da martani, wadda ta fara da misalin karfe 20:00 agogon ƙasar a ranar Litinin.

  10. Matsin Rayuwa: Gwamnatin Najeriya za ta fara raba wa ƴan ƙasar hatsi

    Gwamnatin Najeriya ta ce za ta fara raba hatsi a faɗin ƙasar a wani mataki na rage matsin rayuwa da ƴan Najeriya suke ciki.

    Ministan aikin gona Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a yau Litinin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

    "Ina bai wa ƴan Najeriya da suke cikin halin matsin rayuwa haƙuri. Na san halin ƙunci da ake ciki, musamman ganin fasa rumbunan abinci da kuma wawaso da aka yi," in ji ministan.

    Ya ce yana son ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa gwamnati na ci gaba da ƙoƙari na ganin abubuwa sun kyautata.

    Sanata Kyari ya ce shugaban ƙasa ya amince a fara raba hatsi da ya kai tan 42,000 a faɗin jihohi 36 na ƙasar a wannan mako.

    "Muna aiki hannu da hannu da hukumar NEMA da kuma jami'an tsaro na farin kaya DSS don tabbatar da cewa hatsin ya kai hannun mutanen da ya kamata.

    Ministan ya ƙara da cewa za a fitar da tan 58,500 na shinkafa zuwa kasuwanni a cikin farashi mai rahusa.

    Har ila yau, ministan ya buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da mara wa gwamnatin shugaba Bola Tinubu a kokari da take yi na ganin ta shawo kan matsaloli da ƙasar ke fuskanta.

    • Ko shigar da abinci Najeriya zai samar da mafita ga tsadar rayuwa?
  11. La Liga na bincike kan zargin cin zarafin Vinicius Jr a wasan Real da Valencia

  12. An rufe layukan waya sama da miliyan 11 a Najeriya

    Hukumar da ke sa ido kan harkar sadarwa ta Najeriya, NCC ta tabbatar da rufe layukan masu wayoyin salular da basu haɗa da lambar shaidar zama ɗanƙasa ba.

    A makon da ya wuce ne hukumar ta bai wa kamfanonin wayoyin salula umarnin rufe layin duk wani wanda bai haɗa layin wayarsa da NIN ba ya zuwa ranar 28 ga watan Fabairun, 2024.

    Wasu kafofin watsa labarai na ƙasar sun ce waɗanda lamarin ya shafa sun kai miliyan 11 da dubu 200.

    Sai dai wata hira da wani gidan talabijin na cikin ƙasar, kakakin hukumar , Reuben Muoka ya ce zai yi wuya a ce ga yawan layukan da aka rufe, amma NCC za ta yi kididdiga kafin ƙarshen wannan makon, bayan sun samu alƙaluma daga kamfanonin sadarwar.

    “A ɗauka cewa duk wani wanda bai bayar da NIN ɗinsa ba an rufe layinsa. A haƙiƙanin gaskiya ma tun kafin cikar wa'adin wasu kamfanonin sadarwan suka fara rufe layukan mutane. Ya shaida wa Channels TV.

    Haka kuma ya yi tsokaci kan wasu masu wayoyin da suka ce sun riga sun haɗa NIN ɗinsu da lauyukansu amma duk da hakan an rufe layukansu, inda ya ce an rufe wasu layukan ne saboda ta yiwu NIN ɗin da suka bayar bai zo daidai da wanda suka yi rajista ba.

    Masu irin waɗan nan matsaloli a cewarsa, dole su je kamfanonin sadarwar da kansu domin a gyara matsalolin.

    A baya dai hukumar ta sha sanya ranar rufe layukan mutanen da basu haɗa da lambar shaidar zama ɗanƙasar ba, sai dai a wannan karon ta ce babu batun ɗagewa.

  13. Rundunar sojin ruwan Afirka ta Kudu na neman yarinya ƴar shekara shida da ta ɓata

    Rundunar sojin ruwan Afirka ta Kudu ta bi sahun binciken gano wata yarinya ƴar shekara shida da ɓatan ta ya jefa ƙasar cikin damuwa.

    Joslin Smith ta yi ɓatan dabo ne daga gidansu da ke Saldanha Bay kusa da Cape Town, mako biyu da ya gabata.

    Sojin ruwa ɗari uku ne suka bi sahun masu binciken daga birnin Cape Town da sashen karnuka da kuma jirage maras matuƙa.

    Mutane da dama na tambayar dalilin da ya sa ba a iya gano ta ba. Yaro ɗaya na ɓata duk sa'a biyar a Afirka ta Kudu amma galibi ana gano su.

    Masu bincike na da yakinin samun nasara bayan da aka gano kaya jiƙe da jini a wani buɗaɗɗen wuri da ke kusa.

    Abubuwan da aka gano an aike su ɗakin gwaje-gwaje domin gudanar da ƙarin bincike.

    Kakakin ƴan sanda, Birgediya Novela Potelwa ta faɗa wa BBC cewa an tura sojojin ruwan domin taimakawa wajen gano yarinyar.

    Ba a cika samun sojojin ruwa na taimakawa wajen gano farar hula da suka yi ɓatan dabo ba amma su kan yi haka idan ƴan sanda suka nema.

    An dai yi tayin rand dubu ɗari ga duk wanda ya bayar da bayani kan inda yarinyar take inda shafukan sada zumunta suka cika da fata da addu'oi cewa za a gano Joslin da ranta.

    • 'Abin da ya sa muka tsani baƙi a ƙasarmu'
    • Dalilin da ya sa jam’iyyun siyasa 7 suka ƙulla ƙawance a Afrika ta Kudu domin ƙalubalantar ANC
    • Rashin lantarki ya jefa ƴan Afrika ta kudu cikin ƙaracin ruwa
  14. Trump na da cancantar ci gaba da takara – Kotun Ƙoli

    Kotun ƙolin Amurka ta soke yunƙurin Colorado na haramta wa Donald Trump shiga zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa.

    Babbar kotu a Colorado ta cire sunan tsohon shugaban ƙasar daga takardar ƙuri'a a Disamba inda ta kare matakinta da sashe na 14 na dokar haramcin da aka yi wa gyaran fuska kan masu tayar da rikici da ke neman tsayawa takara.

    Sai dai alƙalan kotun ƙolin na shakku game da matakin a wani zama da aka yi ranar 8 ga watan Fabarairu inda suka zargi jihar da wuce gona da iri.

    Hakan na nufin Trump na iya shiga zaɓen fitar da gwani a gobe, a ranar da yake iya samun tikitin yi wa Republican takara.

    Colorado za ta kaɗa ƙuri'a tare da wasu jihohi 15 a babbar ranar Talata mai muhimmanci a zaɓen 2024.

    Ana sa ran Trump mai shekara 77 zai lashe zaɓen tare da kayar da abokiyar karawarsa ɗaya tilo, tsohuwar jakadar Majalisar Ɗinkin Duniya Nikki Haley.

    Martanin Trump kan hukuncin kotu

    Donald Trump ya mayar da martani game da hukuncin kotun ƙolin cewa Colorado ba za ta iya hana shi shiga zaɓen fitar da gwani ba.

    "Babbar nasara ce ga Amurka!!!", kamar yadda Trump ya wallafa a manhajarsa ta Truth Social

    Bayan nan kuma tsohon shugaban ya aika wani saƙon Imel inda yake kira ga magoya bayansa su bayar da gudummawa a yaƙin neman zaɓensa.

    "Ƙudurin Democrat na goge sunana bai yi nasara ba, amma yaƙinmu na ɗaukaka Amurka, ko kusa bai kare ba," kamar yadda saƙon ya bayyana.

    • Biden da Trump sun lashe zaɓen fitar da gwani a Michigan
    • Trump ya sake yin nasara a zaben Republican
    • Trump ya sake yin nasara a zaben Republican
  15. Aljeriya ta yi alkawarin taimaka wa Mozambique a yaƙi da masu iƙirarin jihadi

    Gwamnatin Aljeriya ta yi alkawarin taimaka wa Mozambique a yaƙi da masu garkuwa da mutane da kuma ayyukan masu iƙirarin jihadi waɗanda suka addabi lardin Cabo Delgado da ke arewacin ƙasar.

    Yarjejeniyar na zuwa ne bayan ziyarar kwanaki huɗu da shugaban ƙasar Mozambique Filipe Nyusi ya kai Aljeriya.

    Shugaba Nyusi ya faɗa wa manema labarai a ranar Lahadi cewa Aljeriya ta yi alkawarin mara wa dakarun ƙasar, musamman waɗanda ke faɗa da ta'addanci.

    Ya ƙara da cewa ƙasar ta Aljeriya za ta horas da sojojinsu da kuma aika musu makamai domin taimaka musu a yaƙi da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.

    Kasashen biyu dai na da kyakkyawar alaka ta tarihi.

    Alkawarin na Aljeriya na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni daga Cabo Delgado suka ce mayakan jihadi sun shiga birnin Quissanga a daren Juma'a, inda suka sace abinci tare da haifar da fargaba.

    Lardin Cabo Delgado mai arzikin iskar gas ​​ya kasance abin jan hankali ga ƙungiyoyin Islama da ke fafutukar iko da albarkatun ƙasar. Kamfanoni da yawa na ƙasashen waje na aiki a yankin.

    • Rikicin Mozambique: Abin da ya sa ƙasashe 24 suka tura sojoji ƙasar
    • Harin 'yan ta'adda a Mozambique: 'Ba zan iya komawa gida ba'
  16. Barcelona ta sake yin tuntuɓe a La Liga

  17. United ba ta cire rai kan Champions League ba - Ten Hag

  18. Kungiyar EU ta ci tarar Apple dala biliyan biyu

    Hukumar gudanarwar tarayyar Turai ta ci tarar kamfanin Apple dala biliyan biyu kan karya dokokin kare masu amfani da wayoyin a Turai.

    Shugaban hukumar da ke sa ido akan gogayya tsakanin kamfanoni, Margarethe Vestager, ta ce a tsawon shekaru kamfanin ya yi amfani da damarsa ta kasancewa mafi shahara wajen hana mutane su san cewa akwai masu manhajoji masu samar da waƙoƙi a farashi mai rahusa.

    "Ya zama dole mu sa ido kan kamfanoni irinsu Apple da ke karya dokokin kare masu amfani da wayoyin a Turai," in ji Vestager.

    Ta kuma umarci kamfanin na Amurka ya cire duk wasu shingaye da yake sawa domin ganin masu amfani da wayoyinsa walwalawa. Sai dai kamfanin Apple ya ce zai daukaka kara.

    • An sayi tsohuwar wayar iPhone kusan naira miliyan 32
    • Brazil ta hana sayar da wayoyin iPhone marasa caja a kasar
  19. PDP ta saka ranar zaben fitar da gwani na gwamna a Ondo

    Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP ya fitar da jadawalin abubuwan da jam'iyyar zata yi gabannin zaɓen gwamna a jihar Ondo.

    Hukumar zabe ta Najeriya ta sanya ranar 16 ga watan Nuwambar,2024, a matsayin ranar da za a yi zaɓen gwamna a jihar ta Ondo.

    Jadawalin wanda ke ɗauke da sa hannun sakataren gudanarwar PDP na ƙasa, Umar Bature, ya ce za a yi zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar a ranar Alhamis 25 ga watan Afrilu, 2025.

    Haka kuma a ranar 9 ga watan Mayu ne kwamitin gunarwar jam'iyyar zai bai wa ɗantakarar mataimakin gwamnan takardar shaida.

    Sannan ranar 20 ga watan na Mayu ce za ta kasance ranar ƙarshe na miƙa sunan wanda zai yi wa jam'iyyar takarar gwamna a jihar ga hukumar zaɓen ƙasar.

    Jadawalin ya kuma ce ranar 10 ga watan Yuni za ta kasance ranar ƙarshe ta musanya sunan ɗantakara.

    • PDP da APC na cacar baki kan sauya sheƙar 'yan majalisar dokokin jihar Rivers
    • Me ya sa PDP ta kasa hukunta Nyesom Wike?
  20. 'Dokar hana auren jinsi za ta shafi tattalin arzikin Ghana'

    Ma'aikatar kuɗi ta Ghana ta bayar da shawarar kada a sanya hannu a dokar haramta auren jinsi da ta janyo cece-ku-ce, wadda kuma majalisar dokokin ƙasar ta amince da shi a makon jiya.

    Ma'aikatar ta bai wa shugaban ƙasar, Nana Akufo-Addo shawarar ya jinkirta sa hannu a ƙudurin dokar kuma ya bari kotun ƙolin ƙasar ta yanke hukunci a kan cewa ya dace ko ya ci karo da kundin tsarin mulkin ƙasar.

    A wata sanrawar da ta fitar, ma'aikatar ta yi gargaɗin cewa Ghana za ta iya yin asarar kusan dalar Amurka biliyan huɗu na kuɗaɗen da babban bankin duniya zai bata a cikin shekaru biyar zuwa shida idan har an zartar da dokar.

    A wannan shekarar kaɗai a cewar ma'aikatar kuɗin, Ghana za ta iya asarar dalar Amurka miliyan 850 na tallafi, abin da jami'an suka ce zai iya shafar tattalin arzikin ƙasar da ke tangal-tangal da asusun ajiyar kuɗaɗen wajenta ya kuma shafi musayar kuɗaɗen wajen.

    Ghana na cin gajiyar wani shiri na asusun lamuni na duniya, IMF na tsawon shekara uku.

    Kuma ƙudurin dokar ya tanadi hukuncin shekara uku a gidan yari ga wanda aka kama da laifin auren jinsi da kuma shekara biyar ga waɗanda suke yaɗa abubuwan da suka shafi hakan.

    Amurka da Burtaniya na daga cikin waɗanda suka yi tur da amincewa da dokar. Yayin da shugaban ƙasar ke da wa'adin kwana bakwai ya sanya hannu a kan ta don ta zama doka ko kuma ƙin sanya hannu daga lokacin da aka kai masa.

    • Ko bashin dala biliyan uku da Ghana za ta ciwo zai fitar da ita daga ƙangin tattalin arziƙi?
    • Yadda Babban Bankin Ghana ya yi asarar dala biliyan 5 a shekara ɗaya