CBN ya naɗa sabbin shugabannin bankunan Polaris da Union da Keystone
Babban bankin Najeriya CBN ya naɗa sabbin shugabannin wasu bankunan kasuwanci a Najeriya.
Wata sanarwa da CBN ɗin ya fitar a ranar Alhamis, ya ce bankunan da aka naɗa shugabannin sun haɗa da Polaris, Keystone da kuma Union.
Sanarwar ta CBN ta ce an naɗa Lawal Mudathir Omokayode Akintola, a matsayin shugaban bankin Polaris, sai Hassan Imam, wanda ya zama sabon shugaban bankin Keystone.
Sai kuma Yetunde Oni a matsayin shugabar bankin Union.
Naɗa sabbin shugabannin na zuwa ne bayan rusa kwamitocin gudanarwar bankunan da CBN ya yi saboda karya dokoki da suka yi, ciki har da shiga ayyukan da suke barazana ga harkokin kuɗi.
- CBN ya ce a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudi
- Me ya sa ake ƙarancin takardun naira a sassan Najeriya?