Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir and A'isha Babangida

  1. Hotunan Rafah bayan mummunan harin Isra'ila

    Ga wasu hotuna na baya-bayan nan na yankin Rafah inda Isra'ila ta shafe dare tana luguden wuta har gomman mutane suka mutu.

    Kimanin Falasdinawa miliyan daya da rabi ne ke samun mafaka a yankin da ke Kudancin Gaza, akasari sun tsere zuwa wasu wuraren a Zirin.

  2. Tinubu ya yaba wa Super Eagles duk da rashin lashe gasar Afcon

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yaba tare da karfafa wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles gwiwa bayan wasan da suka buga da Ivory Coast - mai masaukin baki wadda ta lashe gasar ta cin kofin Afirka ta 2023 da aka kammala ranar Lahadi.

    Super Eagles sun yi rashin nasara a hannun Ivory Coast da ci biyu da daya, abin da ya kawo musu cikas a kokarin neman lashe kofin karo na hudu.

    Duk da rashin nasarar, Shugaba Tinubu ya yaba da jajircewar da Super Eagles suka nuna.

    Cikin wata sanarwa da mai bashi shawara kan yada labarai, Ajuri Ngelale, Shugaba Tinubu ya yaba wa kungiyar saboda kokarin da suka yi a gasar.

    Shugaba Tinubu ya kuma bukaci yan kasa da kada su duba rashin nasarar da kungiyar ta yi, a maimakon haka su yi murna da nasarorin da Super Eagles ta yi.

    A cewarsa, duk da rashin daga kofin a wannan karon, yana da yakinin Super Eagles ta samu babbar nasara a Afirka da duniya da irin kwallon da suka buga a filin wasa.

    Ya kara da cewa bai kamata rashin nasarar ta sagar da gwiwoyin jama'a ba, hakan ya zama wani sanadin hada kan al'umma.

    • Nasarar Super Eagles da Ƙaddamar da sabbin jiregen yaƙi da wa'adin ƙungiyar kwadago
    • Yadda ƙwallo ke haɗa kan ƴan Najeriya, su manta da damuwarsu
  3. Yau wa'adin biyan kuɗin hajjin bana a Najeriya ke cika

    Yayin da yau ke zama ranar karshe da hukumar aikin hajji ta Najeriya ta bayar domin maniyyata su kammala biyan kudin kujerar hajji, bayanai sun nuna cewa da wuya ne kasar ta cike gurbin kujeru dubu cassa'in da biyar da hukumomin Saudiyya suka yi mata tanadi.

    Rahotanni na cewa akwai maniyyata da dama da suka gaza biyan ko dai kafin alkalami ko ma biyan cikon kudin hajjin da NAHCON ta sanar.

    Karyewar darajar takardar naira ta sa kudin kujerar aikin hajji tashi zuwa naira miliyan hudu da dubu dari tara daga kafin alkalamin naira miliyan hudu da rabi da hukumar aikin hajji ta Najeriya ta sanar.

    A ranar 30 ga watan Janairu ne darajar naira ta yi faduwar da ba ta taba yi ba inda a hukumance aka sayar da ita a naira dubu daya da dari hudu da goma sha uku kan kowace dala guda.

    NAHCON ta ce maniyyata hajjin bana daga kudancin Najeriya za su biya naira miliyan hudu da dubu dari takwas da dubu cassa'in da tara a matsayin kudin kujerar hajji yayin da wadanda suka fito daga arewacin kasar za su biya naira miliyan hudu da dubu dari shida da dubu cassa'in da tara sai kuma maniyyata daga Yola da Maiduguri da za su biya naira miliyan hudu da dubu dari shida da dubu saba'in da tara.

    NAHCON ta ware kujeru dubu saba'in da biyar ga jihohi talatin da shida har da Abuja, babban birnin tarayyar kasar sai kuma kujeru dubu ashirin ga jiragen yawo.

    Duk da cewa hukumar ba ta bayyana adadin maniyyatan da suka yi rajista a bana ba, wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ya nuna cewa galibin jihohin Najeriya ba su cike rabin kujerun da aka ware musu ba.

    • Waiwaye: Ƙara wa'adin biyan kuɗin aikin Hajjin bana da soke karɓar digirin jami'o'in Benin da Togo
    • Saudiyya ta bai wa Najeriya kujeru 95,000 a Hajjin 2023
  4. Mutane da dama sun jikkata sakamakon fashewar wani abu a yammacin Kamaru

    Dalibi daya ya mutu wasu da dama kuma sun jikkata bayan da wata nakiya ta tashi a yankin Arewa maso Yamma na kasar Kamaru kamar yadda gwamnan yankin ya shaida wa ƙafafen yaɗa labarai.

    Lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da daliban ke gudanar da tattakin tunawa da ranar matasan ƙasar a garin Nkambe.

    Hotuna da bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ɗalibai ke gudu don tsira bayan fashewar.

    Gwamna Adolphe Lele L’Afrique ya ce ana zargin mayaƙan ‘yan aware ne suka kai harin.

    'Yan awaren Anglophone sun sanya dokar hana fita don tarwatsa bikin tunawa da ranar matasan ƙasar.

    Ana yawan kai hare-hare kan ɗalibai da malamai da cibiyoyin ilimi a Kamaru.

    Ana dai kallon lamarin a matsayin wani yunƙuri na ‘yan awaren na ganin sun tilasta ƙaurace wa harkokin ilimi, wanda suka kafa shekaru bakwai da suka gabata.

    • Yadda fashewar nakiya ta hallaka sojojin Nijar
    • An samu fashewar wani abu a Tehran babban birnin Iran
  5. Hisbah ta kwace kwalaban giya, ta kama mata masu zaman kansu a Kano

    Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kwace kwalaben barasa akalla dubu takwas da dari shida da aka loda cikin wata mota da ta shiga jihar daga Kaduna.

    Jami'in hukumar da ke yaki da kayan maye, Idris Ibrahim wanda ya bayyana haka ga yan jarida a karshen mako, ya ce an kwace barasar ne ranar Alhamis da ta gabata a kauyen Kwanar Dangora da ke kan babbar hanyar Kano zuwa Kaduna.

    Jaridar Vanguard ta ruwaito jami'in na bayyana cewa jami'an Hisbah sun yi ta bibiyar motar daga Kaduna har ta isa Kano.

    Ya ce "mun tsayar da motar a Kwanar Dangora inda direban ya yi yunkurin tserewa sai dai jami'anmu sun kama shi."

    Ibrahim ya kara da cewa tawagar hukumar da ke yaki da kayan maye suna dakon umarni daga manyan jami'an Hisbah.

    A cewarsa, Hisbah ta kuma kama yan mata 15 masu zaman kansu a wurare daban-daban na jihar Kano.

    Bayanai na cewa an kama matan ne a unguwannin Hotoro da Tishama da Sabon Gari da titin Miyangu da titin Hadeja da kuma tsohuwar tashar mota da ke Titin Zoo Road.

    Mataimakin babban kwamandan hukumar, Dr Mujahid Aminuddeen wanda ya tabbatar da kamen ya ce an sha kama wasu daga cikin wadanda ake zargi masu zaman kansu ne inda aka gurfanar da su gaban kotu amma sun ci gaba da aikata haramtacciyar sana'ar.

    • Matar da ke yaƙi da masu safarar mata don yin karuwanci a Sicily
    • Muna neman kotu ta halasta karuwanci karara - Karuwai
  6. Mai rike da kambun gasar gudun fanfalaki ta duniya ya mutu

    Dan wasan da ke rike da kambun gasar gudun fanfalaki na duniya , Kelvin Kiptum ya mutu a wani hatsarin mota.

    Dan wasan na Kenya ya mutu ne tare da kocinsa a lokacin da motarsu ta yi hatsari a wani wuri da ke yammacin kasar Kenyar da yammacin ranar Lahadi.

    Wakiliyar BBC ta cemarigayin mai shekara 24ya kafa tarihi a wasan gudun fanfalaki da aka yi a Chicago a bara inda ya ya yi nasara a cikinsa‘oi biyu da dakika talatin da biyar.

    Ministan wasannin kasar Ababu Nam-wam-ba ya bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi.

    Shi ma jagoran yan hamayya na kasar kuma tsohon Firaiminista Raila Odinga ya ce kasar ta yi rashin babban gwarzo kuma tana jimamin mutuwarsa.

    • Ko mutuwar 'yan Afirka a filin wasa yana da alaka da launin fatarsu?
    • Mo Farah ya janye daga gasar Gudun Fanfalaki
  7. Assalamu Alaikum!

    Maraba da shigowa shafin BBC Hausa na Kai Tsaye da ke kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a duniya.

    Da fatan za ku kasance tare da mu daga yanzu har zuwa lokacin da za mu rufe wannan shafin (na Kai Tsaye).

    Akwai karin labarai a shafukanmu na sada zumunta da muhawara, kuna iya zuwa domin ku karanta har ma ku kalli bidiyo.

    Nabeela Mukhtar Uba tare da Usman Minjibir da A'isha Babangida ne za mu kasance tare da ku kafin mu mika ragama ga sauran abokan aiki domin dorawa daga inda muka tsaya.