Rufewa
Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo karshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
A'isha Babangida and Nabeela Mukhtar Uba
Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo karshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Wannan ne masallaci mafi girma a Afirka, kuma na uku mafi girma a duniya.
Masallacin na da hasumiya mafi tsayi a duniya, kusan ninki biyu na tsayin Dalar Giza.
Hasumiyar masallacin na da tsayin mita 256, sannan zai iya daukar mutum 120,000 a lokaci guda.
Kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC, ta ce ba ta da sha'awar shiga harkokin siyasa ko rike wani mukamin siyasa ciki har da mukamin shugaban kasa.
Kungiyar na wannan batu ne a matsayin martani ga kalaman da shugaban kasar Bola Tinubu ya yi a kan kungiyar lokacin kaddamar da layin dogo na 'Red line' a birnin Legas ranar Alhamis.
A wani jawabi da shugaban kasar ya gabatar a wurin kaddamarwar ya ce bai kamata ƙungiyar ta shirya yajin aiki a watanni tara na mulkinsa ba.
“Ya kamata NLC ta fahimci cewa komai muka san 'yanci da haƙƙinmu, bai kamata ta kira yajin aiki a watanni taran farkon mulkina ba'', in ji Tinubu.
“Idan kuna son shiga zaɓe, ku jira 2027. in ba haka ba kuwa, a ɗore da zaman lafiya, saboda ba ku kuɗai ba ne muryar 'yan Najeriya.''
To sai sai a cikin martanin da kungiyar ta mayar wa shugaban cikin wata sanarwar da shugabanta Kwamared Joe Ajaero, ya sanya wa hannu, kungiyar ta ce ba ta da sha'awar neman kujerar shugaba Tinubu, amma abin da kungiyar ke so, shi ne shugaban ya aiwatar da yarjejeniyoyin da gwamnati ta cimma da kungiyar bayan cire tallafin man fetur.
Kwamared Ajaero ya ce kalaman da Tinubu ya yi kan kungiyar dangane da rawar take takawa a harkokin mulki, sun saba wa wahalhalun da 'yan Najeriya ke fuskanta sakamkon sabbin tsare-tsaren gwamnatinsa.
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce an samu yaro na 10 da aka tabbatar a hukumance, wanda kuma aka yi wa rijista a asibitin Gaza, da ya mutu a sanadiyyar yunwa.
Hukumar lafiyar Gaza da Hamas ke gudanarwa ce ke tattara sunayen.
Sai dai kakakin hukumar ta WHO, ya ce yawan yaran da suka mutu a sanadiyyar yunwar watakila ya fi haka.
Daman hukumomin agaji suna ta gargadi a kan yiwuwar samun ja'ibar yunwa a Gaza, muddin ba a kai karin kayan abinci da ruwa ba.
Kasashe da hukumomin duniya na kara matsa lamba kan Isra'ila dangane da mutuwar gomman Falasdinawa, da ke neman kayan tallafi daga wani jerin gwanon motoci a arewacin Gaza.
Shugabar hukumar gudanarwa ta tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta bi sahun jakudun kasashen Jamus da Faransam kan a gudanar da cikakken bincike kan lamari.
Tawagar likitocin asibitin yara na 'King Abdullah' da ke Saudiyya sun samu nasarar raba wasu tawagyen 'yan Najeriya da aka haifa manne da juna.
Jaridar Saudi Gazzet ta ce aikin raba tagwayen - wanda aka gudanar bisa umarnin Sarkin Saudiyya Salman bin Abdul'aziz da Yariman kasar, Mohammed Bin Salma - ya kasance wani gagarumin ci gaba a fannin lafiya da ayyukan jin kai na kasar.
A ranar 31 ga watan Oktoban 2023 ne aka kai tagwayen Saudiyya, bayan da gwaji ya nuna cewa wasu sassan jikin guda suke amfani da shi, kamar kashin kugu da kashin bayansu.
Aikin raba tagwayen - wanda likitoci 39 suka gudanar -ya kwashe sa'o'i 16.5, kuma shi ne aikin raba tagwaye na 60 da aka samu nasarar gudanarwa a asibitin na Saudiyya.
Asibitin ya kwashe tsawon shekara 30 yana gudanar da aikin taimakon tagwayen da aka haifa a manne daga kasashen duniya 25.
Babban Bankin Najeriya CBN ya sanar da rufe kamfanonin canji BDC 4,173.
Cikin wata sanarwa da CBN ya fitar a ranar Juma'a, ya ce ya rufe kamfanonin ne sakamakon gaza cika wasu ƙa'idoji masu yawa da aka gindaya musu.
CBN ya ce wadannan kamfanoni da aka rufe sun karya ɗaya daga cikin dokokin da ya shimfida na musayar kuɗi ta 2015, waɗanda suka hada da:
CBN dai ya yi alƙawarin ci gaba da bai wa masu kamfanin BDC dala a kowanne mako kamar yadda aka saba a baya.
Sai dai ya kuma lashi takobin hukunta duk wanda ya saɓa ƙa'idar da aka shimfida ta gudanar da hada-hadar a Najeriya.
Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci shugaban kasar Bola Tinubu ya sake nazarin rahoton Stephen Oronsaye - da ya bukaci hade wasu ma'aikatu da hukumomin gwamnati - kafin ya aiwatar da shi.
A farkon makon nan ne dai shugaba Tinubu ya bayar da umarnin yin aiki da rahoton, a wani mataki na rage kudaden da gwamnati ke kashewa.
To sai dai majalisar wakilan ta yi kiran a sake nazari kan rahoton kafin a aiwatar da shi, inda 'yan majalisar suka ce an samu sauyin lokaci daga lokacin da aka gabatar da rahoton.
Yan majalisar sun ce ''shekara 12 bayan gabatar da rahoton, hakan na nuna cewa rahoton ya tsufa, musamman yadda abubuwa ke sauyawa, kama daga mutane da tattalin arziki da tsare-tsare da fasaha da sauran fannoni''.
Sun kara da cewa sabanin imanin da aka yi cewa aiki da rahoton zai rage kashe kudi da gwamnati ke yi, a halin da ake ciki, aiki da rahoton ba zai rage hakan ba, saboda rahoton bai yi la'akari da halin da ake ciki ba yanzu musamman na halin da ake ciki a tsarin aikin gwamnati.
An rushe shalkwatar jam'iyyar adawa ta 'Socialist Party without Borders', to sai dai sojojin mulkin kasar ba su bayar da wani dalili na matakin ba.
A ranar Laraba ne hukumomin kasar suka zargi jam'iyyar Dillo da kai hari kan shalkwatar tsaron ƙasar.
Zargin da Dillo ya musanta, ya janyo buɗe wuta a babban ofishin jam'iyyar adawa inda a nan ne ake tunanin an kashe shi, kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.
An ga babbar motar rusau na rushe ginin shalkwatar jam'iyyar mai hawa uku, inda sojoji suka yi wa ofishin kawanya rike da manyan makamai.
An ce jagoran adawar dan'uwa ne ga shugaban mulkin sojin kasar, Janar Mahamat Idriss Déby Itno.
Ana ci gaba da zaman dar-dar a birnin N'Djamena tun bayan mutuwar Dillo, sakamakon fargabar barkewar zanga-zanga daga magoya bayansa.
Tuni dai kungiyar Tarayyar Afirka ta aike da sakon ta'aziyyarta kan mutuwar jagoran adawar
Akalla utum biyu, ciki har da dan adawar siyasa , aka tsare a lokaci da bayan jana'izar jagoran adawar Rasha Alexei Navalny a birnin Moscow
Kafafen yada labarai sun ruwaito cewa an kama mutane da dama a biranen Ekaterinburg da Novosibirsk da ke tsakiyar kasar.
Hukumomin Rasha ba su ce komai ba kan batun.
Jana'izar jagoran adawar Rasha Alexei Navalny ta kasance taron 'yan jam'iyyar adawa mafi girma a Rasha tun watan Janairun 2021.
Da tsakar ranar Juma'a ne dai aka yi jana'izar jagoran adawar kasar da ya rasu makonni biyu da suka gabata a wani gidan yarin da yake tsare
Kasancewar hukumomin kasar sun bayar da damar jana'izar, Suna iya yin da -na- sanin bai wa iyalan marigayin damar binne shi, ko kama masu nuna alhini a coci da makabarta.
Haka kuma watakila hukumomin Rashan ba su hango jana'izar ka iy zame musu barazana ba.
A yanzu hukumomin za su yi fatan masu alhinin rasuwar su watse, ba tare da barin 'yan adawar su gudanar da jawabai ba.
Shugaban ƙungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya bayyana matukar bakin cikinsa kan abin da ya bayyana a matsayin "mummunan mutuwar Yaya Dilo Djerou," shugaban jam'iyyar Socialist Party Without Borders'' ta Chadi.
Hukumomi a N'Djamena sun ce an kashe madugun 'yan adawar ne tare da "mutane da dama yayin harbi da jami'an tsaro."
A cikin wani sako ga iyalan Dillo, shugaban kungiyar ta AU ya ce, "Ina mika ta'aziyyata ga iyalansa da masu fafutika na jam'iyyarsa."
Ya yi nuni cikin nadama, yadda aka yi amfani da tashin hankalin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da jikkatar maza a ƙasar ta Chadi, ya kuma bukaci mahukunta a kasar ta Chadi da su bi ka'idojin sulhun ta hanyar lumana.
Mahamat ya sake nanata "ka'idar kungiyar Tarayyar Afirka da ba za ta iya canzawa ba, da kuma buƙatar kasar Chadi ta sake hadewa da gaske tare da tattaunawa kan siyasa da zamantakewa da farar hula da na soja domin samun kwanciyar hankali da dimokuraɗiyya da kuma wadata."
Tun bayan da fitaccen malamin addinin musulunci a Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sanar da ajiye aiki a matsayin shugaban hukumar Hisbah a Kano, al'umma ke bayyana ra'ayoyinsu game da matakin da ya ɗauka.
Jama'a sun yi ta tsokaci a shafukan sada zumunta game da matakin yin murabus ɗin da yake ci gaba da yamutsa hazo a jihar Kano.
Matakin da Sheikh Daurawa ya ɗauka na zuwa ne sa'o'i bayan da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nuna rashin gamsuwarsa da yadda Hisbah ke aiwatar da wasu ayyukanta musamman kan yaƙi da baɗala.
BBC ta leƙa shafukan sada zumunta inda ta zaƙulo ra'ayoyin jama'a game da batun.
Salihu Umar, wani mai amfani da shafin X ne inda ya wallafa cewa "game da wannan batu na salon ayyukan Hisbah, Abba yana da gaskiya, Daurawa kuma ya yi kuskure. A wuri na, shugaba ya fito ƙarara yana sukar wanda ya naɗa na nuna bin diddigi. Ku daina damun mutane da cewa shi malami ne, ba za a soke shi ba, ba za ku yi nasara a wajena ba. Babu wanda ya wuce ya yi kuskure. Daurawa ya yi kuskure,"
Shi kuwa Nasir Daniya PhD ya bayyana cewa "da alama Sheikh Daurawa tuni ya wuce wurin.
A shafinsa na Facebook, Jaafar Jaafar ya bai wa gwamna Abba Kabir Yusuf shawara da ya gyara mu'amalarsa da masu riƙe da muƙaman gwamnati inda kuma ya ce "Sukar da gwamna ya yi wa Hukumar Hisba jiya a bainar jama’a kamar mutum ne ya daɓa wa kansa wuka, domin kuwa gwamnatinsa ya zaga."
Majalisar tsaro ta jihar Kaduna ta gargaɗi masu zanga-zanga kan toshe hanyoyin jama’a da kuma musguna wa ƴan kasa da ba su ji ba, ba su gani ba.
Gargadin ya biyo bayan toshe hanyar Gonin Gora ta hanyar Kaduna zuwa Abuja da wasu masu zanga-zanga suka yi a ranar Alhamis, sakamakon harin da wasu ƴan bindiga suka kai a Unguwar Auta da ke yankin Gonin Gora a ƙaramar hukumar Chikun, wanda hakan ya hana matafiya amfani da hanyar.
A cikin wata sanarwa da muƙaddashin kwamishinan tsaro na cikin gida Samuel Aruwan ya fitar, ya ce jami'an tsaro sun tarwatsa shingayen da aka toshe hanyar tare da buɗe ta domin amfanin matafiya.
Aruwan ya kara da cewa mambobin kwamitin tsaro na jihar Kaduna a lokacin da suke zantawa da shugabannin al’umma, sun nuna rashin gamsuwarsu da barazanar da ke tattare da toshe hanyoyin, lamarin da ke tauye haƙƙin ƴan kasa da matafiya masu amfani da waɗannan hanyoyi da sauran kayayyakin amfanin jama’a.
A yau ne ake kada kuri'a a Iran a karon farko tun bayan zanga-zangar kin jinin gwamnati da aka yi a shekarar 2022.
Wadannan zaɓuka na da matukar muhimmanci wajen gwada sahihancin shugabancin ƙasar da kuma nuna goyon baya ga kasar, sai dai ana sa ran za a samu ƙarancin fitowar masu kada kuri'a.
Ana ci gaba da nuna ƙyama ga masu kada kuri'a bayan mutuwar Mahsa Amini - wadda aka tsare saboda sanya hijabi ba daidai ba da ya janyo tashe-tashen hankula
Sama da mutum miliyan 61.2 ne suka cancanci kaɗa kuri'a a zaɓuka daban-daban guda biyu: daya na 'yan majalisar dokoki da kuma wani na Majalisar Kwararru.
Majalisar dokoki ne ke zaɓar da kuma kula da babban jigo a Iran kuma babban shugaba wanda ke yanke shawara mai mahimmanci ga masu kaɗa ƙuri'a kamar 'yancin zamantakewa da yanayin tattalin arziki
Ayatullah Ali Khamenei, babban shugaban na yanzu, ya buƙaci masu kaɗa kuri'a da su fita suyi kaɗa ƙuri'arsu yana mai cewa kauracewa kada kuri'a ba zai magance wasu batutuwa ba.
An ba da rahoton wani faɗa mai tsanani ya ɓarke tsakanin dakarun gwamnati da kuma mayaƙan sa-kai a Bahirdar, babban birnin lardin Amhara da ke arewa maso yammacin ƙasar Habasha.
A cewar mazauna garin da suka zanta da BBC, faɗan da aka fara tun da sanyin safiyar Juma'a ya hada da harba manyan makamai.
An rufe kasuwanni da ofisoshi, da makarantu a birnin, wanda ke ɗaya daga cikin manya-manyan kasar inda aka kuma hana tafiya ko motsi a kan titunan birnin.
Kafofin yada labarai da masu fafutuka da ke da alaka da mayakan da aka fi sani da Fano suna ikirarin shiga birnin.
Tun a makon da ya gabata ne ake gwabza kazamin fada a yankuna da dama a Amhara inda sojoji da mayakan sa kai.
Ta'addancin da ke ta'azzara ya haifar da fargabar kare lafiyar fararen hula.
A jiya ne Somaliland ta sanar da shigar da ƙarar ƙasar Somaliya a gaban wasu ƙungiyoyin ƙasashen duniya da ba a bayyana sunayensu ba, bisa zargin kisan da aka yi wa 'yan Somaliland a Mogadishu, kamar yadda shafin intanet na Hiiraan Online mai zaman kansa ya ruwaito.
Ministan yaɗa labarai na Somaliland Ali Mohamed Hassan, ya zargi gwamnatin Somaliya da "kashe mutane da dama" daga birnin Hargeysa, a wani rikici da ya ɓarke kan sarrafa sararin samaniyar Somaliya.
"A matsayinmu na gwamnati, mun nemi kungiyoyin ƙasashen duniya su riƙe Mogadishu a matsayin waɗanda ke da alhakin kisan," in ji shi.
A ranar 23 ga watan Fabrairu, Somaliland ta shawarci 'yan kasarta da su bar Mogadishu sakamakon mutuwar wani jami'in kula da zirga-zirgar jiragen sama a babban birnin Somaliya, ko da yake hukumomin Mogadishu sun musanta hannu a lamarin.
Saukar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa daga muƙaminsa na shugaban hukumar Hisbah na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce inda fitaccen malamin addinin Musulunci, Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya ya shawarci gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nemi afuwar Malam Aminu Daurawa.
Gadon Kaya ya yi wannan kira ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na facebook.
Ya ce "Muna kira ga gwamna Abba Yusuf da waɗanɗa ke kusa da shi su kai zuciya nesa su kira malam Daurawa, su zauna da shi kuma su ba shi haƙuri kan abubuwan da ya faru."
A safiyar Juma'a ne Sheikh Aminu Daurawa ya sanar da saukar sa daga muƙamin shugaban Hisbah ta jihar Kano.
Daurawa ya ce ya yi hakan ne bayan wasu kalamai da gwamnan jihar Abba Kabir ya furta a ranar Alhamis, waɗanda suka karya masa gwiwa.
A bidiyon nasa, Sheikh Abdallah Gadon Ƙaya ya ce ya kamata gwamna Abba Yusuf ya duba al'ummar jihar Kano da ci gaban da malam Daurawa ya kawo da kuma gudummawar ya yake bai wa ita gwamnatin ta Kano.
"Ya kamata a zauna da shi malam Daurawa a ba shi shawarwari a kan abubuwan ya yake yi ko ake ta cewa Hisbah take yi." in ji Gadon Kaya.
"Matsayin malam Daurawa ya kai kuma darajarsa ta kai."
Gadon Kaya ya ce yana bayar da shawarar ce saboda ci gaban jihar Kano da ci gaban gwantin gaba ɗaya.
Hisbah dai ta riƙa shan suka daga wasu ɓangarori na al'umma bayan da wani faifan bidiyo ya yaɗu a shafukan sada zumunta, inda aka ga jami'an hukumar na jefa wasu matasa da ake zargi da aikata 'rashin tarbiyya' cikin mota.
Sai dai ana kallon ajiye aikin Sheikh Daurawa, wanda ɗaya ne daga cikin malamai mafiya shahara a arewacin Najeriya a matsayin koma-baya ga yunƙurin tabbatar da ɗa'a a jihar ta Kano, kuma wani mummunan tabo ga gwamnatin gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf.