Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Hukumar Alhazan Najeriya ta ƙara wa'adin biyan kuɗin aikin Hajjin 2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Habiba Adamu and Badariyya Tijjani Kalarawi

  1. Rufewa

    Anan muka kawo karshen shafinmu na kai-tsyae da muke kawo muku Labarai da rahotanni daga Najeriya da sauran kasashen duniya.

    Sai kuma gobe Laraba idan Allah ya kai mu.

    A madadin sauran abokan aiki, Badriyya Tijjani Kalarawi da Umar Mikail ke sallama da ku.

    Allah ya tashe mu lafiya.

  2. Ƙazamin faɗan da aka gwabza tsakanin Isra'ila da Hezbollah

    Fadan da aka gwabza a daren Talata tsakanin tsakanin sojin Isra'ila da na Hezbollah a iyakar kasar da Lebanon wani bangare ne na wanda suka fara tun bayan hare-haren Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

    Sojin Isra'ila da na Hezbollah da dama ne suka mutu a fafatawar da suka yi a iyakokin kasashen biyu, inda Isra'ila ta kwashe dubban farar hula daga arewacin kasar mai iyaka da Lebanon.

    A watan da ya gabata, ministan tsaron Isra'ila Benny Gantz, ya ce sojin kasar za su dauki tsattsauran matakin kakkabe Hezbollah daga iyakar kasar idan suka sake kai musu hari.

    Kasashen Yamma da Isra'ila da na Gabas ta Tsakiya har da kungiyar haɗin kan Larabawa na kallon Hezbollah a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

    Ƙasar Iran ce ke daukar nauyin ta da kudade, kuma tana daga cikin kungiyoyi masu karfin soji a duniya.

  3. Iran ta ce kisan jagoran Hamas a Lebanon zai zafafa kai wa Isra'ila hari

    Kasar Iran ta mayar da martani kan kisan babban jami'in kungiyar Hamas Saleh al-Arouri da Isra'ila ta yi a Lebanon.

    Mai magana da yawun ministan harkokin wajen Iran Nasser Kanaani, ya ce babu tantama harin da aka kai Beirut zai kara tunzura su kai wa Isra'ila hari.

    Kafar yada labaran Iran ta ambato Kanaani na cewa suna karfafa wa mayakansu gwiwar kai wa Isra'ila hari ba wai a yankunan Falasdinawa kadai ba har da yankin baki daya, da ma duk masu fafutikar neman 'yanci a duniya baki daya.

    Kasar Iran dai na goyon bayan kungiyar Hamas da Hezbollah da ke Lebanon.

  4. Mutanen da hari ya kashe a Lebanon sun zama shida

    Gidan talabijin na gwamnatin Lebanon ya ce mutanen da suka mutu a harin da ya kashe mataimakin shugaban Hamas a Lebanon sun kai shida.

    Tun farko an ba da rahoton cewa mutum huɗu ne suka mutu a harin.

    Kungiyar Hamas ta ce an kashe mataimakin shugaban reshenta na siyasa da ke Lebanon Saleh Al-Arouri sakamakon harin da Isra'ila ta kai a Beirut, babban birin kasar Lebanon.

    Kafafen watsa labaran Lebanon sun ce harin ya kuma yi sanadin mutuwar wasu mutum biyar.

    Hotunan bidiyo sun nuna wata mota na ci da wuta ga kuma wasu gine-gine a kusa sun yi kaca-kaca a unguwar Dahiyah wata sannaniyar matattara ga 'yan Hizbullah.

    Isra'ila dai ba ta tabbatar ko musanta kai wannan harin ba. Saleh Al-Arouri dai na daga cikin kwamandojin da suka kafa rundunar Al-Qassam - wato bangaren soji na kungiyar Hamas kuma an sha daure shi a gida yari a Isra'ila.

    An sake shi ne a watan Maris na 2010, a wani bangare na musayar fursononin Falasdinawa don sakin sojan Isra'ilan nan Gilad Shalit.

    A bangare guda kuma, Firaiministan Lebanon, Najib Azmi Mikati ya yi Allah-wadai da kai harin.

    Isra'ila ta zafafa kai hare-hare a Lebanon tun bayan afkawar shan mamaki da kungiyar Hamas ta yi ma ta, ranar 7 ga watan Oktobar bara, da ya yi sanadin mutuwar sama da Isra'ila 12,000 da safe sama da 200.

    Ko da ya ke an sako wasu daga ciki, ya yin da har yanzu Hamas din ke tsare da Isra'ilawan kamar dai yadda ita ma Isra'ilar ke tsare da dubban Falasdinawa maza da mata da kananan yara.

  5. Binciken da ya janyo dakatar da 'digiri ɗan Kwatano' a Najeriya

  6. An bukaci 'yan Kenya su sauya hanya saboda ƙarin kuɗin bin titi

    Hukumomi a Kenya sun shawarci direbobi da su yi amfani da wasu hanyoyin bayan ƙorafe-ƙorafen da aka samu game da ƙara kuɗin bin hanya wato toll gate a Turance da ke kan babbar hanyar Nairobi Expressway, a babban birnin ƙasar.

    Gwamnti ta ƙara harajin da ake karɓa na ƙofofin da kusan kashi 39 cikin 100 daga dala 2.29 zuwa dala 3.18 na hanyar da ta fi tsada.

    Matakin ya fusata jama'ar ƙasar, inda wasu ƴan Kenya ke cewa an tsuga kuɗi.

    Wasu kuma sun ce ƙarin na zuwa ne daidai lokacin da ake fama da tsadar rayuwa kuma matakin na zuwa ne bayan ƙarin haraje-haraje da gwamnati ta yi a bara.

    "An yi gyaran ne saboda yarjejeniyar aikin la'akari da faduwar darajar kuɗin ƙasar a kan dalar Amurka a watan Afirilun shekarar 2022,'' in ji Ministan Sufurin Kenya Kipchumba Murkomen, a ranar Litinin.

    An gina babbar hanyar da aka gina da ta lakume dala miliyan 550, saboda rage cinkoson ababen hawa da ya munana cikin shekarun da suka wuce.

    Wani kamfani mai zaman kansa mai suna China Road and Bridge Corporation (CRBC) na hadin gwiwa da gwamnatin Kenya, shi ne ke karbar kudin a matsayin biyan bashin kudin da suka kashe wajen ginin toll gate din.

  7. Hukumar Alhazan Najeriya ta ƙara wa'adin biyan kuɗin aikin Hajjin 2024

    Hukumar Alhazan Najeriya ta tsawaita wa'adin biyan kuɗin aikin Hajji na 2024.

    Cikin wata sanarwa a yau Talata, jami'ar yaɗa labarai Fatima Sanda Usara ta ce yanzu wa'adin ya koma 31 ga watan Janairun 2024.

    Tun da farko hukumar ta haƙiƙance cewa za ta rufe karɓar kuɗin daga ranar 31 ga watan Disamba na 2023 duk da ƙarancin mutanen da aka samu.

    "An ɗauki matakin ne saboda ƙorafin da malaman addini suka yi, da hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi, da gwamnoni, da kuma sauran masu ruwa da tsaki," in ji sanarwar.

    Hukumar ta bayyana naira miliyan 4.5 a matsayin kuɗin aikin Hajjin na bana, farashi mafi tsada ke nan a tarihi.

  8. Labarai da dumi-dumi, Hamas ta tabbatar da mutuwar jagoranta a harin Lebanon

    Ƙungiyar Hamas ta tabbatar da mutuwar mataimakin shugabanta a Lebanon, Saleh al-Arouri, a harin da aka kai a kudancin birnin Beirut.

    An ce al-Arouri na cikin shugabannin ayyukan Hamas na soja.

    Cikin awa ɗaya da ta gabata ne aka samu labarin harin a unguwar Dahiyeh, inda ƙungiyar Hezbollah ke da ƙarfi.

    Kafar yaɗa labarai a Lebanon ta ce Isra'ila ce ta kai harin da jirgi maras matuƙi a kan ofishin na Hamas.

    An ruwaito cewa an jikkata wasu mutanen da dama.

  9. Manyan janar din Sudan na musayar zafafan kalamai gabannin sulhu

    Shugabannin sojin da ke yaki da juna a Sudan sun sha alwashi ci gaba da gwabza fada, daidai lokacin da ake kokarin shawo kan yankin da ya daidaita kasar.

    Manayan janarl din biyu wato Janaral Abdel Fattah al-Burhan da ke jagorantar rundunar sojin Sudan, da Janaral Hamdan Dagalo da aka fi sa ni da Hemete mai jagorantar sojin RSF, sun yi tsokacin a ranar Litinin da ta zamo ta tunawa da shkaru 68 da Sudan ta karbi 'yancin kai.

    Hemeti ya ce za su ci gaba da dannawa babu gudu ba ja da baya, za kuma su kawo karshen yakin bayan yin nasara kamar yadda 'yan Sudan suke muradi, da samar da kasar da za ta bai wa dukkan 'yan kasa 'yanci ba tare da nuna wariya ba.

    ''Sojojinmu za su murkushe sojin gwamnati, mun yi nasara a wurare da dama ciki har da birnin Khartoum, da Darfur, da Kordofan da kuma Jazira,'' in ji Memeti. Ya kuma yi alkawarin kare farar hula musamman a tsakiyar jihar Jazira da anan fadan ya fi zafi a halin yanzu.

    Ana sa bangaren shugaba Abdel Fatta al-Burhan, shi ma alwashin ya ci da jaddada nasarar da na su sojojin suka yi, da alkwarin kubutar da Sudan daga abin da ya kira ''hannun masu cin amanar kasa.''

    A baya dai ya yi kokarin sasantawa da shugabannin RSF, domin dorewar zaman lafiya a Sudan, sai dai hakan ba ta samu ba lokavcin da RSF suka fara kaddamar da yakin karbe iko da kasar a watan Afirilun shekarar 2023.

    Kalaman na su masu zafi na zuwa ne, bayan sun aminta da zaman a teburin sulhu a wannan watan, wanda shi ne karon farko tun bayan barkewar yakin watanni 9 da suka gabata.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane 12,000 aka kashe daga lokacin, ya yin da wasu m,iliyan 6 suka rasa muhallansu.

  10. Red Crescent ta ce harin Isra'ila ya kashe mutum biyar a ofishinta

    Ƙungiyar agaji ta The Palestinian Red Crescent Society (PCRS) ta ce an kashe mutum biyar tare da raunata uku sakamakon hare-haren Isra'ila a kan ofishinta da ke Khan Younis a kudancin Zirin Gaza.

    PCRS ta ce dakarun Isra'ila sun ɗauki lokaci suna kai wa hawa na takwas hari. Ta kuma ce jirgi maras matuƙi ya hari farfajiyar Asibitin Al-Amal da ke maƙwabtaka.

    Ta ƙarada cewa mutum 14,000 ne ke fakewa a wuraren biyu.

    BBC ta nemi ƙarin bayani daga rundunar sojin Isra'ila.

  11. 'Isra'ila ta shafe dare tana kai mana hare-hare a Gaza'

    Al'ummar Gaza sun ce jirage da tankokin yaƙin Isra'ila sun shafe dare suna kai hare-hare a kudancin yankin, kwana ɗaya bayan da Isra'ila ta ce za ta soma janye wasu daga cikin sojojinta.

    Ministocin Isra'ila sun ce yaƙin da ake a Gaza zai ci gaba tsawon watanni da dama amma janye wasu sojojin na nuna wani sabon babi a yaƙin inda wani jami'i ya ce Isra'ila za ta sauya salon dabarunta na yaƙin.

    Amurka ta ce hakan na nuna yadda a hankali aka rage kai hare-hare a arewacin Gaza.

  12. Isra'ila za ta kare kanta a gaban kotun duniya kan zargin kisan ƙare dangi a Gaza

    Isra'ila za ta bayyana a gaban kotun duniya don kare kanta kan zargin da Afrka ta Kudu ta yi mata na aikata "kisan ƙare dangi" a Gaza, a cewar kakakin gwamnatin Isra'ila.

    A ranar Juma'a ne Afrika ta Kudun ta shigar da ƙara a gaban kotun, wadda ita ce babbar kotun duniya.

    Fadar gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce ya zama dole ga ƙasar ta kare aukuwar "kisan ƙare dangi".

    Da yake mayar da martani, kakakin Isra'la, Eylon Levy ya bayyanawa taron manema labarai a ranar Talata cewa: "ƙasar Isra'ila za ta bayyana a gaban kotun duniya da ke Hague don wanke kanta daga ɓata sunan da Afrika ta Kudu ta yi mata na zubar da jini, wanda hankali ba zai ɗauka ba.

    "Muna tabbatar wa shugabannin Afrika ta Kudu cewa, za su ga sakayya abin da suka aikata."

    Afrika ta Kudu tana kakkausar suka ga matakan sojin da Isra'ila ke dauka a Gaza a tsawon yakin da ta kaddamar.

    Harin da Hamas ta kai kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba ne ya haifar da yakin da ake yi a halin yanzu tsakanin bangarorin biyu.

    Hamas ta kashe kimanin mutane 1,200 mafiya yawansu fararen hula.

    Kuma kungiyar ta yi garkuwa da wasu mutane 240.

    Yayin da fiye da mutane 22,000 mafiya yawansu kananan yara da mata aka kashe a Gaza a hare-haren da Isra'ila ke kai wa, a cewar ma'aikatar lafiya ta Hamas.

  13. Birmingham ta sallami Rooney daga matsayin koci

    An sallami tsohon kyaftin din ƙungiyar ƙwallon ƙafan Ingila Wayne Rooney daga matsayin kocin kungiyar Birmingham City; wata uku bayan fara aikin.

    An naɗa tsohon ɗan wasan gaban na Manchester United mai shekaru 38 ne a watan Oktoba bayan wani mataki mai cike da ka-ce-na-ce da Birmingham City ta ɗauka na korar wanda ya gabace shi wato John Eustace.

    Bayan Rooney ya karɓi ragwamar ƙungiyar ne, Birmingham ta ci wasa biyu kawai a cikin 15 abin da ya sa ta rikito zuwa mataki na 20 a teburin gasar Championship; gasar ƙwallon ƙafa mai daraja ta biyu a Ingila.

    Rooney dai ya taba zama kocin Derby County ta Ingila da kuma DC United a Amurka.

    • Wayne Rooney: Na ji tsoron cewa shan giya zai yi sanadin rayuwata ko ta wasu
    • Rooney na yunƙurin dawo da Birmingham Premier
  14. Somaliya ta bayyana yarjejeniyar Habasha da Somaliland a matsayin takalar faɗa

    Somaliya ta bayyana yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kasar Habasha da yankin Somaliland mai kwarya-kwaryar 'yanci kan samun damar shiga teku a matsayin "tsokanar fada".

    Yankin ya balle daga Somalia fiye da shekara 30 da suka wuce, amma kasashen duniya ba su amince da hakan ba.

    An bayyana cewa kasar Habasha za ta amince da cin gashin kan yankin a wani lokaci nan gaba, idan yankin ya bai wa sojojinta damar shiga gabar tekun.

    Sai dai Habashar ba ta bayyana wannan bangare na yarjejeniyar ba mai cike da sarkakiya.

    Amma ofishin firaiministan kasar, Abiy Ahmed ya ce kasar ta sanya hannu a yarjejeniyar da za ta bata damar shiga tekun don fadada hanyoyinta na ruwa.

    A baya Mr Abiy ya bayyana samun damar shiga tekun a matsayin " muhimmin batu" da ya shafi kasar.

    Mai bashi shawara kan sha'anin tsaro, Redwan Hussein, ya rubuta a shafinsa na X cewa, yarjejeniyar za ta bai wa kasar damar kai wa ga hayar sansanin sojin da ke tekun, amma bai yi karin bayani kan hakan ba.

    Yarjejeniyar fahimtar junar za ta iya kai wa ga yarjejeniyar da za a amince da ita a hukumance.

    Matakin da bangarorin biyu ke nuni da cewa wani babban ci-gaba ne ta fuskar diflomasiyya.

    Somalia, ta mayar da martani cikin fushi kan yarjejeniyar, saboda tana daukar yankin Somaliland bangare na kasarta.

  15. 'Rashin tausayi ne a ce sai mace ta je Abuja za a yi mata canjin suna a fasfo'

    Ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, ya soki lamirin jami'an hukumar kula da harkokin shigi da fice na ƙasar da ke neman mutane musamman matan aure su tafi babban ofishin hukumar da ke Abuja don yi musu canjin suna a fasfonsu.

    Da yake jawabi yayin wata liyafar cin abinci a Abuja, Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana lamarin da cewa rashin tausayi ne.

    Ya ce babu inda ake ganawa mata irin wannan wahala a ko'ina cikin faɗin duniya saboda kawai sun yi aure.

    “Akwai wani abin ban haushi da na lura da shi, inda wata mace ta yi aure, tana so ta canza sunanta, amma sai ta taso daga wuri kamar Ƙauran Namoda ko Enugu don kawai ta zo a yi mata canjin suna a fasfo. Wannan shashanci ne.

    “Na kasa gane wannan lamari, wai don kawai mutum yana son canjin suna amma sai ya taso ya zo Abuja. Na tambayi jami'an shigi da fice, shin su jami'anku na Abuja sun fi na jihohi basira ne?” ya tambaya.

    • Shugaban Najeriya ya yi alkawarin samar da biza ga 'yan Afirka
  16. Ƙarin hotuna daga wurin gobarar jirgin saman Japan

    Ga wasu sabbin hotuna daga Filin Jirgin Saman Haneda inda jirgi ya kama da wuta:

  17. Najeriya ta soke tantance takardun digiri na jami'o'in Benin da Togo

    Najeriya ta ce ta ɗauki matakin dakatar da tantance shaidar karatun digiri daga jami'o'in Jamhuriyar Benin da na Togo.

    Matakin ya zo ne bayan wani binciken ƙwaƙwaf da jaridar Daily Nigerian ta yi a baya-bayan nan, inda ta ce wakilinta da ya ɓad-da-kama, kuma ya samu takardar shaidar digiri daga wata jami'a a Jamhuriyar Benin a cikin mako shida kacal.

    Mai magana da yawun ma'aikatar ilimi ta Najeriya, Augustina Obilor-Duru cikin wata sanarwa da ta fitar, na cewa rahoton ya bayyana hanyoyin da wasu ƴan Najeriya ke bi domin samun takardar shaidar karatun digiri da nufin samun damamrmakin aiki da ba su cancanta ba.

    "Ma'aikatar ilimi ta koka da irin wannan ɗabi'a kuma daga ranar 2 ga watan Janairun 2024, ta dakatar da tantance takardun shaidar karatun digiri daga Benin da Togo har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

    "Binciken dai zai haɗar da ma'aikatar harkokin waje ta Najeriya da kuma ƙasashen biyu da ma'aikatun da ke kula da ilimi a ƙasashen da kuma hukumar tsaro ta farin kaya da hukumar kula da shirin matasa 'yan hidimar ƙasa, NYSC."

    Ma'aikatar ta yi kira ga yan Najeriya su ba da gudunmawa wajen samar da bayanan da za su taimaka wa kwamitin yayin da yake neman hanyoyin magance faruwar haka a gaba.

    Ma'aikatar ta kuma yi bayani kan ƙalubalen da take fuskanta game da matsalar bara-gurbin makarantun ƙetare ko a cikin gida waɗanda mutanen da ba su ji ba su gani ba, ke faɗawa tarkonsu ko kuma wasu ƴan Najeriya waɗanda da saninsu suke karatu a makarantun.

    Ma'aikatar ilimin ta ce za ta ci gaba da nazari domin toshe duk wata kafa da hanyoyi da tsare-tsare tare da ladabtar da jami'an da ke da hannu a irin wannan lamari.

    • Jami'ar Birtaniya za ta fara digiri na biyu a fannin tsafi
    • Me ya sa batun NYSC ɗin Hannatu Musawa ke tayar da ƙura?
  18. Bidiyon yadda fasinjoji suka yi fitar burgu daga jirgin Japan da ya kama da wuta

    Fasinjoji 379 da sauran ma'aikata da ke jirgin Japan Airlines sun samu nasarar kuɓuta daga jirgin kafin wuta ta mamaye shi.

    Ga wani bidiyo da ke nuna yadda fasinjojin suke tserewa ta benen roba da ake hurawa.

  19. Mutum biyar ɗin da ke cikin jirgin tsaron gabar teku sun mutu

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito ministan sufuri na Japan na tabbatar da mutuwar mutum biyar da ke cikin jirgin tsaron gaɓar teku da ya yi karo da wani jirgin fasinja da ya kama da wuta.

    Kafar yaɗa labarai ta NHK ma ta ba da rahoton mutuwar mutanen biyar.

    Direban jirgin ya samu tsira sai dai ya ji mummunan rauni.

    Ana tunanin jirgin da ke gadin gaɓar tekun yana kai kayan abinci zuwa yankunan da girgizar ƙasa ta shafa lokacin da ya yi taho mu gama da jirgin kamfanin Japan Airlines lokacin da yake sauka kan titin jirgi.

  20. Tinubu ya dakatar da shugabar hukumar kula da shirin bai wa matasa ƙwarewa ta ƙasa

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da dakatar da shugabar hukumar bai wa matasa ƙwarewa ta ƙasa, Ms Halima Shehu, tare da umarnin a gudanar da bincike a kan ta nan take.

    Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin ne saboda zargin ta da aikata ba daidai ba a lokacin da take shugabancin hukumar.

    Dr Akindele na shirin N-Power a yanzu zai maye gurbinta a matsayin shugaban riƙo har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

    Matakin dakatarwar na zuwa ne kusan watanni uku bayan da majalisar dattawa ta tabbatar da naɗin nata.

    Kafin naɗa ta kan muƙamin, ta yi aiki ƙarƙashin shirin rage wa al'umma raɗaɗin talauci sannan ta yi aiki a ma'aikatar jin ƙai da ci gaban al'umma ta ƙasa tsakanin 2017 da 2022.