'Yan sanda a birnin Kansas na Amurka sun ce an harbi mutum 22 a wani taron gangamin samun nasarar wasan kwallon kafar Amurka.
Akalla mutum daya aka tabbatar da mutuwarsa kawo yanzu yayin da wasu da dama ciki har da yara kanana
ke cikin mawuyacin hali bayan samun munanan raunuka ciki har da yara kanana
An bude wa jama’a wuta ne a harbi irin na kan mai uwa da wabi a lokacin da magoya bayan Kansas city chiefs ke murnar nasara a wasan kwallo mafi girma a Amurka.
Kawo yanzu yan sanda sun ce ba a san dalilin harbin ba amma sun ce sun sun kama mutum uku da suke zargi.
Shugaban yan kwana-kwana na Kansas City, Ross Grundyson ya ce akwai mutum takwas da muke tunanin suna cikin hali na rai kwakwai mutu kwakwai, akwai kuma bakwai da ke da mummunan raunika da kuma shida masu kananan rauni kuma an yi kokarin kai wadanda ke cikin mawuyacin hali asibiti cikin minti 10.
Da take magana da manema labarai yayin da take shirin hawa jirgi zuwa Jamus domin halartar wani taron tsaro a Munich, mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta bayyana kaduwarta.
Ta ce yau ya kamata ta kasance rana ta murna inda mutane suka hadu suna farin ciki amma kuma wata rana ce da Amurka ta shiga tashin hankali na harbin bindiga.
Rikicin bindiga ya fi halaka yara a Amurka, ba wasu cutuka ko kuma hatsarin mota, kuma wani abin da za a iya hanawa.
Magajin garin Kansas City, Quinton Lucas ya ce za su yi bincike. Ya ce ya kadu kamar kowa, kuma "za mu yi cikakken bincike, za a gurfanar da duk wanda ke da hannu tare da tabbatar da kare kanmu.
Lamarin dai ya girgiza Amurka, shugaba Biden a sanarwar da fadarsa ta fitar, ya ce tashin hankali ne ga Amurkawa da kuma wani abin kunya ga rashin daukar mataki kan tashin hankalin da ya shafi bindiga.
-
Harin Texas: Ɗan bindiga ya harbe mutum 21 a Amurka
-
Amurka ta kai harin ramuwa a kan Iraqi da Syria