Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Nabeela Mukhtar Uba and Abdullahi Bello Diginza

  1. An katse intanet a Comoros bayan zanga-zangar da ta barke

    Hukumomin ƙasar Comoros sun katse hanyoyin sadarwa na intanet sakamakon zanga-zangar adawa da sake zaben shugaba Azali Assoumani.

    An bayar da rahoton mutuwar mutum daya tare da jikkata wasu shida yayin da ‘yan sanda ke ci gaba da fafatawa da fusatattun magoya bayan ‘yan adawa a Moroni, babban birnin kasar.

    An killace tituna da dama a babban birnin kasar tare da kama wasu masu zanga-zangar da ba a tantance adadinsu ba.

    An kafa dokar hana fitar dare domin daƙile tashe-tashen hankula da ke yaɗuwa.

    A ranar Talata ne hukumar zaɓen kasar ta sanar da cewa Assoumani ya samu kashi 63 cikin 100 na kuri'un da aka kada a ranar Lahadi domin tabbatar da wa'adinsa na hudu a matsayin shugaban kasar.

    Sanarwar sakamakon zaɓen ta haifar da zanga-zanga a ranar Laraba bayan da jam'iyyun adawa suka ce an tafka maguɗi tare da yin kira da a soke zaɓen.

    An lalata gine-gine a babban birnin ƙasar ta hanyar kone-kone, ciki har da gidan wani minista.

    Ayyukan Intanet sun lalace sosai kuma ba a iya shiga wasu rukunin intanet, kamar yadda shafin sa ido na intanet na duniya Netblocks ya tabbatar.

    • Me ya sa ake yawan samun matsalar katsewar intanet?
    • An katse intanet a wani yanki na ƙasar Kamaru
  2. Kotun koli ta tabbatar da nasarar gwamnonin Kaduna da Kebbi

    Kotun koli ta yi fatali da karar da dan takarar jam'iyyar PDP a gwamnan Kaduna, Isah Ashiru wadda ke kalubalantar nasarar gwamna Uba Sani.

    Kotun ta kuma tabbatar da hukuncin da kananan kotuna suka yanke da ya tabbatar da nasarar Uba a zaben watan Maris din 2023.

    A ranar 24 ga watan Nuwamba ne kotun daukaka kara a Abuja ta tabbatar da nasarar gwamna Uba Sani na jihar Kaduna.

    Sai dai kotun sauraron kararrakin zabe a nata bangaren ta samu rarrabuwar kai game da cancantar karar.

    Kazalika a zaman nata na yau, Kotun koli ta kori karar da dan takarar jam'iyyar PDP Aminu Bande ya daukaka domin kalubalantar nasarar gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi.

    Kwamitin alkalan ya ce karar ba ta cancanta ba.

    • Uba Sani ya lashe zaɓen jihar Kaduna
    • Abin da kotun zaɓen Kaduna ta ce kan zaɓen gwamna
  3. Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe

    Kotun koli ta tabbatar da nasarar Inuwa Yahaya na Jam'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Gombe.

    A ranar Juma’a ne kotun kolin ta yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Jibrin Barde ya shigar na kalubalantar zaben gwamna Yahaya.

    A hukuncin bai-daya da kwamitin alkalai ya yanke, kotun kolin ta ce karar ba ta da inganci.

    • Inuwa Yahaya ya lashe zaɓen jihar Gombe karo na biyu
    • Gwamnati Gombe ta ce ta kwace iko da dukkan burtalan jihar
  4. Gwamna Abiodun ne halastaccen gwamnan Ogun – Kotun koli

    Kotun koli ta yi watsi da karar da Mista Ladi Adebutu na jam’iyyar PDP ya shigar don kalubalantar nasarar gwamna Dabo Abiodun na jihar Ogun.

    Hukuncin kotun kolin na nufin Dabo Abiodun ne halastaccen gwamnan jihar ta Ogun.

    Adebutu ya yi ikirari cewa zaben da ya bai wa gwamna Abiodun nasara bai cika dokokin zabe ba sannan ba shi ne ke da kuri'u mafi rinjaye ba.

    Sai dai kotun kolin a zaman ta na yau ta kori karar saboda rashin cancanta tare da tabbatar da nasarar gwamna Abiodun.

    Hukuncin ya zo ne yan kwanaki bayan da kotun kolin ta ce za ta sanar da ranar raba gardama a karar. Dan takarar na PDP dai ya yi rashin nasara a kotun daukaka kara da kuma ta kararrakin zabe.

    Gwamna Dapo Abiodun ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris bayan da ya samu kuri'a 276,298 inda ya doke manyan abokan takararsa - Adebutu wanda ya samu kuri'u 262,383 da Biyi Otegbeye na jam'iyyar ADC da ya samu 94,754.

    • Dapo Abiodun na jam'iyyar APC ya yi tazarce a Ogun
    • Shin ziyarar da gwamnonin Arewa suka kai Kudancin Najeriya za ta kawo karshen rikicin da ya barke?
  5. Kotun koli ta tabbatar da Abdullahi Sule a matsayin gwamnan Nasarawa

    Kotun koli ta ayyana Abdullahi Sule na jam'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Nassarawa.

    Kotun dai ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP David Umbugadu ya shigar inda yake kalubalantar nasarar Abdullahi Sule.

    Kwamitin alkalai ya yanke hukuncin bai daya inda ya kori ƙarar saboda rashin cancanta.

    A ranar 2 ga watan Oktoba ne, kotun kararrakin zabe a Lafia ta soke nasarar gwamna Sule tare da ayyana David Ombugadu a matsayin wanda ya yi nasara.

    Daga baya kuma gwamna Sule da jam'iyyarsa APC suka garzaya kotu domin kalubalantar hukuncin kotun kararrakin zaben.

    Kotun daukaka kara a hukuncin da ta yanke ranar 23 ga watan Nuwamba ta soke hukuncin farko inda kuma ta ce Sule ne halastaccen gwamnan Nassarawa.

    Kotun daukaka karar ta ce kotun kararrakin zabe ta yi kuskure wajen dogara kan hujjojin shaidun PDP.

    • Kotun ɗaukaka ƙara ta mayar wa Gwamna Sule na Nasarawa nasararsa
    • Al`ummar jihar Nasarawa na korafi game da tallafin kayan abinci
  6. Kotu ta tabbatar da nasarar gwamna Oborevwori na Delta

    Kotun koli ta tabbatar da hukuncin kotun kararrakin zabe da ta daukaka kara da ya ayyana Sheriff Oborevwori a matsayin halastaccen gwamnan jihar Delta.

    Kotun ta yi fatali da karar da dan takarar jam'iyyar APC, Ovie Omo Agege ya daukaka inda yake kalubalantar nasarar gwamnan jihar. A cewar kotun, karar ba ta da gamsassun hujjoji

    Kotun ta ce mai karar ya gaza tabbatar da hujjojinsa na yin aringizon kuri'u da kuma saba dokokin zabe.

    Tun farko, kotun kararrakin zabe da kotun daukaka kara sun tabbatar da nasarar gwamna Sheriff Oborevwori inda suka yi fatali da karar da Ovie Omo-Agege na jam'iyyar APC ya shigar.

    Kotun kolin ta kuma yi watsi da karar da dan takarar jam'iyyar SDP ya shigar inda shi ma yake kalubalantar nasarar Oborevwori.

    Kwamitin karkashin alkalai biyar ya yi watsi da karar saboda rashin cancanta.

    Jam'iyyu uku - APC da SDP da LP, duka yan takarar suna kalubalantar matakin Inec na ayyana Sheriff Oborevwori a matsayin gwamnan Delta.

    • Me ya sa ake samun bambancin hukunci a kotunan Najeriya?
    • Idan an ce PDP azaba ce yanzu daɗi ake sha? - Sule Lamido
  7. Mutanen da suka mutu a fashewar Ibadan sun ƙaru zuwa biyar – Gwamnatin Oyo

    Adadin waɗanda suka mutu sakamakon fashewar nakiya da ya afku a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar Talata, 16 ga watan Janairu, ya ƙaru zuwa biyar, in ji gwamnatin jihar.

    An lalata gidaje da dama sakamakon fashewar, wadda ta kai tsawon kilomita 14.

    A daren jiya, gwamnan jihar, Seyi Makinde, yayin da yake bayar da ƙarin haske a gidan talabijin na Channels, ya ce an samu rahoton mutuwar mutane biyu a ranar Talata, inda ya ƙara da cewa wani wanda abin ya shafa ya mutu a asibiti ranar Laraba.

    Sai dai a wani sabon rahoto da aka fitar a ranar Alhamis, mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin tsaro, Fatai Owoseni, ya ce an sake gano wasu gawarwaki biyu.

    “Har yanzu ana ci gaba da aikin ceto. Ya zuwa jiya, mun samu waɗanda suka samu raunuka uku amma da safiyar yau, na samu labari daga jami’an tsaro da ke tallafa wa tawagar likitoci cewa an sake gano wasu gawarwaki biyu” kamar yadda ya shaida wa gidan talabijin na Channels.

    Mai taimaka wa gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta tabbatar da hukunta waɗanda ke da alaƙa da wannan mummunan lamari.

    Ya ce gwamnati tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na tattara bayanan da suka kamata domin tabbatar da an hukunta waɗanda suka aikata laifin.

    • Yadda fashewar nakiya ta hallaka sojojin Nijar
    • Fashewar Beirut : An jiyo motsin rai a gurin da fashewar ta auku
  8. Kotun koli na zaman yanke hukunci kan zaben gwamnoni

    Kotun ƙolin Najeriya ta soma zama domin yanke hukunci kan zaben gwamnonin jihohin Ogun, da Rivers, da Delta da Taraba, da Nasarawa.

    Tun a farkon makon nan ne kotun kolin ta saurari bangaren masu ƙara da wadanda ke ƙara.

    Cikin hukuncin da ake gani zai fi daukar hankali shi ne na zaben Nassarawa inda dan takarar jam'iyyar PDP David Ombugadu yake kalubalantar nasarar gwamna Abdullahi Sule da hukumar zabe INEC ta ayyana a matsayin wanda ya yi nasara.

    Ombugadu yana ikirarin Inec ta rage masa yawan kuri'un da ya samu a zaben inda kuma karar da ya shigar a kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke cewa shi ne ya yi nasara sabanin Abdullahi Sule da Inec ta ayyana.

    Sai dai a kotun daukaka kara, an soke hukuncin kotun kararrakin zaben inda aka sake ayyana gwamna Sule a matsayin wanda ya yi nasara.

    A jihar Kebbi, Aminu Barde na jam'iyyar PDP yana kalubalantar nasarar Nasir Idris na APC wanda Inec ta ce ya lashe zabe.

    Shari'ar zaben Gombe kuwa tana tsakanin gwamna mai ci Inuwa Yahaya da Jibrin Barde na PDP.

    Barde ya yi zargin an tafka magudi da kura-kurai a zaben gwamnan na ranar 18 ga Maris din 2023 da aka yi a kananan hukumomi tara cikin 11 da ke jihar.

    Sai dai kotun kararrakin zabe da kotun daukaka kara sun kori karar da ya shigar gabansu saboda rashin cancanta.

    A jihar Delta kuwa, kotun kararrakin zabe da kotun daukaka kara sun tabbatar da nasarar gwamna Sheriff Oborevwori inda suka yi fatali da karar da Ovie Omo-Agege na jam'iyyar APC ya shigar.

    A ranar 12 ga watan Janairu ne kotun ta yanke hukunci kan zabukan gwamnonin jihohi bakwai - Kano da Bauchi da Zamfara da Ebonyi da Plateau da Abia da Croos River.

    • Zaɓen Najeriya 2023: Sakamakon zaɓen gwamnoni na dukkanin jihohin Najeriya
    • Ƙuri'un da ba za a iya bayaninsu ba a zaɓen Najeriya mai cike da taƙaddama
  9. Netanyahu ya yi fatali da buƙatar Amurka ta kafa ƙasar Falasɗinawa

  10. Koriya ta Arewa ta ce ta yi gwajin makamin nukiliyarta na ƙarƙashin ruwa

    Koriya ta Arewa ta ce ta yi gwajin “makamin nukiliyarta na karkashin ruwa” a matsayin martani ga atisayen da Amurka da Koriya ta Kudu da Japan suka yi a makon nan kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

    Babu wata shaida da ke nuna gwaje-gwajen da aka gudanar kuma a baya Koriya ta Kudu ta ce an wuce gona da iri a bayanin da Koriya ta Arewa ta yi game da karfin jiragen marasa matuki.

    Japan dai ta ƙi cewa komai kan rahotannin na ranar Juma'a.

    A baya dai Koriya ta Arewa ta yi iƙirarin gwada makamin nukiliyarta “Haeil-5-23”.

    A ranar Lahadin da ta gabata, ta yi ikirarin tura wani sabon makami mai linzami.

    A ranar Juma'a, Koriya ta Arewa ta ce ta tunzura ne ta hanyar atisayen hadin gwiwa da Washington da Seoul da kuma Tokyo suka yi don gudanar da gwajin makamansu na karkashin ruwa, a cewar rahoton da Kamfanin Dillancin Labarai na Koriya KCNA ta fitar.

    Ta zargi atisayen da “ƙara dagula al’amuran yankin” da kuma yin barazana ga tsaron Koriya ta Arewa.

    Ƙasashen Amurka da Koriya ta Kudu da kuma Japan sun ce sun ƙara yin atisaye a cikin shekarar da ta gabata a matsayin mayar da martani ga ƙaruwar hare-haren soji da Koriya ta Arewa ke yi, wadanda suka haɗa da gwaje-gwaje da dama na makamai masu linzami na nukiliya da harba sabbin makamai.

    • Koriya ta Arewa ta yi sabon gwajin makaman Nukiliya
    • Harin Ukraine ya lalata jirgin yaƙin Rasha
  11. Hatsarin jirigin ruwan Gujarat - Ba a bai wa 'yan makaranta rigunan kariya daga nutsewa ba

    Iyayen ɗaliban makarantar da ke cikin kwale-kwalen da ya kife a wani tafkin da ke jihar Gujarat ta Indiya sun yi zargin cewa ba a ba 'ya'yansu rigunan kariya daga nutsewa ba.

    Aƙalla dalibai 12 da malamai biyu ne suka nutse a cikin ruwan, lamarin da ya faru a ranar Alhamis a tafkin Harni da ke cikin birnin Vadodara.

    Jami’an ‘yan sanda sun kama wasu mutane biyu da ke da hannu a lamarin.

    Ana ci gaba da bincike don gano sauran waɗanda abin ya shafa.

    Ya zuwa yanzu dai an ceto dalibai 18 da malamai biyu, kuma suna jinya a wani asibiti da ke kusa, kamar yadda hukumomi suka ce.

    Ministan tarayya Harsh Sanghvi ya ce dalibai 10 da ke cikin jirgin ne kawai suke sanye da rigan kariya daga nutsewa, wanda hakan ke nufin yawancin fasinjojin ba su sanye da shi.

    Yayin da ba a san musabbabin faruwar lamarin ba, shaidun gani da ido sun ce kwale-kwalen ya ɗauki fasinjoji sama da abun da ya kamata ya dauka.

    • Aƙalla mutum 22 sun mutu a haɗarin jirgin ruwa a India
    • 'Yadda na tsira daga hatsarin jirgin ruwan da ya kifar da mutum 160 a Kebbi'
  12. Assalamu Alaikum

    Jama'a, barkan mu da warhaka. Da fatan muna lafiya.

    Kamar kullum, a yau ma za mu wallafa labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai ku biyo mu domin sanin halin da duniya take ciki.