Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Habiba Adamu, Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, Buhari Muhammad Fagge and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Ana taron addu'oi a Nijar kan mutuwar malami a hannun ƴan bindiga

    Malaman makarantu a Jamhuriyar Nijar na zaman addu’o’i ga malamin da ƴan bindiga suka halaka ranar 10 ga watan Janairu.

    Malaman suna gudanar da taron addu'oin a cibiyar ƙungiyar ƙwadago ta malaman makarantu ta SYNACEB.

    Taron ya samu halartar ministar ilimin ƙasar, Dr Elizabeth Cherif.

    A ranar 27 ga watan Oktoban bara ne ƴan bindiga suka yi awon gaba da wasu malaman makaranta biyu inda ɗaya daga cikinsu ya rasa ransa a hannun su.

    A baya-bayan nan ne, malaman ƙarƙashin SYNACEB reshen Makalondi suka gudanar da yajin aiki domin nuna rashin jin daɗinsu game da taɓarɓarewar tsaro a jihar Tillabery.

    Ana ci gaba da samun ƙazancewar matsalar tsaro a jihar Tillabery duk da iƙirarin da majalisar mulkin sojin ƙasar ke yi na samun nasara a yakin da take da mahara.

  2. Mutum biyu sun mutu, 77 sun jikkata a fashewar da ta faru a Ibadan

    Gwamnan jihar Oyo, a kudancin Najeriya, Seyi Makinde ya tabbatar da mutuwar mutane biyu, yayin da wasu mutane 77 suka jikkata a wata fashewar da ta faru a daren ranar Laraba.

    Gwamnan ya bayyana hakan ne a shafinsa na X, inda ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin kula da duka wadanda suka jikkata kuma suke samun kulawa a asibiti.

    Makinde ya kara da cewa kuma su samar da matsuganai na wucin- gadi ga mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon al'amarin.

    Gwamnan wanda ya ziyarci inda lamarin ya faru a Bodija da ke Ibadan babban birnin jihar ya ce, bayanan farko daga jami'an tsaro sun bayyana abun da ya janyo fashewar.

    Inda ya kara da cewa wasu masu aikin hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba ne da ke zaune a wani gida a wurin suka ajiye abubuwa masu fashewa, kuma su ne suka haddasa fashewar.

    Hotunan lamarin da ke yawo a dandalin sada zumunta sun nuna yadda fashewar ta shafi gidaje da motoci da kuma nisan wurin da fashewar ta shafa.

    Hukumar kai agajin gaggawa ta NEMA tace an tura ma'aitakai kai dauki da jami'an tsaro, jami'an kashe gobara, jami'an hukumar civil defence da sauransu, domin ayyukan ceto a wurin da lamarin ya auku.

    Wasu daga cikin hotunan inda fashewar ta shafa

  3. Ya kamata a miƙa wa Ukraine biliyoyin kuɗaɗen Rasha – Shugaba Zelensky

    Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya buƙaci gwamnatocin ƙasashen yammacin duniya su miƙa biliyoyin dala na kuɗaɗe da kadarorin Rasha da aka dakatar domin amfani da su wajen sake gina ƙasarsa.

    Shugaban na Ukraine na wannan kiran ne a wajen taron duniya na tattalin arziki a birnin Davos na Switzerland, ganin irin ɗumbin ɓarnar da Rasha ta yi wa ƙasarsa a yaƙin da ta ƙaddamar a kanta na kutse, tun daga watan Fabarairun 2022.

    Shugaba Zelensky ya ce bai kamata a yi amfani da kuɗaɗen al'umma masu biyan haraji na wasu ƙasashen wajen sake gina ƙasarsa kasancewar akwai sama da dala miliyan dubu ɗari uku na Rasha tun bayan da ta mamayi Ukraine.

    Bankunan ƙasashen Turai kuma na ɗari-ɗari game da kalaman shugaban Ukraine - suna ganin idan suka bita za su saka ɗamba na dambarwar shari'a da ka iya haddasa matsalar tattalin arziki a duniya da rashin yadda a bankunan ƙasashen yamma.

  4. Yawan al'ummar China ya ragu karo biyu jere

    Yawan al'ummar kasar China ya sake raguwa a shekara na biyu a jere Alkaluma sun nuna cewa an samu raguwar yawan mutane miliyan biyu a bara -- fiye da ninki biyu na raguwar da aka samu a shekara ta 2022.

    An kuma samu ƙarin mace-mace da galibi ake alaƙanta wa ga annobar korona.

    Halin da ake samu na yawan tsofaffi a al’ummar ƙasar ya sa gwamnatin China ta buƙaci iyalai da su ƙara yawan yaran da suke haifa.

    A shekarar da ta gabata ne wani ƙiyasi na Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna cewa ƙasar Indiya ta wuce China a matsayin ƙasa mafi yawan al’umma a duniya.

  5. Assalamu Alaikum

    Jama'a, barkan mu da warhaka. Da fatan muna lafiya.

    Kamar kullum, a yau ma za mu wallafa labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai ku biyo mu domin sanin halin da duniya take ciki.