Yadda yara ke farautar abinci a Gaza
A wasu wuraren kuma a wasu lokutan kasancewa a raye wani abun jin daɗi ne ga yaro - bare kuma a ce a kullum sai ya fita don samo abincin da zai ci shi da iyalinsa don kaucewa matsananciyar yunwa.
Yayin da kayyakin agajin da ke isa zirin Gaza ke ƙara raguwa, ana samun rahotannin ƙaruwa matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki.
Mohammed Zo'rab, ɗan shekara 11, a kullum safiya yana fita zuwa birnin Rafah da ke kudancin Gaza don cimma wani muradi.
Ya kan ɗauke kwanon roba ya nufi makarantun da suka juye zuwa sansanonin wucin gadi a gefen tituna, inda mutane ke shan wahala kamar na shi iyalin, amma ana fatan samun wani abu don ciyar da yaran baƙi.
Mohammed na kuma zuwa asibitoci, inda ako da yaushe ake kai waɗanda suka samu raunuka, da kuma duk inda ya san ake ɗora tukunya a murhu.
"Idan na koma gida ga iyalina da wannan abincin suna farin ciki matuƙa kuma muna zama mu ci tare," in ji shi.
"Wasu lokutan kuma na kan koma ba komai, kuma bana jin daɗi."
Mohammed shi ne ɗa na fari a cikin ƴaƴa huɗu a gidansu, kuma suna zaune tare da mahaifansu a wata shemar da aka yi da leda da robobi.
Mahaifinsa Khaled na yawo a Rafah don neman ɗan aikin da zai yi ya samu shekel biyar kuɗin zirin don sayen ƙunzugu ga jaririyarsa Howaida ƴar wata biyu.
Mohammed ɗaya ne daga cikin dubban yaran da suka zama masu farautar abinci don ciyar da iyalansu.
"Idan ina cikin layi mai cunkososn mutane, na ga mutum kamar ɗari a gabana, sai na kurɗa ta cikin mutane na je gaba, " yana bayanin irin hikimar da yake bi ba tare da yin faɗa ba.
Da ya koma gida sai ya mika kwanon da waken ke ciki ga mahaifiyarsa, Samar wadda ita kuma ke raba musu. Duk ta kyamushe ba ta iya cin abinci sosai ita kanta.
Tace tana fama da cutar sankara, abin da yasa idan ka ganta sai ka yi tsammani tana da shekara 60 ne a duniya, nan kuwa shekarunta 31 ne.
- Dole a bar Falasɗinawa su zauna a Gaza - Blinken
- Halin da yaran Gaza ke ciki: An raunata su kuma an kashe iyayensu