Sai gobe!
Masu bibiyar mu ta wannan shafi a nan ne muka kawo ƙarshen shafin namu na abubuwan da ke gudana a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin.
Da fatan za ku biyo mu a shafinmu na ranar Talata idan Allah Ya kai mu.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir and A'isha Babangida
Masu bibiyar mu ta wannan shafi a nan ne muka kawo ƙarshen shafin namu na abubuwan da ke gudana a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin.
Da fatan za ku biyo mu a shafinmu na ranar Talata idan Allah Ya kai mu.
Haɗaɗɗiyar kungiyar masu abinci da masu fataucin dabbobi ta ƙasa ta Miyetti Allah ta koka kan tashinsu daga kasuwanni a kudu-maso-gabashin ƙasar.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa hukumomin na tashinsu daga kasuwanninsu ba tare da an yi musu tanadin wasu wurare na daban da zasu koma ba.
A baya-bayan nan ne gwamnatocin jihohin Enugu da Abia suka yi zargi cewa ana samun wasu daga cikin mazauna wadannan kasuwannin da hannu wajen a kai hare-hare da garkuwa da mutane da ake yi a yankin.
Sannan a cewar hukumomin kasuwannin dabbobin na kuma zama mafaka ga irin waɗannan ɓata gari.
Zargin da ƙungiyar ta sha musantawa.
Matsalar tsaro babbar matsala ce a Najeriya, wadda ta ƙi-ci-ta-ƙi-cinyewa duk kuwa da matakan da hukumomin suke cewa suna ɗauka.
Ɗanwasan kwallon ƙafa na Najeriya, Ahmed Musa ya yi kira da mutane da su daina zagi da aibata ɗanwasa, Alex Iwobi, a shafukan sada zumunta.
A cewar ɗanwasan tsakiyar, zagin ba kawai keta mutuncin Iwobi ya ke yi ba, hakan wani babban laifi ne.
"Wannan alama ce ta munafurci muna ikirarin cewa kwallon ƙafa na haɗa kanmu amma muna nuna wannan hali."
Inda ya ƙara da cewa rashin nasarar da ƙungiyar kwallon ƙafar ƙasar ta samu abu ne mai matuƙar ciwo, amma ɗora alhakin hakan kan ɗankwallo guda ɗaya rashin adalci ne.
Ahmed ya bayyana cewa nasara ta su ce gaba ɗaya ƙungiyar, haka kuma rashinta ta shafe su ne gaba ɗaya.
Yana mai kare Iwobi da cewa ya yi iya bakin ƙoƙarinsa a filin wasa kamar sauran takwarorinsa.
"Maimakon yaɗa abubuwa marasa daɗi, ya kamata mu nuna ƙauna ta haƙiƙa da goyon baya ga ƴanwasanmu, suna buƙatar mu basu kwarin guiwa a yanzu fiye da kowane lokaci..."
Tun bayan kammala gasar kwallon ƙafa zagayen ƙarshe da aka yi tsakanin Ivory Coast da Najeriya, ake ta zagi da aibata Alex Iwobi a kafafen sada zumunta.
Lamarin da ya kai shi ga ƙauracewa shafukansa tare da goge wasu abubuwan da ya wallafa.
Najeriya ta sha kaye a hannun mai masaukin baƙi da ci 2-1 a gasar wasan kwallon ƙafar ta nahiyar Afrika wadda aka kammala a ranar Lahadi.
Gwamnonin jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya sun yi kira da a kafa rundunonin ƴansanda na jihohi a karkashin wata doka da zata hana yin katsalandan daga duka matakan gwamnati.
Sun jaddada hakan ne a wurin wani taro da suka yi a ranar Litinin a Abuja, babban birnin ƙasar.
Taron ya kuma tattauna yanayin da ƙasar ta tsinci kanta game da wahalhulun da mutane ke fuskanta ta fuskar tattalin arziki da kuma tsaro.
Inda suka buƙaci gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa wajen ɓullo da wasu shirye-shirye da za su haɗa da duka ɓangarorin gwamnati don samar da mafita mai ɗorewa.
Gwamnonin na PDP sun kuma sha alwashin ci gaba da taka rawar da ta dace domin samar da tsaro ga al'ummansu, abun da a cewarsa ya sa suka jaddada buƙatar kafa ƴansandan jiha.
Taron ya kuma koka kan karyewar darajar kudin ƙasar wato naira, inda suka nemi hukumomin da abun ya shafa da su ɗauki matakan da suka dace domin magance matsalar.
Sai dai jihar Zamfara da ta Filato na daga cikin jihohin da jam'iyyar ta PDP ke mulki, kuma suke kan gaba wajen fuskantar matsalar tsaro da tashe-tashen hankula a tsawon shekaru.
Lamarin da ya yi sanadiyyar asarar dubban rayuka da ta dukiyoyi.
Babban jami'in hukumar kai ɗauki ta Majalisar Dinkin Duniya, Philippe Lazzarini ya ce an raba yara 17,000 da iyayensu, sannan yankuna da dama na Gaza na fama da ƙarancin abinci.
Lazzarini ya shaida wa manema labaru cewa "Ana maganar cewa akwai mutum 300,000 a arewacin Gaza waɗanda ke fama da yunwa, kuma mun kasa shirya yadda za a kai musu abinci tun daga ranar 23 ga watan Janairu."
"Haka nan kuma gudanar da aiki a yankin Rafah ya yi matuƙar wahala saboda yadda aka ƙara ƙaimi wajen kai farmaki a yankin."
Ya ƙara da cewa a cikin ƴan kwanakin nan an kwashe kayan da motocin hukumar ke ɗauke da su.
"Nan gaba kaɗan za mu gane cewa ko za mu iya ci gaba da aikin."
Dakarun tsaron ƙasar Tunusiya sun ce akalla bakin haure 17 'yan kasar Tunisiya da ke cikin kwale-kwalen da ke kan hanyar zuwa Italiya ne suka bace.
Waɗanda ke cikin jirgin da suka haɗa da wani yaro dan shekara biyar sun tashi ne a cikin wani jirgin kamun kifi daga Bizerte da ke arewacin Tunisiya a makon jiya.
Jami'an tsaron teku da na ruwa da ke samun goyon bayan jirage masu saukar ungulu na neman su.
Tunisiya ta karɓe iko daga Libya a matsayin babbar hanyar tashi da bakin haure da ke kokarin shiga Turai daga Afirka.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yero ya koma jam'iyyar APC, watanni kaɗan bayan ficewarsa daga jam'iyyar PDP.
Ramalan Yero ya sanar da ficewar tasa ne a wani bayani da ya yi wa manema labaru, yau Litinin a garin Kaduna.
A bayanin nasa, tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya ce ya koma APC ne bisa dalilai na ƙashin kansa bayan ya tattauna da waɗanda ke kusa da shi a harkar siyasa.
A cikin watan Oktoban shekarar 2023 ne Yero ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar PDP.
Ramalan Yero ya riƙe gwamnan jihar Kaduna ne ƙarƙashin jam'iyyar PDP daga shekara ta 2012 zuwa 2015 bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar Patrick Yakowa a wani hatsarin jirgin helikwafta.
Daga nan ne ya yi takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin inwar jam'iyyar ta PDP sai dai bai yi nasara ba,
Daga baya Ramalam Yero ya sha yunƙurin sake yin takarar gwamnan jihar, sai dai bai samu nasarar hakan ba, inda ya gaza yin nasara tun a matakin zaɓen fitar da ɗan takara.
Hare-haren da Isra'ila ta kai cikin dare sun kashe mutane da dama tare da lalata gine-gine a kudancin birnin Rafah, inda Falasdinawa kimanin miliyan 1.5 suka nemi mafaka.
Masallacin Al-Huda da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Yabna na daya daga cikin gine-ginen da suka lalace.
Ga wasu sabbin hotuna da ke nuna yadda harin Isra'ila ya lalata masallacin.
Ana ci gaba da aikin ceto a wani ƙauye mai nisa a arewacin Habasha inda sama da masu aikin hako ma'adinai 20 suka maƙale a cikin wani kogo.
Kwanaki uku kenan da kogon ya rufta kan masu hakar ma’adinan a gundumar Delanta.
Jami’an yankin ba su da tabbas game da ainihin adadin masu hakar ma’adinan da suka makale, wadanda ke neman duwatsu masu daraja na opal.
Hukumomin yankin sun shaida wa BBC cewa tsaunukan yankin sun dagula ayyukan ceton da suke yi.
Ɗaruruwan mazauna yankin na kokarin tona wuraren da masu hakar ma’adinan suke, saboda yanayin kauyen ya sa da wuya a samu tallafi daga injuna.
Ba a samu nasara ba kawo yanzu wajen yunƙurin ceto su,amma hukumomi na ci gaba da fatan ceto waɗanda suka tsira.
Jami’an sun ce a wani al’amari da ya faru a baya, an gano wani mai haƙar ma’adinan da rai bayan an binne shi a cikin kogon na tsawon kwanaki bakwai.
Rahotanni daga Turai na cewa wata kotun daukaka kara a Netherlands ta yanke hukuncin cewa dole ne kasar ta daina siyar wa Isra'ila jirgin yaki kirar F-35.
Wasu kungiyoyin kare hakkin bil'adama ne da suka hada da Oxfam suka shigar da gwamnatin Neitherlands din kara a watan Disambar bara.
Sun ce shigar da jirgin kirar F-35 ya saba dokar yaki kasancewar ana amfani da jiragen ne wajen kai hare-hare a zirin Gaza.
A baya dai wata kotun lardi ta yanke hukuncin cewa shigar da jiragen batu ne na siyasa a saboda haka bai kamata alkalai su shiga lamarin ba.
To sai dai a safiyar yau wata kotu ta ce "abu ne a bayyane take cewa akwai hadari shigar da jiragen saboda irin keta dokokin kasa da kasa na yaki da hakan yake haifarwa."
An sake bude makarantu a kasar Zambiya a karon farko a bana, bayan da aka samu jinkiri da dama bayan barkewar cutar kwalara.
An jinkirta buɗe makarantu da makwanni biyar a wani ɓangare na matakan kariya na dakile bazuwar cutar mai saurin yaduwa.
Ma’aikatar ilimi ta ce ta na gudanar da aikin duba makarantu a fadin kasar domin auna shirinsu na sake bude makarantu.
An samu saukin yaɗuwar cutar a cewar hukumomi.
Kimanin mutum 500 ne suka mutu tun bayan barkewar cutar a watan Oktoban da ya gabata.
Ya zuwa yanzu an samu rahoton bullar cutar fiye da 15,000, da yawa daga cikinsu yara ne.
Ƙasar Zambiya ta yi fama da ɓarkewar cutar kwalara da dama amma cutar a yanzu ita ce mafi muni cikin shekaru 20, a cewar gwamnati.
Ɓarkewar cutar ta kuma haifar da kamuwa da cutar da kuma mace-mace a makwabciyarta Zimbabwe da Mozambique.
Kungiyar Save the Children ta ƙasashen duniya ta ce wannan sabuwar matsalar lafiya barazana ce ga ilimin yara da kuma kariyar da ba a gani ba tun bayan ɓarkewar cutar korona.
Gawarwakin jami'an soji uku na Hadaddiyar Daular Larabawa - wadanda aka kashe a wani harin da 'yan bindiga suka kai Somaliya - sun isa birnin Abu Dhabi.
Sanarwar da aka fitar ta ce jami'in na hudu da ya samu raunuka yayin harin na ranar Asabar ya mutu a lokacin da ya isa Hadaddiyar Daular Larabawa.
Jami'an Masarautar sun ce jami'an sojin sun kasance a Somalia suna horar da sojojin kasar lokacin da aka kai harin.
Haka kuma, an kashe wani sojan Bahrain a harin, wanda kungiyar al-Shabab ta ce ta kai.
Barhrain dai ta yi allawadai ta harin a cikin wata sanarwa da ta fitar tare da bayyana shi a matsayin "aiki na zalunci" yayin da take makokin sojanta da aka kashe a harin.
Kafofin yaɗa labaran cikin gida sun ruwaito cewa wanda ake zargi da kai harin, wani sojan Somaliya ne da ke zaune a sansanin, wanda ya fice daga kungiyar al-Shabab a kwanakin baya.
An kai harin ne kan sojojin a sansanin soji na Janar Gordon da ke Mogadishu babban birnin Somalia.
Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya yi allawadai da harin, ya kuma umurci jami'an tsaron ƙasar da su gudanar da "bincike mai zurfi kuma cikin gaggawa".
Al-Shabab na ci gaba da kai munanan hare-hare a Somaliya duk da hare-haren soji da dakarun gwamnatin tarayya ke kai wa kungiyar tun a watan Agustan 2022.
Rundunar yan sanda a Abuja, babban birnin Najeriya ta ce ta kai samame wata matattarar miyagu inda ta kama mutum dari uku da bakwai da ake zargi da aikata laifuka.
Kwamishinan yan sanda a Abuja, CP Benneth C. Igwe ne ya jagoranci tawagar rundunar 'Operation Velvet' wajen kai samame kan matattarar da ke Gidan Dambe a yankin Dei-Dei zuwa Zuba.
Yayin binciken, an gano bindiga daya da alburusai goma sha biyar a hannun wani da yake ikirarin shi jami'in hukumar tsaro ta farin kaya ne.
A cewar sanarwar da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta wallafa a shafin X, sauran kayayyakin da aka gano sun hada da babura da kunshin tabar wiwi da haramtattun kwayoyi da ake zargi mutanen sun sace ne daga hannun mutanen da ba su ji ba su gani ba.
Kwamishinan yan sandan ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan mutanen da aka kama.
A makon da ya gabata ne aka kaddamar da rundunar ta musamman domin kawo karshen duk wasu miyagun laifuka a Abuja.
Kwamishinan ya kuma gargadi yan sanda kan tatsar jama'ar sannan su nuna kwarewa wajen aiwatar da ayyukansu.
Matar nan yar Najeriya, Pelumi Nubi ta isa Afirka a kokarin da take na zuwa Legas daga London a mota.
Ta tsara bi ta kasashe 17 cikin nisan da bai wuce kilomita dubu bakwai ba da burin isa Legas cikin wata biyu.
Matar mai shekara 29 tana wallafa bayanan yadda bulaguron nata ke kasancewa daga Paris a Faransa bayan da ta bar Ingila a farkon watan nan.
A ranar Lahadi, ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Instagram bayan da ta isa Moroko.
Hanyoyin da za ta bi sun hada da Yamma da hamadar Sahara da Mauritaniya da Senegal da Gambia da Guinea Bissu da Saliyo da Laberiya da Mali da Burkina Faso da Ivory Coast da Ghana da Togo da Benin sai Najeriya inda za ta yada zango a Legas.
Ms Nubi na ganin ita ce mace bakar fata ta farko da ke wannan yunkuri.
Ta jaddada cewa burinta ba shi ne kafa tarihi ba sai dai tana son nunawa duniya cewa za ta iya abin da ba a yi zato ba.
Shugaban rundunar sojin Sudan, Leftanar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya ce ba zai ba da kofar kai kayan jin kai zuwa yankunan da dakarun RSF suka mamaye ba har sai kungiyar ta fice daga wuraren.
Rundunar, a wani sako ta shafin Facebook, ta ce Burhan ya bayyana cewa yan tawaye suna kashewa tare da sace kayayyaki sannan su bukaci kungiyoyin agaji su kai dauki.
Ya jaddada cewa irin wannan ba za ta sake faruwa ba har sai an murkushe yan tawayen, an kuma fatattake su daga gidajen al'umma da cibiyoyin gwamnati da hukumomi sannan daga dukkan biranen da suka mamaye.
Jagoran RSF Mohamed Hamdan Dagalo a baya-bayan nan ya yi kira ga kungiyoyin agaji da su kai dauki zuwa yankunan Sudan musamman yankunan da rikicin ya fi shafa kamar Darfur da Kordofan.
Burhan wanda ke magana a sansanin sojoji a jihar arewa, ya musanta rahotannin baya-bayan nan na yunkurin yi masa juyin mulki.
Akasarin yankunan Sudan na ci gaba da fuskantar katsewar hanyoyin sadarwa, kwana biyar kenan. Sai dai an dawo da hanyoyin sadarwar a wasu yankunan kasar kamar yadda gidan rediyon Dabanga ya ruwaito.
Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce mutum sittin da bakwai aka kashe a hare-haren da aka kai cikin dare kan Rafah, kamar yadda kakakin kungiyar Asharf Al-Qudra ya bayyana.
Akwai rahotanni mabanbanta kan adadin mutanen da hare-haren na Isra'ila suka kashe.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce adadin mutanen da suka mutu sun kai kusan 100 inda ta ruwaito ma'aikatar lafiya ta Hamas ke fada.
Gwamman ma'aikatan jinya da ungozama ne suka hau titunan birnin Abuja domin nuna kin amincewarsu ga wasu sabbin dokoki da hukumar kula da ma'aikatan jinya da ungozoma ta kasa ta shimfida musu.
Sabbin dokokin dai sun hada da kwashe shekaru biyu wadanda suka karanci aikin jinya a jami'a suna suna aiki a Najeriya kafin hukumar ta tantance su a matsayin kwararrun ma'aikatan jinya. Hukumar ta kuma kara kudin tantancewar daga dubu 29 zuwa dubu 300.
To sai dai kungiyar ma'aikatan jinyar ta ce kudin ya yi yawa kasancewar a cikinsu akwai wadanda suke daukar albashin da bai wuce naira dubu 50 ba a wata.
Ma'aikatan lafiya dai a Najeriya na yawan ficewa daga kasar da zarar sun samu lasisin aiki zuwa wasu kasashen ketare.
Sau da dama dai ma'aikatan lafiya a Najeriya na kokawa kan rashin isasshiyar kulawa da suke samu ciki har da albashi.
Isra'ila ta ce ta kubutar da wasu maza biyu da Hamas ta yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoban 2023 a yankin Rafa da ke kudancin Gaza.
Mutanen dai su ne Fernando Simon Marman mai shekara 60 da Louis Har mai shekara 70.
Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar sojin Isra'ila, Daniel Hagari ya ce sojojin kasar sun kutsa cikin wani gini da ke tsakiyar Rafah, inda kuma suka gano mutanen biyu a hawa na biyu na ginin.
Hagari ya kara da cewa daga lokacin da suka shiga gidan, sojoji sun yi wa Marman da Har garkuwa da jikinsu inda suka soma harbe-harbe.
An kubutar da mutanen biyu daga gidan lokacin da ake musayar wuta, in ji kakakin, yayin da dakarun IDF suka ba su kariya a yankin Rafah har suka kai wurin da yake da tsaro.
Hagari ya kara da cewa an kai samamen da sassafe inda ya bayyana cewa hari ne da suka shirya masa.
A ranar 7 ga watan Oktoba ne, Hamas ta yi garkuwa da mutanen biyu daga Niir Yitzhak kibbutz.
Jam'iyyar adawa ta kasar Ghana karkashin mai yi mata takarar shugabancin kasar a 2024, John Mahama ta yi watsi da shirin dage ranar zaben kasar daga watan Nuwamba zuwa Disamba a wannan shekara.
Hukumar zaben kasar ta ce shirin dagewar dai tun farko daga jam'iyyun siyasa yake domin bai wa hukumar isassshiyar dama wajen shiryawa tsaf musamman idan aka samu yanayin da za a je zagaye na biyu na zaben.
To sai dai jaogran adawar kasar, John Mahama na jam'iyyar NDC ya ce dage zaben da sabon lokacin gudanar da shi da aka saka ba zai yiwu ba.
"Ba mu da amannar cewa an dage ranar zaben ne da kykkyawar niyya," in ji Mahama, inda ya kara da zargin hukumar zaben da rashin zama cikin ko-ta-kwana.
Tsohon shugaban kasar ya kuma ja hankalin hukumar da ta shirya gidanta domin tabbatar da karbabben zabe.
Harwayau dai hukumar zaben na duba yiwuwar sanya ranakun zaben su kasance ranakun hutu na kasa domin samun fitowar jama'a.
Dubban 'yan kasar Marocco sun gudanar da zanga-zanga a birnin Rabat suna kira ga ƙasar da ta kawo ƙarshen alaƙa da Isra'ila, saboda ayyukan yaƙin da take yi a Gaza.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun daga allunan da ke cewa "a dakatar da kisan kiyashi" yayin tattakin na Lahadi.
Rahotanni sun ce ‘yan siyasa daga sassa daban-daban na cikin jerin masu zanga-zangar.
Ƙasar Marocco dai ta ƙulla huldar diflomasiyya da Isra’ila a shekarar 2020 karkashin yarjejeniyar Abraham da Amurka ta kulla.
A wani ɓangare na yarjejeniyar, Morocco ta samu amincewar Amurka game da iƙirarin da take yi na samun ikon mallakar yankin yammacin Sahara da ake takaddama a kai.
Amma tun bayan da aka fara yaƙin Gaza ne aka fara adawa da yarjejeniyar.