Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An gano sabon nau'in sauro da ke zagon-ƙasa ga yaƙi da Maleriya - WHO

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Kenya ta kama jami'an ƴan sanda bisa zargin sace wani ɗan ƙasar China

    An kama jami'an ƴan sandan uku a Kenya bisa zargin su da hannu a sace wani dan kasar China domin neman kudin fansa.

    Ana zargin su da yi wa ɗan kasar Chinan kwanton-ɓauna yayin da yake kan hanyarsa zuwa aiki a ranar 8 ga watan Janairu, inda suka daure shi tare da dauke shi.

    Daga nan ne jami’an ‘yan sandan suka yi masa fashi kafin su sake shi, kamar yadda ‘yan sanda suka ce.

    Hukumomin ƙasar na kuma neman wani dan kasar China da ake kyautata zaton shi ne jagoran waɗanda suka sace shi.

    "Wanda ya jagoranci garkuwan ya kira dangin wanda aka sace a China yana neman kudin fansa wanda aka aika zuwa wani asusun banki a China," in ji 'yan sandan a kan shafin X.

    "Bayan an aika da kudin fansar ne, kuma masu garkuwan suka tabbatar da cewa dangin sun yi biyayya, shi ne aka sako wanda aka yi garkuwa da shi."

    ‘Yan sanda sun ce lamarin ya “bankado wasu gungun masu aikata laifuka na kasashen duniya waɗanda ke yin bincike kan ƙarfin arzikin wanda suke hari kafin aikata laifin.

    Hukumomin kasar Kenya suna aiki tare da hukumar ƴan sandan duniya ta Interpol domin gano wadanda suka aikata laifin a China.

    • Shugaban Kenya ya nemi afuwar al'ummar ƙasar kan mace-macen masu azumi
    • Yadda azabtar da ɗalibai a makarantu ta zamo annoba a Kenya
  2. NCC ta dakatar da shirin hana masu layin Glo kiran layin MTN

    Hukumar sadarwa ta Najeriya - NCC ta dakatar da shirin ta na hana masu amfani da layin kamfanin Glo kiran layukan kamfanin MTN na tsawon kwanaki ashirin ɗaya.

    A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Daraktan hulda da jama’a na hukumar NCC, Reuben Mouka, ya ce hukumar ta yanke shawarar dakatar da matakin ne bayan da kamfanonin sadarwa suka amince da warware duk wadansu matsalolin da ke tsakaninsu.

    Tun da farko dai, hukumar ta ce ta amince da kamfanin MTN ya fara yanke kira da layin kamfanin Globacom daga ranar 18 ga Janairu, 2024, saboda takaddamar bashin da ya daɗe a tsakanin ɓangarorin.

    “Hukumar ta yi farin cikin sanar da cewa a yanzu kamfanonin MTN da Glo sun cimma matsaya don warware duk wata matsala da ke tsakaninsu, saboda haka, hukumar ta dage dakatarwar da aka yi na tsawon kwanaki 21 daga yau 17 ga Janairu, 2024.

    “A wajen bayar da amincewar hukumar, hukumar tana sane da illolin da shawarar za ta iya haifarwa ga masu amfani kamfanonin sadarwar biyu, don haka ta ci gaba da jan hankalin bangarorin biyu don saukaka wani kuduri wanda ya ba da fifiko da kuma kare muradun mabukaci da kuma tafiyar da harkokin sadarwa ta kasa baki daya,” in ji NCC.

    “Yayin da hukumar ke sa ran MTN da Glo za su warware duk wata matsala da ta kunno kai a cikin kwanaki 21, hukumar ta ce dole ne duk kamfanonin da ke aiki su warware basussuka a matsayin wani abin da ya dace don bin ka'idojin doka na duk masu lasisi."

    • Kasashen Afirka da manyan kamfanonin sadarwa suka bude ofisoshinsu
    • Yadda za ku yi 'taka tsan-tsan' da sabbin sharuɗɗan WhatsApp
  3. An gano sabon nau'in sauro da ke zagon-ƙasa ga yaƙi da Maleriya - WHO

    Wani sabon nau’in sauro da ake yi wa lakabi da “steve,” wanda ya samo asali daga Kudancin Asiya, yana haifar da karuwar masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro a kasashen Afirka bakwai da suka hada da Djibouti, da Habasha, da Kenya, da Najeriya, da kuma Ghana, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO)

    Ba kamar sauran sauro na yau da kullun ba, “steve” yana bunƙasa ne a cikin birane kuma ba ya bukatar danshi mai yawa kafin ya hayayyafa.

    Wannan nau'in sauron na cizo da rana, yana da juriya ga magungunan kashe ƙwari na yau da kullun, kuma yana haifar da ƙalubale ga dabarun yaƙi da zazzabin cizon sauro a halin yanzu, in ji Dr Dorothy Achu shugabar WHO kan cututtuka masu addabar mutanen da ke zaune a yankunan duniya masu zafi na Afirka, inda ta ƙara jaddada wahalar ganowa da kuma kawar da wannan sauro mai saurin jure yanayin.

    • Abu huɗu da suka kamata ku sani kan zazzaɓin Dengue da ya ɓulla a Najeriya
    • Ghana ta zama ta farko a duniya da ta amince da sabon riga-kafin maleriya
  4. Kotu ta yanke wa yar Amurka shekara 26 a kurkuku kan kisan mahaifiyarta

    An yanke wa wata Ba'Amurkiya da ta taimaka wajen halaka mahaifiyarta tare da cusa gawarta cikin akwati yayin hutu a 2014 hukuncin shekara 26 a gidan yari.

    An samu Heather Mack da laifi a Indonesia a 2015 inda aka yanke mata shekara 10 a gidan yari amma aka sake ta a 2021.

    An kuma kama ta lokacin da ta isa Amurka inda aka tuhume ta da hannu a kisan wata yar Amurka.

    Mack ta shafe shekara biyu da suka gabata a gidan yari da ke Chicago inda ta yi jiran a yanke mata hukunci.

    A ranar Laraba ne alkali Mathew Kennelly ya yanke cewa Mack mai shekara 28 za ta samu sassauci zuwa shafe shekara 23 a gidna yari.

    Masu gabatar da kara sun ba da shawarar a yanke hukuncin shekara 28 ga Mack wadda ta hada baki da tsohon saurayinta Tommy Schaefer don kashe mahaifiyarta, Sheila von Wiese-Mack wadda ke da arziki.

    Bayanai sun ce sun kashe ta ne domin samun damar amfana da gidauniya ta dala miliyan daya da rabi.

    Masu gabatar da kara sun zargi Ms Mack wadda a lokacin take yar shekara 18 dauke da juna biyu - ta rufe bakin mahaifiyarta yayin da Mr Schaefer ya maka mata kwano a kanta.

    Daga bisani kuma aka gano gawarta cikin wani akwati.

    Bayan kisan Wiese-Mack a otal in, Ms Mack da Mr Schaefer suka yasar da akwatin a bayan wata tasi, kamar yadda masu gabatar da kara suka ce. Daga baya ne kuma direban tasi din ya ankarar da yan sanda.

    Daga bisani an gano masoyan sun koma zama a wani otal da ke Bali.

    Tun farko Mack ta musanta zargin amma daga baya ta sauya matsaya bayan da masu gabatar da kara suka yi mata tayi mai kyau da tun farko suka nemi a yanke mata hukunci mai tsawo.

    Yayin yanke hukuncin, dan uwan Wiese-Mack, Bill Wiese ya nemi kotu ta yanke mata hukunci mai tsauri inda ya ce Mack ba ta yi da na sanin abin da ta aikata ba.

    "Don ta ni ne, Heather za ta shafe rayuwarta a tsare," in ji Mr Wiese.

    Mr Schaefer wanda aka bayyana yana da hannu, har yanzu yana tsare a Indonesia.

    • Matar da ta 'mutu' ta farfaɗo lokacin jana'izarta
    • Hukuncin kisa da aka yanke wa ɗan sandan Najeriya na tayar da ƙura
  5. Kotu ta bai wa Emefiele damar fita daga Abuja

    Mai shari’a Hamza Muazu na babbar kotun birnin tarayya ya bai wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele damar yin tafiya zuwa wasu garuruwan Najeriya daga Abuja, babban birnin kasar.

    Sai dai kotun ta ce dole ne Emefiele ya ci gaba da zama a ƙasar.

    A kan sharuɗɗan belinsa, an taƙaita zamansa a Abuja kaɗai amma Emefiele, ta bakin lauyansa, Mathew Bukka, SAN, ya buƙaci a sauya sharuddan.

    Lauyan Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), Rotimi Oyedepo, bai ce komai ba kan lamarin amma ya buƙaci kotu da ta tabbatar da Emefiele ya rubuta alkawari cewa zai ci gaba da zama a ƙasar idan aka amince da buƙatarsa.

    An dai bayar da belin Emefiele ne a ranar 24 ga watan Disamba, 2023, kan kudi naira miliyan 300 da kuma mutum biyu masu tsaya masa.

    • Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN Emefiele
    • CBN ya ce a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudi
  6. An ayyana dokar hana fita a Comoros bayan zaɓen ƙasar

    Gwamnatin tsibirin Comoros ta ba da umarnin kafa dokar hana fita na dare bayan 'yan sanda da sojoji sun yi arangama da masu zanga-zangar da suka fusata da sake zaben shugaba Azali Assoumani.

    Jam’iyyun adawar dai sun yi kira da a bayyana zaben a matsayin wanda ba shi da tushe, suna masu zargin an tafka magudi.

    An harba hayaƙi me sa hawaye kuma masu zanga-zangar sun kona tayoyi da shingen hanyoyi a kan titunan babban birnin kasar Moroni.

    An kuma bayar da rahoton gudanar da zanga-zanga a wasu garuruwan da ke gabar tekun Indiya.

    An ce an kama wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba yayin zanga-zangar.

    Mai magana da yawun gwamnati ya zargi 'yan adawa da kawo cikas ga zaman lafiyar jama'a. Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a tabbatar da doka da oda.

    A ranar talata ne hukumar zabe ta ƙasar, Ceni ta sanar da Mr Assoumani a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar a karo na huɗu bayan samun kashi 63 cikin dari na ƙuri'un da aka kaɗa a ranar Lahadi.

    Kashi 16 cikin 100 na wadanda suka cancanci kada kuri'a ne kawai suka shiga.

    • Abin da dokar ta-ɓaci kan samar da abinci ke nufi ga talakan Najeriya
    • Coronavirus a Comoros: An harba hayaki mai sa hawaye cikin masallaci
  7. Gwamnatin Qatar ta kai wa Falasɗinawa kayan agaji

    Gwamnatin Qatar ta ce manyan motoci ɗauke da kayan agaji zuwa ga Falasdinawa a Gaza, wadanda suka haɗa da magunguna sun shiga Zirin wanda ke cikin mawuyacin hali.

    Ministan harkokin wajen Qatar Majed al-Ansari, bai yi ƙarin bayani kan ko an rarraba kayan agajin ba ko kuma a'a.

    Tun da farko shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteresh ya ce bai taba ganin inda aka hana shigar da agaji a yanayi irin na Gaza ba inda ya ƙara da cewa ana take dokokin ƙasashen duniya har da na yaki.

    Duniya dai na tare da farar hula wadanda yawancinsu da aka kashe mata da ƙananan yara ne.

    Babban jami'in kungiyar Hamas, Musa Abu Marzuk, ya wallafa a shafinsa na X cewa kowanne kwali ɗaya na maganin da aka bai wa marasa lafiyar Isra'ila, za a kai kwali 1000 ga irin shi ga marasa lafiya a Gaza.

    • Isra’ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar kai agaji Gaza
    • Hatsarin mayar da martanin Houthi ga harin Amurka da Burtaniya a Yemen
  8. Pakistan ta kai harin ramuwar gayya a Iran

    Pakistan ta sanar da kai harin ramuwar gayya kan Iran da tsakar dare, kwana guda bayan Iran ta kai hari cikin Pakistan, wanda rahotanni suka ce ya yi sanadin mutuwar mutum bakwai.

    Pakistan ta ce harin da ta kai ya afka wa maɓoyar 'yan ta'adda a lardin Sistan-Baluchestan na Iran.

    Gidan talabijin na ƙasar Iran ya ce an kashe mata uku da yara huɗu.

    Hare-haren ta sama na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya tare da rikice-rikice.

    Isra'ila na yaƙar ƙungiyar Falasdinawa ta Hamas a Gaza tare da yin musayar wuta da ƙungiyar Hizbullah da ke samun goyon bayan Iran a Lebanon.

    Ƙungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran a Iraki da Siriya suna kai wa sojojin Amurka hari, sannan Amurka da Birtaniya sun kai hari kan 'yan Houthi na ƙasar Yemen da ke samun goyon bayan Iran.

    Ƙasashen Pakistan da Iran dai sun daɗe suna zargin juna da bai wa kungiyoyin 'yan ta'addan da ke kai hare-hare daga yankunan da ke kan iyakar kasashensu goyon baya.

    A ranar Alhamis, ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ta tabbatar da kai hare-haren, wanda kafafen yada labaran Iran suka ce an kai harin ne a kusa da birnin Saravan.

    • Iran ta kai hari cikin Pakistan
    • Manyan jami’an Amurka na ƙoƙarin hana bazuwar rikici a Gabas ta Tsakiya
  9. Majalisar Dinkin Duniya ta buƙaci taimakon gaggawa don yaƙi da fari a Habasha

    Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta damu da matsalar fari da ake fama da ita a ƙasar Habasha, kuma tana buƙatar ƙarin kuɗaɗe domin ƙara kaimi wajen magance matsalar.

    Hukumar ta sanar a jiya Laraba cewa fari ya shafi mutane miliyan huɗu a yankunan Amhara da Oromia da ke fama da rikici da kuma Afar da Tigray.

    Hukumar ta ƙara da cewa, "Rikici da dama sun yi matuƙar raunana ƙarfin mutane wajen tinkarar bala'in yanayi kamar fari - yana barin miliyoyin mutane cikin mawuyacin hali har ma da ƙara fadawa cikin tsananin buƙata."

    A baya dai gwamnatin tarayya a Addis Ababa ta kawar da fargabar ɓarkewar yunwa, kuma ta ce tana ƙokarin bayar da agaji.

    A wannan makon ma, hukumomin yankin na Tigray sun bayyana cewa sama da mutane 200 ne suka mutu sakamakon yunwa, bayan da suka yi gargaɗi a watan da ya gabata cewa yankin na daf da fadawa cikin bala'i na jin kai.

    • Fari ya haifar da kaurar Zalɓe a Sifaniya
    • Mummunar ambaliyar da ta shafe wani gari a tsakiyar Somaliya
  10. Assalamu alaikum!

    Jama'a, barkan mu da safiyar Alhamis. Da fatan muna cikin ƙoshin lafiya.

    A wannan shafi, kamar kodayaushe, za mu kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa musamman Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai ku kasance tare da mu, kuna kuma iya zuwa shafukanmu na sada zumunta inda za ku ga ƙarin labarai.