Mawakiyar Afirka ta Kudu Tyla ta lashe kyautar Grammy ta wakar da ta fi shahara a duniya da wakarta mai taken 'Water'.
Tyla ta doke fitattun mawakan Najeriya irin su Burna Boy da Davido da Ayra Starr da Asake.
Nasarar Tyla ta faranta ran 'yan Afirka ta Kudu duk da dai ta janyo takaddama a tsakanin 'yan Najeriya.
Bayan sanar da Tyla a matsayin wadda ta lashe wannan kyauta, wasu 'yan Najeriya sun garzaya shafukan sada zumunta domin bayyana mamakinsu kan yadda matashiyar mawakiyar Tyla wadda 'sabon -shiga' ce a fagen rera wakoki ta yi zarra kan zaratan mawakan Najeriya da aka dade ana jin wakokinsu.
Magoya bayan mawakiya Tyla sun ce ta cancanci nasarar da ta samu inda suka ba da misali da yadda wakar tata ta 'Water' ta samu karbuwa a duniya.
A bara ne, wakar 'Water' ta karade ko ina a fadin duniya inda ta kafa tarihi a shafukan sauraron wakoki tare da yin fice a jerin wakoki 100 da suka shahara.
"Wannan abu ne na ba-zato! Ban taba tunanin zan lashe Grammy a shekara 22 ba!" in ji Tyla a lokacin da ta karbi kyautar a Amurka ranar Lahadi da daddare inda take sanye da kayatacciyar doguwar riga ta kamfanin Versace.
Wasu 'yan Afirka a shafukan sada zumunta sun yaba da gasar ta Grammy a matsayin wani muhimmin lokaci na tarihi ga nahiyar, inda Tyla ta yi nasara sai Burna Boy da ya gwangwaje da wakarsa sai kuma mai wasan barkwancin nan dan Afirka ta Kudu Trevor Noah da ya gabatar da taron wakokin mafi girma karo hudu a jere.
-
Yadda TikTok ya sauya kasuwancin waƙoƙi a ƙasar Hausa
-
Afrochella: Masu zuwa babban casun Ghana sun kaɗu jin cewa an daina shi