An yaba wa shahararren mai daukar hoto na Afrika ta Kudu kuma dan rajin yaki da nuna wariyar launin fata, Peter Magubane a kan gudunmawar da ya bayar wajen ƙwato 'yancin ƙasar, bayan rasuwarsa a ranar Litinin.
Ya mutu yana da shekara 91 a duniya.
Magubane ya dauki hoton wasu manyan abubuwan da suka faru a lokacin yaƙi da wariyar launin fata, ciki har da juyin-juya-halin Soweto na 1976, lamarin da ya kai ga kisan daruruwan dalibai bakaken fata.
Aikinsa ya janyo masa bakin jiji a wurin hukumomin wariyar launin fata, abin da ya kai ga tsare shi a kebe har tsawon kwana 586 kuma aka haramta masa daukar hoto na tsawon shekara biyar.
Ministan harkokin wasanni da al'adu na kasar, Zizi Kodwa ya yaba wa Makubane da cewa " zakakurin dan jarida ne mai daukar hoto kuma mai fafutukar samun 'yanci, wanda kuma ba tare da tsoro ba ya fito da irin zaluncin da aka yi a lokacin wariyar launin fata."
"Dr Magubane ya yi amfani da abin daukar hotonsa a matsayin wani makami na nuna kin amincewa, kuma bai taba bayar da kai ba ga masu mulkin danniya," Inji Mista Kodwa.
"Za a yi kewar hazakar Magubane da bajintarsa da kuma fitacciyar gudunmawar da ya bayar a aikin jarida," A cewar kungiyar Editoci ta kasar Afrika ta Kudu (Sanef).
Magubane ya taba zama mai daukar hoton gwarzon nan kuma jagorar neman 'yancin kai, Nelson Mandela na shekara hudu, bayan Mandelan ya fito daga gidan kurkuku a shekarar 1990.