Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida and Usman Minjibir

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa Kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnn abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labaran.

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Isra'ila na shirn kwashe fararen hula daga birnin Rafah

    Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce ya gaya wa sojojin ƙasar da su samar da shirin yadda za su kwashe farar hula daga birnin Rafah, domin share fagen faɗaɗa yaƙin da suke yi da Hamas.

    Sama da Falasɗinawa miliyan ɗaya ne suke cushe a birnin na Rafah, yawancinsu masu neman mafaka da suka baro Gaza saboda hare-haren Isra'ila a can.

    Gwamnatin Amurka ta bukaci Isra'ila ta bi a sannu domin gudun illata farar hula. Kungiyoyin agaji sun ce ba abu ne mai yuwuwa ba a iya kwashe dukkanin mutanen da ke rafah.

    Sun ce yawanci daman mutanen na cikin yanayi ne na kaka-ni-kayi, tare da cewa ina ma za su sake nufa idan aka ce su fita daga birnin.

  3. Gwamnatin Madagascar ta kare kudurin dandaƙe masu fyaɗe

    Ministar shari'ar Madagascar ta kare sabon ƙudurin dokar da ƙasar take neman ɓullowa da ita, wadda za ta bayar da damar fiɗiye duk mutumin da aka kama da laifin yi wa yaro fyade.

    A makon nan ne majalisar dattawan ƙasar ta amince da hukuncin yin dandaƙa ta hanyar tiyata ga masu laifin fyade, musamman idan wanda aka yi wa 'yan ƙasa da shekara 10 ne.

    Kudurin ya tanadi zaɓin amfani da maganin asibiti wajen fiɗiyar idan wanda ko wadda aka yi wa fyaɗen mai shekara tsakanin 10 zuwa 18 ne.

    Sai dai ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Amnesty International ta soki ƙudurin da cewa, dokar ta saɓa wa dokar hana azabtarwa da sauran nau'ikan gallaza wa mutane.

    Ƙungiyar ta ƙara da cewa dokar ba za ta magance matsalar yi wa yara fyaɗe ba a Madagascar.

    To amma kuma ministar shari'ar ta ce, ya zama dole ne hukuma ta tashi tsaye ta ɗauki mataki saboda yawan fyaɗen da ake yi wa ƙananan yara.

    Kafin dokar ta tabbata sai kotun tsarin mulki da kuma shugaban ƙasar ta Madagascar sun amince da ƙudurin kafin ya zama doka a ƙasar.

  4. Zan taimaka wa al'ummar Kano yayin da ake cikin matsin rayuwa - Ɗangote

    Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya alƙawarta tallafa wa tsare-tsaren manunfofin taimaka wa al'umma da ci gabansu, don magance matsalolin tattalin arziki a jihar Kano.

    Dangote ya yi wanna alƙawarin ne a lokacin da ziyarci gwamnan jihar Kano Abba Yusuf a gidan gwamnatin jihar ranar Juma'a.

    Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya ce Dangote ya ce yana sane da halin matsin rayuwa da talakawan ƙasar ke fuskanta.

    Dangote ya alƙwarta bayar da tallafi don inganta fannonin lafiya da ilimi da hanyoyin yaƙi da talauci ga masu ƙaramin ƙarfi a jihar.

    Attajirin ɗan kasuwar ya alƙawarta yin aiki kafaɗa dakafaɗa da gwamnatin jihar don bunƙasa ci gaban al'ummar jihar.

    A nasa ɓangare gwamnan jihar ya gode wa hamshaƙin ɗan kasuwar bisa manyan ayyukan ci gaba da ya samar musamman sashen kula da masu buƙatar gaggawa da ɗakunan tiyata da na haihuwa da na yara a asibitin Murtala da ke jijar.

    Sannan kuma gwamnan ya buƙacin Dangote ya tallafa wa jihar don gina tashar samar da wutar lantarki mai zaman kanta domin farfaɗo da masana'antun jihar don bunƙasa har tattalin arziki da kuma ƙarffa jihar.

    Haka kuma Gwamna Abba Kabir ya shaida wa Dangoten cewa jihar na cikin tsananin buƙatar asibitin kula da masu lalalar cutar sikila domin samar da magunguna kyauta ga masu lalurar.

    A ɓangaren ababen more rayuwa, gwamnan jihar ya buƙaci tallafin Dangote don gina tituna na zamani, da gidaje, da ci gaban al'umma da sauran fannoni.

  5. Tinubu ya sanya hannu kan dokar lantarki da aka yi wa gyara

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar lantarki da aka yi wa gyaran fuska.

    Dokar - wadda majalisun dokokin ƙasar biyu suka amince da ita a shekarar da ta gabata - na buƙatar magance matsalolin muhalli da yankuan da ake samar da lantarkin ke fuskanta.

    Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasan, Ajuri Ngelale, ya fifat, ya ce sabuwar dokar ta yi tanadin cewar za a riƙa ware kashi biyar cikin 100 na abinda kamfanonin samar da lantarkin ke samu a shekara domin gina ababen more rayuwa a yankunan.

    Haka kuma sabuwar dokar ta yi tanadin samar da wani asusu na musamman da al'ummar yankunan da haɗin gwiwar kamfanonin samar da lantarkin za su gudanar, don gina abubuwan maore rayuwa a yankunan.

  6. Jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga a Senegal

    Jami'an tsaro sun harba tiyagas tare da gurnetin bayar da tsoro don tarwatsa masu zanga-zanga da suka yi maci a Dakar babban birnin ƙasar ranar Juma'a

    Zanga-zangar na zuwa ne bayan matakin ɗage zaɓe da shugaban ƙasar Macky Sall ya ɗauka da a baya aka shirya yi cikin wannan wata zuwa ƙarshen shekarar da muke ciki.

    An kuma samu rahotonnin tashin hatsaniya a tashar jirgin ƙasa da ke birnin Dakar.

    Bidiyon da aka ɗauka a tsakiyar birnin ya nuna yadda masu zanga-zangar ke jifan 'yan sanda da duwatsu yayin da suke kora su.

    Masu zanga-zangar sun zargi shugaba Macky Sall da yunƙurin ci gaba da mulki, zargin da ya musanta.

    Martabar da Senegal ke da shi na ƙasar da ta fi kowace ƙasa a Afirka cikakken tsarin dimokraɗiyya ya gamu da cikas cikin makon nan, bayan matakin ɗage zaɓen da shugaban ƙasar ya yi.

    Shugaba Macky Sall ya ce ɗaukar matakin ya zama wajibi ne sakamakon matsalolin hana 'yan takara da dama tsayawa takara, lamarin da ya ce na barazana ga ƙasar.

  7. Matatar Ɗangote za ta fara sayar da man fetur a Najeriya

    Matatar mai ta Dangote za ta fara sayar da man fetur a Najeriya, a cikin makonni masu zuwa.

    Kamfanin dillancin labarai na Rauters ya ce wasu majiyoyi a kamfanin sun tabbatar masa da hakan, a ƙoƙarin da aka jima ana yi, na ganin Najeriya ta dogara da kanta a ɓangaren makamashi.

    Rauters ya ce ana sa ran fara sayar da man fetur ɗin 'kowane lokaci daga yanzu'.

    Hakan dai na nuni da cewar akwai yiwuwar Najeriya za ta rage yawan man fetur, da kuma man disel domin harkokin yau da kullum, daga manyan kamfanonin sayar da mai, da take shigar da shi, wata harka da ta ƙunshi biliyoyin nairori da aka jima ba a iya magance ta ba.

    Haka kuma wata majiya ta shaida wa Rauters cewar kamfanin samar da man fetur a Najeriya NNPC, ya ce zai samar wa matatar ta Ɗangote ɗanyen mai ganga miliyan huɗu a watan Maris, wanda hakan ke nufin, matatar Ɗangoten ta karɓi ɗanyan man fetur ganga miliyan 12 tun daga watan Disambar, bara.

  8. An soke dokokin shari'ar Musulunci 16 a Malaysia

    Kotun tsarin mulki a Malaysia ta soke wasu dokokin shari'ar Musulunci 16 a jihar Kelantan da ke arewa maso gabashin ƙasar.

    Dokokin sun haɗa da hukuncin luwaɗi da cin zarafin mutum ta hanyar lalata da caca da kuma muzuntawa ko lalata wurare masu tsarki ko na ibada.

    Kotun ta ce jihar ba ta da hurumin da za ta yi doka a kan harkokin da suke ƙarƙashin iko ko dacewar majalisar dokokin tarayya.

    Hukuncin zai iya shafar dokokin shari'ar Musulunci da aka amince da su a wasu jihohin da Musulmi ke da rinjaye a ƙasar ta Malaysia, inda bin tsarin Musulunci sau da kafa, da ke ƙaruwa ke zama ƙalubale ga gwamnatin haɗakar ƙasar ta kabilu daban-daban.

    Firaminista Anwar Ibrahim, ya ce ba hannun gwamnatin tarayya a hukuncin da kotun ta yi.

  9. An gudanar da zangar-zanga kan matsin rayuwa da rashin tsaro a Osun

    Mutane da dama sun fito kan tituna a garin Osogbo na jihar Osun domin gudanar da zanga-zanga kan matsin rayuwa da ƴan Najeriya ke fama shi.

    Matasan da suka yi zanga-zangar sun buƙaci gwamnati ta magance halin ƙunci da al'ummar Najeriya suka faɗa ciki a baya-bayan nan.

    Masu zanga-zangar sun fito ne ɗauke da katakai da kwalaye ƙunshe da saƙonni daban-daban.

    Duk da cewa an jibge jami'an ƴansanda da dama kan titunan, hakan bai hana masu zanga-zangar ci gaba da tattakin nasu ba.

    Lokacin da ya zanta da manema labaru, shugaban gamayyar ƙungiyoyin farar hula na jihar, Waheed Lawal ya nuna takaici kan yadda matsalar tsaro ke ƙara ƙamari a jihar da faɗin Najeriya.

    Ya ce "wajibi ne gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace, dole ne su nemo hanyar da al'umma za su riƙa rayuwa cikin kwanciyar hankali."

  10. 'Macky Sall dan kama-karya ne'

    Tsohuwar Firaministar Senegal Aminata Touré ta zargi shugaban kasar Macky Sall da yin abubuwa kamar "ɗan kama-karyan a nahiyar Afirka".

    Ta shaida wa sashen BBC Newsday cewar, "Shekaru 12 da suka gabata tare muka yi gwagwarmayar yakar yunƙurin mulki wa'adi na uku na tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade, amma yau ga shi yana aikata abin da ya kalubalanta a baya, in ji tsohuwar Firaministar Aminata Touré.

    An fara gudanar da wani taron gaggawa a Najeriya, inda shugabanin kasashen yankin na Afirka ta yamma, za su samar da mafita kan rikicin siyasa da Senagal ke fuskanta.

    Taron na ECOWAS, na zuwa mako guda da Macky Sall ya bayar da sanarwa cewar za a dage zaben shugaban kasar, da aka tsara gudanarwa a watan Fabrairu.

    A ranar Litinin, ƴansandan kwantar da tarzoma suka harba barkono mai sa hawaye, don tarwatsa gungun masu zanga-zanga, a gaban Majalisar wakilan Senegal.

    'Yan takarar hamayya a kasar sun ce sauya lokacin gudanar da zaben shugaban kasar, ya ci karo da kundin tsarin mulkin kasar.

  11. Hayakin janareto ya kashe ɗalibai biyu a Lokoja

    Wasu daliban kwalejin fasaha ta Lokoja da ke jihar Kogi sun mutu sakamakon shakar hayakin janareto da suka kunna wanda ya cika dakinsu.

    Kakakin 'yansanda a jihar ta Kogi SP William Ovye Aya ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels faruwar lamarin, inda ya ce salansar janaretan ya kasance yana fuskantar tagar ɗakin da suke kwana.

    Sannan ya ce akwai daliba guda daya da ke kwance a dakin ita ma wadda ba ta rasa ranta ba, inda yanzu take kwance a asibiti.

    SP William Ovye Aya, ya ce daliban da suka mutu sun hada da Bilikisu Tijjani Eleojo, mai shekaru 20, da Ibrahim Haliru mai shekaru 26, sai Mercy Ojochegbe wadda ke kwance a asibiti.

  12. Ba zai yiwu a zartar da dukkan buƙatun NLC a lokaci guda ba - Gwamnatin Tarayya

    Gwamnatin Najeriya ta ce ba abu ne mai yiwuwa ba a zartar da wasu daga cikin bukatun kungiyar kwadago da aka cimma a watan Oktoban 2023, da gaggawa ba.

    Karamar ministar kwadagon kasar, Nkeiruka Onyejeocha ce ta shaida wa 'yan jaridu a yau Juma'a yayin amsa tambayoyi ga 'yan jaridun.

    Gwamnatin ta tarayya ta kara da cewa daya daga cikin yarjeniyoyin wadda take neman a samar da cibiyoyin sauya motoci zuwa masu amfani da iskar gas zai dauki lokaci kafin cibiyoyin su wadata ko'ina kuma kwamitin da ke kula da samar da cibiyoyin yana aiki tukuru.

    A watan Oktoban bara ne dai bangarorin biyu suka cimma jerin yarjejeniyoyi da suka kunshi ragewa 'yan kasar radadin talauci sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi.

    Sauran bukatun sun hada da samar da mafita ga darajar naira da tashin farashi da kuma matsalar tsaro da dai sauransu.

    Kungiyar kwadago dai ta bai wa gwamnati wa'adin mako biyu da ta zartar da yarjeniyoyin ko ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

    • Abu bakwai da gwamnatin Najeriya ta cimma da 'yan ƙwadago
    • Kalaman 'yan Najeriya bayan sake ƙara kuɗin man fetur
  13. Ƴan Habasha kusan miliyan 10 na fuskantar matsananciyar yunwa – Oxfam

    Wata kungiyar bayar da agaji ta Birtaniya ta Oxfam ta ce daya daga cikin mutum uku da ke arewacin Habasha na fuskantar matsananciyar yunwa.

    Wanda hakan ke nuni da cewar akwai mutum milliyan 10 a yankunan Tigaray da Amhara da ke fama da yunwa.

    Rikicin da ake fama da shi a yankin da fari sun taka muhimmiyar rawa wajen rage yawan girbin kayan amfanin gona, wanda hakan ya tilastawa miliyoyin jama'a komawa abin da kungiyar ta bayana da rayuwa a cikin mawuyacin hali ta hanyoyi da "ba a ta ba tunani ba".

    Wani rohoton hukumar gwamnatin tarrayyar ya ce mutum 400 ne suka mutu a yankunan biyu saboda rashin abinci.

    Kungiyar ta Oxfam ta yi gargadin cewar akwai bukatar a kara yawan tallafin da ake bayarwa, saboda barazanar da Habashan ke fuskanta da koma baya a bangaren ayyaukan jinkai.

    Gibin da ake samun a bangaren kudi da rikicin da ake fama da shi a Amhara, na haifar da cikas ga ayyukan jinkai.

    A shekarar da ta gabata, Majalisar Dinkin Duniya, iya kashi daya bisa ukun kawai ta iya samu na abun da ta ke bukata na dalla biliyan 4 (Fan billiyan 3.2), na ayyuakan jinkai a Habasha.

    Hukumomi a Tigaray sun ce akwai barazanar za a iya fuskantar fari, ammam gwamnatin tarayyar kasar ta yi watsi da hasashen.

  14. Hotunan ɓarnar harin Isra'ila kan birnin Rafah

    Isra'ila ta kaddamar da sabbin hare-hare kan birnin Rafah da ke kan iyaka, cike da jama'a da suka rasa matsugunansu a kudancin Zirin Gaza a yau Juma'a, wanda ya yi sanadiyar hasarar dukiya, da mace-mace, da kuma jikkata wasu mutane.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta yi gargadin cewa wani bala'i ya kunno kai.

    Ga wasu hotuna da kai nuna ɓarnar da harin ya haddasa.

  15. Jami'an sirrin Isra'ila na kokarin razana ni - Ministar Afirka ta Kudu

    Rahotanni na cewa Ministar harkokin wajen kasar Afirka ta kudu, Naledi Pandor ta zargi jami'an sirrin kasar Isra'ila da kokarin razana ni saboda karar da muka shigar a kotun duniya.

    Misis Pandor ta shaida wa kafar jaridar intanet ta Mail & Guardian cewa ta damu da tsaronta da na iyalanta sakamakon sanya mata ido da aka yi a soshiyal midiya.

    Ministar ta ce ta yi magana da ministan 'yan sanda Bheki Cele dangane da inganta min harkar tsaro bayan samun wasu sakonnin razanawa.

    "Haka halayyar jami'an tsaron Isra'ila take, suna kokarin razana ka to ina kira da cewa ka da mu razana".

    Har yanzu dai Isra'ila ba ta uffan ba kan wannan zargi.

  16. 'Yar Nawaz Sharif ta lashe kujerar Majalisar Dokoki a Pakistan

    An bayyana ɗiyar tsohon firaministan Pakistan, Nawaz Sharif kuma shugabar kungiyar musulmi ta Pakistan, Maryam Nawaz ta jam'iyyar Pakistan Muslim League a matsayin wadda ta lashe zaɓen kujerar Majalisar Dokokin Pakistan a Lahore.

    Maryam Nawaz dai ta samu kuri'u 83,855, yayin da abokin takararta na jam'iyyar PTI Shahzad Farooq ya samu kuri'u 68,376.

  17. Malawi ta ɗage takunkumin hana biza ga kasashe 79

    Malawi ta dage takunkumin hana bizar shiga ƙasar ga matafiya daga kasashe 79 da nufin karfafa yawon bude ido da kasuwanci.

    Wannan matakin wanda ministan tsaron cikin gida na ƙasar, Ken Zikhałe ya sanar, ya hada da kasashe kamar Birtaniya da China da Rasha da Jamus da Australia da Kanada da Belgium da Ghana da Gambia da Saliyo da Faransa da dai sauransu.

    Bugu da ƙari, ƴan ƙasa daga Ƙungiyar Cigaban Kudancin Afirka (Sadc) da Kasuwar Gabas da Kudancin Afirka (Comesa), an keɓe su daga buƙatun biza.

    Sauye-sanjen sun kuma shafi jami'an diflomasiyya, jami'an gwamnati, da kuma kasashen da ke da yarjejeniyar musayar ra'ayi.

    Biza ta masu shiga da yawa a Malawi yanzu suna aiki har zuwa watanni 12.

    Ministar yawon bude ido, Vera Kamtukule na kallon wannan matakin a matsayin wata hanya ta nuna karfin Malawi ga duniya.

    Ofishin jakadancin Burtaniya yana ƙarfafa 'yan ƙasarsa wajen yin amfani da wannan damar da Malawi ta bayar wajen yawon buɗe ido a ƙasar.

    Wannan matakin dai ya yi daidai da Kenya da Rwanda, wadanda su ma suka bude kofofinsu ga matafiya na Afirka ba tare da bukatar biza ba.

  18. Asibitin Kenya ya yi nasarar gudanar da aikin dashen koda na farko a ƙasar

    Babban asibitin Kenyatta na Kenya ya yi nasarar gudanar da aikin dashen ƙoda na Laparoscopic na farko, wanda ke nuna wani muhimmin cigaba a matsayin cibiyar jama'a ta farko a kasar da ta gudanar da wannan aiki.

    An yi dashen ne a kan Dickson Njoroge mai shekaru 36, wanda dan uwansa ya ba shi kyautar koda.

    An yi amfani da ƙayan aiki na musamman na asibiti da wasu da suka haɗa da kyamarorin na kwamfuta wajen aikin dashen ƙodar.

    Likitocin da suka jagoranci aikin sun haɗa da Dokta Charles Waihenya da Dokta Paul Njogu kuma sun ce dashen kodar na laparoscopic yana ba da fa'idoji da yawa gami da jin ƙarancin zafi da ƙarancin zubar jini, da saurin farfadowa da ƙarancin farashi da kuma samun sakamako mai kyau tare da kawar da bukatar 'yan Kenya su nemi magani a ƙasashen waje.

    Dashen koda na Laparoscopic ya zama ruwan dare a sassa da dama na duniya amma har yanzu bai samu karbuwa sosai a kasashen Afirka ba saboda gazawar kayan aikin kiwon lafiya da kwarewar aikin tiyata.

  19. Amurka ta yi kira da a gudanar da bincike kan kisan fararen hula a Habasha

    Amurka ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan ‘kashe-kashen da aka yi wa fararen hula a wani gari a yankin Amhara da ke arewa maso yammacin Habasha mai fama da rikici.

    A baya dai shedun gani da ido sun shaida wa BBC cewa aƙalla fararen hula 50 ne jami’an tsaro suka kashe a cikin kakin sojoji a yayin bincike na gida-gida.

    Lamarin dai ya faru ne bayan da mayakan sa-kai na yankin suka yi wa sojojin da ke kusa da garin kwanton bauna.

    Wani rahoto da wata kungiyar kare hakkin yankin ta fitar ya bayyana cewa adadin wadanda suka mutu zai iya kai 80.

    Yunkurin da BBC ta yi na samun martani daga gwamnati game da zargin bai yi nasara ba.

    Sai dai kungiyar kare hakkin bil adama da gwamnatin ƙasar ta naɗa ta shaida wa BBC cewa ta samu rahotannin kashe-kashen kuma tana gudanar da bincike.

    • Abin da ya sa yaƙin Ethiopia ya sake zama sabo a Tigray da Amhara
    • 'Kuraye na cin gawarwakin waɗanda suka mutu a yaƙi'
  20. Jihohin arewacin Najeriya bakwai da za su fuskanci yunwa - Bankin Duniya