Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Habiba Adamu, Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, Mukhtari Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Jama'a a nan muke cewa Allah Ya ba mu alkhairinsa.

    Da fatan kun ji daɗin labaran da muka kawo muku a yau.

    Sai kuma gobe cikin yardar Allah.

    Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.

  2. Fashewar wani abu ya janyo ruɗani a Ibadan

    Fashewar wani abu ya janyo ruɗani a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

    Fashewar da ta faru a yammacin Talatar nan, ta ruguza gine-gine da dama saboda mummunar jijjiga.

    Kafofin yaɗa labarai a Najeriya sun ruwaito cewa motoci da gidaje sun tarwatse a yankunan Awolowo, Bodija, Akobo da kuma sauran yankuna.

    Sai dai har yanzu ba a kai ga tabbatar da yawan waɗanda suka jikkata ba a lamarin.

    A wani sako da ta wallafa a shafin X, gwamnatin jihar ta Oyo ta ce ta samu labarin fashewar da ta afku a jihar.

    Gwamnatin ta buƙaci mazauna jihar da su kwantar da hankali yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike domin gano abin da ya janyo fashewar.

  3. Ƴan ci-rani 40 sun yi ɓatan dabo a tekun Italiya

    Dakaru a Tunisiya sun ce kusan ƴan ci-rani 40 sun yi ɓatan dabo yayin da da suke kan hanyarsu ta zuwa Italiya a jirgin ruwa a makon da ya gabata.

    Jami'an tsaron bakin teku tare da jiragen sama na ci gaba da laluɓen mutanen.

    Tunisiya ta zama babbar hanyar da bakin haure daga Afrika ke amfani da ita don shiga Turai da nufin tserewa fatara da tashe-tashen hankula.

  4. Rufe iyakar Nijar yana cutar da tattalin arziƙin Najeriya — Sanata Aliero

    Ɗan majalisar dattawa da ke wakiltar tsakiyar jihar Kebbi, Sanata Adamu Aliero, ya bayyana cewa ci gaba da rufe iyakar Jamhuriyar Nijar yana cutar da tattalin arzikin jihohin Najeriya da ke mawakbtaka da ƙasar.

    Aliero ya faɗi haka ne yayin tattaunawa da gidan talabijin na Arise, inda ya ce rufe iyakar Nijar bisa umarnin da ƙungiyar Ecowas ta bayar a matsayin abin da bai dace ba da kuma ya kamata a sake dubawa.

    Ya ce ƴan majalisa daga jihohin da abin ya shafa da ke arewacin ƙasar sun zauna sun tattauna kuma sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta buɗe iyakar da gaggawa domin ci gaba da harkokin kasuwanci.

    "Mutanen mu da ke zaune cikin al'ummomi da ke makwabtaka da iyakar Nijar su ne waɗanda ke ɗanɗana kuɗarsu.

    "Idan ka je kan iyakar a yau, za ka ga ɗimbin motocin dakon kaya da ke dawowa tare da kayayyaki daga ƙasashe daban-daban na tsaye a kan iyaka sun ƙasa wucewa saboda takunkumin Ecowas," in ji ɗan majalisar.

    Ya ce an take yarjejeniyar da aka cimma da Nijar kan yashe madatsar ruwan da ke samar da wutar lantarki lokacin da gwamnati ta yanke shawarar katse hanyoyin samar da wutar lantarki ga Nijar ɗin.

    Sanata Aliero ya ce yawancin ƙasashe ba su saka wa Nijar takunkumi ba kamar yadda Ecowas ta yi.

  5. Shirin 'yan wasan Super Eagles kan wasansu da Ivory Coast

  6. Amurka ta ce tana neman hanyoyin kwantar da tarzoma a Gabas Ta Tsakiya

    Amurka ta ce tana neman hanyoyin kwantar da tarzoma a yankin Gabas ta Tsakiya duk da hare-haren da take kai wa kan 'yan tawayen Houthi a Yemen.

    Mashawarci kan harkokin tsaron Amurkan Jake Sullivan, ya ce za a dogara kan Iran saboda irin tasirin da ta ke da shi kan 'yan tawayen da suke kai wa jiragen ruwa hare-hare a tekun Maliya da gaɓar tekun Aden.

    Jami'an ƙasashen Yammaci sun zargi Iran da aika wa ƴan tawayen Houthi da makamai da horas da su da kuma ba su bayanan sirri don su yi nasara a hare-haren da suke kai wa masu yi wa tattalin arzikin duniya barazana.

    Washington ta sanar da cewar dakarunta sun yi nasarar lalata makamai huɗu masu linzami na Houthi a sabon harin da ta kai.

  7. Buhari bai taɓa min katsalandan ba - Tinubu

    Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa wanda ya gada tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari bai taɓa yi masa katsalanda a gwamnatinsa ba tun bayan barin mulki.

    "Bayan miƙa mulki kai (Buhari) ka ce, 'Zan yi nesa da Abuja inda zan koma Daura amma idan kana buƙata ta, ka tuntuɓe ni. Ban yi katsalanda kan duk abin da kake yi ba. Ba zan matsa maka ba ko rike ka a wuya," kamar yadda Tinubu a taron kaddamar da wani litaffin kan sha'anin mulkin Buhari.

    Tinubu ya ce maimakon katsalanda, Buhari ya haɗa gwiwa da shi don ganin dimkraɗiyya ya wanzu a kasar.

    "Mun haɗa-kai don tabbatar da cewa dimokraɗiyya ya wanzu a Najeriya, Ina godiya.

  8. An tsare ƴan ci-ranin Habasha a Mozambique

    Mozambique ta tsare ƴan ci-rani 82 waɗanda suka fito daga Habasha bayan sun shiga ƙasar ba bisa ka'ida ba, a cewar jami'ai.

    Ƴan ci-ranin, waɗanda aka tsare a birnin Chimoio da ke lardin Manica, sun shirya bulaguro zuwa Afrika ta Kudu, in ji wani jami'in hulɗa da jama'a na hukumar kula da ƴan ci-rani a lardin, Abílio Mathe.

    Sassan Habasha ya fuskanci fari da kuma rikici mafi muni, abin da ya janyo ƙaruwar buƙatar jin-kai.

    Jami'ai a yankin Tigray da ke arewacin ƙasar sun ce mutum 225 ne yunwa ta kashe tun watan Yulin bara.

  9. Masana kimiyya sun yi halittar biri don binciken likitanci

    Masana kimiyya a ƙasar China sun yi halittar biri don binciken likitanci, wani nau'in da ake amfani da shi wajen binciken likitanci saboda ilimin halittarsa ​​yana kama da na mutane.

    Sun ce hakan zai iya hanzarta gwajin magunguna, kamar yadda dabbobi iri ɗaya suke ba da sakamako iri-iri, da ba da tabbaci sosai a cikin gwaji.

    Ƙoƙarin da aka yi a baya na samar da tagwaita halittar bai iya samar da abin da ake so ba ko kuma ana haifar birin ya mutu bayan 'yan sa'o'i.

    Wata ƙungiyar kare hakkin dabbobi ta ce ta damu matuka da ci gaban da aka samu.

  10. Ministocin Zambiya sun karɓi riga-kafin kwalera

    Wasu ministocin gwamnatin Zambiya huɗu sun karɓi riga-kafin cutar kwalera, yayin da ake ci gaba da ɗaukar matakan daƙile yaɗuwar cutar.

    Ministocin karkashin jagorancin ministar lafiya Sylvia Masebo, sun karɓi riga-kafin ɗigon baki ne a garin George da ke Lusaka, babban birnin ƙasar, bayan da Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar da tallafin allurar miliyan 1.7.

    Cutar ta lakume rayukan mutum kusan 400 tun watan Oktoba.

    "Masu kamuwa da cutar na raguwa wanda alama ce mai kyau. Ku daina kula da mutane a gidajenku, ku garzaya da su zuwa asibiti," in ji Ms Masebo a wani taron kaddamar da riga-kafin. Abun da za mu bai wa fifiko shi ne bai wa mutane riga-kafin a wuraren da cutar ta yi tsanani a Lusaka, wanda kiyasi yana da mutane miliyan uku, ta ƙara da cewa.

    A n samu mutuwar mutum 23 a Lusaka cikin sa'o'i 24 da suka wuce inda yara ƴan ƙasa da shekara biyar da kuma tsofaffi suka fi yawa,' a cewar Ms Masebo.

  11. Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaro

    Shugaba Bola Tinubu ya gana da hafsoshin tsaron Najeriya da kuma wasu manyan hukumomin tsaro a fadarsa da ke Abuja, a yau Talata.

    Hafsoshin tsaron da suka halarci ganawar sun haɗa da babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa, shugaban rundunar sojin ƙasa, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, shugaban sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar, da kuma shugaban sojojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla.

    Shi ma mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu na cikin waɗanda suka halarci taron.

    Sun tattauna kan batun ƙaruwar aikata ta'addanci, garkuwa da mutane da kuma kashe-kashe a faɗin ƙasar da nufin magance su.

  12. Ba a ga zuwan Ministan cikin gida hukumar ɗa’ar ma’aikata ba

    Ministan harkokin cikin gidan Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo, bai bayyana gaban hukumar ɗa’ar ma’aikata ta Najeriya ba, wadda ta gayyace shi don jin ba’asin zargin da ake yi masa na karɓar kwangila ta naira miliyan 438 a ma’aikatar jin ƙai.

    Tun a makon da ya gabata ne hukumar ta aika wa minsitan wasikar , inda take buƙatar ganinsa don yi mata bayani game da zargin.

    Sai dai yayin da hukumar ta sa ido don ganin mnistan a yau Talata, sai ya aika mata wasikar cewar ba zai samu damar halarta ba saboda wasu ayyuka da suka sha kansa, inda ya buuƙaci a ba shi wata rana da zai bayyana a gabanta.

    Ga rahoton Khalifa Shehu Dokaji

  13. Zargin ɗauke-ɗauke ya tilasta wa ƴar majalisa yin murabus a New Zealand

    Sabuwar 'yar majalisar New Zealand ta yi murabus saboda zarge-zargen cewa ta yi dauke-dauke, zargin da 'yansanda ke bincike a kai.

    An yi zargin cewa Golriz Ghahraman, 'yar jam'iyyar Green Party, ta yi sata har sau uku a wasu shagunan sayar da kayan sawa da dangoginsu biyu- daya a Auckland, dayan kuma a Wellington.

    Tsohuwar lauya a hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta kafa tarihi ne a 2017 a matsayin 'yar hudun hijira ta farko da ta shiga gwamnatin.

    Ta taba rike mukamin sashen shari'a na jam'iyyarta.

    Sai dai ta ce galabaitar da aikinta ke jefa ta ne ya sa ta aikata abin da ba halinta ba ne.

    "Na bai wa mutane da dama kunya don haka ina mai basu hakuri," In ji ta.

    Ms Ghahraman ta tsere ne daga kasar Iran lokacin tana yarinya tare da iyalinta, wadanda aka ba mafakar siyasa a kasar New Zealand.

    Murabus dinta a ranar Talata ya zo ne bayan wasu hotunan CCTV sun nuna lokacin da ake zargin ta dauki wata jakar mata ta kawa a shagon sayar da kayayyaki na Auckland.

    Ba a taba samun 'yar majalisar mai shekara 42 da aikata wani laifi ba.

    Yayin da yake mayar da martani kan murabus dinta, daya daga cikin shugabannin jam'iyyarta, James Shaw ya ce Ms Ghahraman ta fuskanci "munanan barazana da suka shafi cin zarafi, duka da kuma kisa tun lokacin da aka zabe ta a matsayin 'yar majalisa".

  14. Yunwa ta kashe sama da mutum 225 a Habasha

    Kimanin mutane 225 ne suka rasa rayukansu sakamakon fari da ya janyo yunwa a yankin Tigray da yaki ya daidaita a kasar Habasha, a cewar jami'ai.

    Jami'an lafiya a yankin sun sake yin gargadi kan karancin abinci da rashin ruwan sama da yakin basasa suka haifar.

    Kafar yada labaran yankin ta sanar da mutuwar akalla mutane 225 da suka hada da yara kanana da mata a birnin Edga Arbi kawai.

    Gwamnatin Tarayya ta musanta cewa ana gab da samun yunwa, wanda ka iya tsanani kamar wanda aka taba fuskanta a cikin shekarun 1980.

    Amma ta amince fari na shafar miliyoyin al'umma.

    A wani wurin kuma mutane 16 da yakin ya raba da muhallansu sakamakon yake-yaken basasan biyu sun rasa rayukansu saboda yunwa.

    A makonnin baya-bayan nan gundumomi da garuruwa a fadin Tigray sun bayar da rahotannin mace-mace a yankin.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutune miliyan 20 ne ke bukatar tallafin abinci saboda tashe-tashen hankula da fari da kuma ambaliya.

  15. 'Mai ƙwacen waya' da mota ta buge a Kano ya rasu

    Wani matashi da ake zargi da ƙwace wa wata mata waya a Kano ya rasa ransa sanadiyyar raunukan da ya samu bayan mota ta buge shi a lokacin da yake yunƙurin tserewa.

    A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na facebook, mai magana da yawun ƴan sandan Najeriya a jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce mutumin ya rasu ne a yau Talata a sibitin Murtala da ke Kano.

    A ranar Litinin rundunar ƴan sandan ta tabbatar da cewa wata mota ta kaɗe wani ɗan ƙwacen waya a titin zoo road da ke Kano.

    Bayan haka ne aka garzaya da shi asibiti, inda aka tabbatar cewa ya samu karyewar kashin baya da kuma fashewar kai.

  16. Ɓangaren marasa rinjaye a majalisar wakilan Najeriya ya nemi a hukunta wasu alƙalai

    Bangaren marasa rinjaye a majalisar wakilan Najeriya ya yi kira da a sanya takunkumai a kan wasu alkalan kotun daukaka karan kasar, wadanda ke da alhakin cire 'yan majalisar jihar Filato.

    Dan majalisa Chinda Kingsley, shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilan ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa a ranar Talata a Abuja.

    Inda ya jaddada cewa ya kamata a daure alkalan da suka yi shari'ar don ya zamo darasi ga sauran alkalan masu irin wannan tunani a nan gaba.

    A watan Nuwambar 2023 ne kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta kori baki-daya 'yan majalisar dokoki jihar ta Filato16, na jam'iyyar PDP.

    Kotun ta kore su ne saboda wasu dalilan da suka shafi matsaloli kafin zabe, zargin kin biyayya ga kotu da kuma rashin iya gudanar da mulki.

    Kafin sannan, kotun daukaka karar ta cire wasu 'yan majalisar wakilai daga jam'iyyar PDP su hudu da kuma sanatoci biyu.

    Kingsley ya kuma taya 'yan jam'iyyar adawar da suka samu nasara a kotun kolin kasar murna.

  17. Jiragen sama biyu sun sake yin karo a Japan

    Makonni biyu bayan karon da jirage biyu suka yi a Tokyo, babban birnin kasar Japan, an sake samun karon wasu jiragen biyu a ranar Talata.

    A cewar kafar watsa labarai ta gwamnatin kasar 'NHK', lamarin ya faru ne a filin jiragen sama na New Chitose a Hokkaido da misalin karfe 5:30 agogon kasar.

    Sai dai a wannan karon babu wanda hatsarin ya shafa.

    A cewar NCHK, hatsarin ya faru ne yayin da jirgin Koriya Ta Kudu da na Hong Kong, Cathay Pacific suka yi karo a filin jiragen.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani jami'in kamfanin jirgin saman Koriyan na cewa, yayin da jirginsu ke tashi ya yi karo da na Cathay Pacific, kuma akwai fasinjoji 289 a cikin jirgin saman Koriya Ta Kudun.

    Kafar watsa labarai ta NHK ta ambato kamfanin Cathay Pacific na cewa babu kowa a cikin jirginsa a lokacin da hatsarin ya auku.

    An soke tashin jirage da dama a filin jiragen saman na New Chitose bayan an samu hatsarin.

    • Yadda fasinjoji 379 suka fice daga jirgin sama mai ci da wuta cikin daƙiƙoƙi
    • Hatsarin jirgin Nepal: 'Direban jirgin bai bayar da rahoton komai ba kafin hatsarin'
  18. Wike ya kira taron gaggawa kan taɓarɓarewar tsaro a Abuja

    Ministan babban birnin Najeriya Nyesom Wike ya kira taron gaggawa kan taɓarɓarewar tsaro a Abuja.

    Ƴan bindiga a baya-bayan nan suna kai farmaki kan gidaje tare da sace mutane.

    Lamarin da ke ɗaga hankalin al'umma, ya kai maƙura ne bayan da aka samu labarin kisan Nabeeha - ɗaya daga cikin ƴan mata shida 'yan gida daya da ƴan bindiga suka sace a farkon watan nan na Janairu.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito Wike, a jawabin da ya yi a taron, yana yi wa mazauna birnin Najeriyar albishir da cewa za a tabbatar da tsaro a birnin.

    Ya ce gwamnati tana aiki da hukumomin tsaro domin dakile matsalar rashin tsaron.

    Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugabannin hukumomin tsaro a Abuja da kuma sarakunan gargajiya.

    Wike ya jaddada buƙatar hukumomin tsaro su sake lale su kuma ƙara ƙaimi domin shawo kan matsalar tsaron a yankin.

    • Yadda matsalar tsaro ta addabi al’ummomin Bwari a Abuja
  19. Jamhuriyar Benin ta karɓi kashin farko na riga-kafin maleriya

    Mahukunta a Jamhuriyar Benin sun ce ƙasar za ta karɓi kashin farko na rigakafin zazzaɓin cizon sauro - cutar da ke kan gaba wajen haifar da mutuwar yara ƙanana a ƙasar, kuma nan ba da jimawa ba za a fara yin rigakafin.

    Ministan lafiya na Benin, Benjamin Hounkpatin ya shaida wa manema labarai a filin jirgin sama na Cotonou cewa, maleriya cuta ce da ke yawan addabar mutane a ƙasar.

    Ya ce gwamnati a hukumance, ta karɓi allurai 215,900 na rigakafin cutar.

    A cewarsa za a soma ba da allurar nan da wasu ƴan watanni.

    A ƙasar ta Benin, kashi 40 cikin 100 na masu zuwa asibiti da kashi 25 cikin 100 na mutanen da aka kwantar na da alaƙa da zazzabin cizon sauro, a cewar ministan.

    Ya ce jarirai za su karɓi alluran sau huɗu - suna wata shida da wata bakwai da wata tara da kuma wata 18.

    Benin ce ƙasar Afirka ta uku da ta samu alluran rigakafin maleriya bayan Kamaru da Saliyo, bayan da aka ƙaddamar da shirin a Ghana da Kenya da Malawi ƙarƙashin kulawar hukumar lafiya ta duniya bisa tallafin shirin kawance kan alluran rigakafi na GAVI.

    An yi wa yara fiye da miliyan biyu rigakafin cutar a waɗannan ƙasashen Afirka uku abun da ya kawo raguwar mace-macen da ke da nasaba da maleriya, kamar yadda shirin GAVI ya bayyana.

    A cewar WHO, kusan kowane minti guda, ana samun yara ƴan ƙasa da shekara biyar da ke mutuwa sanadin cutar.

  20. Ana ci gaba da aikin ceton mutanen da suka nutse a hatsarin jirgin ruwa a Niger

    Hukumar kai agajin gaggawa ta jihar Niger, a Najeriya ta ce an samu ceto mutane goma, yayin da aka gano gawawwaki takwas.

    Mai magana da yawun hukumar, Ibrahim Hussaini ya tabbatar wa da BBC hakan.

    Ana ci gaba da aikin ceto don gano wadanda suke da sauran numfashi da kuma wadanda suka rasa rayukansu.

    Jirgin ruwan ya yi hatsari ne a karamar hukumar Borgu, kuma ana fargabar yana dauke da mutane kimanin 100 a lokacin da ya yi hatsarin.

    Hatsarin ya faru ne a ranar Litinin bayan jirgin ya taso daga Dugga Mashaya a jihar Niger da nufin zuwa kasuwar Wara da ke jihar Kebbi a arewa-maso-yammacin kasar.

    Rahotanni sun bayyana cewa jirgin na dauke da hatsi da wasu kayayyaki, baya ga mutanen da ke cikinsa.

    Matsalar hatsarin jiragen ruwa na sanadin mutuwar gwamman mutane duk shekara a kasar, lamarin da ake alakantawa da daukar mutane da kayayyaki fiye da kima da rashin ingancin jiragen ruwan da kuma rashin kyawun yanayi.

    • Ana ci gaba da aikin gano mutum 104 da jirgin ruwa ya kife da su a Taraba
    • Garuruwan da aka fi yawan samun hatsarin jiragen ruwa a Najeriya