Ƙasar Rwanda ta caccaki Amurka kan sukar da ta yi game da ƙaruwar tashe-tashen hankula a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, yayin da ta nuna matukar damuwa kan abin da ta kira watsi da shirin samar da zaman lafiya a yankin.
A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar Rwanda ta fitar, Rwanda ta kuma ce kasashen duniya ba su nuna halin ko-in-kula da "aikin da sojin DR Congo ke yi ba", ta kara da cewa gagarumin aikin da kasar ta yi a gabashin yankin Kivu da ke gabashin kasar ya saba wa shawarwarin da wasu hanyoyin yankin suka dauka.
Dakarun kungiyar raya kasashen kudancin Afirka (SADC) na taimakawa sojojin DRC wajen tunkarar kungiyoyin da ke dauke da makamai ciki har da kungiyar M23.
A makon da ya gabata ne wasu sojojin Afirka ta Kudu biyu da ke cikin dakarun SADC suka mutu, yayin da uku suka jikkata bayan da wani bam ya fado a sansaninsu.
A karshen mako, Amurka ta yi Allah wadai da zargin goyon bayan da Rwanda ke yi wa dakarun M23 na Congo tare da yin kira ga kasar da ke gabashin Afirka da ta gaggauta janye dukkan dakarunta daga DR Congo.
Rwanda ta musanta goyon bayan M23.
Sanarwar da kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya fitar ta bukaci Rwanda da ta cire na'urorinta na makami mai linzami da ke DR Congo, lamarin da ta ce yana barazana ga rayukan fararen hula, da dakarun wanzar da zaman lafiya da jiragen kasuwanci.
Rwanda ta ce furucin na Amurka ya gurbata gaskiyar lamarin, inda ta ƙara da cewa matakin da DR Congo ke yi na barazana ga tsaronta, kuma tana da hakkin daukar matakan kare kanta daga wannan barazana.
Ta ce za ta nemi ƙarin haske daga Amurka saboda sanarwar ta saɓawa salon tsarin karfafa gwiwa da daraktan tattara bayanan sirri na Amurka ya kaddamar a bara.