Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Nabeela Mukhtar Uba and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa Kai-tsaye, nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Pakistan da Iran sun warware matsalar diplomasiyya da ta gitta tsakaninsu

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Ofishin firaministan rikon ƙwaryar Pakistan, Anwaar-ul-Haq Kakar, ya ce an warware matsalar diplomasiyya da ta gitta tsakanin ƙasar da Iran.

    Matakin na zuwa ne bayan da duka ƙasashen biyu suka kai wa juna hare-haren jirage marasa matuƙa da na makamai masu linzami kan sansanonin 'yan bindiga da ke ƙasashen biyu.

    Sakamakon abin da ya farun ne kuma ƙasashen biyu suka janye jakadunsu a ƙasashen biyu.

    A yanzu ana sa ran jakadun za su koma kan ayyukansu bayan cimma masalahar.

    A ranar Alhamis ne Iran ta ce hare-haren da Pakistan ta kai wa ƙasarta sun kashe mutum tara ciki har da ƙananan yara huɗu a kusa da kan iyakar ƙasashen biyu.

    A nata ɓangare tun da farko Pakistan ta ce harin da Iran ta kai ƙasarta a ranar Talata ya kashe ƙananan yara biyu.

    To sai dai kawo yanzu Iran ba ta ce komai ba game da wannan batu.

    Da safiyar Juma'a ne dai Pakistan ta bayyana aniyarta na yin aiki da Iran don ''magance matsalar'' sakamakon kiran hakan daga ministocin harkokin wajen ƙasashen biyu.

  3. Mun kama masu bai wa 'yan garkuwa da mutane bayanai - Wike

    .

    Asalin hoton, Facebook/ Wike

    Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce jami'an tsaro sun kama wasu mutane da ake zargi da bai wa masu garkuwa da mutane bayanan sirri a birnin Abuja.

    Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin wani babban taro da ya yi da shugabannin ƙananan hukumomi da sarakunan gargajiya da jami'an tsaro da mazauna yankin Gwagwalada a birnin.

    Duk da cewa ministan bai bayyana adadin mutanen da aka kaman ba, ya buƙaci mazauna yankin Gwagwalada su kwantar da hankalinsu, saboda a cewar za a samu ci gaba a yanayin tsaron birnin cikin kwanaki masu zuwa.

    Mista Wike ya kuma umarci kwamishinan 'yan sandan birnin ya gaggauta samar da ƙarin ofisoshin 'yan sanda har guda biyu a ƙaramar hukumar Gwagwaladan.

    Birnin Abuja dai a baya-bayan nan na ci gaba da fuskantar matsalar tsaro musamman a makonnin baya-bayan nan inda masu garkuwa da mutane ke ci gaba da sace mutane domin neman kuɗin fansa.

  4. Afcon: Cape Verde ta zama ƙasa ta farko da ta kai zagayen gaba

  5. Dubban mutane ne suka yi maci a Yemen don nuna goyon baya ga Houthi

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban magoya bayan mayaƙan Houthi a Yemen sun yi wani maci a Sana'a babban birnin ƙasar.

    Wannan zanga-zanga na zuwa ne mako guda bayan harin saman da Amurka ta kai wa mayakan Huothi da shirin dakatar da su daga kai hare-hare kan jiragen ruwa a maliya.

    A ranar Laraba, Amurka ta ce za ta sake ayyana ƙungiyar a matsayin ta "'yan ta'adda".

    An dai ta zanga-zanga a Yemen tun farkon fara yaƙin tsakanin Isra'ila da Yemen, sai dai zanga-zangar ta ƙara ta'azzara ne a kwanan nan bayan da Amurka ta fara kai hare-hare kan mayakan Houthi.

    Houthi ta fara kai hare hare ne kan jiragen ruwan kasuwanci a maliya domin nuna goyon baya ga Hamas a yakin Gaza.

  6. Gobara ta tashi a wurin ajiye man Rasha bayan harin jirgi maras matuƙi na Ukraine

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin Rasha sun tabbatar da tashin mummunar gobara a manyan rumbunan ajiye manta da ke kudancin ƙasar, bayan da wani jirgi maras matuƙi na Ukraine ya kai hari wurin.

    Kafofin yaɗa labaran Rasha sun ce tankokin mai huɗu ne suka kama da wuta, inda wutar ta bazu zuwa wuraren da ke kusa da yankin.

    Hukomomin jihar Bryansk sun ce babu wanda ya jikkata sakamakon gobarar

    Gwamnan jihar ya ce "An harbo jirgin Ukraine maras matuƙi a kusa da birnin Klinstsy, inda kuma ya faɗa a rumbun adana man da ke yankin''.

    Wannan ne harin jirgi maras matuƙi na biyu da aka kai kan rumbunan yaƙin Rasha a cikin kwana biyu.

    A ranar Alhamis ne wani jirgi maras matuƙi ya kai hari kan ma'ajiyar mai da ke St. Petersburg, birni na biyu mafi girma a Rasha.

  7. Tankokin Isra'ila na ci gaba da kai hare-haren Khan Yunis

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Tankokin Isra'ila sun ƙaddamar da sabbin hare-hare a Khan Yunis, babba birnin yankin Kudancin Gaza, baya ruwan hare-hare ta sama da fadan da aka fafata.

    Cikin kwanaki takwas da aka shafe babu sadarwa a yankin, ana ci gaba da nuna damuwa kan rayuwa haruruwan fararen hula da ke yankin, wadanda da yawansu suka rasa muhallansu daga Gaza.

    Da yawa sun tsere asibitin Nasser, daya daga cikin asibitotci kadan da suke aiki a Gaza.

    Dakarun Isra'ila sun zargi Hamas da amfani da asibitocin a matsayin sansanin sojinsu, wani zargi da likitoci a Gaza suka musanta.

  8. 'Yan sanda sun kama Chinaza gawurtaccen mai garkuwa da mutane

    .

    Asalin hoton, Nig.police

    Rundunar 'yan sandan Abuja babban birnin Najeriya ta tabbatar da kama Chinaza Phillip, wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna.

    Cikin wata sanarwa da rundunar 'yan sandan birnin tarayyar ta wallafa a shafinta na X ta ce 'yan sandan jihar Kaduna ne suka kama mai garkuwa da mutanen.

    Sanarwar ta ce tuni aka miƙa shi hannun rundunar 'yan sandan Abuja a ranar Juma'a, domin ci gaba da gudanar da bincike.

    A ranar Alhamis 18 ga watan Janairu ne 'yan sandan jihar suka kama ɗan fashin a daidai lokacin da shi da sauran abokan sana'arsa suke kan hanyar zuwa Kano daga Abuja, lokacin da suka yi garkuwa da wani mutum a Abujan, suka kuma tafi da shi a motarsa.

    Rundunar ta ce ta kuma gano wasu makamai da wayar hannu da kuma motar mutumin da suka yi garkuwar da shi ɗin.

    .

    Asalin hoton, X/FCT Police Command

  9. Afcon: Cape Verde ta zama ƙasa ta farko da ta kai zagayen gaba bayan doke Mozambique

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Cape Verde ta kasance ƙasa ta farko da ta kai zagayen gaba na 'yan 16 bayan doke Mozambique da ci 3-0, a gasar kofin Afirka ta Afcon 2023 da ake gudanarwa a ƙasar Ivory Coast

    Tsohon ɗan wasan Manchester United, wanda a yanzu ke taka leda a Rayo Vallecano, Bebe ne ya fara buɗe ragar Mozambique, bayan da ya ci ƙwallo mai ƙayatarwa a bugun tazara.

    Daga nan Kaftin ɗin tawagar ƙasar, Ryan Mendes ya ƙara ta biyu.

    Kafin daga bisani Kevin Pina ya ƙara ta uku daga wajen yadi na goma sha takwas.

    Da wannan nasara Cape Verdeta kasance ta farko a rukunin B, sama da Masar da Ghana, yayin da ya rage wasa guda a kammala wasannin rukunin.

    A ranar Litinin ne ƙasar za ta kara da Masar kafin kammala wasan cikin rukunin.

  10. An ɗaure wani mutum a Thailand shekara 50 saboda batawa basarake suna

    f

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Thailand ta yanke wa wani mutum hukuncin daurin shekaru 50 a gidan yari bisa samun sa da laifin kalaman batanci ga wani basarake - hukunci mafi girma da aka taba yankewa a karkashin wata fitacciyar dokar kasar da ake kira Lese majeste.

    Da farko dai, an yanke wa Mongkol Thirakot dan shekaru 30 hukuncin daurin shekaru 28 bisa samunsa da laifin rubuce-rubucen da ya yi shekaru uku da suka gabata a shafin Facebook.

    Amma a ranar Alhamis kotun daukaka kara ta daɗa masa shekaru 22 a kan hukuncin.

    Dokar lese majeste ta haramta duk wani mummunan sharhi game da masarautar ƙasar.

  11. IGP ya bayar da naira biliyan biyu ga iyalan 'yan sandan da suka mutu

    .

    Asalin hoton, X/Nig.Police

    Babban sifeton 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya bayar da chekin naira biliyan 2.08 ga iyalan 'yan sandan da suka mutu a bakin aiki cikin shekara biyar da suka gabata.

    Cikin wata sanarwa da mai magana yawun rundunar 'yan sandan ƙasar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ya ce an bayar da chekin kuɗin ga mutum 785 da za su amfana da kuɗaɗen.

    “Rundunar 'yan sandan Najeriya, ta hanyar ofishin kula da inshora, ya samu damar warware haƙƙoƙin mamata kusan 2,533 wanda ya kama kusan naira biliyan 6.01 tsakanin watan Yunin 2023 zuwa yau'', in ji sanarwar.

    Babban sifeton 'yan sandan ya kuma yaba wa shugaban ƙasar Bola Tinubu, saboda sanya walwalar 'yan sanda cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.

    A Najeriya dai iyalan jami'an tsaro kan shiga tasku bayan mutuwar iyayensu ko mazajensu waɗanda suka sadaukar da rayukansu wajen bauta wa ƙasar.

  12. Dole a sake nazari kan masarautun Kano - Kwankwaso

  13. 'Za a riƙa yin gwajin HIV kafin aure a Kano'

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a jihar Kano sun ce shirye-shirye sun yi nisa don kafa dokar da za ta tilasta a waɗanda suke shirin aure yin gwajin cututtuka ciki har da cuta mai karya garkuwar jiki.

    Sun ce ɗaukar matakin ya zama wajibi don daƙile bazuwar cutuka tsakanin ma'aurata a jihar Kano.

    Dakta Usman Bashir shi ne darakta janar na hukumar yaƙi da cutar HIV ko Sida na jihar Kano ya shaida wa BBC cewa an ɗauki matakin ne domin tabbatar da kare ma'aurata daga yaɗa cutukan da ake iya ɗauka ta hanyar auratayya, da kuma haihuwar 'ya'yan da ke ɗauke da cutukan da ake iya gada.

    Ya kuma ce yawanci cuta mai karya garkuwar jiki ana iya ɗaukarta ne ta hanyar saduwa, ''inda za ka ga mutum na da mata uku, amma daga ƙarshe sai ya auro matar da ke ɗauke da cutar ya kuma zo ya yaɗa wa sauran matan nasa''.

    ''To hanyar da za a iya kauce wa wannan shi ne a riƙa yin gwaji kafin aure''.

    Ya kuma ce dokar gwajin da za a yin ba ta HIV ce kaɗai ba, har da sauran cutukan da za a iya ɗauka ta hanyar saduwa waɗanda su ma ke da illa.

    Sauran cutukan da gwajin zai shafa, sun haɗar da cutar ciwon hanta da cutar sikila da cutar da cutar sifilis.

    ''Za kuma mu haɗa da gwajin shaye-shaye, ta hanyar gwada ƙwaƙwalwar mutum don tabbatarwa da cewa lafiyarsa kalau'', in ji Dakta Usman.

    Ya ƙara da cewa an kwashe tsawon shekara bakwai ana fafutikar kafa wannan doka, inda ta riƙa samun tangarɗa a baya, amma ya ce a yanzu dokar ta wuce karatu na biyu a majalisar dokokin jihar.

    ''Yanzu abin da ya rage shi ne a zauna da masu ruwa da tsaki, ciki har da malaman addini domin yi wa dokar kallon tsakani kafin a sake mayar da ita majalisa don a amince da ita, kafin a kai wa gwamna ya sanya mata hannu ta fara aiki a jihar Kano''.

    Ya kuma ce idan batun ya zama doka to za a tanadi hukunci ga duk malami ko limamin da waliyyan da suka ɗaura aure ba tare da takardar gwajin ba.

    Dakta Usman ya ce ƙiyasi ya nuna cewa jihar Kano na da masu fama da lalurar cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV kimanin mutum 120,000, to sai dai ya ce kimanin mutum 42,000 ne ke kan magani.

  14. Tsohon shugaban Saliyo zai tafi Najeriya don neman lafiya

    Koroma

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ernest Bai Koroma ya kwashe shekara 11 yana jagorantar Saliyo

    Tsohon shugaban Saliyo zai tafi Najeriya domin neman lafiya, duk kuwa da shari'ar da yake fuskanta a ƙasar bisa zargin hannu a yunƙurin juyin mulkin ƙasar cikin shekarar da ta gabata.

    A ranar Laraba ne babbar kotun ƙasar ta bai wa Ernest Bai Koroma damar ficewa daga ƙasar na aƙalla wata uku.

    To sai dai ana ganin cewa an cimma yarjejeniyar barinsa ya je zaman gudun hijira.

    A watan Maris ake sa ran fara shari'ar da ake yi masa kan zargin cin amanar ƙasa.

    Mista Koroma ya kwashe shekara 11 yana jagorantar Saliyo, har zuwa shekarar 2018 lokacin da aka zaɓi shugaba Julius Maada Bio a matsayin sabon shugaban ƙasar.

    An ga jirgin saman shugaban Najeriya ɗauke da Mista Koroma, lokacin da yake barin filin jirgin saman birnin Freetown ranar Juma'a da rana.

    Matakin na zuwa ne bayan da aka yi ta samun rahotonnin da ke cewa ƙungiyar Ecowas ta shiga tsakani domin cimma matsaya da gwamnatin Saliyo wanda ya bai wa tsohon shugaban ƙasar mai shekara 70 damar ficewa daga ƙasar.

  15. Masu garkuwa sun sace mutum uku a Abuja

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutum uku a rukunin gidajen da ke bayan gidajen tsoffin sojojin ƙasar da ke rukunin gidaje na Kurudu a babban birnin tarayyar ƙasar Abuja.

    Rahotonni daga ƙasar sun ambato daraktan hulɗa da jama'a na rundunar sojin ƙasar, Birgediya Onyema Nwachukwu na tabbatar da faruwar lamarin.

    Birgediya Janar Nwachukwu ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Alhamis

    Mazauna rukunin gidajen sun ce maharan sun buɗe wuta a rukunin gidajen kafin daga bisani su arce da mutanen da suka yi garkuwar da su.

    Cikin wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels a ƙasar, Birgediya Janar Nwachukwu ya ce dakarun soji sun garzaya rukunin gidajen a lokacin da suka samu kiran gaggawa dangane da abin da ke faruwa.

    Ya ƙara da cewa jami'ansu na ci gaba da farautar maharan domin kuɓutar da mutanen.

    Unguwar Kurudu na ɗaya daga cikin garuruwan da ke kan iyakar Abuja da jihar Nasarawa

    A baya-bayan nan dai birnin Abuja na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro, inda ke samun ƙaruwar ayyukan masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

    Ko a makon da ya gabata ma an samu ɓullar labarin garkuwa da wani mutum tare da 'ya'yansa biyar a unguwar Bwari ke birnin Abujan, inda masu garkuwar suka kashe ɗaya daga cikin 'ya'yan nasa bayan gaza biyan naira miliyan 60 a matsayin kuɗin fansa.

    Batun ya ja hankalin mutane musamman a shafukan sada zumunta inda 'yan ƙasar da dama suka riƙa tara kuɗaɗe a shafukan da nufin taimaka wa iyalan don kuɓutar da su.

  16. Zanga-zanga ta ɓarke a Nasarawa kan hukuncin Kotun Koli

    Zanga-zanga ta ɓarke a Lafia, jihar Nasarawa bayan hukuncin da kotun koli ta yanke da ya tabbatar da nasarar gwamna Abdullahi Sule a matsayin halastaccen gwamnan jihar a zaɓen da aka yi a ranar 18 ga watan Maris na 2023.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an toshe hanyar Lafia zuwa Jos gaba daya yayin da masu zanga-zangar suka kunna wuta don hana matafiya da sauran masu amfani da hanyar.

    Masu ababen hawa sun bi wasu hanyoyin don su samu su fita daga Lafia.

    An kuma rufe shaguna da wuraren sana'a harda makarantu sakamakon zanga-zangar.

    Kotu dai ta yi watsi da ƙarar da ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP David Umbugadu ya shigar inda yake ƙalubalantar nasarar Abdullahi Sule.

  17. Masoyan Madonna sun maka ta a kotu saboda soma taron holewa a makare

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu masoyan shahararriyar mawakiyar nan, Madonna sun maka ta gaban kotu saboda kin fara wani taron nishadantarwa da ta tsara yi watan da ya gabata kan lokaci inda ta kara fiye da sa'a biyu, kamar yadda wasu takardun kotu suka nuna.

    A cewarsu, za a share dare uku ana taron chashiyar - inda aka tsara farawa da karfe 20:30 EST sai dai babu wanda aka soma a kan lokaci sai bayan karfe 22:30 inda kuma aka kammala da karfe 01:00.

    Sun ce "da ba za su biya kudin tikiti ba" da sun san cewa ba a kan lokaci za a gama ba.

    BBC ta nemi jin ta bakin Madonna da Live Nation da cibiyar taron Barclays.

    Karar da Micheal Fellows da Jonathan Hadden ta bayyana cewa "akasarin masu tikiti da suke halartar taron holewa cikin dare suna tashi da wuri su tafi aiki sannan wahsegari kuma su yi hidimar iyali".

    Suna karar kamfanin nishadantarwa na Live Nation da kuma wurin taron - Cibiyar Barclays kan yin "tallan karya da rashin adalci da sakaci kuma ayyukan kasuwanci na yaudara".

  18. 'Yanzu dala ɗaya ta kai naira 1,360 a Najeriya'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Darajar kuɗin Najeriya naira na ci gaba da durƙushewa yayin da farashin dala ke sake hawa inda a safiyar yau, Juma'a ake sayar da dala daya kan naira 1,360 a kasuwannin canji da ke Abuja, babbar birnin taraya, kamar yadda, Alh Abbdullahi Abubakar, shugaban ƴan canji na Abuja ya shaida wa BBC.

    Alhaji Abubakar ya ce tun makon da ya gabata har zuwa yanzu, farashin dala bai sauka ba.

    "Tun da aka shiga wannan sabuwar shekarar, farashin dala ke hauhawa, tun ana siyar da dalar kan naira 1,215, a yau Juma'a, farashin dala ta haura zuwa naira 1,360 a kan ko wacce dala kasuwan bayan fage da ke Abuja."

    Abubakar ya ce wasu dalilan da ke haifar da durƙushewar naira kan dala sun haɗa da rashin sa ido daga ɓangaran gwamnati da kuma mutane da dama da ke siyan dalar suna ajiye wa a matsayin kadara.

    Ya ce ga dukkan alama, idan har gwanati ba ta tashi tsaye ba, dalar za ta ci gaba da tashi.

    A legas kuma, Liman, wani ɗan canji a can ya ce dalar ta tashi itama a kan naira 1,360, a safiyar yau, Juma'a, amma ya ƙara da cewa yanzu da rana dalar ta fara ƙasa inda ta sauka zuwa naira 1355.

    Ya ce a jiya Alhamis, an rufe dalar a kan naira 1,349.

    A Kano kuma, Yusuf Nabahani, tsohon shugaban kasuwan ƴan canji, shi ma yace kusan kullum farashin dalar ƙaruwa ya ke yi inda ya ce a safiyar yau, Juma'a, dalar ta tashi a kan naira 1,353.

    Ya ce a jiya Alhamis, an siyar da dalar kan naira 1,350

    • Me ya sa darajar naira ke daɗa karyewa?
    • Mummunar faɗuwar darajar naira a tarihi
  19. Emefiele ya musanta sabbin tuhume-tuhume a kansa

    ..

    Asalin hoton, CBN

    Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya musanta aikata tuhume-tuhume 20 da hukumar EFCC mai yaki da yi wa arzikin kasa ta'annati take masa wadanda aka sabunta.

    A yanzu tuhume-tuhumen da ake yi wa Emefiele sun hada da zargin cin amana da zamba da hada baki wajen aikata babban laifi da jabu.

    Tsohon gwamnan babban bankin wanda aka ba shi beli ya samu izinin fita daga Abuja amma ba kasar ba kamar yadda alkali Hamza Muazu na babbar kotu a Abuja ya yanke.

    Lauyan hukumar EFCC, Rotimi Oyedepo bai kalubalanci hukuncin ba shi beli ba.

    Da yake amincewa da bukatar ba da beli, Alkali Muazu ya dage karar zuwa 12 da 13 ga watan Fabarairu domin ci gaba da zama.

    • Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN Emefiele
    • Waiwaye: Ci gaba da amfani da tsoffin kuɗi da sakin Emefiele
  20. Mun nuna wa duniya ƙarfinmu - Osimhen