Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba and Habiba Adamu

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, Usman Minjibir da Aisha Babangida ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Yadda sabbin ƙa’idojin CBN za su shafi kasuwar canjin kuɗi

  3. Abu biyar da majalisar zartarwa ta Najeriya ta amince da su ranar Litinin

    A zamanta na ranar Litinin, Majalisar Zartarwa Najeriya karkashin jagoranci shugaba Tinubu, ta amince da wasu batutuwa guda biyar kamar haka:

    • Gina titin ruwa da ya hada Legas da Fatakwal da Kalaba wanda aka bai wa kamfanin Hitech Construction Africa. Zangon farko na titun na da nisan kilomita 47.
    • Za a fara raba tallafin rage radadi ga masu karamin karfi nan ba da jimawa ba. Sai dai an togace cewa dole ne wadanda za su ci gajiyar shirin su samu lambobin NIN da BVN.
    • Za a shigar da masu takrdun shaidar koyarwa ta NCE a tallafin na rage radadi
    • Za a kafa shirin bayar da rance nan ba da jimawa ba, inda kuma shugaban ma'aikata zai jagoranci kwamiti kan hakan. Sauran 'yan kwamitin sun hada da ministocin kasafin kudi, shari'a da na tallain arziki domin tabbatar da shirin.
    • Harwayau, majalisar zartarwa a kokarinta na rage yawan kashe kudaden gudanarwa na gwamnati ta amince da zartar da shawarwarin da rahoton kwamitin Steve Oronsaye ya bayar na rage yawan hukumomi da ma'aikatun Najeriya.
  4. Uzbekistan: An ɗaure mutum 23 kan yaran da gurɓataccen maganin tari ya kashe

    Wata kotu a Uzbekistan ta yanke wa wasu mutum 23 hukuncin dauri a gidan yari bisa samunsu da laifin mutuwar yara 68 da ake alakanta su da gurbataccen maganin tari.

    An samu waɗanda ake tuhumar da laifin ƙin biyan haraji da sayar da magunguna marasa inganci ko na jabu da cin zarafin ofis da sakaci da aikita jabu da kuma cin hanci.

    Hukuncin ya kasance daga shekaru biyu zuwa 20.

    Adadin waɗanda suka mutu da aka sanar a kotun birnin Tashkent ya haura fiye da yadda aka ruwaito a baya.

    An sami rahoton mutuwar mutum 65 a farkon shari'ar na watanni shida, kuma masu gabatar da ƙara sun ƙara ƙarin uku a watan da ya gabata.

    Marion Biotech ne ya kera gurbatattun magungunan a Indiya kuma Quramax Medical ne ya raba su a Uzbekistan.

    An yanke wa Singh Raghvendra Pratar, wani babban darektan kula da lafiya na Quramax hukuncin daurin shekaru 20.

    Hakazalika an yanke wa tsoffin manyan jami'an da ke da alhakin ba da lasisin magungunan da aka shigo da su daga ketare, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

    A watan Janairun da ya gabata, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce biyu daga cikin maganin tari na Marion Biotech "ba su da inganci" bayan da yaran Uzbekistan 18 suka mutu sakamakon shan su.

  5. Hukumar kwastam ta dakatar da sayar da kayan abinci a farashi mai rahusa

    Hukumar hana fasakwauri ta Najeriya, ta dakatar da sayar da kayan abinci da ta fara sayarwa a kan farashi mai rahusa, sakamakon turmutsitsin da ya yi sanadin salwantar rayuka a hedikwatarta da ke unguwar Yaba a birnin Legas a ranar Juma’ar da ta gabata.

    Kakakin hukumar ta Kwastam Abdullahi Maiwada ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

    A ranar 20 ga Fabrairu, 2024 ne Hukumar ta ce za ta sayar da kayan abincin da aka kama a farashi mai rahusa, domin rage wahalhalu da tsadar rayuwa a kasar.

    "An fara sayar da kayan abincin a farashi mai rahusa a natse kuma cikin kamala da misalin karfe 0800," in ji Maiwada

    “Mun ji daɗin haɗin kan ɗimbin jama’a da suka haɗa da tsofaffi da nakasassu da mata masu juna biyu, da sauran ’yan Najeriya masu rauni", inda ya kara da cewa "sayar da kayan abincin ya kasance har zuwa kusan ƙarfe 5 na yamma, kamar yadda sama da masu cin gajiyar 5000 da 'yan jarida suka tabbatar."

    Sanarwar ta kuma kara da cewa duk da haka, rikici da tashin hankali da ba a taɓa zata ba ya ɓarke a lokacin da muka ce mun rufe sayar da kayan abinci a ranar da cewa za mu ci gaba washegari, wanda ya haifar da sakamako mara daɗi.

    "Dandazon mutanen sun kasance cikin zaƙuwa inda suka riƙa ture shingayen da muka gindaya domin neman buhunhunan shinkafa wanda aka samu asarar rayuka da jikkata wasu da dama." In ji Maiwada.

    Hukumar dai ta mika ta'aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan lamari.

  6. Shugaban Somaliland ya zargi Somaliya da mutuwar ƙwararre a harkar jiragen sama

    Shugaban ƙasar Somaliland ya zargi gwamnatin Somaliya da hannu wajen mutuwar wani kwararre a harkar sufurin jiragen sama daga jamhuriyar da ta ayyana kanta a matsayin mai cin gashin kanta.

    An tsinci gawar Abdinasir Dahable, ma’aikacin Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Somaliya, a ranar 18 ga Fabrairu.

    Binciken da aka gudanar ya tabbatar da alamun azabtarwa a jikin gawar, wanda aka gano a gidansa da ke Mogadishu babban birnin Somalia.

    Da yake jawabi a wajen jana'izar bayan an kai gawarsa zuwa garin da aka haife shi a birnin Gabilay, shugaba Muse Bihi Abdi ya bayyana buƙatar gaggawar tabbatar da gaskiya da adalci.

    Ya zargi gwamnatin Somaliya da "kashe" Mista Dahable, ya kuma buƙaci a yi ƙarin haske kan yanayin mutuwar kwararen.

    Gwamnatin Somaliya ba ta amsa buƙatar BBC News Somali na neman karin haske ba, amma a baya ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan kisan mista Dahable, kuma an tsare mutane shida da ake zargi.

    Zargin da shugaba Biixi ya yi ya ƙara dagula rigingimun da ake fama da su a halin yanzu kan takaddamar da ke tsakanin kasashen Somaliland da Somaliya kan batun mallakar sararin samaniya da jirgi zai iya tashi da tafiya.

    Ƙasashen biyu kuma suna takun-saka ne a kan yarjejeniyar da Habasha ta kulla da Somaliland kan hanyar shiga teku, wadda bai yi dade da Somaliya ba.

    Somaliya dai na ɗaukar Somaliland a matsayin wani yanki na ƙasarta, ta kuma sha alwashin kare ikonta.

  7. Tinubu ya yi umarnin zartar da rahoton da zai rage da haɗe ma'aikatu a Najeriya

    Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin aiwatar da cikakken rahoton Oronsaye wanda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa tun a 2011, a kokarin gwamnati na rage yawan kashe kudaden gudanarwa.

    An dai kafa kwamitin ne a lokacin sake fasalin tsarin mulki da kwamitoci da hukumomin gwamnatin tarayya karkashin shugabancin tsohon shugaban ma'aikata na Najeriya, Stephen Osagiede Oronsaye.

    Kwamitin ya gabatar da rahoto mai shafuka 800 a ranar 16 ga Afrilu, 2012, inda ya bankado yadda ake gudanar da gasa a tsakanin hukumomi da dama, wanda ba wai kawai ya haifar da rashin kwanciyar haknali a tsakanin hukumomin gwamnati ba, har ma ya haifar da almubazzaranci.

    Rahoton ya ba da shawarar dakatar da tallafin da gwamnati ke bai wa wasu hukumomi da majalisu wajen bayar da kuɗi don gudanar da manyan ayyuka.

    Rahoton na Oronsaye ya tabbatar da cewa akwai ma’aikatun gwamnatin tarayya 541 da kwamitoci da hukumomi (na doka da na shari’a), inda ya bayar da shawarar cewa a mayar da 263 daga cikin ma’aikatun zuwa 161, yayin da rahoton ya ce a soke hukumomi 38 sannan a hade guda 52.

    Kwamitin ya kuma ba da shawarar cewa 14 daga cikin hukumomi su koma sassan ma'aikatu.

    Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, da yake jawabi ga manema labarai a fadar shugaban ƙasa a ranar Litinin a Aso Rock, Abuja, ya ce “a cikin wani gagarumin yunkuri a yau, gwamnatin shugaban Tinubu ta dauki matakin aiwatar da rahoton da ake kira Oronsaye Report don amfanin Najeriya"

    “Yanzu, abin da hakan ke nufi shi ne, an soke wasu hukumomi da kwamitoci, da wasu sassa a zahiri. Wasu kuma an gyara su, kuma an yi musu alama yayin da wasu kuma an rage su. Wasu kuma, ba shakka, an dauke su daga wasu ma’aikatun zuwa wasu inda gwamnati ke ganin za su yi aiki sosai.”

    Da take tsokaci kan wannan lamari, mai bai wa shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin siyasa Hadiza Bala Usman, ta ce hakan ya yi daidai da buƙatar rage yawan kudaden gudanar da harkokin mulki da kuma daidaita yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati.

    Ta kara da cewa an kafa tawaga don aiwatar da rahoton cikin makonni 12.

    • Gwamnatin Najeriya na nazarin zabtare albashin ma’aikata
    • Ma'aikatan Najeriya sun shiga tasku lokacin mulkin Buhari - NLC
  8. Wane zaɓi ya ragewa ɗaliban da ke karatu a Ukraine kafin yaƙi?

  9. Yadda yajin aiki ya tsayar da al'amura cak a birnin Conakry

    Al'amura sun tsaya cik a rana ta farko ta yajin aikin sai-baba-ta-gani a babban birnin Guinea, wato Conakry. An rufe yawancin harkokin kasuwanci, kuma tituna da dama sun kasance fayau, ba jama'a ba ababen hawa.

    Kungiyoyin kwadago da suka shirya yajin aikin sun gabatar wa da hukumomi bukatunsu, wadanda suka hada da rage farashin kayan abinci da kuma sakin wani dan jarida dan-gwagwarmay Sekou Jamal Pendessa.

    A makon da ya wuce sojojin da ke mulki a kasar ta yankin Afirka ta Yamma suka kawar da gwamnatin kasar ta rikon-kwarya ba tare da wani bayani ba.

    Haka ita ma Najeriya, wadda ke yankin, kungiyoyin kwadago sun lashi takobin fara zangaza-zanga ta kwana biyu, a gobe Talata da kuma jibi Laraba, su ma dai kan tsadar rayuwa.

  10. Muna kiran gwamnati ta fitar da sabon tsarin albashi mafi ƙaranci - TUC

    Ƙungiyar Kwadago ta TUC ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta saka sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan Najeriya domin magance tsadar rayuwa a kasar.

    Tun bayan cire tallafin man fetur, tsadar rayuwa ta yi kamari sannan kuma an samu ƙarin hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar.

    Duk da cewa an gudanar da zanga-zanga da tarurruka tsakanin kungiyoyin kwadago da hukumomi domin fitar da matakan sassauta wahalhalun da ake fama da su, shugaban TUC, Festus Osifo ya yi kira da a sake duba mafi karancin albashi na N30,000.

    Ya yi wannan magana ne a Abuja ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai sa’o’i 24 kafin fara zanga-zangar da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta gudanar a fadin kasar kan tsadar rayuwa.

    Osifo ya shaida wa mahalarta taron cewa kiran da aka yi na neman sabon mafi karancin albashi na daga cikin hanyoyin da ƙungiyar ta fitar domin magance taɓarɓarewar tattalin arzikin kasar.

    Ya ce faduwar darajar Naira a kan dala a kasuwannin canji ya kara dagula darajar mafi ƙarancin albashi.

    Don haka shugabannin TUC suna yin kira da a amince da aiwatar da sabuwar dokar mafi karancin albashi da zai yi daidai da yanayin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.

    A cewarsa, ya kamata tawagar gwamnatin ƙasar a fannin tattalin arziki ta yi kokarin ganin an samu daidaiton darajar Naira zuwa dala, wanda suka sanya tsakanin dala ɗaya kan naira 500 zuwa 800.

    Osifo ya kuma ba da shawarar cewa ya kamata gwamnati ta sake duba haraji kan wasu muhimman kayayyaki da ake shigo da su cikin ƙasar domin a samu sauƙin wahalhalun da ake ciki.

    Shugaban na TUC ya dora alhakin rashin tsaro ne da ya jawo tashin farashin kayan masarufi a halin yanzu, inda ya ce manoma da dama ba su zuwa gonakinsu ta dalilin hakan.

    • Abu bakwai da gwamnatin Najeriya ta cimma da 'yan ƙwadago
    • Kalaman 'yan Najeriya bayan sake ƙara kuɗin man fetur
  11. An kashe mutum 15 a wani harin coci a Burkina Faso

    Aƙalla mutum 15 ne aka kashe a wani hari da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka kai a wata majami’a a yankin Sahel na ƙasar Burkina Faso, kamar yadda kafar yada labarai ta Lefaso.net mai zaman kanta ta rawaito.

    Intanet ɗin ta rawaito jami’an cocin na yankin na cewa a cikin wata sanarwar da suka fitar: “Malamin cocin da ke yankin Sahel ya sanar da kai harin kan al’ummar Katolika na kauyen Essakane a ranar Lahadi 25 ga watan Fabrairun 2024 a lokacin da suke gudanar da adu'arsu ta Lahadi.

    Sanarwar ta ce, "Mutum 15 ne suka mutu 15, 12 suka fara mutuwa nan take yayin da ukun kuma suka mutu sanadiyyar raunin da suka samu."

    Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma mayaƙan da ke aiki a yankin Sahel da wasu sassan ƙasar ta Burkina Faso a baya sun kai hari kan majami'un kiristoci tare da yin awon gaba da malaman addini.

    Ƙauyen Essakane na cikin yankuna uku na kan iyaka na Burkina Faso da Mali da kuma Nijar.

    • 'Yan bindiga sun kashe mutum 20 a Burkina Faso
    • 'Rashin haɗin kan gwamnatoci dama ce ga 'yan bindiga'
  12. Amurka ta fara atisayen soji mafi girma a gabashin Afirka

    A yau litinin ne aka fara wani atisayen soji da Amurka ke jagoranta mai suna "Justified Accord" a kasar Kenya, inda ƙasashe sama da 20 za su halarci wani taron da aka gabatar a matsayin irinsa mafi girma a gabashin Afirka.

    Atisayen na kwanaki 11, wanda zai kawo karshe a ranar alhamis mai zuwa, na da nufin ƙara shirye-shiryen kasashe masu shiga cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya, da magance rikici da kuma taimakon jin kai, kamar yadda kafar yaɗa labaran Somaliya ta SNTV da kafofin yada labarai na kasar Kenya suka bayyana.

    Ɗaruruwan kwamandojin Somaliya da Amurka ta horas da su ne za su halarci atisayen, wanda wani shafin yaɗa labarai mai zaman kansa na Kenyas.co.ke ya ce zai haɗa ma'aikata 1,000 da sassan kasashe 23.

    Rundunar sojin Amurka ta ce Justified Accord ita ce atisayenta mafi girma a gabashin Afirka.

    "Atisayen ta nuna sha'awar Amurka da kasashe abokan hadin gwiwa don ƙara shiri da hadin gwiwa wajen samar da tsaro da magance rikici," in ji sojojin.

    Amurka ta jagoranci atisayen makamancin haka a gabashin Afirka a shekarun baya bayan nan a daidai lokacin da yankin ke fama da munanan hare-haren kungiyar Al-Shabab da sauran ƙalubalen tsaro.

    • Ambaliyar ruwa ta shafi mutum miliyan shida a Gabashin Afrika
    • China ta harba makamai a kusa da Taiwan bayan ziyarar Nancy Pelosi
  13. Za mu bai wa masu zanga-zanga a Najeriya kariya - Ƴansanda

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce za ta bai wa masu zanga-zangar tsadar rayuwa a ƙasar kariya, sai dai ta ce za ta ɗauki duk wasu matakan hana ɓarkewar rikici.

    Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa, kwanaɗaya kafin zanga-zangar tsadar rayuwa da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar (NLC) ta kira a faɗin ƙasar.

    A cikin sanarwar wadda ta samu sa hannun mai magana da yawun rundunar ƴansandar ta ƙasa, ACP Olumuyiwa Adejobi, ta ce "Rundunar ƴansanda na sane da ƴancin da al'umma ke da shi na yin zanga-zanga cikin lumana kamar yadda doka ta tanada."

    Sai dai rundunar ta ce "yayin da take martaba ƴancin yin zanga-zanga cikin lumana, rundunar ƴansandan ta Najeriya ta ce za ta sanya ido kan duk wanda ya shiga zanga-zangar da mummunar manufa."

    "Sabida haka, rundunar ta ce ba za ta ɓata lokaci ba wajen murƙushe su ta duk hanyar da ba ta saɓa wa doka ba."

    • Zanga-zangar da 'yan ƙwadago suka yi a sassan Najeriya
    • 'Yan Najeriya na tunawa da harbe-harben Lekki shekara ɗaya da zanga-zangar
  14. 'Yan adawar Chadi za su gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa

    Gamayyar jam'iyyun adawar ƙasar Chadi da kungiyoyin farar hula na shirin jagorantar zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a kasar, kamar yadda gidan rediyon Faransa RFI ya ruwaito a jiya.

    Mai magana da yawun kungiyar 'We The People (Nous le Peuple) Yaya Dillo Djerou Betchi, ya ce zanga-zangar na da nufin aikewa da wata babbar alama ga gwamnatin mulkin soji da ke nuna cewa mutanen ƙasar sahn wahala.

    "Hakika gidaje da yawa za su ji rauni, amma muna sane da cewa idan muka bar mulkin soja ya ci gaba a haka, zai kara azabtar da mu shekaru da yawa masu zuwa," in ji Betchi.

    Gwamnatin ƙasar ta haramta irin wannan zanga-zangar a baya, saboda rashin mutunta ka'idojin da suka shafi zanga-zangar da kuma hatsarin da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya.

    Ƙungiyoyin farar hula da jam'iyyun adawa sun zargi gwamnatin da sojoji ke jagoranta da rashin tafiyar da ƙasar yadda ya kamata, lamarin da gwamnatin ta musanta.

  15. 'Navalny ya mutu ana gab da yin musayarsa da wani fursuna '

    Madugun ƴan adawan Rasha, Alexei Navalny ya mutu ne gab da samun ƴanci, a wata musayar fursunonin da aka shirya yi, a cewar wata abokiyarsa, Maria Pevchikh.

    Ta ce ana shirin musayar mista Navalny da wani gwanin kisa ɗan ƙasar Rasha, Vadim Krasikov, wanda aka yi wa ɗaurin rai da rai a Jamus.

    Haka kuma wasu Amurkawa biyu da Rasha ke tsare da su na cikin waɗanda ake shirin yin musayar da su, a cewar Maria.

    Ta ƙara da cewa tattaunawar ta kai mataki na ƙarshe a ranar 15 ga watan Fabairun wannan shekarar.

    Kashegari ne kuma mista Navalny ya mutu a ɗakin da ake tsare da shi a kurkukun colony da ke Siberia, inda yake zaman hukuncin shekara 19 da aka yanke masa, bayan samunsa da laifi kan tuhume-tuhumen da mutane da dama ke kallo a matsayin siyasa.

    Jami'an gidan yari sun ce Navalny mai shekara 47 ya yi rashin lafiya gabannin mutuwarsa.

    A wani bidiyon da ta wallafa a shafin YouTube na mamacin, Maria wadda ita ce shugabar asusunsa mai yaƙi da cin hanci da rashawa (FBK) ta ce an kwashe tsawon shekara biyu ana tattaunawa kan batun musayar fursunonin.

    Inda ta ƙara da cewa bayan fara yaƙin da Rasha ta yi a Ukraine a watan Fabairun 2022 "Ya bayyana cewa Putin ba zai sassauta ba," don haka dole shi mista Navalny " a fitar da shi daga kurkuku ko ta halin ƙaƙa, kuma cikin gaggawa."

    • Taron G20: Ƙasashe sun soki Rasha kan mutuwar Alexei Navalny
    • Shugabannin duniya na ci gaba da alhihin rasuwar Alexei Navalny
  16. Bahaushiya mai aiki da NSCDC da ke burge matan arewa

  17. Tinubu ya gana da hamshaƙan ƴankasuwan Najeriya

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wata ganawa da manyan ‘yankasuwa masu zaman kansu da wasu gwamnonin jihohin ƙasar, inda suka tattauna halin da tattalin arzikin kasar ke ciki da kuma tsadar rayuwar da ‘yanƙasar ke fuskanta.

    Taron ya kuma tattauna kan yadda darajar kuɗin kasar, Naira ke faɗuwa yayin da darajar dalar Amurka ke ƙara tashi, a yayin ganawar ta ranar Lahadi.

    Baya ga batun tattalin arziki taron ya kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi wadata ƙasar da abinci da kuma na tsaro.

    Shugaba Tinubu ya jaddada cewa "kamar yadda na sha faɗa al’ummar kasar nan su ne kaɗai mu ke da su, kuma muke son kyautatawa, mun damu matuƙa da halin da suke ciki"

    Cikin waɗanda suka halarci taron a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja, sun haɗa da attajirin ɗankasuwan nan, Alhaji Aliko Dangote.

    "Mun tattauna kan batun samar da ayyukan yi da wasu batutuwa da dama... abin alfaharin shi ne Najeriya ƙasa ce mai albarka, kuma mu na da kyakkayawan fata kan za mu iya sauya tattalin arzikinmu kuma za mu tabbatar da hakan." In ji Dangote.

    Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar ƙwadago ta NLC ke shirye-shiryen yin zanga-zanga kan tsadar rayuwa.

    Miliyoyin ƴan ƙasar ne ke rayuwa cikin ƙangin talauci da yunwa, lamarin da ake alaƙantawa da cire tallafin mai da kuma sauran gyaran fuskar da shugaban ƙasar ya yi tun bayan hawansa mulki.

    • Yadda farashin kayan masarufi ya tashi a lokacin mulkin Tinubu
    • Shin samamen jami’an tsaro a kasuwannin canji zai farfaɗo da darajar naira?
  18. Gumurzu tsakanin ƴanbindiga ya kai ga kisan gaggan ƴanfashin dagi a Zamfara

    Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa-maso-yammacin Najeriya na cewa akalla fitattun shugabannin ‘yan bindiga biyar ne aka kashe.

    Hakan ya faru ne a yayin wani rikici da ya barke a tsakanin mayakan Dogo Bali da Kachalla Mai ‘Yankuzo, abun da ya yi sanadiyyar halakar gwamman mayaƙan tare da jikkata wasu da dama.

    Rahotannin na cewa bangarorin ‘yan bindigar sun gwabza fada ne a ranar Lahadi a garuruwan Mada da Munhaye da kuma a ‘Yan awaren Daji, dukansu a ƙaramar hukumar Mulki ta Tsafe da ke jihar Zamfarar.

    Rahotanni sun ce rikicin ya kazance har ya kai ga wani ɓangare na Makama da tawagarsa suka nufi dazukan Hayin Allhaji da Munhaye da ke karamar hukumar Mulki ta Tsafe domin daukar fansar Dogo Bali da aka kashe.

    A can ne suka hadu da daruruwan mayaƙan Ado Aleru da suka yi musu kwanton ɓauna kuma aka kashe da dama daga cikinsu.

    Daga cikin gaggan shugabannin ‘yan bindigar da mayaƙan Aleru suka kashe har da waɗanda ake yi wa laƙabi da ƊanMakaranta da Malam Gainaga, da Mallam Tukur da Malam Jaddi.

    Mai Magana da yawun hedikwatar tsaron sojin Najeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya tabbatar wa da BBC aukuwar gumurzun.

    • Mutanen gari sun yi garkuwa da iyalan ‘yan bindiga a Zamfara
    • 'Babu mu babu Sulhu da 'yan fashi a Zamfara'
  19. Pakistan: Matar da ta sa riga mai rubutun larabci ta sha da kyar

    A Pakistan, wasu gungun mutane sun zargi wata mata wadda ta sa wata riga da aka yi wa ado da rubutun arabiyya da cewa ta yi ɓatanci, saboda sun zaci ayoyin Al-ƙur'ani ne a rigar.

    Ƴansanda ne suka ƙwace ta suka kuma raka ta zuwa inda bata fuskantar barazana, bayan ɗaruruwan mutane sun taru a kanta. Daga bisani ta bai wa al'umma haƙuri.

    An rubuta "Halwa" da Arabiyya a jikin rigartata, abun da ke nufin kyakkyawa da larabci.

    Ana hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da aikata ɓatanci a Pakistan. Wasu a kan kashe su tun kafin a kai ga gurfanar da su.

    Ƴansanda sun shaida wa BBC cewa an kira su ta waya da misalin ƙarfe 13:10 agogon ƙasar, a ranar Lahadi, inda aka gaya musu cewa ga wasu mutane sun taru a kan wata mace, a wani gidan abinci da ke Lahore, babban birnin lardin Punjab da ke ƙasar ta Pakistan.

    Kimanin mutane 300 ne suka yi cuncurundu a wajen gidan abincin a lokacin da ƴansanda suka isa wurin, a cewar jami'in ƴansanda, Syeda Shehrbano.

    An yita yaɗa faifai bidiyon abun da ya faru a shafukan sa da zumunta, inda a wani aka ga matar a firgice ta ɓoye a wani lungu a cikin gidan abincin, ta kare fuskarta da hannu.

    A wani bidiyon kuma an ga matar, ƴansanda sun kewaye ta, yayin da dandazon jama'a ke ƙaruwa suna yi mata ihun cewa ta cire rigar.

    Yayin da a wasu bidiyon kuma ake jin wasu na rera cewa wanda ya yi ɓatanci dole a cire masa kai.

    • Abin da ya janyo hari kan masallaci a Pakistan
    • Me ya sa Pakistan ke korar ƴan Afghanistan daga ƙasarta?
  20. Najeriya: Ana zanga-zangar tsadar rayuwa a jihohin Edo da Osun

    Mambobin ƙungiyoyi masu zaman kansu sun bazu kan tituna a jihohin Edo da Osun a ranar Litinin suna zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Najeriya.

    Hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ya kai kashi 29 cikin ɗari, tun bayan janye tallafin mai ne rayuwa ke ƙara tsada.

    Masu boren sun bazu kan tituna a Benin da Osogbo, manyan biranen jihar Edo da Osun da ke kudancin ƙasar.

    A birnin Benin, masu zanga-zangar sun yi tattaki daga dandalin Kings zuwa titin Akpakpava, suna ɗauke da kwalaye waɗanda aka yi wa rubuce-rubuce kan batun tsadar rayuwa da ƴan ƙasar ke fuskanta da kuma buƙatar da ke akwai na magance matsalar yunwa a ƙasar.

    A jihar ta Edo ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam'iyyar hamayya ta NNPP a zaben da ke tafe a jihar, Dr Azemhe Azena na daga cikin waɗanda suka fito zanga-zangar, inda ya nemi gwamnati ta ɗauki matakan kawo ƙarshen tsadar rayuwa a ƙasar.

    A birnin Osogbo na jihar Osun, masu boren sun yi gangami a wurin shaƙatawa na Nelson Mandela, inda su ma suka yi kira ga gwamnati da ta kawo ƙarshen tsadar rayuwa.

    A baya-bayan nan an yi irin wannan zanga-zangar a wasu sassan ƙasar, kamar a jihohin Legas da Neja da birnin Ibadan na jihar Oyo da kuma jihar Kano.

    • Wace dabara ta rage wa Tinubu game da tsadar rayuwa a Najeriya?
    • Abubuwan da JNI ta faɗa kan tsadar rayuwa a Najeriya
    • Ƙarin hauhawar farashin da aka daɗe ba a gani ba na gigita ƴan Najeriya