Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An yi jana'izar limamin masallacin Juma'a da aka harbe a jihar Filato

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Habiba Adamu and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafi, nan muka kawo karshensa a yau Laraba. Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    A madadin sauran abokan aiki, Umar Mikail da Badriyya Tijjani Kalarawi ke sallama da ku.

    Asuba ta gari.

  2. 'Yan sandan Kano sun kama matashi da zargin yi wa 'yar uwarsa ciki da kisanta

    Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta ce ta kama wani matashi mai shekara 19 da zargin yi wa 'yar uwarsa ciki a ƙaramar hukumar Tofa da kuma zargin haɗa baki wajen kashe ta.

    Wata sanarwa daga runundar ta ce ta kama Ukasha Muhammed ne bayan ta samu rahoton cewa ya yi wa Amina Bala mai shekara 19 ciki, sannan ya kai ta wajen wani mai suna Chidera Ugwu don ya yi mata allurar zubar da cikin.

    Sanarwar ta ce Mista Ugwu, wanda likitan boge ne, ya yi mata allura tare da ba ta wasu ƙwayoyin magani da zimmar zubar da cikin, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta.

    "An kama waɗanda ake zargin kuma sun amsa laifukan da ake zargin su da aikatawa," in ji runudnar.

    Ta ƙara da cewa da ma Ugwu ya saba yi wa mata masu ciki "allurar da ke kaiwa ga rasa rayukansu".

  3. Za a haramta wa Pistorius shan barasa idan an yi masa afuwa

    Za a haramtawa tsohon zarakaran wasan nakassau a Afirka ta Kudu, wato Oscar Pistorius da ke zaman kaso kan kisan budurwarsa Reeva Steemkamp , shan barasa ko hira da 'yan jarida idan aka sake shi daga kurkuku karkashin afuwar da za a yi masa.

    A na sa ran za a saki Pistorius a ranbar Juma'a, kamar yadda hukumomin gidan yarin da ake tsare da shi suka fitar da sanarwa.

    A shekarar 2013 ne, Pistorius ya yi harbi har sau hudu daga kofar bandaki a gidansa da ke babban birnin kasar Pretoria, a daren ranar masoya wato Valentines Day, harbin da ya yi ajalin Reeva.

    Kotun kolin Afirka ta Kudu ce ta yanke masa daurin shekara 13 a gidan kaso. A yanzu dai shekarun Pistorius 37, kuma tun da fari ya musanta zargin kisan na ta inda ya ce ya dauka wani ne ya yi mu su kutse a gidan.

    Karkashin dokokin Afirka ta Kudu, za a iya yi wa mai laifi afuwa, matukar ya yi rabin shekarun da aka yanke ma sa hukunci, wanda Pistorius ya yi hakan.

  4. Babu iyaka ko bin doka a hare-harenmu idan Isra'ila ta kawo mana yaƙi - Hassan Nasarallah

    A jawabin da ya gabatar kai-tsaye a gidan talbijin din Lebanon, shugaban kungiyar Hezbollah Hassan Rasrallah ya mika sakon ta'aziyya ga kungiyar Hamas kan mutuwar mataimakin shugabanta a Lebanon, Saleh Al-Arouri, inda ya ce kisansa "babban hadari ne".

    Ga kaɗan daga cikin muhimman batutuwan da ya taɓo a jawabin nasa:

    • Ya ce idan aka kuskura aka kaddamar da yaki kan Lebanon to za su fafata yaƙin da "ba shi da iyaka balle wat doka"
    • Nasrallah ya yi ikirarin matakin gaggawa da Hezbollah ta dauka ranar 8 ga watan Oktoba, da barin wuta a iyakokinta, ya taka wa hare-haren bama-bamai da Isra'ila ta yi nufin kai wa birki
    • Ya kara da cewa, shi ne karon farko da hakan ta faru tun shekarar 2006; lokacin yakin Lebanon, kuma Isra'ila za ta yi da-na-sani
    • Nasrallah ya sha alwashin daukar fansa, kuma ya ce kungiyarsa za ta mayar da martani matukar Isra'ila ta kaddamar da yaki a Lebanon
    • Ya kuma jinjina wa 'yan tawayen Houthi na kasar Yemen kan matakin da suka dauka na kai wa jiragen ruwa da ke ketara Tekun Maliya hari
    • Ya bayyana Al-Arouri da ''jajirtaccen shugaba'', kuma harin Isra'ila na yankan kauna ne ya kashe shi
  5. An yi jana'izar limamin masallacin Juma'a da aka harbe a jihar Filato

    Rahotanni daga jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya na cewa an yi janai’izar babban limanin masallacin Juma’a na Ndun da ke garin Tangur na ƙaramar hukumar Bokkos.

    An harbe Liman Muhammad Sani Idris ne a ranar Litanin da dare yayin wani hari da aka kai musu tare da ɗan uwansa, wanda a yanzu haka ke kwance a asibiti sakamakon raunin da aka ji masa.

    Kisan limamin na zuwa ne mako ɗaya bayan 'yan bindiga sun kashe mutum kusan 200 a garuruwa kusan 20, ciki har da Bokkos.

    Kazalika, rahotonni sun ce an kashe wani ɗan-acaɓa a kasuwar garin na Bokkos da misalin ƙarfe 7:00 zuwa 8;00 na safiyar yau Laraba.

    BBC ta yi ƙoƙarin ji daga bakin rundunar 'yan sanda reshen jihar ta Filato, amma kwamashinan 'yan sanda da kakakin rundunar ba su ɗaga kiran da aka yi musu ta waya ba.

    Shugaban ƙungiyar Fulani ta Miyyati Allah a yankin tsakiyar Najeriya na cikin mutanen da suka halarci jana’izar limanin, ya kuma faɗa wa BBC cewa suna zargin harin na ramuwar gayya ne.

  6. Shugaban Somaliland ya gana da shugaban Masar al-Sisi kan dambarwa da Habasha

    Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud ya shirya tattaunawa ta musamman tare da Shugaban Masar Abdul Fattah Al-Sisi, da kuma sarkin Qatar Tamim Bin Hamad Al Thani.

    Lamarin na zuwa ne kwana ɗaya bayan Jamhuriyar Somalialand ta sa hannu kan wata yarjejeniya domin bai wa Habasha damar shiga Tekun Maliya.

    Gidan talabijin na SNTV da ke ƙarƙashin kulawar gwamnati sun ce Mohamed da Sisi sun tattauna batun a wani shirinsu, wanda zai ƙarfafa hadin kai da kuma wasu abubuwan da za su amfani bangarorin biyu.

    Somalia ta yi alƙawarin kare iyakokinta sannan ta buƙaci majalisar tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Ƙungiyar Ƙasashen Afrika da su yi taron gaggawa kan batun.

  7. An tuhumi tsohon Shugaban Saliyo Emest Koroma da yunƙurin juyin mulki

    An tuhumi tsohon Shugaban Saliyo Ernest Bai Koroma da laifuka huɗu na cin amanar ƙasa da ke da alaƙa da yunƙurin juyin mulki.

    A watan Nuwamban da ya gabata ne 'yan bindiga suka kutsa rumubun ajiyar makamai da wasu wurare a birnin Freetown, inda suka saki fursunoni kusan 2,000.

    Ya musanta hannu a dukkan zarge-zargen da aka yi masa a harin, wanda ya yi sanadiyyar kisan mutum 20.

    BBC ta fahimci cewa wasu shugabannin Afirka ta Yamma sun yi ƙoƙarin ƙulla yarjejeniyar da za ta bai wa Mista Koroma damar komawa Najeriya idan aka amince a jingine tuhumar da ake yi masa.

    An nuna wa BBC wata wasiƙa wadda a ciki Koroma ya amince da yarjejeniyar, wadda ƙungiyar Ecowas ta ƙulla.

    Sai dai babu tabbas ko shugaban Saliyo Julius Maada Bio ya ba da umarnin aiwatar da yarjejeniyar ko kuma a'a.

  8. Wurin da bam ya kashe sama da mutum 100 a Iran

    Abin da muka sani zuwa yanzu shi ne bama-baman sun tashi ne a kusa da masallacin Saheb al-Zaman a kudancin birnin Kerman na Tehran.

    Kafar yaɗa labaran gwamnatin ƙasar ta ce harin na ta'addanci ne, wanda aka kai yayin da mutane ke taruwa don yin addu'o'in cika shekara huɗu da kisan Janar Qassim Soleimani na Iran.

    Bama-baman sun tashi a kusa da ƙabarin nasa.

    Amurka ce ta kashe janar ɗin a wani harin jirgi maras matuƙi a Iraƙi a watan Janairun 2020.

  9. Labarai da dumi-dumi, Mutanen da harin bam ya kashe a Iran sun haura 100

    Akalla mutum 103 ne suka mutu a harin bama-bamai biyu da aka kai kusa da kabarin Janar din Iran, Qassem Soleimani, ranar addu'o'in cikarsa shekara hudu da rasuwa.

    Kafar yada labarai Irib ta Iran ta ce gwamman mutane sun jikkata lokacin da bam din ya tashi cikin dandazon mutane a masallacin Saheb al-Zaman a kudancin birnin Kerman.

    Kafar yada labaran ta ambato mataimakin gwamnan Kerman na cewa harin na ta'addanci ne.

    Wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta ya nuna gawawwakin mutane birjik yashe a kasa.

    Kawo yanzu ba bu wata kungiya da ta dauki nauyin kai harin ko dalilin hakan.

    Sai dai a shekarun da suka gabata, kungiyoyi masu ikirarin jihadi da ba sa jituwa a yankin Gabas ta Tsakiya wato IS da na mabiya Sunni sun sha ikirarin kai munanan hare-hare kan jami'an tsaro da wurin bautar mabiya mazhabar Shi'a.

    Ana kallon Soleimani a matsayin babban mai fada-aji a Iran baya ga jagoran addini Ayatollah Ali Khamenei kafin kisan da Amurka ta yi masa a harin jirgi maras matuki a kasar Iraƙi a shekarar 2020,

  10. 'Na shafe wata ɗaya cur ban yi wanka ba'

    Yayin da ake ci gaba da gwabza yaƙi a Gaza, wasu da faɗan ya tilasta musu ƙauracewa gidajensu sun ce yanayin da suke ciki ya ta'azzara.

    Da take hira da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Zayda al-Breem ta ce rashin matsugunansu abu ne da za su iya jurewa sai dai jure wa rashin muhalli haɗi da matsanancin yanayi na sanyi abu ne da ke neman gagararsu.

    Al-Breem wadda asalinta 'yar Khan Younis ceamma yanzu tana Rafah, yankunan da ke kudancin Gaza - ta ce tana shafe dare tana rufe ƴaƴanta tare da matso da su kusa da ita. "Akwai wahala, matuƙar wahala."

    Wani ɗan Falasɗinu da shi ma ya rasa muhalli, Yaser Abu Riyaleh, ya ce ya shafe wata guda cur bai yi wanka ba.

    "A gida ina yin wanka sau huɗu a rana kuma ina iya shafe rana ɗaya cikin kogi," a cewar Riyaleh, wanda ya fito daga al-Shati da ke arewacin Gaza amma a yanzu yake samun mafaka a Rafah.

    Alia Ghaban daga Beit Lahiya a arewacin Gaza, ita ma ta yi magana kan makamantan batutuwan - sai dai ta ƙara da cewa ƴaƴanta sun yi rashin lafiya sosai.

    "Sun yi fama da amai da gudawa da tari da karkarwa saboda sanyi da ruwa ga shi babu kaya da bargo," kamar yadda ta shaida wa Reuters. "Babu komai, ba mu da lafiya, ƙirjinmu na ciwo saboda sanyi, babu abin da za mu ɗumama jikinmu."

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasta Falasɗinawa kusan miliyan biyu - kashi 85 cikin 100 na al'ummar Gaza sun rasa gidajensu tun bayan da yaƙi ya ɓarke a watan Oktoba.

  11. Ministar gwamnatin Buhari Sadiya Farouq za ta bayyana a gaban EFCC

    Rahotonni sun ce ministar jin-ƙai a gwamnatin Muhammadu Buhari, Sadiya Umar Farouq, za ta bayyana a ofishin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, bisa zargin almundahanar naira biliyan 37.

    Bayanai sun ce a makon jiya ne hukumar ta aika wa tsohuwar ministar goron gayyata sakamakon wani bincike da hukumar ta ƙaddamar a kan aikace-aikacen ma'aikatarta lokacin da take riƙe da muƙamin tsawon shekara shida.

    Ana bincikenta ne a kan zargin hannu a badaƙalar halasta kuɗin haram na fiye da naira biliyan 37 da miliyan 170, da wani ɗan kwangila James Okwete ya aikata.

    Wata majiya a EFCC ta tabbatar wa BBC cewa ba shakka hukumar ta gayyaci tsohuwar ministar amma bai yi wani ƙarin haske ba.

    Sadiya Umar Farouq ta fitar da wata sanarwa a ranar Litinin cikin makon jiya tana musanta zargin hannu a badaƙalar da ake zargin James Okwete da aikatawa, ta jaddada cewa ba ta ma san mutumin da ake magana a kansa ba.

    Jaridar Punch ta ce tuni hukumar EFCC ta gayyaci ƙarin jami'ai da suka yi aiki da Sadiya don samun ƙarin haske a kan yadda ma'aikatar ta tafiyar da al'amuranta a cikin shekara shida.

  12. Labarai da dumi-dumi, Bama-bamai sun kashe mutum 73 a kusa da kabarin Janar Qassem Soleimani

    A ƙalla mutum 73 ne suka mutu sanadin fashewar wasu abubuwa guda biyu, a kusa da kabarin Janar ɗin ƙasar Iran Qassem Soleimani a ranar tunawa da kisan da Amurka ta yi masa, kamar yadda kafofin labaran Iran suka ruwaito.

    Tashar yaɗa labaran, Irib ta ce mutum 171 ne suka ji raunuka sanadin fashewar, yayin wani jerin gwano a kusa da masallacin Saheb al-Zaman cikin birnin Kerman na kudancin ƙasar.

    Ta ruwaito mataimakin gwamnan Kerman na cewa abin da ya faru wani "harin ta'addanci ne".

    Wani bidiyo da ya karaɗe intanet ya nuna gawawwaki da dama a kan wani titi.

    Ɗaruruwan mutane ne aka ba da rahoton suna tattaki zuwa kabarin Souleimani ranar Laraba a wani ɓangare na zagayowar ranar tunawa da Janar Soleimani, wanda aka kashe a wani harin jirgin Amurka maras matuƙi a ƙasar Iraqi mai maƙwabtaka a shekara ta 2020.

    Ana ganin Soleimani a matsayin wani ƙusa mafi ƙarfin iko a Iran bayan Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

    A matsayinsa na kwamandan Rundunar Juyin-Juya-Hali da ke kula da ayyukan dakarun Ƙudus da kuma samar makamai, kuma shi ne jami'in da ke tsara manufofin Iraƙi a faɗin yankin Gabas ta Tsakiya.

  13. Hisba ta ce ta kama babbar mota maƙare da dubban kwalaben giya a Kano

    Hukumar hisba a jihar Kano ta ce ta kama wata babbar mota maƙare da kwalaben barasa sama da 24,000.

    Daraktan gudanarwar hukumar, Alhaji Abba Sufi ne ya bayyana haka ranar Laraba lokacin da yake duba motar da jami'ansa suka kama cikin dare a kan titin zuwa Zaria.

    Mallam Abba Sufi ya ce jami'an Hisba suna aiki tuƙuru wajen yaƙar masu safarar miyagun ƙwayoyi da barasa zuwa jihar ta iyakokin ƙasashe maƙwabta.

    Ya kuma yaba wa jami'an hukumar kan yadda suke haɗa kai da masu ruwa da tsaki wajen yakar masu safarar giya a Kano bisa tsarin shari'a.

    A nasa jawabin, wani jami'in hukumar Fu'ad Ɗorayi ya ce an kama matuƙin babbar motar da ƙarin mutum biyu.

    Hukumar Hizbah ta Kano ta saba kamawa da fasa kwalaben giya a jihar, saboda a cewarta yin hakan ya safara da shan barasa sun saɓa wa koyarwar Musulunci.

  14. An kashe Falasɗinawa 22,313 tun fara yaƙi a Gaza – Ma'aikatar lafiyar Hamas

    Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta saki sabuwar ƙididdiga kan yawan mutanen da suka mutu sakamakon yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza.

    Ma'aikatar ta ce mutum 22,313 ne aka tabbatar da mutuwarsu tun bayan da yaƙi ya ɓarke ranar 7 ga watan Oktoba sai wasu 57,296 da suka ji rauni.

    Sashen BBC na tantance sahihancin labarai a baya ya yi bincike kan yadda ake tattara alkaluman mutanen da suka mutu a Gaza.

    Isra'ila ta afka wa yankunan Falasɗinawa bayan da Hamas ta kai mata hari a jerin hare-haren da ta kai lamarin da ya halaka aƙalla mutum 1,200 sai mutum 240 da aka yi garkuwa da su.

  15. Jirgin helikwafta na sojin Uganda ya rikito kan wani gida

    Wani jirgi mai saukar ungulu mallakin rundunar sojin Uganda ya rikito kan wani gida da ke Lardin Ntoroko a yammacin ƙasar, lamarin da ya kashe gaba ɗaya mutanen da ke jirgin da mutum guda da ke cikin gidan, kamar yadda kakakin rundunar sojin Brigediya Janar Felix Kulayigye ya sanar.

    Kawo yanzu, ba a tantance abin da ya haddasa haɗarin ba.

    Jirgin ya yi hadari ne kusa da iyakar Uganda da Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo.

    Rundunar sojin ta Uganda ta sha kai hare-hare ta sama kan ƙungiyar IS da ke da alaƙa da mayaƙan ADF da suka kai hare-hare da dama a Ntoroko.

    Shugaba Yoweri Museveni ya buƙaci a samar da rundunar jami'ai masu sa kayan sarki domin tallafawa sojojin a yaƙin da suke da ƴan tawaye.

    • Yaran da ke ɗaukar ciki na ƙaruwa a Uganda saboda rashin ɗaure masu fyaɗe
    • Amurka na barazanar hukunta Uganda saboda dokar hukunta masu luwaɗi
  16. Yadda iska mai ƙarfin gaske ta yi ɓarna a sassan Birtaniya

    Bayan wata mahaukaciyar iska haɗe da ruwa da aka yi a wasu sassan Birtaniya ranar Talata, hukumomi sun gargaɗi jama'a game da yanayi da kuma tsaikon da za a fuskanta ta ɓangaren sufuri.

    A Ingila, hukumomi sun yi gargaɗin fuskantar ambaliyar ruwa a wuraren fiye da 300 yayin da iskar mai ƙarfin gaske ta kaɗa zuwa Scandinavia.

    Ga wasu hotuna da ke nuna irin ɓarnar da iskar ta yi a wasu yankuna.

  17. EFCC ta titsiye Halima Shehu ta hukumar NSIPA mai ba da tallafin dogaro da kai

    Bayanai sun ce hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC na ci gaba da binciken shugabar hukumar ba da tallafin dogaro da kai ta Najeriya - wato Social Investment Programme - da aka dakatar.

    A jiya Talata ne jami'an hukumar suka dira a ofishin Hajiya Halima Shehu tare da gudanar da bincike, daga bisani kuma ta isa ofishin EFCC, inda suka yi mata tambayoyi har cikin dare.

    Shugaba Tinubu ne ya dakatar da ita daga muƙamin babbar jami'ar hukumar NSIPA wata uku kacal bayan naɗa ta, da kuma tabbatar da ita a cikin watan Oktoba.

    A baya ta taɓa aiki da ma'aikatar jin ƙai ta tarayya daga 2017 zuwa 2022.

    Rahotanni sun ce shugabar ta NSIPA da aka dakatar na shirin gudanar da taron manema labarai ne a ranar Talata, lokacin da jami'ai daga hukumar EFCC suka je ofishinta a birnin Abuja.

    Jaridar Punch ta ambato wata majiya na cewa an samu rashin jituwa tsakanin Halima Shehu da ministar jin ƙai ta yanzu, Dr. Betta Audu tun lokacin da ta kama aiki saboda zargin cewa ziƙau ita kaɗai tana yin amfani da kuɗaɗen hukumar waɗanda aka tanada don bayar da tallafi ga ƙungiyoyin jama'a masu rauni.

    An kafa shirin ba da ƙwarewar dogaro da kai ne don tallafa wa miliyoyin 'yan Najeriya su fita daga cikin talauci da inganta harkokin cuɗanyar al'umma da kuma samar da sana'o'i ga talakawa da 'yan ƙasa masu rauni.

    Hukumar ce kuma ke da alhakin kula da shirye-shiryen yaƙi da talauci kamar shirin ciyar da ɗalibai 'yan makaranta na ƙasa.

    An ambato Halima Shehu a baya-bayan nan yayin wani taron manema labarai a Abuja, tana jaddada ƙudurinta na tabbatar da gaskiya wajen aiwatar da shirin ba da tallafin kuɗi dala miliyan 800 na Bankin Duniya.

  18. Masar ta goyi bayan Somalia a takun saƙar da take da Habasha

    Shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ya yi alƙawarin mara wa Somalia baya daidai lokacin da take takun saƙa da Habasha game da yarjejeniyar samun damar shiga teku da ta ƙulla da yankin Somaliland.

    A ranar Litinin ne Habasha ta ƙulla yarjejeniyar amfani da ɗaya daga cikin tashoshin jiragen ruwan Somaliland mai kwarya-kwaryar 'yanci, lamarin da ya janyo suka daga Somalia.

    Somalia wadda ke kallon Somaliland a matsayin yankinta, ta yi allah-wadai da yarjejeniyar inda ta bayyana matakin amatsayin tsokanar faɗa da kuma take ƴancin cin gashin kanta.

    Somaliland ta ɓalle daga Somalia a 1991 sai dai ƙasashen duniya ba su amince da ita a matsayin ƙasa ba.

    A wani kiran waya da ya yi da shugaban Somalia, Hassan Sheikh Mohamud, Mr Sisi ya yi alƙawarin Masar za ta tsaya a bayan Somalia tare da tallafa mata ta ɓangaren tsaro kamar yadda kakakin Mr Sisi, Ahmed Famy ya bayyana jiya Talata.

    Ya ƙara da cewa shugabannin biyu sun kuma tattauna batutuwan da suka shafi yankunansu da kuma ci gabansu.

    Shugaba Mohamud ya kuma yi magana ta waya da Sarkin Qatar, Tamim bn Hamad game da alaƙar ƙasashen biyu, in ji Fadar shugaban Somalia.

    Ƙungiyar Tarayyar Turai ta soki yarjejeinyar inda ta nemi a mutunta hadin kan Somalia da ƴancinta.

    Cikin sanarwar, Tarayyar Turai ta ce wannan muhimmin abu ne ga zaman lafiyar ƙasar ta kusurwar Afirka.

  19. Ana zargin Boko Haram da kashe fararen hula 12 a Chibok

    Wasu mutane sanye da kakin soji da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutane 12 a kauyukan Tsiha da kuma Gatamarwa da ke karamar hukumar Chibok a jihar Borno, Najeriya.

    Mazauna kauyukan sun bayyana wa jaridar Daily Trust cewa maharan sun dinga harbin mai uwa-da-wabi, lamarin da ya kai ga mutuwar mutanen, sannan suka yi awon gaba da mutum guda.

    Rundunar 'yan sandar jihar ta ce an samu gawarwakin mutanen da suka rasa rayukansu a harin.

    Yayin da kuma ta fara bincike kan lamarin domin gurfanar da wadanda ake zargi da kai harin.

    Bayanai sun nuna cewa maharan masu yawan gaske sun aukawa kauyukan ne a ranar Litinin da ta wuce.

    • Matsalar rashin tsaro ta fara sauƙi a jihar Katsina
    • Yadda ƴan bindiga ke karban haraji daga 'yan gudun hijira a Neja
  20. Hukumar ICPC ta fara bincike kan 'digiri ɗan Kwatano'

    Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC, a Najeriya ta ce ta fara bincike kan zargin samun shaidar karatun digiri ba bisa ka'ida ba a jami'ar Cotonou da ke jamhuriyar Benin.

    ICPC ta bayyana hakan ne a shafinta na intanet, inda ta ce shugaban hukumar Dr. Musa Adamu Aliyu, SAN, ya kira wani taro a kan batun, a ranar Talata.

    Binciken zai shafi jami'ar Ecole Superieure de Gestion et de Technologies (ESGT) ta Cotonou wadda ake zargin tana bayar da shaidar digiri a kasa da mako shida.

    Hukumar ta ce za ta yi binciken don gano hanyoyin da ake bi domin yin badakalar da zummar kawo gyara a tsarin karatun.

    Sannan za ta yi hadin guiwa da hukumomi na cikin gida da na waje domin tabbatar da ingancin shaidar karatun tare da zakulo wadanda ke da hannu a al'amarin.

    Rahotan da ya bankado hakan ya yi zargin cewa ana samun kwalin karatun ba tare da bin hanyoyin da suka dace ba, kamar rashin gabatar da takardar bukatar yin karatu da rijista da karatun da kuma rashin rubuta jarrabawa.

    Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin Najeriyar ta sanar da dakatar da karbar shaidar digiri daga Cotonou da kuma Togo sakamakon badakalar.