Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Habiba Adamu, Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, Mukhtari Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. An samu raguwar masu shan taba sigari a duniya - WHO

    An samu raguwar masu shan taba sigari daga mutum guda cikin kowanne uku zuwa mutum daya cikin kowanne biyar a duniya, a cewar hukumar lafiya ta duniya.

    Hakan na kunshe ne a wani rahoto da hukumar ta fitar a ranar Talata.

    Rahoton shi ne na baya-bayan nan da ya yi nazari a kan shan taba a shekarar 2022.

    WHO ta ce fiye da mutane miliyan bakwai ne ke mutuwa duk shekara a duniya sakamakon shan taba sigari.

    Inda a ciki hukumar lafiyar ta yi kiyasin cewa sama da mutum biliyan daya da miliyan 200 ne ke shan taba a duniya.

    Rahoton ya nuna cewa kasashe 150 na duniya sun samu nasarar rage masu shan taba, inda kasar Brazil da Netherlands ke kan gaba.

    Nasarar da ta alakanta da aiwatar da manufofin da ke dakile shan sigari, duk da yukurin da kamfanonin sigarin ke yi na kawo nakasu.

    Rahoton ya kuma ce kudu-maso-gabashin Asiya shi ne kan gaba da 26.5% na masu shan sigari a duniya.

    Sai nahiyar Turai da ke biye da ita da kashi 25.3%.

    Amma rahoton ya nuna cewa mata masu shan tabar yawansu ya ninka ne a nahiyar Turai.

    Haka kuma ba a samu wani sauyin azo a gani ba dangane da raguwar masu zukar taba sigari a wasu kasashen duniya tun 2010.

    Yayin da kasashe shida kuma karuwa masu shan tabar suka yi, wato a Congo, Egypt, Indonesia, Jordan, Oman, da jamhuriyyar Moldova.

    Masana kiwon lafiya sun ce shan taba sigari na janyo wasu manyan cututtuka da suka hada da cutar sankara ko kansa, ciwon zuciya, ciwon huhu da sauransu.

  2. AS Roma ta raba gari da Jose Mourinho

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta A.S Roma ta kori Jose Mourinho daga aikin kocinta inda kulob ɗin ke mataki na tara a gasar Serie A.

    Mourinho ɗan asalin Portugal mai shekara 60 ya karɓi ragamar ƙungiyar a Mayun 2021 inda bayan shekara ɗaya ya jagoranci Roma ga lashe kofin Europa Conference League da kofin Europa League a 2023.

    Sai dai maki biyar kawai ya rage wa Roma ta samu shiga wasan ƙarshe na gasar zakaru ta Serie A kuma a makon da ya gabata ne aka fitar da su daga gasar Coppa Italia.

    Mamallakan kungiyar Dan da Ryan Friedkin sun yaba wa Mourinho saboda "jajircewar da ya nuna a matsayin shugaban ƙungiyar.

  3. Kotun ƙoli za ta sanar da ranar yanke hukunci kan zaɓen Nasarawa

    Kotun ƙoli ta ce za ta sanar da ranar da za ta raba gardama a ƙarar da David Ombugadu na jam'iyyar PDP ya ɗaukaka domin ƙalubalantar nasarar gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.

    A ranar Talata ne kotu ƙarƙashin mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta ce za ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci a ƙarar.

    A shekarar da ta gabata, hukumar zaɓe INEC ta ayyana Sule a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen ranar 18 ga watan Maris.

    Sule ya samu ƙuri'u 347,209 inda ya doke abokin karawarsa na PDP Ombugadu wanda ya samu 283,016.

    Sakamakon zaɓen da bai yi masa daɗi ba ne ya sa ɗan takarar na PDP ya je kotun ƙararrakin zaɓe don ƙalubalantar matakin INEC na ayyana Sule a matsayin wanda ya yi nasara.

    Wata bakwai bayan nan, kotun ta soke nasarar Sule inda ta ayyana Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaɓen na ranar 18 ga watan Maris.

    Hakan ya sa gwamna Sule ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara a Abuja wadda ta soke hukuncin kotun ƙararrakin zaɓen inda ta sake ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

    A yau ɗin ne kuma, Kotun ƙolin ta ɗauki irin wannan matakin kan ƙarar da ɗan takarar gwamna a zaɓen Kebbi, Manjo Janar Aminu Bande na PDP ya shigar yana ƙalubalantar nasarar Nasir Idris na APC a matsayin gwamnan jihar.

  4. Kotu ta yanke hukuncin mayar wa Najeriya fam miliyan 6.9 da aka sace

    Hukuncin kotun ya ce za a iya maido wa Najeriya kadarorin satar da darajarsu ta kai £6.9m ($8.9m).

    Hakan ya zo ne bayan atoni-janar na Jersey ya miƙa wa kotun Ingilar da ke tsibirin takardar sallamawa a watan Nuwamba.

    Kotun ta yanke hukuncin cewa kuɗaɗen da aka ajiye a wani asusun banki a Jersey, akwai yiwuwar jami'an gwamnatin (Goodluck Jonathan) da ta yi mulki a shekarar 2014 ne suka sace su.

    Za a yi yarjejeniya da gwamnatin Najeriyar kan maido da kuɗaɗen.

    An tura kuɗaɗen ne inda aka fake da cewa na wasu kwangilolin sayen makamai ne da gwamnati ta amince da su a lokacin rikicin Boko Haram a ƙasar, tsakanin shekarar 2009 zuwa 2015.

    'Mutanen da aka zalunta'

    Gwamnatin Jersey ta ce akwai yiwuwar mafi yawan kuɗaɗen an yi niyyar sayen makamai da su ne, amma aka karkatar da aƙalarsu ta asusun bankunan ƙasar waje ta hanyar kamfanonin Shell.

    Ofishin babban mai shari'ar ya kuma ce ya yi amanna cewa an ba iyalan jam'iyya mai mulki (PDP) a Najeriya kuɗaɗen, kuma aka rarraba su ga ƴan jam'iyyar a lokacin babban zaɓen 2015.

    Haka kuma an yi niyyar amfani da kuɗaɗen ne ta hanyar da "bata dace ba".

    Babban mai shari'ar, Mark Temple KC, ya ce gwamnatin Jersey ta yi aiki "kafaɗa-da-kafaɗa" da gwamnatin Najeriya don ganin an karɓo kuɗaɗen a madadin ƴan ƙasar ta Najeriya.

    Ya ƙara da cewa: "Wannan shari'ar tana ƙara nuna tasirin dokar sallamawa ta shekarar 2018 wajen karɓo kuɗaɗen rashawa tare da mayar da su ga mutanen da aka zalunta.

    "A halin yanzu na yi niyyar shiga yarjejeniyar yadda za a mayar da kuɗaɗen Najeriya ."

  5. Yadda gobara ta ƙona masallaci tare da ɗaiɗaita mutum 120 a Kwara

    Wata gobara da ta tashi a ƙaramar hukuar Ilori ta Kudu a jihar Kwara ta ɗaiɗaita mutum 120 tare da ƙona ɗakuna 44 na wani gini da masallaci.

    Shugaban sashen yaɗa labarai na hukumar kashe gobara, Hassan Adekunle ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Litinin a Illorin, babban birnin ƙasar.

    Jaridar Premium Times ta ruwaito jami'in yana cewa hukumar kashe gobara ta jihar ta kai ɗauki zuwa gidan Megida Onikanhun a ƙaramar hukumar Illorin ta Kudu.

    "Masu kashe gobara da isar su sun ga wuta ta laƙume ginin baki ɗayansa saboda an yi kiran wayar a makare." a cewar sa.

    Ya ce masu kashe gobarar sun rushe katangar ginin domin samun damar kashe gobarar yadda ya kamata.

    A cewar snarwar, bincike ya nuna cewa wani mutum ne ya kyasta wa shara wuta inda aka yi rashin sa'a wutar ta mamaye ginin.

    Mr Adekunle ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa zuwa wakilin Magaji Megida Onikanhun, Kuranga Adebayo.

    Ya kuma yaba wa jami'an kashe gobarar sai dai ya ce wutar ta ɗaiɗaita mutum 120 har da masallaci amma kuma ba a samu asarar rai ba a ginin mai ɗaki 75.

    Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Falade Olumiyiwa ya buƙaci jama'a da su ama masu taka tsan-tsan musamman a yanayin da ake ciki na hunturu.

  6. Trump ya lashe zaɓen fitar da gwani a jihar Iowa

    Donald Trump ya tabbatar da matsayinsa na wanda ke kan gaba a neman takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Republican inda ya lashe zaɓen fidda gwani na jihar Iowa.

    Duk da cewa ana kan ƙirga ƙuri’u ana hasashen cewa tsohon shugaban ƙasar zai doke abokan hamayyarsa da tazara mai yawa.

    Ana ci gaba da fafatawa a neman matsayi na biyu tsakanin tsohuwar jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley, da gwamnan jihar Florida, Ron DeSantis.

    Ƴan jam'iyyar Republican sun jure matsanancin sanyi a Iowa don halartar tarukan zaɓen da suka gudana a sassa daban-daban na jihar.

  7. Firaiministan Nijar ya isa Rasha domin haɓaka alaƙar soji – Rahotanni

    Firaministan Nijar ƙarƙashin mulkin sojoji, Ali Mahaman Lamine Zeine ya isa Moscow, babban birnin Rasha domin tattauna alaƙar tattalin arziki da ƙawancen soji tsakanin ƙasashen biyu, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

    Firaministan ya samu rakiyar Ministan tsaro Salihou Mody da takwarorinsa na mai da kasuwanci.

    Kafar yaɗa labarai ta intanet Mondafrique ta ruwaito cewa Zeine zai kuma je Turkiye da Iran da kuma Serbia.

    Majalisar tabbatar da tsaron ƙasa ta Nijar CNSP da ke fuskantar tsauraran takunkumai daga ƙasashen Yammacin Afirka, na neman faɗaɗa ƙawancenta, a cewar Mondafrique.

    Jaridar ta ce CNSP ta bayyana burinta ƙarara na janyewa daga tasirin ƙasashen yammacin Afirka farawa da janye alaƙar soji da take da shi da Faransa.

  8. Na girgiza matuƙa da kisan Nabeeha a hannun masu garkuwa – Oluremi Tinubu

    Mai ɗakin shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana kaɗuwarta kan mutuwar Nabeeha Al-Kadriyar, da ƴan bindiga suka halaka.

    A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, Sanata Oluremi ta bayyana mutuwar Nabeeha a matsayin rashi mai matuƙar sosa zuciya inda kuma ta miƙa ta'aziyyarta ga iyalan marigayiyar.

    Sanata Oluremi ta kuma buƙaci ƴan Najeriya su haɗa kansu wajen yin addu'oi da za su kai ga sakin ƴan'uwan Nabeeha, waɗanda har yanzu ke a hannun masu garkuwa.

    Da take magana kan ƙaruwar matsalar tsaro da sace-sacen jama'a, Oluremi ta yi kira ga hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi wajen hana satar jama'a su kuma yi duk mai yiwuwa domin kuɓutar da ƴan'uwan Nabeeha.

    A ranar 2 ga watan Janairu Nabeeha da ƴan'uwanta suka faɗa hannun ƴan bindiga a yankin Bwari da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

    Mahaifinsu Mansoor Al-Kadriyar, wanda shi ma ya shiga hannun masu garkuwar daga bisani sun sake shi domin ya dawo gida a haɗa kuɗin fansar ƴaƴansa.

    Sai dai masu garkuwa sun ƙara kuɗin fansar tare da kashe Nabeeha bayan da aka gaza haɗa kuɗin fansar.

    Sun kuma yi barazanar kashe ragowar ƴan matan da ke hannunsu idan aka ƙi biyan su kuɗi kafin wa'adin da suka ɗiba.

  9. 'Yan bindiga sun kai hari sansanin soji a Katsina

    Mazauna ƙauyen mahuta a jihar katsina a arewa-maso-yammacin Najeriya na tserewa daga gidajensu bayan wasu mahara sun auka wa wani sansanin soji da ke ƙaramar hukumar Batsari.

    Masu ɗauke da makaman fiye da ɗari sun kuma cinnawa motoci wuta a sansanin sojin, sannan suka bincike wurin gaba-ɗaya.

    Sansanin sojin na ɗauke da sojoji da kuma ƴansanda da sauran jami'an tsaro a lokacin da aka kai harin a daren Litinin.

    Jaridar Premium Times ta ambato wata majiya da ke cewa maharan sun ƙona motocin soji guda biyu, amma babu wani jami'in sojin da ya rasa ransa a lamarin.

    Wani mazaunin yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa masu ɗauke da makaman sun je yankin ne a kan babura da kuma wata babbar mota, sannan sun kwashe tsawon sa'oi uku suna bata-kashi da sojojin, kafin su ci ƙarfinsu.

    Haka kuma bayan harin kan sansanin sojin ne suka faɗa wa kauyen na Mahuta suka farfasa shaguna da gidaje suka kwashe kayan abinci da dabbobi da darajarsu ta kai miliyoyin naira.

    Harin ya janyo tashin hankali a tsakanin mazauna kauyen, lamarin da ya sa suka tsere zuwa wasu ƙauyukan maƙwafta domin su tsira da rayukansu, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

    Gungun masu ɗauke da makamai da ƴan fashin daji da ke satar mutane domin neman kuɗin fansa sun kashe ɗaruruwan mutane a ƙasar, duk da yunƙurin da sojoji suka ce suna yi na magance matsalar.

  10. Assalamu alaikum!

    Jama'a, barkan mu da safiya. Da fatan muna cikin ƙoshin lafiya.

    A wannan shafi, kamar kodayaushe, za mu kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa musamman Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai ku kasance tare da mu, kuna kuma iya zuwa shafukanmu na sada zumunta inda za ku ga ƙarin labarai.