Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi and A'isha Babangida

  1. Dakarun RSF sun yi iƙirarin harbo jirgi mara matuki kirar Iran

    Dakarun RSF sun ce sun harbo wani jirgi maras matuki kirar Iran da ake zargi na sojin Sudan ne yayin da yaki ke ci gaba da kazanta tsakanun bangarorin biyu a Khartoum, babban birnin kasar da wasu yankuna.

    RSF a sakon da ta yi a shafinta na X ta ce "ta yi gagarumar nasara da safiyar nan, ta harbo wani jirgi mara mautki na sojojin Sudan".

    "Jirgin da aka bayyana da Mohajer-6 kirar Iran, ya zama jirgi na uku da a baya-bayan nan aka dakile bisa kokarin jajirtattun sojojinmu. Duk da wannan nasara, za mu ci gaba da fuskantar kalubale," kamar yadda kungiyar ta ce.

    Rundunar sojin ta Sudan ba ta kai ga cewa komai ba game da al'amarin.

    Kafafen yada labarai na kasar sun ba da rahoton samun karuwar hare-hare na jirgi maras matuki da sojoji ke kai wa kan wuraren dakarun RSF a Khartoum da birnin Omdurman da Bahri.

    Sojoji sun kara yawan hare-haren da suke kai wa kan RSF a makonnin baya-bayan nan yayin da yakin da ake a kasar ya shiga wata na tara.

    • 'An mayar da mata tamkar ganimar yaƙi a Sudan'
    • An kashe gwamnan jihar Darfur ta Yamma a Sudan
  2. Kalli yadda wani farfesa ya rungumi sana'ar walda a Najeriya

    Farfesa Kabir Ahmed da ake yi wa laƙabi da Abu Bilal ya bambanta da sauran farfesoshi a Najeriya, waɗanda ke dogara kawai da sana'ar koyarwa a jami'o'i, shi a nasa ɓangare yana gudanar da sana'ar walda a matsayin sana'a ta biyu a garin Zariya da ke arewacin ƙasar.

  3. Manoman Faransa na ci gaba da zanga-zanga kan karancin kudaden shiga

    Manoma a Faransa na shirin datse tittuna a birnin Paris a yau Litinin, yayin da suke ci-gaba da zanga-zanga kan karancin kudaden shiga da matsalar masu hana ruwa guda a gwamnati da kuma gogayyar da suke fuskanta daga kayayyakin da ake kai wa kasar daga ketare.

    Manoman sun yi gargadin za su yi amfani da wani tsari na sojoji ta hanyar shigo da daruruwan tiractoci a yunkurin hana zirga-zirgar ababen-hawa.

    Sun kuma ce burinsu shi ne hana kai kayan abinci manyan kantuna.

    Kafin wannan lokaci, 'yan sanda ba su shiga zancen ba, ko kokarin hana a datse tittuna kasar.

    Ministan cikin gida, Gerela Darmanin, ya ce tuni tattalin arzikin Faransa ya soma amsawa saboda wannan takaddama.

    A Jamus da Belgium da Netherlands ma manoma sun shiga irin wannan zanga-zangar.

    • Hotunan yadda ake gudanar da zanga-zanga a Faransa kan shekarun ritayar ma'aikata
    • Ana zanga-zanga a Isra'ila gabanin yin sauye-sauye kan ɓangaren shari'ar ƙasar
  4. Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan masu yi wa Isra'ila leken asiri

    Iran ta kashe wasu mutane hudu da ta samu da laifin yi wa Isra'ila leken asiri.

    Kafar yada Labaran kasar ta ce kotu ta samu mutanen hudu maza da kokarin kitsa yadda za a kai harin bam kan wani sansaninta na makamai da ayyukan soji na Isfahan.

    Iran ta ce tun a shekara ta 2022 aka tsara kai harin, a madadin hukumar tattara bayanan sirri ta Isra'ila, Mossad.

    An zargi masu laifin da shiga Iran ta yankin Kurdawa a Iraki.

    Wata Kungiyar kare hakkin bil adawa a Norway, na ce mahukunta Iran su aiwatar da irin wannan hukunci na kisa kan mutum 60 a wannan shekarar.

    • Jerin mutanen da ke jira a aiwatar musu da hukuncin kisa a Iran
    • Ana tuhumar mutum takwas da laifin tayar da gobarar da ta kashe 'yan ci-rani a Mexico
  5. Yadda fashewa ta halaka yara 'yan makaranta a Borno

    Bayanai na ci gaba da fitowa kan wata fashewa da ta janyo mutuwar wasu yara shida a karamar hukumar Gubio, da ke jihar Borno.

    ‘Yan sanda da jami’an yankin sun ce fashewar ta faru ne a wani gini da ke makarantar Islamiyya a ranar Asabar.

    ASP Nahun Daso, kakakin rundunar yan sanda a jihar ta Borno ya shaida wa BBC cewa an tara wasu kayayyakin gwan-gwan da aka yi rashin sa'a wasu matasa da suka je wajen suka taru, a nan ne kuma aka samu abubuwan fashewa da suka tashi.

    Rahotanni sun ce yaran kan tara ƙarafa da kuma sayar wa al’ummar yankin.

    Duk da haramcin da aka yi kan sana'ar gwan-gwan, har yanzu ana cinikin lalatattun karafa a yankin da ke fama da tashe-tashen hankula na masu tayar da ƙayar baya.

    ASP Nahun ya ce suna wayar da kan mutane game da "na'urorin fashewa" tare da hana saye da sayar da kayan gwan-gwan.

    Ya kuma kara da cewa rundunarsu za ta yi bincike a kan lamarin.

    • Boko Haran sun kashe mutune a Borno, ƴan bindiga na yi wa manoma barazana a Birnin Gwari
    • Sojoji sun kashe manyan kwamandojin Boko Haram a Najeriya da wasu 'yan bindiga a Nijar.
  6. Shugabannin ƙasashen Afirka sun hallara a birnin Rome domin halartar taron Italiya

    Shugabannin ƙasashen Afirka da dama sun hallara a birnin Rome na ƙasar Italiya domin halartar taron kolin Italiya da Afirka da ke da nufin inganta dangantaka tsakanin Afirka da kasashen Turai.

    A yayin taron na kwanaki biyu, ana sa ran Italiya za ta ɓullo da wani sabon salo na yin haɗin gwiwa da ƙasashen Afirka in ji firaministan Italiya Giorgia Meloni.

    Ɓangarorin da aka yi niyya don haɗin gwiwar sun haɗa da ɓangaren makamashi da haɓaka tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa da na al'adu da samar da abinci da ilimi da koyar da sana'o'i.

    Taron wanda aka fara a ranar Lahadin da ta gabata, yana da nufin bunƙasa zuba jari a ƙasashen Afirka a matsayin dabarun daƙile kwararar bakin haure daga nahiyar.

    Wasu ƙasashe da dama sun shirya irin wannan taro domin ƙarfafa alaƙa da ƙasashen Afirka da suka haɗa da Jamus da Rasha da kuma China.

    • Yadda faɗa-a-jin Ƙasashen Yamma ke daɗa raguwa a Afirka
    • John Kerry: Taron ƙoli na Birtaniya kan sauyin yanayi shi ne damarmu ta ƙarshe
  7. Ana neman wata sarauniyar kyau a Najeriya kan zargin safarar kwaya

    Hukumomi a Najeriya sun bayyana wata sarauniyar kyau a shekarar 2015 a matsayin wadda ake nema ruwa a jallo saboda zarginta da hannu a safarar miyagun kwayoyi.

    Bayanai na cewa Aderinoye Queen Christmas da aka fi sani da Sarauniya Oluwadamilola Aderinoye ta tsere wa jami'ai daga hukumar yaƙi da sha da fataucin haramtattun ƙwayoyi, NDLEA a lokacin da suka kai samame gidanta da ke Legas a makon da ya gabata.

    Cikin wata sanarwa, hukumar ta ce an kai samamen ne bayan wasu sahihan bayanai da suka nuna cewa tsohuwar sarauniyar kyan tana da hannu a ta'amali da haramtattun kwayoyi.

    "Abubuwan da aka gano a gidanta bayan binciken da jami'ai suka yi akwai gram 606 na kwayar Canadian Loud sai tabar wiwi da abin gwada nauyi da manya-manyan ma'ajin magunguna na roba," kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Wadda ake zargin ta taba lashe gasar kyau ta Miss Commonwealth Nigeria Culture a shekarar 2015/2016 kuma ita ce ta kafa gidauniyar Queen Christmas.

    Kawo yanzu dai ba ta ce komai ba game da zargin da ake mata.

    Shi ma wani da ake zargi, da ya dawo daga Brazil a makon da ya gabata, an cafke shi a filin jirgin sama na Murtala Muhammed saboda hadiye manyan kullin tabar wiwi 60, kamar yadda hukumar ta NDLEA ta bayyana.

    • "Kasashen da ke da dokoki masu tsauri kan safarar kwaya"
    • An kashe 'yar Najeriya da aka kama da kwaya a Saudiyya
  8. An kashe sojin Amurka a hari kan sansanin sojinta da ke Gabas ta Tsakiya

    An kashe sojojin Amurka uku, gommai kuma sun jikkata sakamakon harin jirgi maras matuki da aka kai kan sansanin sojinta da ke kusa da iyakar Jordan da Syria.

    Shugaban Amurka Joe Biden ya zargi mayakan da ke samun goyon bayan Iran da kai harin. Ya kara da cewa "za mu mayar da martani."

    Iran ta musanta hannu a harin.

    Wannan ne karon farko da wani hari ya kashe sojojin Amurka a yankin tun bayan da Kungiyar Hams ta kai hari kan Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.

    Jordan ta ce harin ya faru ne a Syria ba a cikin kasarta ba.

    Akwai wasu hare-hare da aka kai kan sansanonin sojin Amurka a yankin sai dai kafin ranar Lahadi, ba a samu asarar rayuka ba, kamar yadda rundunar sojin Amurka ta bayyana.

    Kawo yanzu, babu masaniya kan wanda ke da hannu a kai harin na baya-bayan nan.

    Shugaba Biden ya ce Amurka za ta hukunta masu hannu a lamarin a lokacin da ya fi dacewa.

    Iran ta musanta zarge-zargen da Amurka da Burtaniya suke cewa ta tallafa wa mayakan da ake zargi da kai harin.

    "Wannan ikirarin ana yin su ne da wata manufa ta siyasa domin karkatar da hankula game da halin da ake ciki a yankin," kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje Nasser Kanaani ya ce wanda kamfanin dillancin labaran IRNA da ke Iran ya ruwaito.

    Fadar White House ta ce Sakataren harkokin tsaron Amurka, Lyod Austin tare da sauran jami'an gwamnati ya yi wa Mr Blinken karin bayani game da harin.

    • An kashe sojojin Amurka a Afghanistan
    • Yadda ake amfani da sojojin haya na Amurka wurin kashe-kashe a Yemen
  9. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu, barkan mu da warhaka. Da fatan mun wayi gari a wannan safiya ta Litinin Lafiya.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Akwai shafukanmu na sada zumunta da za ku iya zuwa domin karanta karin labarai da kuma kallon bidiyo.