An sake komawa tattaunawar tsagaita wuta a Gaza yayin da Isra'ila ke kai hari a Rafah

Asalin hoton, Reuters
An koma kan teburin tattaunawa kan yadda za a cimma tsagaita wuta a Gaza, a birnin Alƙahira na ƙasar Masar, kamar yadda kafofin watsa labaru na Masar suka ruwaito.
Manyan jami'an Amurka da Isra'ila da Masar da kuma Qatar ne ke yin ganawar, yayin da Isra'ila ke fuskantar ƙarin matsin lamba da ta daina ruwan bama-bamai a birnin Rafah da ke kudancin Gaza.
Kimanin mutane 1.5 miliyan ne ke cunkushe a ƙaramin garin da ke bakin iyaka, cikin fargabar hare-haren da Isra'ilan ke kaiwa ta ƙasa.
Firai ministan Isra'ilan ya yi watsi da tayin tsagaita wutar da ya kira ta "yaudara" da Hamas ta yi a makon jiya.
Benjamin Netanyahu ya ce "an kusa samun gagarumar "nasara" ta ƙarshe a Gaza a cikin ƴan watanni.
Inda daga bisani ya umarci dakarunsa da su faɗaɗa hare-haren da suke kaiwa ta ƙasa, yana mai cin alwashin sai ya ga bayan mayaƙan Hamas da ke Rafah.
Amma shugaban hukumar kare haƙƙin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk, ya ce duk wani harin da za a kai birnin zai "munana" kuma akwai yiwuwar kashe mutane da dama."
Shugaban Amurka, Joe Biden ya yi kira da a kare rayukan fararen hular da ke yankin.
Birnin na Rafah ya fuskanci zafafan hare-hare ta sama a cikin kwanakin nan daga Isra'ila, inda aka bayar da rahotannin rasa rayuka.


















