An kama ƴan sandan Kenya kan zargin fataucin bil adama
Jami'an tsaro sun cafke ƴan sanda huɗu a Kenya yayin kai samame wani gida da ke da tazarar kilomita 16 daga Nairobi, babban birnin ƙasar inda aka samu ƴan Habasha 37 a ciki.
Ana zargin ƴan sandan na da hannu a safara da kuma fataucin bil'adama.
A rahoton da gidan jaridar The Star ya fitar ƴan Habashan sun shaida wa jami'an Kenya cewa suna kan hanyarsu ta zuwa Afrika ta Kudu ne don neman rayuwa mafi inganci.
Ana ci gaba da bincike kan mai gidan da aka samu mutanen da kuma sauran masu hannu a safarar.
Hukumar kula da ƴan gudun hijra ta majalisar ɗinkin duniya IOM ta ce Kenya ta kasance sananniyar hanya ga ƴan ci-ranin Habasha masu son tsallakawa Afrika ta Kudu ta haramtacciyar hanya.
Hukumar ta ce ƴan gudun hijarar waɗanda mafi yawansu maza ne da suka fito daga ɓangaren Oromia da SNNP na Habasha na shiga Kenya ta iyakar Moyale sannan su shiga Tanzania sai kuma su faɗa Afrika ta Kudu.
- Yadda kisan wata matashiya ya fito da ƙiyayyar da ake nuna wa mata a intanet
- Yadda ake kashe miliyoyin jakai duk shekara don haɗa maganin gargajiya
- Fashewar gas a Nairobi ta kashe mutum uku da jikkata kusan 300