Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, Habiba Adamu and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Kotu ta soke kasafin kuɗin jihar Ribas na naira biliyan 800

    Babbar kotu a Abuja ta soke kasafin kuɗin jihar Ribas da ya kai naira biliyan 800 wanda majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin ɓangaren Edison Ehie ta amince da shi kuma ya samu sa hannun gwamna Siminalayi Fubara.

    Kotun ta tabbatar da ƙarar da majalisar da shugabanta Martin Amaewhule suka shigar don kalubalantar Fubara da suka nemi a dakatar da gwamnan daga yi wa ayyukan majalisar a karkashin jagorancinsa makarkashiya.

    Ken Njemanze wanda lauyan Amaewhule ne ya zargi gwamnan da yin katsalandan ga ayyukan yan majalisa saɓanin yadda doka ta bambance ayyukansu.

    Wanda ya shigar da karar ya nemi kotu ta hana wanda ake kara daga hana majalisar kudaden da take bukata na tafiyar da ayyukanta har da biyan albashi da alawus-alawus.

    Da farko alkali James Omotosho ya ce Ehie ta hannun lauyansa Oluwole Aladedoye ya ce ya yi murabus daga majalisar dokokin Ribas.

    Omotosho ya ce Ehie ba shi da ikon shigar da kara saboda ba shi ne shugaban majalisar dokokin Ribas ba sannan kuma ba dan majalisa ba ne.

    A ranar 13 ga watan Disamba, lokacin da rikicin siyasa ya yi zafi a jihar mai arzikin man fetur har ta kai ga rushe ginin majalisar, Fubara ya gabatar da kasafin 2024 na N800bn gaban yan majalisa biyar karkashin Edison Ehie.

    Ya gabatar da kasafin kudin a fadar gwamnati da ke Fatakwal sakamakon rushe ginin majalisar da gwamnatin jihar ta yi sannan bayan kotu ta hana abokin hamayyar Ehie, Martins Amaewhule daga amfani da harabar majalisar.

    Ehie da sauran yan majalisa masu goyon bayan Fubara sun amince da kasafin kudin inda kuma gwamnan ya sanya hannu a kai. Ya ce an yi haka ne domin habaka tattalin arziki da kuma magance matsalolin da suka shafi al'umma.

    Daga baya ne kuma Ehie ya ajiye mukaminsa daga majalisar inda aka mayar da Amaewhule a matsayin shugaban majalisar bayan duka bangarorin biyu sun gana da shugaba Bola Tinubu a Abuja.

  2. Firaiministan Indiya ya kaddamar da wurin bautan Hindu don maye masallacin da aka rushe

    Firaministan Indiya, Narendra Modi ya kaddamar da wani makeken wurin bauta na mabiya addinin Hindu a birnin Ayodhya.

    Ginin zai maye dadadden ginin masallaci da gungun mabiya Hindu suka rushe a 1992. Rushe masallacin dai ya janyo gagarumar zanga-zanga a fadin kasar inda kusan mutum 2,000 suka mutu.

    Dubban mutane ne suka halarci bikin kaddamar da ginin a Ayodhya har da yan fim da masu kwallon cricket.

    Sai dai mabiya addinin Hindu, kuma akasarin yan hamayya sun kauracewa wurin inda suka ce Mr Modi yana amfani da hakan domin manufa ta siyasa.

    Cikin yan watanni masu zuwa ne za a yi zabe a Indiya kuma abokan hamayyar Mr Modi ya ce jam'iyyar BJP mai mulki za ta yi amfani da wannan wurin bauta wurin samun kuri'u inda kashi 80 cikin 100 na al'ummar yankin mabiya addinin Hindu ne.

    Masu suka sun zargi gwamnatin da wuce gona da iri.

    An yi amfani da dala miliyan 217 wajen gina wurin bautar - gidauniyar wurin bautar ta ce kamfanoni masu zaman kansu ne suka ba da gudummawa.

  3. Gwamnatin Legas za ta sa takunkumi kan masu magungunan gargajiya

    Gwamnatin jihar Legas da ke kudancin Najeriya ta ce za ta sanya takunkumi kan masu magungunan gargajiyan da ke harkokinsu a jihar.

    Hukumomi a jihar sun sanya wa'adin ranar 6 ga watan Fabrairu mai kamawa, cewa idan har masu maganin suka ƙi yin rijistar wuraren sana’oinsu da hukumar kula da magungunan gargajiya ta jihar, za su fuskanci takunkumi.

    Hakan dai wani mataki ne na kawar da masu magungunan gargajiya na bogi a jihar, a cewar jami'ai.

    Magatakardar hukumar kula da magungunan gargajiya ta jihar, Babatunde Aderemi, ya ce yin rajistar zai taimaka wajen tantance masu gaunguna na gaskiya da kuma na jabu.

    Haka kuma ya kƙara da cewa duk wasu masu magungunan gargajiyan da dangoginsu da suka kasa sabunta lasisinsu zuwa wannan lokaci, za a cire sunayensu a rajistar.

    A cewarsa za a yi hakan ne kamar yadda dokar harkokin lafiya ta jihar ta tanada.

    Wasu masu magungunan gargajiya da ke jihar sun yi maraba da matakin, inda suka bayyana buƙatar a yi tantancewar ba tare da wata manufa ba.

    Dubban ƴan Najeriya ne ke amfani da magungunan gargajiya saboda dalilan da suka hada da talauci da ƙarancin ƙananan asibitoci a kusa, lamarin da ke jefa rayukansu cikin haɗari.

  4. Boakai zai sha rantsuwar kama aiki a Liberia

    Joseph Boakai mai shekara 79, wanda masu suka ke yi wa kirari da "Joe mai gyangyaɗi" zai sha rantsuwar kama aiki, a matsayin shugaban Liberia mafi tsufa bayan lashe zaɓen da aka yi a watan Nuwambar, 2023.

    Shan rantsuwar wata manuniya ce ga babban sauyin da aka samu na shekaru, inda zai karɓi mulki a hannun shugaba mafi ƙarancin shekaru da ƙasar ta taɓa zaɓe, George Weah.

    Tsohon ɗan wasan kwallon ƙafa na ƙasar waje ya samu nasarar zama shugaban ƙasar yana da shekara 51 bayan ya doke Mr Boakai a zaɓen da aka yi shekaru shida da suka wuce, amma a yanzu kuma ya sha kaye a hannunsa da ƙuri'un da yawansu suka ɗara 20,000.

    Wani editan jaridar ƙasar, FrontPage Africa, Rodney Sieh, ya ce nasarar da Mista Boakai ya samu bai zo da mamaki ba.

    "Mutane sun gaji da gwamnatin Weah - cin hanci da rashawa da facaka da arziki da ake yi, motocin alfarma, gidajen abinci na gani-na-faɗa.

    Wani jami'i da ke aiki a fadar gwamnati ya yi wa motar alfarmar da ya saya wa matarsa wanka da wata giya mai tsadar gaske kuma ya sanya hoton a shafukan sada zumunta.

    "Masu kada ƙuri'a na ɗora ayar tambaya kan irin rayuwar ƙasaita da jami'ai ke yi, yayin da talakawa ke faɗi-tashin neman abun sanyawa a bakin salati, ga kuma biyan kuɗin makarantar ƴaƴansu. " Editan ya shaida wa BBC.

    Mr Boakai ya samu nasarar ce duk da cewa abokan hamayyarsa sun sha yi masa dariya da wasu ƴan ƙasar a dandalin sada zumunta, bayan an sha ganinsa yana gyangyaɗi a yayin taruka - abun da wani mai taimaka masa ya musanta, yana mai cewa ƙanana idanusa da yadda saman idonsa yake ne yasa mutane suke ganin kamar barci ya ke yi.

    Lamarin da ya sa, Mista Boakai sanya tabarau baƙi a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

    Sai dai damuwa na ƙaruwa kan ƙoshin lafiyarsa, musamman ganin zai kammala mulki ne yana da shekara 85 a duniya.

  5. Kamaru ta zama ta farko a duniya da ta sanya rigakafin maleriya cikin na yau da kullum, Paul Njie daga Yaoundé

    A yau ne hukumomin kasar za su fara yi wa yara rigakafin zazzabin cizon sauro, cutar da a cewar Hukumar lafiya ta duniya ke kisan yara kusan dubu dari shida duk shekara a duniya.

    Kamaru ta zama kasa ta farko a nahiyar Afrika da ta karbi rigakafin a watan Nuwamban shekarar da ta gabata.

    Rigakafin Maleriyar da WHO ya amince da shi, kamfanin hada magunguna na GSK ne ya samar da shi kuma za a diga wa yara kanana a yankunan Kamaru 42 da cutar ta maleriya ta fi kamari.

    Jami'an kiwon lafiya sun bayyana matakin a matsayin gagarumin ci gaba a shekarun da aka shafe ana fafutukar kawo karshen cutar maleriya a Afirka.

    Karin kasashe 20 gaba a wannan shekarar za su fara amfani da wannan rigakafin, a cewar shirin kawance na Gavi.

    Rigakafin cutar ya kunshi mataki hudu kuma yana da karfin magance maleriya da kashi 30 cikin 100 inda kuma karfin aikinsa zai ragu bayan wasu watanni.

    Kamfanin GSK ya ce a wannan shekarar zai iya samar da kusan allurai miliyan 15.

    • Ghana ta zama ta farko a duniya da ta amince da sabon riga-kafin maleriya
    • Rigakafin Malaria: Abubuwan da suka kamata ku sani kan riga-kafin cutar maleriya
    • Yadda riga-kafin maleriya zai rage kisan da cutar ke yi wa yara
  6. Mutun takwas sun mutu, 47 sun bace bayan zaftarewar kasa a China

    Rahotanni daga kafafen yada labarai a China sun nuna cewa akalla mutum takwas ne suka mutu, wasu 47 suka yi batan dabo bayan wata zaftarewar kasa da ta faru a kudu maso yammacin kasar.

    An kuma kwashe daruruwan mutane daga yankin da ke Lardin Yunnan.

    Zaftarewar kasar ta faru ne a birnin Zhaotong kafin ketowar alfijir. Gomman mazauna yankin ne suka bata kuma ana ta aikin agaji domin kubutar da mutane.

    Fiye da mutum 500 aka yi nasarar sauyawa wuri. Babu tabbaci kan abin da ya haddasa zaftarewar kasar amma ibtila'in na yawan faruwa a yankin na Yunnan mai yawan tsaunuka.

    Ana kuma fama da matsanancin sanyi gami da dusar kankara da ke zuba.

    • Me ya sa China ke rufewa tare da ruguza masallatai
    • Burin China a yaƙin Isra'ila da Hamas
    • Yadda matan da suka haihu ba tare da miji ba ke more rayuwa a China
  7. Amurka: Ron DeSantis ya fice daga takara ya mara wa Trump baya

    Gwamnan jihar Florida, Ron DeSantis ya fice daga neman tsaya wa jam'iyyar Republican takarar shugabancin Amurka.

    A wani sakon bidiyo da ya sanya a shafinsa na X, DeSantis ya ce a yanzu yana goyon bayan tsohon shugaban ƙasar Donald Trump.

    Mista DeSantis ya ce ba shi da wata tabbatacciyar hanya samun nasarar tsaya wa jam’iyyar tasa takara.

    Ana yi wa Ron DeSantis kallon babban abokin hamayya da ya zama wani kalubale ga tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, a wajen tsaya wa jam’iyyarsu ta Republicans takara a zaben 2024.

    Ana yi masa zaton ne ganin irin gagarumar nasarar da DeSantis ya samu a zaben rabin wa’adi na 2022.

    Mista Trump ya yi maraba da mara masa bayan da gwamnan na Florida kuma tsohon abokin hamayyar tasa ya yi.

    Yanzu takarar ta rage tsakanin Trump da tsohuwar jakadiyar Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya, Nikki Haley.

    Kuma tsohon shugaban ƙasar ya ce a yanzu zai mayar da hankalinsa kan fafatawarsa da Ms Haley.

    Haka kuma Mista Trump ya doke shi da tazara sosai a zaɓen fidda gwanin da aka yi a jihar Iowa, a makon da ya gabata.

    A ranar Talata Trump zai kara da Ms Haley a New Hampshire, a ci gaba da zaben fidda gwani na jam’iyyar Republican da ake yi a jihohin ƙasar.

    • Me ya sa Trump ya fi sauran ƴan takarar Republicans farin jini?
    • Kotun Ƙolin Amurka za ta yanke hukunci kan takarar Donald Trump
    • Kotu ta haramta wa Trump tsayawa takara
  8. Marhabun!

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na Kai Tsaye, barkan mu da safiya. Da fatan muna lafiya.

    A yau Litinin, kamar kullum, za mu kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Sai ku kasance tare da mu domin karanta wainar da ake toyawa a duniya. Akwai sauran shafukanmu na sada zumunta - Fesbuk da X da Intagram inda za ku iya zuwa domin karanta karin labarai da kallon bidiyo.