Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida and Usman Minjibir

  1. Kwamitin Majalisar Dattijai ya fara tattaunawa da shugaban babban bankin Najeriya

    Kwamitin hadin gwiwa na Majalisar Dattawa mai kula da harkokin kudi da Banki da Inshora da cibiyoyin hada-hadar kudi na Najeriya ya fara tattaunawa da jami’an babban bankin Najeriya (CBN) da Gwamnan bankin Yemi Cardoso ke jagoranta.

    A ranar 31 ga watan Janairu ne dai kwamitin ya gayyaci gwamnan babban bankin kasar ya bayyana a gabansa.

    Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake nuna damuwa kan halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki da kuma faduwar darajar Naira a kasuwar canji.

    Sanatocin sun bukaci babban bankin kasar na CBN ya yi bayani kan dimbin kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a halin yanzu.

    Kasancewar talauci da rashin tsaro a kodayaushe sakamakon matsalar karancin abinci a ƙasar, ‘yan majalisar sun yi imanin cewa CBN ba zai iya gamsar da ‘yan Najeriya cewa manufofinsa suna aiki ba.

    • Hasashen Bankin Duniya kan jihohin Najeriya bakwai da za su fuskanci yunwa
    • Yadda farashin kayan masarufi ya tashi a lokacin mulkin Tinubu
  2. Wata kungiya ta kalubalanci masu son a rushe masarautun Kano

    Wata kungiya mai suna Inuwar Masarautun Kano Biyar (IMAK) ta yi kira ga majalisar dokokin jihar Kano da ta yi watsi da rokon wata kungiya mai suna 'Yan Dagwalen Kano - wadda a baya-bayan nan ta bukaci a rusa masarautun jihar guda hudu tare da mayar da tsohon sarki Khalipha Sanusi Lamido Sanusi.

    Kiran na kunshe cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar ta IMAK, Nasiru Ibrahim Rano ya aike wa shugaban majalisar dokokin jihar Kano.

    Kungiyar ta IMAK ta ce rushe masarautun kamar mayar da hannun agogo baya ne duba da rawar da suke takawa wajen samar da ci gaba ga al'ummarsu.

    Sanarwar ta bayyana illar rushe masarautun da ta ce yin hakan ka iya rikidewa zuwa matsalar tsaro da za ta jefa rayuka da dukiyoyin jama'a cikin wani hali.

    A cewarta, kyale masarautun zai ba da dama wajen farfado da martabarsu wanda hakan hanya ce da za ta taimaka wajen gaggauta aiwatar da manufofin gwamnati.

    Ta kara da cewa ana girmama duka sarakunan inda sanarwar ta ce a shirye suke su yi iya karfinsu domin tabbatar da zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki a jihar Kano.

    "Babu wani sarki da aka taba samu da hannu a cin hanci da rashin da'a ko yin ba daidai ba, a don haka kyale su a kan mukamansu shi ne abu mafi dacewa a wannan lokaci." kamar yadda sanarwar kungiyar ta bayyana.

    A karshe kungiyar ta yi kira ga majalisar dokokin da ta saurari bukatarsu ta kuma duba kiran saboda zaman lafiya a Kano.

    • Mece ce makomar masarautun Kano bayan tafiyar Ganduje?
    • Masarautar Kano: An tsunduma ta cikin siyasa – Masana Tarihi
  3. Sudan ta ce Saudiyya ce kaɗai za ta iya yin mata sulhu da dakarun RSF

    Majalisar mulkin soji da ke mulkin Sudan ta bayyana cewa, tattaunawar zaman lafiya tsakanin sojojin kasar da dakarun Rapid Support Forces (RSF) za ta iya gudana ne kawai ta hanyar shirin zaman lafiyar Jeddah da Saudiyya da Amurka ke jagoranta, kamar yadda gidan talabijin na Sudan TV mallakar gwamnati ya ruwaito.

    Duk da tattaunawar da aka yi da dama da sasantawa na wucin gadi a Jeddah, rikicin, wanda ya fara a watan Afrilun 2023, ya ci gaba, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 13,000, da jikkata 26,000, da kuma raba kusan mutane miliyan 7.6 da matsugunansu.

    Rashin jituwa kan yadda RSF ke iko da yawancin birnin Khartoum ya sa aka dage zaman tattaunawa a watan Disamba.

    "Gwamnatin Sudan ta tabbatar da cewa Saudiyya ce kaɗai za ta iya musu sulhu da dakarun RSF" in ji ministan yada labaran Sudan Graham Abdel Qadir a jiya a wani taron manema labarai.

    "Gwamnatin Sudan ba za ta zauna da ko tattaunawa da dakarun RSF ta wata kafa ba idan dai ba shirirn zaman lafiya na Jeddah ba."

    Wadannan kalamai sun biyo bayan gayyatar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi wa bangarorin biyu na wani taro a kasar Switzerland domin tattauna batun kai agaji ga mutanen da rikici ya shafa.

    A watan Janairu, shugaban gwamnatin Sudan Abdel Fattah al-Burhan, ya yi watsi da sabon yunkurin samar da zaman lafiya da kungiyar Igad ta yi, tare da dakatar da zama mamba a kungiyar.

    • 'Gwamnatin kasarmu ta wofintar da mu a Sudan'
    • 'Sai mun sayar da rai muke zuwa binne matattu a Sudan'
  4. Ƙungiyar ƴan ƙasar Senegal ta buƙaci jama'a da su yi gangami kan ɗage zaɓen ƙasar

    Sabon dandali na siyasar kasar Senegal mai suna Aar Sunu Election (Mu kare zabenmu) ya bukaci 'yan kasar da ke cikin kasar da ma na kasashen waje da su tashi tsaye don nuna adawa da dage zaben shugaban kasa da ya kamata a yi a wannan wata na Fabrairu zuwa Disamba.

    Kungiyar ta yi kira da a gudanar da zanga-zanga domin yin allawadai da jinkirin da aka samu, tare da jaddada bukatar kiyaye jadawalin zaben ƙasar.

    Dandalin ya kuma karfafa gwiwar Musulmi da su halarci sallar juma'a sanye da fararen kaya da nuna launin kasar, yayin da ta kuma bukaci malaman addini na yankin da su yi tir da ɗage zaben.

    Shugaba Macky Sall ya sanar da ɗage zaɓen ne a ranar 3 ga watan Fabrairu, saboda rashin jituwar da aka samu tsakanin majalisar dokokin ƙasar da majalisar tsarin mulkin ƙasar dangane da batun soke wasu ‘yan takarar shugaban kasa.

    Wannan shawarar ta haifar da damuwa game da yiwuwar rikicin siyasa a Senegal, kasar da aka sani da kwanciyar hankali ta dimokradiyya, tare da janyo kalubale da rikici a yankin.

    • Senegal na dab da shiga ruɗani bayan ɗage zaɓe
    • ƙasashe shida da dakarun Ecowas suka taɓa kai wa yaƙi
  5. Tinubu ya wajabta karanta alkawarin biyayya ga Najeriya a wurin taruka

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya wajabta karanta alkawarin biyayya ga Najeriya wato National Pleadge a turance a duk tarukan gwamnati da na jama'a a kasar.

    Kakakin shugaban kasar Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa ranar Alhamis, inda ya ce yin hakan nuna girmamawa ne ga kasa da kuma karfafa biyayya ga dokokin kasa tare da alkinta al'adu da martaba kasa.

    Shugaban ya jaddada bukatar yin biyayya ga manufofin kasa da nuna kima ga dokokin kasa.

    Taken na yi wa Najeriya alkawarin biyayya wanda Tinubu ya ce a rinka yin sa bayan rera taken kasa, na neman yan kasa su zama masu gaskiya da biyayya ga kasarsu.

    Umarnin ya zo ne daidai lokacin da Najeriya ke fama da rikice-rikice da tashin hankali da kuma tsananin rayuwa.

    • Bidiyon ƴanbindigar da suka sace amarya farfaganda ce – Gwamnatin Katsina
    • Ko yajin aikin ƴan kasuwar Najeriya zai samar da mafita kan tsadar rayuwa?
  6. 'Yan sanda sun kashe masu taimaka wa 'yan fashin daji da makamai

    Rundunar yan sandan Najeriya ta ce ta halaka wasu rikakkun yan bindiga da suka addabi Abuja da Kaduna da Kogi da Nassarawa a kokarin da jami'anta ke yi na murkushe masu garkuwa da yan bindiga a kasar.

    Ta ce jami'anta karkashin rundunar FID-IRT ta musamman ne suka kai samame kan maboyar yan bindigar a Gitata da ke jihar Nassarawa.

    Wata sanarwa da kakakin hedikwatar rundunar yan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar ta ce an gano bindigogi kirar AK47 da muggan makamai da leda makare da alburusai.

    Rundunar ta ce mutanen da aka halaka suna da hannu wajen kai wa yan fashin daji makamai.

    Rundunar ta ce za ta ci gaba da daukar matakai na kawar da masu aikata miyagun laifuka tare da tabbatar da doka da oda da kuma zaman lafiya a fadin Najeriya.

    • 'Yan bindiga sun 'kashe DPO na 'yan sanda na Jibiya da soja a Jihar Katsina'
    • 'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda 'bakwai' a Abuja
  7. Mutum hudu sun mutu a rikici kan rushe masallaci a Indiya

    Akalla mutum hudu ne suka mutu a wani tashin hankali da ya faru a wata jiha da ke arewacin Indiya bayan da hukumomi suka rushe wani masallaci bisa zargin gina shi ba bisa ka'ida ba.

    Rikici ya barke a garin Haldwani da ke jihar Uttarakhand saboda abin da yan sanda suka kira shirin dakile masu yin kutse.

    Hukumomi sun ce an kaddamar da shirin domin rushe gine-ginen da aka yi su ba bisa ka'ida ba ciki har da masallaci da wata makarantar Islamiyya da ke kusa da nan.

    Sai dai musulmai da ke sallah a masallacin sun ce ba a yi musu adalci ba.

    Daruruwan masu zanga-zanga da yan sanda ne suka ji rauni a rikicin da ya barke ranar Alhamis da daddare.

    Hotunan bidiyo sun nuna masu zanga-zangar na cinna wa motoci wuta tare da jefa duwatsu inda kuma yan sanda suka harba musu hayaki mai sa hawaye.

    An saka dokar hana fita an kuma bai wa jami'an tsaro umarnin harbin duk wanda suka gani domin kaucewa kazancewar al'amarin.

    • Indiya: Yadda maƙwabtakar masallaci da wurin bautar addinin Hindu ke rikiɗewa zuwa rikici
    • Kalli sabon wurin bautar Hindu da aka gina kan filin masallaci
  8. Kwakwalwata lafiya kalau take – Shugaba Biden

    Shugaban Amurka Joe Biden ya dage kan cewa shi ne mutum mafi cancanta da zai jagoranci kasar.

    Kalaman nasa na zuwa ne bayan wani bincike da ya gano cewa ya yi sakaci kan wasu manyan bayanan sirri tare da danganta hakan ga matsalar shugaban ta kasa tuno abubuwa.

    A wajen wani taron manema labarai da ya kira, shugaba Biden ya ce ƙwaƙwalwarsa lafiya lau take inda ya yi kakkausar suka ga mai binciken.

    "Ya kafa hujja da cewa ba na iya tuno lokacin da ɗana ya mutu, waye shi da zai ce haka? bani buƙatar sai wani ya tuna mani da lokacin da ɗana ya mutu," in ji Shugaba Biden na Amurka.

    • Yadda Shugaba Biden ya yi tuntuɓe sannan ya faɗi a bainar jama'a
    • Joe Biden: Trump ya yi wa hukumomin Amurka 'gagarumin ta'adi'
  9. Barka da Juma'a!

    Masu bibiyar BBC Hausa barkan mu da safiyar Juma'a - babbar rana.

    A wannan shafin na kai-tsaye na BBC Hausa, za mu kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu. Akwai shafukanmu na sada zumunta inda za ku iya duba karin labarai da bidiyo.