Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Habiba Adamu, Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, Buhari Muhammad Fagge and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Jama'a a nan muke cewa Allah Ya ba mu alkhairinsa.

    Da fatan kun ji daɗin labaran da muka kawo muku a yau.

    Sai kuma gobe cikin yardar Allah.

    Ahmad Tijjani Bawage ke cewa asuba ta gari.

  2. Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ayyana Houthis a matsayin ƙungiyar "yan ta'adda"

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da ayyana ƙungiyar "Ansarullah" wadda aka fi sani da "Houthis" a matsayin "ƙungiyar 'ya ta'adda".

    Za su ɗabbaƙa hakan cikin kwana 30 masu zuwa.

    Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen ta fitar ta ce Houthi na kai hare-hare kan jiragen dakon kaya da ke yawo a ruwan maliya tun watan Nuwamba ba tare da wani dalili ba.

    A sanarwar an ce hare-haren da Houthi ke kai wa kan jiragen ƙasashen duniya yana sanya kasuwanci cikin haɗari, kuma yana tauyewa ƙasashen 'yancinsu na kasuwanci ba tare da wata matsala ba.

    Amurka ta ce idan Houthi ta daina kai hare-haren za ta iya cire sunanta daga jerin 'yan ta'addan.

    Sai dai idan sun zarce kwanaki 30 ɗin da aka ba su na wa'adi,

    A 2021 ne ma'aikatar ta cire sunan Houthi daga jerin ƙungiyoyin 'yan ta'adda.

  3. 'Yaƙin da aka gwabza a Gaza a sa'o'i 24 da suka wuce ya kasance mafi wahala'

    Jami'ai a Gaza sun bayyana rikicin da aka gwabza a sa'o'i 24 da suka gabata a matsayin mafi wahala da tsanani.

    Ma'aikatar lafiya ta Falasɗinu ta ce sama da mutane 160 aka kashe, yawancinsu kuma sun mutu ne a hare-haren da Isra'ila ta kai cikin dare da kuma arangamar da ta faru a titunan birnin Khan Yunis da ke kudanci.

    Duk da tserewa da farar hula su ka yi daga yankin, sojojin Isra'ila sun ci gaba da kai wa yankunan da 'yan Hezbollah da Iran take goyon baya suke a Kudancin Lebanon.

    Ƙungiyoyin agaji sun ce katsewar sadarwa wadda ta shiga kwana na shida a yanzu, ta haifar da wahalar aikin agaji har fararen hula da suke tserewa sun kasa samun taimako.

    Tun da farko mayakan Hezbollah sun harba makami mai linzami sansanin sojojin Isra'ila da ke kan iyaka.

  4. Ƴan bindiga za su ɗanɗana kuɗarsu a Abuja - Wike

    Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana a yau Laraba cewa ƴan bindigar da ke addabar mutane a Abuja, za su ɗanɗana kuɗarsu.

    Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Bwari wanda ya samu halartar shugaban karamar hukumar, sarakuna da kuma mazauna yankin, Wike ya ce shugaba Bola Tinubu ya ba shi umarni tare da dukkan hafsoshin wajen ganin sun laluɓo hanyar kawo karshen ayyukan masu garkuwa da mutane da kuma masu kashe-kashe a karamar hukumar da sauran yankuna na babban birnin tarayyar.

    Ya ce shugaban ƙasa ya amince da samar da dukkan kayayyaki da jami'an tsaro ke buƙata domin shawo kan matsalar rashin tsaro a Abuja.

    "Don haka babu wata hujjar da jami'an tsaro za su bayar na cewa sun ƙasa magance matsalar," in ji Wike.

    Ministan ya tabbatarwa mazauna yankin na Bwari cewa a cikin kwanaki masu zuwa za su fara ganin sauye-sauye dangane da matsalar ta tsaro, inda ya buƙace su da su bai wa jami'an tsaro haɗin-kai da ya kamata don taimaka musu wajen yin aikinsu.

    "Ina kira ga mazauna Abuja da su guji amfani da kafafen yaɗa labaru musamman radio ko kafafen sada zumunta don yin magana kan ayyukan ƴan bindigar ko kuma neman taimako don biyan kuɗin fansa. Hakan yana ƙara musu kwarin gwiwa da kuma yaɗa ayyukansu," in ji Wike.

    Ayyukan masu garkuwa da mutane dai na ƙaruwa a Abuja, inda na baya-bayan nan shi ne wanda aka sace ƴan mata ƴan gida ɗaya guda shida a gidansu da ke karamar hukumar Bwari ranar 5 ga watan Janairu.

    Buƙatar biyan naira miliyan 600 da masu garkuwa da ƴan matan suka yi, ya janyo ce-ce-ku-ce, inda ƴan sanda suka sha alwashin kuɓutar da su.

  5. Sojojin Isra'ila sun ce sun kashe wani jami'in leken asirin Hamas

    Sojojin Isra'ila sun ce hare-haren da suka kai cikin Gaza a sa'o'i kalilan da suka wuce, sun janyo mutuwar mayakan Falasɗinawa guda shida, ciki har da wani jami'in leƙen asiri na Hamas.

    Wata sanarwa da sojojin suka fitar, ta ce kisan Bilal Nofal, wanda ke da alhakin tattara bayanan sirri, "zai yi matukar shafar ayyukan Hamas."

    Sai dai babu wani martani daga ƙungiyar Hamas kan wannan iƙirari na Isra'ila.

  6. Dalilin da ya sa Pakistan ta yi wa jakadanta kiranye daga Iran

    Iran ta kai harin makami mai linzami kan wasu wurare a yammacin Pakistan tare da kashe yara biyu, a cewar jami'ai daga Islamabad.

    Harin ya nufi kan wasu yankuna biyu a lardin Balochistan da ke da alaƙa mayakan Jaish al-Adl, in ji gidan talabijin na kasar Iran.

    A farkon makon nan ne Iran ta far wa yankunan Iraqi da Siriya.

    Jami'ai a Pakistan sun ce harin ya hallaka yara biyu da jikkata wasu guda uku.

    Islamabad ta ce bai dace a kai harin ba inda ta yi gargaɗin abin da zai biyo baya.

    Sai dai ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian, ya bayyana a birnin Davos na Switzerland cewa harin bai nufi kan wani ɗan Pakistan ba, sai kan mambobin mayaka na Jaish al-Adl.

    Harin na zuwa ne a daidai lokacin da fargaba ke ƙaruwa a faɗin Gabas Ta Tsakiya, yayin da Isra'ila ke ci gaba da gwabza faɗa da mayakn Hamas a Gaza.

    Tehran ta ce ba ta son tsoma kanta cikin wani babban rikici.

    Sai dai gungun masu bijirewa da suka haɗa da ƴan tawayen Houthi a Yemen, Hezbollah a Lebanon da kuma ƙungiyoyi da dama a Siriya da Iraqi, na ci gaba da ka hare-hare kan Isra'ila da ƙawayenta don nuna goyon baya ga Falasɗinawa.

    Amurka da Birtaniya sun kaddamar da hare-hare kan ƴan Houthi bayan da suke kai farmaki kan jiragen ruwa.

  7. Ya kamata mutane su daina biyan kuɗin fansa - Badaru

    Ministan tsaron Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya ce lokaci ya yi da za a daina biyan kuɗin kansa saboda haka ne kaɗai hanyar kawo karshen masu garkuwa da mutane.

    Ministan ya bayyana haka ne a taron majalisar zartaswa ta ƙasa da aka gudanar a yau Laraba.

    Ya ce shugaban ƙasa ya bai wa dukkan hafsoshin tsaro goyon baya da ta kamata don ganin an kawo karshen garkuwa da mutane da ya yi ƙamari a ƙasar.

    Ministan tsaron ya ce dokar Najeriya ta hana bayar da kuɗin fansa kuma bai kamata mutane su rika biyan kuɗi ba saboda ba shi da amfani.

    "Babbar matsalar ita ce yadda mutane ke fitowa a kafafen yaɗa labarai suna neman taimako, har a zo a tara domin biyan fansa. Hakan bai dace ba.

    "Idan muka daina biyan kuɗin fansa, sannu a hankali ayyukan masu garkuwa da mutane zai zama tarihi," in ji Badaru.

    Dangane da yadda rashin tsaro ke ƙara ta'azzara a Abuja, babban birnin ƙasar da kuma garkuwa da mutane da ake yi a yankunan gefen birnin, Ministan ya ce ayyukan da ake yi na korar ƴan bindiga a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya shi ya sa suke ta ƙaura da guje-guje.

    "Shugaban ƙasa ya ba mu umarni tare da duka hafsoshin tsaro, ya kuma ce lallai a je a tsayar da wannan abu da ke faruwa. Kuma mun sa ƙaimi don ganin mun kawo ƙarshensu," in ji Badaru.

    Ya ce ana ci gaba da fatattakar ƴan bindigar a jihohin Zamfara da Borno don ganin an daƙile ayyukansu.

  8. A shirye nake na mayar da dalolin da Burtaniya ta ba mu - Kagame

    Shugaban Rwanda Paul Kagame ya ce a shirye ya ke ya mayar da miliyoyin dalolin Burtaniya, idan ƙalubalen shari'a ya ci gaba da tarnaƙi tsakanin ƙasashen biyu a batun musayar 'yan cirani.

    Ƙarkashin yarjejeniyar dai gwamnatin Burtaniya ta shirya aikawa da masu neman mafaka zuwa Rwanda kafin a kammala amincewa da bukatarsu.

    Duk wadanda aka aika Rwanda ba su da damar samun mafaka a Burtaniya.

    Yayin taron tattalin arzikin duniya a Davos, Mista Kagame ya tsame kansa daga dambarwar siyasar da yarjejeniyar ta haifar a Burtaniya.

  9. Jiragen Qatar ɗauke da magunguna sun isa Masar

    Wasu jirage biyu na Qatar ɗauke da magungunan mutanen da aka yi garkuwa da su, sun isa Masar.

    Za a shigar da kayan ne ƙarkashin wata yarjejeniya tsakanin Isra'ila da Hamas, wadda Faransa ta jagoranci ƙullawa.

    Wani matakin da gwamnatin Biden ta yaba da shi.

    An fahimci za a rarraba su a cikin Gaza ne.

    A daren jiya fadar White House ta ce, wakilinta na Gabas ta Tsakiya na Qatar inda ake tattauna yiwuwar sakin ƙarin fursinoni.

    Mai magana da yawun gwamnatin Amurka Adrienne Watson, ta bayyana cewar Washigton za ta yi duk abin da za ta iya don a sako waɗanda aka yi garkuwa da su.

    A nata bangaren Doha ta jaddada aniyar ci gaba da ƙoƙarin ganin an kawo ƙarshen rikicin a Gaza.

  10. Sojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa bakwai

    Rahotanni sun bayyana cewar sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa 7 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

    Ƙungiyar Agaji Red Cresent Falasdin ta ce mutane 4 sun rasa rayukansu ne sakamakon fashewar wani abu da asuba, bayan tankokin yaƙi sun yi wa sansanin Tulkarm ƙawanya a Arewa maso Yammacin Gabar yamma da Kogin na Jordan.

    Karin Falasdinawa 3 kuma sun mutu ne biyo bayan wasu hare-haren sojin Isra'ila kusa da sansanin 'yan gudun hijira na Balata a Gabashin birnin Nablus.

    Sai dai Sojojin sun bayyana cewar ɗaya daga cikin mutanen da suka mutu ya na shirya wani harin ta'addanci.

    Ma'aikatar Lafiya ta Falasdin ta ce dakarun Isra'ila ko Yahudawa sun kashe sama da Falasdinawa 300 a Gabar Yamma da Kogin Jordan daga lokacin da aka fara yaƙin a Gaza.

  11. Yadda nakiya ta yi kaca-kaca da wata unguwa a Ibadan

    Al'ummar jihar Oyo na ci gaba da alhini bayan wata fashewar da ta yi sanadin mutuwar mutum biyu da kuma jikkata 77.

    Gwamnan jihar Seyi Makinde ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta ɗauki nauyin kula da duka waɗanda suka jikkata kuma suke samun kulawa a asibiti.

    Mazauna jihar na ta bayyana yadda al'amarin ya faru.

    Latsa ƙasa don kallon bidiyon.

  12. Za a yi wa faston masu azumin mutuwa a Kenya gwajin ƙwaƙwalwa

    Kotu a Kenya ta yanke hukuncin cewa za a yi wa jagoran wata ƙungiyar asiri wanda ke da alaƙa da mutuwar mutum sama da 400 gwajin ƙwaƙwalwa gabanin fara shari'arsa kan zargin kisan kai.

    Mutum 31 da ake zargi ne suka bayyana gaban kotu.

    Kotun ta buƙaci ƙarin lokaci domin aiwatar da gwajin ƙwaƙwalwa a kan limamin cocin.

    An kama Shugaban cocin ta Good News International, Paul Mackenzie Nthenge a watan Afrilu bara, bayan da ƴan sanda suka fara gano gawawwaki da aka binne ckin manyan ƙaburbura a dajin Shakahola da ke kusa da birnin Malindi da ke gaɓar ruwa.

    Paul Nthenge Mackenzie wanda ya kasance tsohon mai tuƙin tasi da ya kafa cocin ne shekaru 25 da suka wuce, ya bayyana gaban kotun ne tare da wasu mutum 30 da ake zargi kan lamarin.

    Mr Mackenzie ya kasance hannun ƴan sanda tsawon watanni goma da suka wuce.

    Ƴan ƙasar ta Kenya na mamakin yadda shari'ar ke tafiyar hawainiya bayan gano gawawwaki da yawa.

  13. Pakistan ta nemi jakadanta a Iran ya koma gida

    Pakistan ta yi wa jakadanta kiranye daga Iran a matsayin martanin harin makamai masu linzamin da jirage marassa matuƙa da Iran ta kai.

    An kuma hana jakadan Tehran komawa Islamabad.

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta ce harin na ranar Talata ya kashe yara biyu.

    Mai magana da yawun gwamnati ya ƙara da bayyana harin da Iran ta kai a matsayin karya dokar ƙasa da ƙasa.

    Pakistan dai ta dakatar da duk ziyarce-ziyarcen da aka tsara gudanarwa tsakanin kasashen biyu a kwanaki masu zuwa.

    Sai dai har yanzu Iran ba ta ce komai ba kan wannan lamari a hukumance.

    Wannan ce-ce-ku-ce na zuwa ne bayan kafar yaɗa labaran Iran ta fidda rahoton cewar an shirya kai harin ne kan ƙungiyar 'yan ta'adda ta Jaish al Adl wadda ke da sansani a Balochistan.

    A farkon wannan makon ne, Iran ta ƙaddamar da hare-hare a iyakokinta, waɗanda suka sauka a yankunan ƙasashen Iraq da Siriya.

  14. Jirgi ya yi saukar gaggawa bayan fasinja ya gartsa wa ma'aikaciya cizo

    Wani jirgin sama da ke kan hanyarsa ta zuwa Amurka, ANA, dole ya sauya akala ya koma Tokyo, bayan wani fasinja da ya bugu mai shekara 55 ya gartsa wa wata ma'aikaciyar jirgin cizo a hannu har ya yi mata ɗan rauni.

    Mai magana da yawun kamfanin jirgin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP afkuwar lamarin.

    A cewar kafar watsa labarai ta Japan, mutumin ya faɗa wa ƴansanda ya sha maganin bacci don haka ba zai iya tuna abin da ya faru ba.

    Lamarin shi ne na baya-bayan nan cikin jerin matsalolin da fannin sufurin jiragen sama na ƙasar ya fuskanta a ƴan kwanakin nan.

    Jirgin da ke ɗauke da fasinjoji 159 na saman tekun Pacific a lokacin da lamarin ya faru, abun da ya tilasta wa matuƙan jirgin juyawa suka koma filin jirgin Haneda da ke Tokyo.

    Kamfanin jirgin ya ce a filin jirgin suka miƙa mutumin hannun ƴan sanda.

    A ranar asabar jirgin saman ANA da ke zirga-zirga a cikin gida a ƙasar ta Japan ya juya inda ya fito bayan an gano ɗaya daga cikin tagogin jirgin ya tsage.

    Mafi munin lamarin da ya faru da jiragen sama na Japan shi ne na ranar 2 ga watan Junairu, a filin jiragen sama na Haneda lokacin da jirgin ƙasar ya yi karo da ƙaramin jirgi na masu tsaron gaɓar teku.

    Duka fasinjoji 379 da ke cikin jirgin sun kuɓuta, bayan ya kama da wuta, amma mutane biyar cikin shida da ke ƙaramin jirgin sun mutu.

  15. Kotun ƙoli za ta sanar da ranar yanke hukuncin zaɓen Sokoto

    Kotun ƙolin Najeriya ta ce zata sanar da ranar da zata yanke hukunci kan ɗaukaka ƙarar da ɗan takarar jam'iyyar PDP, Sai’du Umar, ya shigar inda ya ƙalubalanci nasarar gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu a babban zaɓen da ya gabata.

    Alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ne suka saurari ƙarar.

    A shekarar da ta gabata ne, hukumar zaɓe ta ƙasa(INEC) ta bayyana ɗan takarar jam'iyyar APC, Ahmad Aliyu, a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen gwamnan da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.

    Sai dai Sa'idu Umar ya shigar da ƙara kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamnoni ta Sokoto, inda ya ƙalubalanci nasarar Aliyu da zargin rashin cancantarsa da kuma maguɗi yayin zaɓen.

    Amma kotun ta kori ƙarar bisa dalilan da suka hada da cewa masu ƙarar sun gaza gabatar da gamsassun hujjoji a gaban kotun.

    Ɗan takarar PDP a zaben na watan Maris ya kuma garzaya kotun daukaka ƙara a Abuja, wadda ita ma ta sake tabbatar da nasarar Ahmad Aliyu.

    Kwamitin tace ba ta da wata hujja da zata saka ta sauya hukuncin da kotun zaɓe ta zarce kan nasarar gwamnan.

    Lamarin da ya sa ya sake daukaka ƙara zuwa kotun ƙolin ƙasar.

    • Me ya sa ake samun bambancin hukunci a kotunan Najeriya?
    • Shari'ar kotunan Najeriya ta zama tufka da warwara - PDP
  16. Yadda fasinjan jirgi ya shafe fiye da sa'a ɗaya garƙame a bayi

    Wani fasinja ya tsinci kansa garƙame cikin banɗakin jirgin sama inda ya shafe fiye da sa'a ɗaya bayan da ƙofar banɗakin ta samu matsala ana tsaka da tafiya.

    Mutumin na cikin jirgin SpiceJet da ya taso daga Mumbai zuwa Bengaluru - tafiyar mintuna 105 lokacin da ya maƙale a banɗakin.

    Jami'ai sun kuɓutar da shi jiya Talata bayan da jirgin ya sauka a Bengaluru.

    SpiceJet ya nemi afuwa inda ya ce bai ji daɗin halin da fasinjan ya tsinci kansa ciki ba.

    Kakakin SpiceJet ya faɗa wa BBC cewa zai mayar wa da fasinjan kuɗin jirginsa inda ya ƙara cewa "ma'aikatanmu sun yi ta taimaka wa fasinjan tare da ba shi shawarwari a lokacin da jirgin ke tsaka da tafiya. Da aka isa, wani injiniya ya buɗe ƙofar bayin inda aka gaggauta bai wa fasinjan kulawa."

    Kamfanin jirgin bai yi ƙarin bayani kan fasinjan ba amma wata jarida ta ruwaito cewa mutum yana cikin "yanayi na ruɗewa".

    Lamarin ya faru ne a lokacin da ministan sufuri na Indiya ya ce za su samar da wasu ɗakuna a muhimman filayen jiragen sama shida da ke Indiya domin magance matsalolin da suka shafi rashin jin daɗin fasinjoji.

  17. Isra'ila ta zafafa hare-hare a Kudancin Gaza

    Mazauna birnin Khan Younis a Kudancin Gaza sun ce sun fuskanci ɗaya daga cikin darare mafi muni a rayuwarsu saboda luguden wutar da Isra'ila ta riƙa yi.

    Bidiyo ya nuna hayaƙi ya mamaye sararin samaniya yayin da ake jiyo ƙarar tashin bama-bamai da musayar wuta a sassan birnin.

    Iyalan da suka ɗaiɗaita sun yi ta tserewa daga wani asibiti da ke birnin yayin da yaƙin ke tunkaro su.

    A gefe guda, ana aika magunguna ga ƴan Isra'ila da Hamas ta tsare a matsayin musaya domin kai ƙarin agaji ga Falasɗinawa farar hula ƙarƙashin yarjejeniyar da Qatar ta shiga tsakani.

    Fadar White House ta ce Qatar tana sa ido kan tattaunawa mai muhimmanci game da yiwuwar cimma sabuwar yarjejeniyar sakin ƴan Isra'ila.

    "Yasser Zaqzouq wanda ke samun mafaka tare da iyalinsa a asibitin Nasser da ke Khan Younis ya shaida wa BBC cewa "wannan ne karon farko da muke ganin yanayin luguden wuta. Mun shiga cikin firgici. Yara suna ihu da kuka."

  18. Gobara ta ƙona 'rumfuna 250' a kasuwar Fanteka da ke Kaduna

    Wata gobara da ta tashi a tsohuwar kasuwar Fanteka da ke jihar Kaduna ta yi sanadin ƙonewar rumfuna aƙalla 250 tare da salwantar dukiya mai ɗumbin yawa.

    Shugaban kasuwar ta fanteka, Alhaji Sulaiman Shehu ya shaida wa BBC cewa ibtila'in da ya faru a daren Laraba, ya shafi wani ɓangaren ƴan katako cikin tsohuwar kasuwar ta Fanteka.

    Shugaban kasuwar ya ce zuwa yanzu ba a iya tantance abin da ya haddasa gobarar ba sai dai ya bayyana cewa masu gadin kasuwar sun bayyana musu cewa cikin dare sun lura wuta na tashi ta wani ɓangaren kasuwa bayan da aka kawo wutar lantarki.

    A cewarsa, an yi ƙoƙarin kashe wutar a kan lokaci sai dai yunƙurin bai kai ga nasara ba don jami'an kashe gobarar da ke kusa da kasuwar "ba su da kayan aiki".

    A bayanin da ya yi wa BBC "sun kira jami'an kashe gobara na gwamnatin tarayya waɗanda suka zo suka kashe wutar."

    Shugaban kasuwar ya ce an kafa kwamiti domin tabbatar da ƙiyasin shagunan da lamarin ya shafa.

    Ya kuma yi kira ga gwamnati ta taimaka wa mutanen da lamarin ya shafa kasancewarsu masu ƙaramin karfi.

    • Gobara ta ƙona kimanin shaguna 50 a kasuwar Singa
    • Me yake jawo gobara a kasuwannin Najeriya kuma yaya za a magance ta?
  19. An umarci shugabannin ƴan sanda su tsaurara matakan murƙushe ƴan bindiga

    Babban Sufeton ƴan sanda na Najeriya, Kayode Egbetokun ya yi kira kan ƙara tsaurara matakai domin yaƙar masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata miyagun laifuka a Abuja, babban birnin ƙasar.

    Babban Sufeton ya yi magana ne jiya Talata bayan taron da ya yi da rundunoni na musamman da ke yaƙar laifuka a Abuja game da ƙaruwar matsalar tsaron da babban birnin ke ciki.

    "Ya bayyana damuwarsa matuƙa kan abubuwan takaicin da suka faru sannan ya jaddada buƙatar ɗaukar matakan da za su kawo ƙarshen waɗannan miyagun laifuka" a cewar kakakin rundanar ƴan sanda ta ƙasa, Muyiwa Adejobi.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa a taron da ya mai da hankali kan nazarin ƙalubalan tsaro da ake fuskanta yanzu da kyawawan tsare-tsare da kuma samar da kayan aiki domin shawo kan barazanar da ke ƙara ƙaimi, Babban sifeton ya jaddada buƙatar bin tsarin haɗin gwiwa da kuma tattara bayanan sirri domin shawo kan matsalar tsaron.

    Shugaban ƴan sandan ya umarci mataimakinsa da "ya ja ragamar fito da dabarun kawo ƙarshen masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata miyagun laifuka a birnin na Abuja tare da dawo da zaman lafiya nan take".

    • 'Rashin haɗin kan gwamnatoci dama ce ga 'yan bindiga'
    • ‘Yan bindiga sun hana mu girbe amfanin gona‘
  20. Kundin Guinness na binciken tabbatar da shekarun karen da ya fi tsufa a duniya

    Wani kare mai suna Bobi ya karaɗe manyan shafukan jaridu a shekarar da ta gabata a lokacin da kundin bajinta na Guinness World Records ya naɗa shi a matsayin kare mafi tsufa a duniya - inda ya ƙwace kambun daga karen da ya shafe tsawon ƙarni kan matsayin.

    Bobi ya mutu a watan Oktoba yana da shekara 31 da kwana 165. Sai dai a yanzu ana kokonto kan wannan matsayi bayan da wasu likitocin dabbobi suka yi ayar tambaya kan shaidar da ta tabbatar da shekarun Bobi.

    Kundin bajintar ya dakatar da matsayin inda ya ƙaddamar da bincike.

    Bobi nau'in kare ne da ke iya rayuwa tsawon shekara 12 zuwa 14.

    A shekarar da ta gabata, Guinness ya ce shafin ƙididdigar dabbobi na gwamnatin Portugal da ƙungiyar likitocin dabbobi ke kula da shi ne ya tabbatar da shekarun karen.

    Sai dai yaɗuwar labarin naɗa shi kan wannan matsayin ya janyo shakku.

    Wani bincike da mujallar Wired ta yi ya gano cewa an yi wa Bobi rajista a shafin ƙididigar dabbobin a Portugal kasancewar an haife shi a 1992 sai dai babu alƙaluma da za su iya tabbatar wa ko musanta hakan.

    Akwai kuma tambayoyin da aka yi game da tsofaffin hotunan karen da ke nuna mabanbantan alamomi a kan gashinsa inda wasu ke cewa wani karen ne na daban.