Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir and A'isha Babangida
Muna kokarin magance matsalar karancin abinci a kasarmu - Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinibu ya ce gwamnatinsa na kokarin magance matsalolin karancin abinci da kasar ke fuskanta.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin ganawarsa da kungiyar gwamnonin kasar a fadarsa, yana mai cewa ya samar da wasu shirye-shirye da za su inganta samar da abinci a cikin kasar tare da hana bayar da bashi don shigar da kayan abinci cikin kasar.
Mista Tinubu ya kara da cewa ''mun samu rahoto daga Kano, na yadda ake boye kayan abinci mai yawa a gidajen ajiya. Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da babban sifeton 'yan sanda da daraktan hukumar tsaro ta farin kaya su yi aiki tare don tabbatar da sanya idanu wajen gidajen ajiye kayan abincin.''
Dole mu tabbatar da cewa masu boye kayan abinci da masu neman rance don shigo da kaya ba su yi zagon-kasa ga kokarinmu na wadata kasa da abinci ba, kamar yadda shugaba Tinubu ya bayyana.
Shugaban ya ce ba zai samar da hukumar kayyade farashi ba, sannna ba zai amince da shigar da abinci cikin kasar ba.
Za mu kokari don fitar da kanmu daga halin da muke ciki, saboda shigo da abinci zai bayar da dama ga masu neman bashi su dakile mana kokarin da muke yi.
A maimakon haka shugaban ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen tallafa wa manoma ta hanyar bullo da tsare-tsaren da za su karfafa musu giwwa wajen noma abincin da zai wadatar da kasar da abinci.
Venezuela ta dakatar da ayyukan hukumar kare hakkin dan adam ta MDD
Venezuela, ta ce ta dakatar da ayyukan ofishin hukumar kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya a Caracas, babban birnin kasar, sannan ta bayar da umarni ga ma'aikatan da su bar kasar cikin sa'oi 72.
Ministan harkokin wajen kasar Ivan Gil, ya zargi hukumar da sa kanta a abin da bai kamata ba, sannan kuma ta ya zarge ta hada baki da wasu mutane kamar masu shirya wa kasar juyin mulki da 'yan ta'adda don a ba ta kasar.
A ranar Talatar da ta wuce, ofishin hukumar ya wallafa labari a shafinsa na X inda ya nuna damuwarsa a kan rashin sanin halin da mai fafutukar kare hakkin dan adam din nan ta kasar Rocio San Miguel take.
Daga nan kuma ya yi kira da a gaggauta sakinta.
Mahammane Salissou Hamissou na RFI Hausa ya rasu
Dan jaridar gidan radiyon RFI Hausa, Mahammane Salissou Hamissou ya rasu, sakamakon hatsarin mota da ya rusa da shi.
Shafin intanet na kafar yada labaran RFI Hausa ne ya tabbatar da rasuwar dan jaridar, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Kano daga Katsina, a kokarinsa na komawa ofishin RFI da ke Legas.
''Yan uwa da abokan arziki sun shafe tsawon lokaci suna ta kokarin neman sa ta wayar salula, amma abin ya ci tura, lamarin da ya jefa hatta abokan aikinsa na RFI cikin firgici, yayin da suka fara gudanar da bincike don sanin halin da ya ke ciki'', kamar yadda RFI ta wallafa a shafinta na intanet.
Tuni dai aka dauki gawar Mahammane Salissou Hamissou zuwa birnin Maradi na Jamhuriyar Nijar, inda za a yi masa jana'iza a gobe Juma'a kamar yadda addinin Islama ya tanada.
Hezbollah ta harba rokoki zuwa arewacin Isra'ila
Hezbollah ta ce ta harba gwamman makaman roka zuwa arewacin Isra'ila.
Kungiyar ta ce wannan martanin farko ne na kisan da aka yi wa mutum 10 a kudancin Lebanon a hare haren ta saman da Isra'ila ta kai a ranar Laraba.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kashe wani kwamandan kungiyar ta Hezbollah a hare haren na jiya a inda aka kashe akalla yara 5.
Ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant, ya ce dukkansu wato Isra'ilan da Hezbollah sun kara zafafa hare haren da suke kai wa juna.
CBN ya dakatar da bayar da alawus din tafiye-tafiye a hannu
Babban Bankin Najeriya, CBN ya ce daga yanzu ya dakatar da bayar da alawusn din tafiye-tafiye a hannu, a maimakon haka za a rika tura kudin ne zuwa asusun ajiyar jami'an gwamnati.
Cikin wata sanarwa da daraktan sashen kasuwanci da musayar kudi na CBN din, Hassan Mahmud ya fitar ranar Laraba ya ce an dauki matakin ne don dakatar da tashin farashin dalar a fadin kasar.
“A kokarin da CBN ke yi don tabbatar da daidaita farashin dala a kasuwar musayar kudade, babban bankin ya umarci duka bankunan da su rika tura kudaden alawus-alawus na tafiye-tafiye ta asusun banki'', in ji sanarwar.
A baya-bayan nan dai farashin dala na ci gaba da tashi a Najeriya, inda ya kai matakin da bai taba kai wa ba.
Lamarin da masana ke alakantawa da tashin farashin kayayyaki da haddasa tsadar rayuwa a kasar.
Ana alhinin rasuwar fitaccen dan jaridar Sudan Mahjoub Mohamed Salih
Ana ci gaba da alhinin rasuwar fitaccen dan jaridar nan na kasar Sudan, Mahjoub Mohamed Salih, wanda ya rasu yana da shekara 95.
Dan jaridar ya rasu ne a asibitin birnin Alqahira da ke Masar.
'Yan jaridar Sudan da Sudan ta Kudu sun yi ta bayyana alhinin rasuwar dan jaridar a shafukansu na sada zumunta
Marigayin ya zama an jarida tun a shekarar 1949 bayan ya shiga gangamin neman 'yancin Sudan.
Mista Salih ya zama fitaccen dan jarida ne a lokacin da ya fara kawo labaran yakin yankin Darfur da ke yammacin kasar a shekarar 2003.
Lamarin da ya sa gwamnatin kasar ta tilasta masa rufe kafar yada labransa mai suna Al-Ayaam tsakanin watan Nuwamban 2003 zuwa Janairun 2004, sakamakon yawaitar rahotonnin yakin da yake bayarwa.
To sai dai hukumomin kasar sun ce sun rufe kafar yada labaran saboda ta gaza biyan haraji.
Haka kuma an sha daure shi a gidajen yari sau da dama saboda yadda bayar da rahotonnin yakin.
A shekrar 2005 Kungiyar Kamfanonin Jaridu ta Duniya ta ba shi kyautar 'Golden Pen of Freedom Award'.
Sojojin Isra'ila sun ƙaddamar da samame a asibitin Gaza
Dakarun Isra'ila sun kaddamar da samame a babban asibitin da ke kudancin Gaza, bayan da suka samu bayanan sirri cewa akwai gawarwakin mutanen da ake garkuwa da su a asibitin.
Daraktan asibitin Nasser ya shaida wa BBC cewa asibitin na cikin mummunan yanayi, kuma sauran marasa lafiyar da ya ce na cike a dakunan asibitin, na cikin hatsari.
An kori wani likitan kungiyar likitoci ta Medecins Sans Frontieres daga asibitin, inda ya bar marasa lafiya.
Kungiyar ta ce dakarun Isra'ila sun kakkafa shingayen bincike domin tantance mutanen da ke ficewa daga asibitin, inda aka tsare daya daga cikin ma'aikatan kungiyar likitocin.
Matsayin Najeriya da Ivory Coast ya ƙaru a kwallon ƙafa bayan Afcon
Gwamnan Kaduna ya umarci a yi bincike kan 'yan KASTLEA da suka karbi kudi a hannun Hausa Guy
Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan jami'an hukumar tabbatar da bin dokokin tuki na jihar, wato KASTLEA da aka zarga da saba ka'idar aiki.
Cikin makon nan ne fitataccen mai amfani da shafukan sada zumuntar nan mai suna Hausa Guy ya fitar da wani bidiyo da a ciki ya zargi jami'an hukumar KASTLEA da kama shi da laifin da a cewarsa bai aikata ba, inda suka rubuta masa tarar naira 20,000.
To sai dai Hausa Guy ya yi ikirarin cewa a maimakon jami'an hukumar su ba shi asusun gwamnati domin tura kudin tarar a ciki, sai suka ba shi asusun wata mata, wanda ya ce ya tura kudin a ciki ta hanyar amfani na na'urar POS.
To sai dai a cikin wata sanarwar da sakataren yada labaran gwamnan jihar Muhammad Lawal Shehu ya fitar, gwamnan ya ce ba zai lamunci kowane irin nau'in cin hanci a ma'aikatu da hukumomin gwamnatin jihar ba.
''Gwamnatinmu a shiye take wajen kare 'yan kasa daga ayyukan wasu bata-gari a cikin al'umma, don haka ne muke kira da al'umma da su kai rahoton duk wani nau'in cin hanci daaka yi musu zuwa ga hukumomi, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci'', in ji sanarwar.
'Yan sanda sun kama mutanen da ake zargi da garkuwa da wani yaro tare da kashe shi a Kano
Rundunar 'yansandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutum hudu bisa zargin garkuwa da wani yaro.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce a ranar 8 ga watan Fabrairun da muke ciki ne ta samu rahoto daga wani mutum mai suna Alhaji Rabi'u Abdullahi da ke unguwar Hotoron Fulani cewa wasu mutane sun sace dansa mai suna Abdullahi Sani, inda suka bukaci ya biya naira miliyan hudu don sakin dan nasa.
Sanarwar ta ce daga nan ne kwamishinan 'yan sandan jihar ya umarci sashen yaki da garkuwa da mutane na rundunar 'yansandan jihar su tabbatar da kubutar da yaron tare da kama maharan.
Cikin binciken farko ne ya kai ga kama wani mutum mai suna Ismail Adamu, mai shekara 22 a unguwar Hotoron Fulani, inda bayan tuhumarsa ne ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, yana mai cewa ya hada baki ne wani mutum mai suna Risi da ke unguwar Mariri wajen sace yaron.
Ya ce sun boye yaron ne a kauyen Sabuwar Zara, inda suka yanka shi a wuya tare da jefa shi cikin wani masai na wani gidan da ba a kammala ba, sai kuma daga baya suka kira mahaifinsa suka bukaci ya biya naira miliyan hudu kafin su saki yaron.
Sanarwar 'yan sandan ta kara da cewa 'yan sanda sun ziyarci wajen da suka boye yaron, inda suka ciro gawarsa daga cikin masan da suka boye shi, tare da kai shi asibitin Abdullahi Wase da ke jihar, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Binciken 'yansanda ya kai ga kama wasu mutum biyu a unguwar Hotoron Fulanin da wadanda suka sace yaron suka yi amfani da wayoyinsu don daidaitawa kan kudin fansar da za a biya su.
'Yan sandan sun ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Tinubu na duba yiwuwar kafa 'yan sandan jihohi
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da a duba yiwuwa kafa rundunar ‘yansandan jihohi a kasar.
Wannan dai na daga cikin batutuwan da aka tattauna a wajen wani taron gaggawa da ya yi da gwamnonin jihohin kasar 36 ranar Alhamis a fadarsa.
Taron dai ya mayar da hankali ne kan nazarin muhimman matsalolin da ke addabar kasar yanzu da zimman nemo bakin zaren warware su.
Batutuwan dai sun hada da na tsaro, da tsadar rayuwan da karancin abinci da makamantansu kamar yadda ministan watsa labarai da wayar da kan jama’a Mohammed Idris ya sanar da manema labarai bayan tashi daga zaman.
Ya ce zaman ya kunshi shawarwari kan yadda za a hada kai tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya domin magance matsalolin da ke ci wa kasar tuwo a kwarya.
''Ba ma son rabe-rabe tsakanin jihohi da gwmnatin tarayya, ko da a wace jam'iyya kake, an yi shawawara kan yadda za a ciyar da kasar gaba'', in ji shi.
Dangane da 'yan sandan jihohi, ministan ya ce shugaba Tinubu ya amince cewa a duba maganar yiwuwar kafa 'yan a fadin jihohin kasar, maimakon dogara da 'yan sandan gwamnatin tarayya.
''To sai dai wani abu ne da yake bukatar nutsuwa a duba a kuma tantance, ba abu ba ne da kawai za a fada cikinsa kai tsaye, yana bukatar nazari sosai'', in ji ministan yada labaran.
Ministan ya kara da cewa taron ya amince da shugabannin hukumomin tsaron kasar su yi aiki tare da gwamnonin jihohi wajen sa kafar wando daya da wadanda suka boye kayan abinci da muhimman kayan masarufi domin su yi tsada sannan su sayar da su.
Hka kuma shugaban kasar da gwamnonin sun kuma amince cewa kasar ba ta bukatar shigo da kayan abinci daga waje, domin sauko da farashinsa, suna masu cewa kasar na iya dogara da abincin da al’ummarta ke nomawa.
Wannan taron dai na zuwa ne ‘yan kwanakki bayan da gwamnonin babbar jam’iyyar adawa ta PDP suka yi wani taron inda suka kwatanta halin da kasar ta shiga ta fuskar tabarbarewar tattalin arziki da tashin farashin kaya da rashin tsaro da irin wanda kasar Venezuela ta shiga a shekarun baya.
Ko a jiya ma dai majalisar sarakunan gargajiya ta kasar ta yi wani taro Kaduna a inda ta nuna damuwa game da karuwar matsalolin tsaro da talauci da kuma rashin aikin yi tsakanin al’ummar kasar musamman a yankin na arewa.
Sojojin Afirka ta Kudu biyu sun mutu a wani harin bam da aka kai a DR Congo
Sojojin Afrika ta Kudu biyu ne suka mutu sannan wasu uku kuma suka jikkata bayan da wani bam ya tashi a ɗaya daga cikin sansanonin sojinsu a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, inda aka tura dakarunsu domin kwantar da tarzoma.
Wannan dai shi ne karon farko da aka samu hasarar rayuka tun bayan da sojojin Afirka ta Kudu suka fara zuwa DR Congo a watan Disambar da ya gabata.
An kai harin ne a garin Sake, mai tazarar kilomita 27 daga yammacin Goma.
"Babu cikakken bayani kan afkuwar lamarin, za a cigaba da bincike domin gano abun da ya janyo tashin bam ɗin". in ji rundunar sojojin Afirka ta Kudu a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X a ranar Alhamis.
Sojojin Afirka ta Kudu tare da dakarun Tanzaniya da Malawi na cikin tawagar Kudancin Afirka a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo (SAMIDRC), da aka tura domin taimaka wa gwamnati wajen samar da zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali a gabashin kasar.
A ranar Litinin din da ta gabata ne shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayar da umarnin tura sojoji 2,900.
Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce, tura sojojin kasar Afirka ta Kudun za su lashe kudin kasar Rand biliyan biyu wato dala miliyan 105 kenan kuma zai ci gaba da aiki har zuwa watan Disamba na wannan shekara.
Kafin lokacin harin da aka kai sansanin na Afirka ta Kudu, kungiyar 'yan tawayen M23 ta yi kira ga mazauna garin Sake da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na kasuwanci tare da kara da cewa M23 na zuwa ne domin kwato su da kuma kare su daga wadannan manyan bindigogi da jirage marasa matuka da kuma tankokin yaki da ke ci gaba da kashe mata da yara da tsofaffi".
Har yanzu DR Congo ba ta mayar da martani ga sanarwar M23 ba.
Wani fada da ya sake barkewa a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a baya-bayan nan ya raba dubunnan mutane da muhallansu.
Adadin mutanen da ake zargin sojoji sun kashe a Habasha ya zarce 200
Adadin fararen hula da ake zargin jami'an tsaron ƙasar Habasha sun kashe a wani gari da ke arewa maso yammacin kasar ta Amhara ya zarce 200, kamar yadda cibiyar watsa labarai ta Amhara mai goyon bayan ABC ta ruwaito a jiya.
Shaidun gani da ido sun ce adadin mutanen da sojojin gwamnatin suka kashe a garin Merawi ya haura 200," in ji cibiyar.
Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan da wani fitaccen dan jarida ya yi iƙirarin cewa akalla fararen hula 157 ne jami'an tsaro suka kashe a garin biyo bayan ƙazamin faɗa tsakanin sojoji da 'yan kungiyar Fano a ranar 29 ga watan Janairu.
Hukumar kare haƙƙoƙin ɗan Adam ta Habasha da gwamnati ta naɗa ta kuma zargi dakarun gwamnati da kashe fararen hula akalla 45 a garin.
Har yanzu dai gwamnatin Habasha ba ta ce uffan ba kan wannan zargi.
Kungiyar fano dai na fafatawa da dakarun gwamnatin tarayya a yankin bayan da ta ki amincewa da shirin gwamnati na kwance damarar mayakan ta.
Isra'ila ta kaddamar da hare-haren sama kan Hezbollah a Lebanon
An kwashe awowi 24 ana mummunar musayar wuta a kan iyakar Isra'ila da Lebanon wadda ta fara tun bayan fara yakin Gaza.
A safiyar yau wani jirgin yakin Isra'ila ya kai hari kan wasu wuraren 'yan kungiyar Hezbollah a garin Wadi Saluki da ke kudancin Lebanon.
Da ma dai ana sa ran faruwar Irin wadannan hare-haren tun bayan da kungiyar Hezbollah ta ayyana goyon bayanta ga kungiyar Hamas, inda kuma ta rinka antaya rokoki zuwa cikin Isra'ila ita ma Isra'ilar na mayarwa.
Akalla mutum 10 da suka hada da kananan yara guda biyar suka mutu sakamakon wani harin sama a ranar Laraba bayan da kungiyar Hezbollah ta kashe wani sojan Isra'ila ranar Talata.
Da safiyar yau kungiyar Hezbollah ta sanar da cewa an kashe mata mayaka guda uku.
Shugaban rundunar sojin Isra'ila, IDF, Laftanar Janar Herzi Halevi ya ce sojojinsu "suna samun gagarumar nasara a yakar kungiyar Hezbollah a Lebanon kuma hakan zai ci gaba.
A wani mabban kwamanda a kungiyar Hezbollah ya ce Isra'ila "za ta dandana kudarta dangane da ayyukan da ta aikata."
- Hassan Nasrallah: Abin da ya kamata ku sani kan jagoran kungiyar Hezbollah
- Su wane ne 'yan Houthi kuma me ya sa suke kai hari kan jiragen ruwa?
Likitoci a Rafah sun ce 'tankokin yaƙi da gwanayen harbi' sun zagaye asibitin Naseer
Dr Khaled Aslerr, kwararren likita mai tiyata a asibitin Nasser, ya aike da sakon murya zuwa ga daya daga cikin wakilanmu a Jerusalem, inda yake cewa "tankokin yaki da gwanyen harbi" sun yi wa asibitin kawanya daga dukkanin bangarori.
Asler ya kara da cewa dakarun Isra'ila sun yi sanarwa guda uku a yau da safe cewa dukkannin mutanen da ke asibitin su fice da gaggawa.
Wani mutum ne ya yi sanarwa a cikin asibitin, sannan kuma wani shi ma ya sake ta hanyar lasifika da ke manne da wani jirgi maras matuki.
Farashin kaya ya tashi zuwa kaso 29.90 a Najeriya - NBS
Farashin kayayyaki a Najeriya ya haura zuwa kashi 29.90 cikin 100 a watan Janairun 2024, a cewar sabon bayanan da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar, ranar Alhamis.
Rahoton na NBS ya ce "a cikin watan Janairun 2024, farashin kayan masarufi ya karu zuwa 29.90% idan aka kwatanta da hauhawar farashin kayayyaki a watan Disamba na shekarar 2023 wanda ya kai 28.92%,"
Hakan na nufin cewa hauhawar farashin kayan masarufi a watanJanairun 2024 ta ƙaru da maki 0.98 cikin 100 idan aka kwatanta da farashin Disamban 2023.
Hakazalika, a kowace shekara, hauhawar farashin kayayyaki ya kasance da kaso 8.08 sama da adadin da aka rubuta a watan Janairun 2023, wanda ya kai kashi 21.82 cikin 100.
A cewar NBS, hauhawar farashin abinci, a duk shekara ya kai kashi 35.41 cikin 100 wato da maki 11.10 cikin 100 idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Janairun 2023.
"Samun ƙarin farashin kayan abinci a kowace shekara na faruwa ne sakamakon hauhawar farashin burodi da hatsi da dankali da dawa da mai da kifi da nama da 'ya'yan itace da dai sauran su." in ji hukumar a rahotonta.
- Abubuwan da suka haifar wa duniya tsadar rayuwa
- 'Farashin kayan abinci zai ci gaba da tashi a Najeriya'
Hotunan yadda Falasɗinawa ke rayuwa a kudancin Gaza
Fiye da Falasɗinawa miliyan ɗaya da aka ɗaiɗaita ne ke samun mafaka a birnin Rafah da ke kudancin Gaza inda Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce yanayin jin ƙai na cikin mawuyacin hali.
"Suna da ƙarancin abinci, ba sa iya samun kulawa ta lafiya, babu wurin barci sannan babu wajen tsira," in ji shuagaban hukumar jin ƙai ta MDD, Martin Griffiths.
Ga wasu hotuna na baya-bayan nan daga Rafah.
Tinubu ya gana da gwamnoni kan taɓarɓarewar tattalin arziƙi da tsaro
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da gwamnonin ƙasar a zauren majalisar dokoki da ke Abuja.
Taron wanda aka fara da misalin karfe 11:30 na safe, ya samu halartar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike; da Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun.
Taron dai bai rasa nasaba da damuwar da ake nunawa a fadin kasar dangane da tsadar kayan abinci da rashin tsaro da sauran batutuwan da suka shafi tattalin arziki.
Taron dai ya biyo bayan taron Majalisar Tattalin Arzikin Kasa (NEC) na wata-wata, wanda mataimakin shugaban kasa Shettima ya jagoranta.
Bayan koke-koke da al'ummar kasar suka yi kan tabarbarewar tsaro da tabarbarewar tattalin arziki, shugaban kasar ya umarci ma'aikatar noma da samar da abinci ta saki kimanin tan dubu arba'in da biyu na masara da gero da sauran kayayyakin masarufi a cikin tsare-tsare don magance hauhawar farashin kayan abinci a kasar.
Shugaban ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da zuba ido kan ƙalubalen tattalin arziƙi da tsaro da Najeriya ke fuskanta.
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta yi ciki har da cire tallafin man fetur ya zama dole, inda ta kara da cewa wadannan matakan za su haifar da riba nan ba da jimawa ba.
- Matsalar hare-haren ƴan bindiga ta ɗauki sabon salo a jihar Zamfara
- Me dawo da canjin dala ga masu shiga da shinkafa Najeriya yake nufi?
Faransa ta gargaɗi 'yan kasar kan yin tafiya zuwa arewacin Mozambique
Ofishin jakadancin Faransa da ke Mozambik ya gargadi 'yan kasarsa kan yin tafiya zuwa lardin Cabo Delgado da ke arewacin kasar saboda rashin tsaro a wannan yanki na kasar.
"Muna ba da shawara mai karfi game da tafiya zuwa garuruwan Mocimboa da Praia da Pemba da Palma, da hanyoyin da suka hada su saboda barazanar ta'addanci da sace-sacen jama'a," in ji wata sanarwa da aka raba a shafin intanet na ofishin jakadancin.
Gargadin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka buɗe wuta a kan mazauna garin tare da ƙona majami’u huɗu da wata makarantar Kirista a wani hari da suka kai a gundumar Chiure.
Cabo Delgado ya sami karuwar ayyukan tsageru a cikin watan da ya gabata, yayin da kafofin yaɗa labarai na cikin gida suka ba da rahoton hare-hare sama da 12 a cikin makonni biyu na farkon shekarar 2024.