Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Ahmad Tijjani Bawage and Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Sojojin ruwan Maroko sun ceto baƙin haure ƴan Afirka 141

    Sojojin ruwan Maroko sun ceto bakin haure 141 ‘yan Afirka da ke cikin kwale-kwale da suka gamu da matsala yayin da suke tafiya daga Mauritania zuwa tsibirin Canary na Spain.

    An ceto mutanen ne a ranar Lahadi, kimanin kilomita 274 kudu maso yammacin Dakhla a cikin hamadar yammacin sahara.

    'Yan baƙin hauren sun tashi ne daga gabar tekun Mauritaniya a ranar 10 ga watan Fabrairu, kamar yadda rahotanni daga sojojin ruwan Morocco suka ruwaito a kamfanin Dilancin labaran reuters.

    A bara, tsibirin Canary ya karƙi kusan baƙin haure 32,000, wanda ya zama mafi yawan adadin da aka samu tun shekara ta 2006.

    A watan Janairu, hukumomin Spain sun ba da rahoton ci gaba da ƙaruwar bakin haure zuwa tsibiran, inda aƙasarin jiragen ruwa suka fito daga Mauritania.

    • Bakin-haure 626 sun makale a kan teku
    • Abin da ya sa ba ma so mu koma gida — ‘Yan gudun hijira
  2. 'Sakin' Murja Kunya ya bar baya da ƙura a Kano

    Al'umma a jihar Kano na ci gaba da ce-ce-ku-ce kan rahoton da ke nuna fitacciyar ƴar Tiktok ɗin nan, Murja Ibrahim Kunya - da a baya-bayan nan kotu ta tasa ƙeyarta zuwa gidan yari ta shaƙi iskar ƴanci.

    A makon da ya gabata ne kotun shari'ar musuluncin da ke Gama ta bayar da umarnin a tsare Murja a gidan gyaran hali na Kurmawa bayan da Hukumar Hisbah ta kama ta bisa zargin nuna rashin ɗa'a da yunƙurin jefa ƴanmata cikin karuwanci.

    Kotun dai ta nemi a tsare ƴar Tiktok ɗin ne har zuwa ranar Laraba 27 ga watan Fabarairu sai dai bayanai na cewa an bayar da belin ta, lamarin da ya fusata wasu al'ummar jihar.

    Mutane da dama a shafukan sada zumunta sun yi ta bayyana ra'ayinsu kan yadda ake cewa Murja Kunya ta samu beli duk da cewa kotu ta bukaci a tsare ta har ranar Laraba.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito kakakin kotun, Muzammil Ado Ibrahim Fagge na cewa bai san da faruwar lamarin ba.

    Ya ce "mun kuma ji cewa an sake ta daga gidan yari. Alƙalin kotun ya ce zai yanke shawara kan ko ya ba ta beli ko a a, a ranar 20 ga watan Fabarairu. "Ba mu san abin da ya faru ba. Ba za a iya sauya abin da ya faru a kotu ba musamman kan wannan yarinyar da ba wannan ne karon farko ba."

    A nashi ɓangaren, mai magana da yawun hukumar gidan gyaran halin, Musbahu Kofar Nassarawa ya ce an sake ta ne bayan samun umarni daga kotu.

    Ya ce hukumar gidan gyaran halin na tafiya ne bisa tsarin doka kuma tana aiki ne kamar banki, "takardu ke shigar da kai, irin takardun kuma ke fitar da kai."

    "Dole ne alƙali ya sa hannu a tura ka gidan yari, haka nan idan za a sake ka."Kan batun Murja, babu wanda ya tsere daga gidan yari. Idan ka hau katanga a ƙoƙarin tserewa, daidai yake da a ɗauki matakin harbe mutum kuma muna da ƙofofi da jami'ai ke tsaronsu.

    Wani jami'i a hukumar hisbah da ke Kano wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce lamarin ba zai shafi ayyukan jami'ansu ba saboda ba za su naɗe hannu ba a yaƙi da baɗala a jihar Kano.

    Tuhumar da ake yi wa Murja:

    A wata tattaunawa da manema labaru bayan kama ƴar tiktok ɗin, kwamandan Hizba a jihar Kano, Sheikh Ibrahim Daurawa ya ce tuhume-tuhumen da ake yi wa Murja Kunya sun haɗa da: Razana al'umma, ayyukan baɗala, tayar da hatsaniya, tayar da hankalin al'umma, kawo ɓatagari cikin unguwa, iƙirarin cewa ita ce shugaban karuwai da ƴan kwalta.

  3. 'Masu garkuwa na amfani da macizai domin tsoratar da mu'

    Mutanen da suka shaƙi iskar ‘yanci daga hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da su sun bayyana cewa mutanen da suka sace sun a amfani da macizai masu dafi domin tsorata su.

    Wasu a cikinsu da suka bayyana halin da suka tsinci kansu a ciki a hirar da suka yi lokuta daban-daban da kamfanin dillancin labarai na NAN sun ce akwai macizai masu tarin yawa a cikin dajin da ‘yan bindigar suka mamaye.

    Sun ce macizan suna yawan sarar masu garkuwar da mutanen da aka sace.

    Ɗaya daga cikin mutanen da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa NAN cewa masu garkuwar sun jefa su cikin matattarar macizai.

    “Masu garkuwar sun san wuraren da macizai suke kuma suna ajiye mutanen da suka sace a nan.

    “Da zarar sun ga macizai, masu jin tsoronsu sai su yi ta neman guduwa. Ganin macizan na tsoratar da su.

    “Lokacin ne waɗanda aka sace suke neman ‘yan uwa da abokan arziki su sayar da komai – gida da fili da motoci da kayan gida da takalma, komai ma – kawai don a haɗa kuɗin fansa.”

    Binciken da NAN ya yi ya gano dazukan da ke da mafi yawan macizai suna Birnin Gwari a jihar Kaduna da Kala-Balge kusa da tafkin Chadi a jihar Borno.

    Wasu yankunan sun haɗa da Shaki a jihar Oyo da Borgu da Kagara a jihar Neja sai Karim Lamido a Adamawa da Lau a jihar Taraba.

    Wasu cikin mutanen da suka kuɓuta daga hannun ‘yan bindigar sun shaida wa NAN cewa lamarin ya ƙazanta a yanzu ganin yanayin zafin da ake ciki yayin da macizan ke barin ramukansu da nufin neman abinci da shan iska.

    • An kama wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Taraba
    • Mutanen da ƙungiyar Hamas ke garkuwa da su tsawon shekaru
  4. Barka da Safiya

    Masu bibiyar mu barka da wannan lokaci da fatan an tashi lafiya.

    Muna fatan kasancewa da ku a wannan yini, domin kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye daga sassan duniya.

    Sai ku biyo mu.