Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo labaran abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya daban-daban.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Badariyya Tijjani Kalarawi and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Baturiyar zaɓe a jihar Maine ta kare matakin cire Trump daga takara

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Babbar jami'ar zaɓe a jihar Maine ta ce "wajibinta" be ta tabbatar da doka bayan wani hukunci da ya ce a cire Donald Trump daga ƙuri'un masu zaɓen 2024 a jihar.

    Shenna Bellows ta kafa hujja da tanadin dokar hana tawaye a Tsarin Mulkin Amurka don cire sunan Donald Trump, inda ta tunasar da matsayin da ya taka a boren da aka yi a Majalisar Dokokin Amurka a 2021.

    'Yar jam'iyyar Dimokrat ɗin ta faɗa wa BBC cewa tana fatan Kotun Ƙolin Amurka za ta fitar da matsaya a kan wannan batu.

    Kwamitin yaƙin nema zaɓen Trump ya ci alwashin ɗaukaka ƙara kan wannan shawara mai cike da ka-ce-na-ce.

    Jihohi guda biyu ne, Maine da Colorado a yanzu suka haramta wa tsohon shugaban ƙasar daga shiga takardun ƙuri'a. Duka hukunce-hukuncen za su dakata, har sai ƙararrakin da ke ƙalubalantarsu a kotuna sun samu shiga.

    Steven Cheung, wani mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen Trump ya bayyana shawarwarin Maine da Colorado a matsayin katsalandan a harkar zaɓe. Ya bayyana a ranar Alhamis cewa hukunce-hukuncen "wani farmakin ƙiyayya ne ga dimokraɗiyyar Amurka".

    Abokan neman takarar Mista Trump a jam'iyyarsu ta Rifablikan da wasu masanan shari'a su ma sun soki lamirin hukuncin. Sai dai Shenna Bellows ta nanata cewa ita ta bi doka kuma ta yi aiki ne da shaidun da aka gabatar mata.

    Ta faɗa a cikin umarnin da ta bayar, wanda aka wallafa a ranar Alhamis cewa dole ne a cire Mista Trump daga ƙuri'ar zaɓen fid da gwani na jam'iyyar Rifablikan saboda tanadin dokar hana tawaye mai lamba 14. Ta faɗa wa BBC cewa "alaƙar siyasa ko al'amura na baya" ba su da dangantaa da shawarar.

  2. Darajar Naira ta yi karyewar da ba ta taɓa yi ba a farashin gwamnati

    Naira bundles

    Asalin hoton, PRESIDENCY

    Darajar naira ta faɗi ƙasa warwas zuwa matsayi mafi ƙasƙanci da aka gani a shekarun baya-bayan nan, inda aka canzar da dala ɗaya a kan naira 1,043.09 a cibiyar hada-hada da farashin hukuma ranar Alhamis.

    Jaridar Daily Trust ta ce sabon farashin ya zarce na 872.59 a kan dala ɗaya da aka canzar da naira ranar Laraba a cibiyar hada-hadar kuɗaɗen waje ta Najeriya (NAFEM).

    Alƙaluma daga cibiyar hada-hadar kuɗaɗen ƙasashen waje ta FMDQ sun nuna cewa an samu ƙarin shigar dalar Amurka da kashi 38.81 zuwa dala miliyan 127.93 a ranar Laraba daga dala miliyan 92.16 a ranar Juma'a ta makon jiya.

    Masu saye da sayarwa da ke hada-hadar kuɗaɗen ƙasashen waje a cibiyar ta NAFEM ne suke kai dalar.

    Masharhanta sun fitar da ƙididdigar cewa Naira na cikin kuɗaɗen duniya waɗanda darajarsu ke ta yi matuƙar faɗuwa a shekara ta 2023.

  3. An kashe aƙalla mutum 28 a Ukraine sanadin hare-haren Rasha

    Rahotanni sun ce adadin mutanen da suka mutu sun sake ƙruwa bayan hare-haren makamai masu linzami da Rasha ta kai.

    Aƙalla mutum 28 aka kashe, a cewar gwamnatin Ukraine da kuma jami'an yanki.

    Sai dai, alƙaluman gaba ɗaya na yawan mutanen da suka mutu, suna shan bamban.

    Adadi mafi yawa na ɓarnar da hare-haren suka yi a wani yanki guda ɗaya shi ne wanda ake ji daga Zaporizhzhiaa, inda mutum suka mutu, a cewar Gwamnan yankin Yuriy Malashko.

  4. Birtaniya za ta bai wa Ukraine sabbin makaman tsaron sararin samaniya 200

    Birtaniya za ta samar da makamai masu linzami na tsaron sararin samaniya kimanin 200 ga Ukraine don taimaka mata wajen kare kanta daga hare-haren makamai da na jirage marasa matuƙan Rasha.

    Makaman masu linzami waɗanda aka yi su a Birtaniya, an tsara za a iya harba su daga jiragen yaƙi kamar Typhoon da kuma F-35, a cewar ma'aikatar tsaron ƙasar.

    Tallafin ƙari ne a kan na'urorin tsaron sararin samaniya da Birtaniya ta ƙera, waɗanda kuma aka bai wa Ukraine a shekarar da ta wuce.

    Birtaniya zuwa yanzu ta samar da tallafin dala biliyan 5.8 ga ƙoƙarin yaƙin da Ukraine ke yi.

  5. Bidiyon ɓarna da turnuƙewar hayaƙi bayan hare-haren Rasha a Kyiv

    Wani gidan ajiyar kaya na ɗaya daga cikin gine-gine da yawa, waɗanda hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙi suka faɗawa a birnin Kyiv.

    'Yan sanda sun buƙaci mutane su nemi mafaka yayin da aka lalata motoci, gobara ta tashi, ɓurɓushin wuta ya riƙa zubowa daga sama.

    Bayanan bidiyo, Hare-haren Rasha: Bidiyon na nuna tsananin ɓarnar da aka yi a Kyiv
  6. 'Yar Ghana mai son shiga kundin tarihi ta shafe kwana biyar tana rera waƙa

    Ghanaian TV Personality
    Bayanan hoto, Afua Asantewaa 'yar jarida ce, kuma furodusar talbijin sannan tana kasuwanci

    Ma'aikaciyar gidan talbijin a Ghana, Afua Asantewaa ta kammala bajintar rera waƙa tsawon kwana biyar da fatan hakan zai ba da ta damar shiga Kundin Tarihin Duniya na Guinness.

    Buɗaɗɗiyar murya, kuma lulluɓe da tutar ƙasarta, Afua ta gode wa ɗumbin magoya baya a Accra, babban birnin Ghana.

    A bayyane ƙarara cikin gajiya tilis, matashiyar 'yar shekara 33 da ƙyar take iya tuna ko wacce rana ce yau.

    Ta fara rera waƙa ne a ranar jajiberen Kirsimeti, inda ta zarce bajintar da wani mawaƙi a baya wanda ya yi ta waƙa kusan tsawon sa'a 24, amma dai sai ta jira don ta gani ko za a ga ƙoƙarin nata a sanya cikin kundin tarihin na duniya.

    Masu shirya bajintar waƙar, sun ce Misis Asantewaa ta yi ta zuba waƙa tsawon awa 126 da minti 52. Bisa ƙa'idojin da masu kula da kundin tarihi na Guinness World suka kafa, an ba da dama na yin hutun minti biyar ne a cikin duk awa ɗaya ko kuma minti 20 bayan awa huɗu.

    Da take jawabi cikin shaƙaƙƙiyar murya, Afua Asantewaa, wadda 'yar kasuwa ce kuma tsohuwar sarauniyar kyau, ta ce tana fata bajintar da ta yi "za ta kasance zaburaswa ga dukkan mata... su sauka daga kan abin da suka saba, su je su gwada sabbin damammaki... idan kika sa kanki, za ki iya komai".

  7. Shugaban 'yan sandan Najeriya ya kai ziyara Filato a kan hare-haren jajiberen Kirsimeti

    Nigeria police chief

    Asalin hoton, Nigeria Police Force

    Babban sufeton 'yan sandan Najeriya ya ba da umarnin tura jami'ai da kayan aiki na musamman zuwa jihar Filato kwanaki ƙalilan bayan hare-haren da suka yi sanadin kashe kusan mutum 200.

    Babban Sufeton Kayode Adeolu Egbetokun ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na sada zumunta, wadda ta sanar da ziyarar da shugaban 'yan sandan ya kai zuwa jihar ta Filato.

    Ya kuma ba da umarni ga mataimakin babban sufeto shiyya ta 4 ya koma jihar Filato da aiki nan take.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira ga hukumomin Najeriya su gudanar da bincike kan hare-haren na jajiberen Kirsimeti

  8. Ana fargabar Habasha za ta fuskanci yunwa saboda yaki

    Mata sun fi shan wuya lokacin yaki

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'ai a Habasha sun ce mummunann yakin da ake fama da shi a yankin Tigrayzai janyo annobar yunwa da aka jima ba agani ba tun shekarun 1984-85, da ya sanya sai da aka bude kokon bara domin tara kudin talklafawa kasar.

    A wata sanarwa da gwamnatin rikon kwarya a yankin Tigrayda aka samar a farkon wannan shekarar ta fitar, ta ce shekaru biyu da aka dauka ana tashin hankalin, ya janyo bakar yunwa ta samu wurin zama a yankin baya ga mace-macen da rashin abincin ya haddasa.

    Ana jin radadin yakin da ya tilastawa dubun-dubatar farar hula tserewa muhallansu, sannan fari ya janyo kashi 91 cikin 100 na al'ummar yankin ke barazanar shiga mawuyacin hali.Jami'an yankin sun sha fadar sama da mutane 1,000 ne suka mutu sakamakon bakar yunwa a watannin da suka gabata.

    A watan Nuwamba da ya wuce, Amirka da Majalisar Dinkin Duniya suka sanar da dawo da shirin tallafin abincin da suke kai wa Habasha wanda aka dsakatar da shi sakamakon zargin sacewar da ake yi.

    A karshe gwamnatin rikon yankin Tigray din ta yi kira ga gwamnatin Habasha da kasashen waje su kawo musu dauki.

  9. 'Ƴan sandan Sarauniya suna zubar da mutuncin 'yan sandan Najeriya'

    ...

    Asalin hoton, FACEBOOK/NIGERIA POLICE FORCE

    Hukumar kula da aikin 'yan sanda a Najeriya ta koka kan abin da ta kira rashin nuna ƙwarewa da ƴan sandan sarauniya ko kuma 'yan sandan sa-kai ke nunawa, a ƙoƙarin da suke yi wajen tallafa wa tsaron al'umma.

    Hukumar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwar da shugaban yaɗa labaranta, Ikechukwu Ani ya fitar, inda ta nemi a canza wa 'yan sandan sarauniya kaki ko inifom, ko kuma a rushe ayyukansu a jihohi matuƙar ba za a riƙa biyan su haƙƙoƙin aiki da kuma kula da su ba.

    A cewar hukumar, akwai hatsari a bai wa 'yan sandan sarauniya bindiga, kuma a ba su lasisin samar da tsaro da tabbatar da doka da oda a jihohi da yankunan ƙasar, ba tare da biyan su albashi ba.

    Hukumar ta gano cewa 'yan sandan sarauniya suna karɓar cin hanci a hannun ƴan Najeriya ta hanyar tilastawa da kuma tsoratarwa.

    Ta kuma ce hankalinta bai kwanta ba da tsarin rundunar 'yan sandan sarauniya ta musamman da kuma yadda take tafiyar da ayyukanta a faɗin Najeriya.

    Ta ce tuni ta tuntuɓi babban sufeton ƴan sandan Najeriya game da buƙatar sauya fasalin rundunar da kuma ayyukanta.

    A cewar hukumar, sauya musu kaki, zai taimaka sosai wajen sa ido kan ayyukansu, da ma sauran jami'an ƴan sanda tare da tsame rundunar ƴan sandan Najeriya daga zargin da take sha saboda rashin ɗa'ar 'yan sandan sarauniya.

    An ruwaito Shugaban hukumar ta PSC, Solomon Arase wanda tsohon jami'in ɗan sanda ne yana cewa hukumarsa za ta yi aiki tare da shugabancin rundunar ƴan sanda ta ƙasar domin tsaftace ayyukan 'yan sandan sarauniya.

  10. Adadin yaran da aka haifa a Gombe cikin wata goma a sanin hukuma

    Hukumar ƙidaya ta Najeriya ta ce yaran da aka haifa 424,302 ta yi wa rijista a cikin jihar Gombe, tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamba.

    Daga cikin jariran da aka yi wa rijistar haihuwar, 187,283 ko kashi 44.13 mata ne, yayin da maza suka kasance 237,019 ko kuma kashi 55.86.

    Jaridar Punch ta ruwaito shugaban sashen yin rijista da tattara muhimman alƙaluma na hukumar ƙidaya ta ƙasa reshen jihar Gombe Mista Adedeji Adeniyi lokacin da yake bayar da ƙarin bayani kan alƙaluman yau Juma'a a jihar Gombe.

    Ya ce an yi rijistar haihuwar ce a cibiyoyi fiye da 100 na jihar kuma an yi ƙananan yara daga kan jarirai sabbin haihuwa har zuwa 'yan shekara 17.

    Mista Adedeji Adeniyi ya ce mutum 76,900 na waɗanda aka yi wa rijistar ƙananan yara 'yan ƙasa da shekara ɗaya, kuma ya ce 33,760 daga cikinsu mata ne sai maza kuma 43,140.

  11. Ukraine ta tabbatar da mutuwar mutum 16 bayan hare-haren Rasha

    Babban mai gabatar da ƙara a Ukraine ya ce zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutum 16 a luguden wutar da Rasha ta kai Ukraine.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, Andriy Kostin ya ce Rasha ta ci gaba da kai hare-hare kan farar hula inda ya ce mutum 97 ne suka ji rauni, har da ƙananan yara biyu.

    Ya bayyana cewa ɓarnar ta shafi gine-ginen jama'a da makarantu da asibitoci da wasu muhimman wuraren.

  12. MDD ta yi allah-wadai da munanan hare-haren da Rasha ta kai Ukraine

    ..

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    Wakiliyar Majalisar Ɗinkin Duniya ta musamman kan ayyukan agaji a Ukraine ta yi allah-wadai da munanan hare-haren da Rasha ta kai kan farar hula a Ukraine.

    Cikin wata sanarwa, Denise Brown ya ce hare-haren sun yi ɓarna sun haifar da asarar rayuka da jefa mutane cikin ƙunci sannan hare-haren misalai ne na irin yanayi na ta da hankali da a'ummar Ukraine ke fuskanta.

    Ta ce Rasha ta lalata gidaje da makarantu da asibitoci da kuma wani kanti da tashar jirgin ƙasa da cibiyar makamashi sannan ta ce hare-haren sun kashe tare da raunata farar hula a kusan dukkan yankunan ƙasar.

    A cewarta, "a yanzu iyalai da masu taimakon gaggawa na ta ƙoƙarin zaƙulo mutane daga ɓuraguzon gine-ginen da suka ruguje. Ga al'ummar Ukraine, wannan wani misali ne na irin mummunan yanayin da suke fuskanta kuma hakan ya sa shekarar 2023 ta zama shekarar matsanancin ƙunci.

  13. Kamata ya yi a riƙa jefe 'yan luwadi - Shugaban ƙasar Burundi

    ..

    Shugaban Burundi, Evariste Ndayishimiye ya ce ya kamata a jefe 'yan luwaɗi da masu neman jinsi, abin da a cewarsa yin hakan ba zai zama laifi ba.

    Yayin wani taron manema labarai a ranar Juma'a, inda yake mayar da martani kan tambayar da wani ɗan jarida ya yi masa, Shugaba Evariste Ndayishimiye ya ce Burundi ba ta buƙatar tallafin manyan ƙasashe masu ƙarfin iko "su riƙe taimakonsu" idan dai yin hakan na tare da sharaɗin a bai wa 'yan luwaɗi da maɗigo 'yanci.

    A jawabin nasa, shugaban ya yi misali da Littafin Injila, inda ya ce Ubangiji ya yi hani da neman jinsi kuma ya ce neman jinsi kwata-kwata ba ma maganar da ake tattaunawa ba ce a ƙasarsa ta Burundi.

    "A wajena, ina ganin idan muka ga masu irin wannan aƙida a Burundi, a kai su filin wasa a jefe su, kuma yin hakan ba zai zama laifi ba," cewar shugaban ƙasar Burundi.

    Mista Ndayishimiye ya ce luwaɗi da maɗigo kamar yin zaɓi ne tsakanin hanyar shaiɗan da ta Ubangiji".

    "Idan kana son zaɓar Shaiɗan, toh ka je ka yi rayuwa a irin ƙasashen, kuma ina tunanin masu fafutukar zuwa can suna son rungumar ɗabi'un, ya kamata su tsaya a can kada su kuskura su kawo mana su." in ji shugaban.

    Burundi dai ta haramta neman jinsi kuma laifi ne da ke iya janyo hukuncin ɗauri na kusan shekara biyu a gidan yari.

    A watan Agusta, mutum bakwai aka yankewa hukuncin shekara tsakanin daya zuwa biyu a gidan yari bayan kotu a Gitega ta same su da laifin neman jinsi, ko da yake,sun musanta tuhumar.

  14. Hotunan yadda masu aikin ceto ke ƙoƙarin kashe gobara a Kyiv

    Ga wasu hotunan rumbun ajiye kayayyaki a Kyiv da aka samu asarar ran mutum ɗaya bayan hare-haren Rasha.

    Masu aikin ceto suna ƙoƙarin kashe gobarar da ta tashi tare da lalubo masu sauran numfashi da ɓuraguzon gini ya danne.

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    ..

    Asalin hoton, Reuters

  15. Mutum 12 sun mutu a luguden wutar da Rasha ta yi a yankunan Ukraine

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Ukraine ta ce hare-haren makamai masu linzami da Rasha ta kai sassan Ukraine da safiyar yau Juma'a sun halaka mutum 12 tare da raunata sama da mutum 75.

    Gwamnan Odesa a Kudancin Ukraine, Oleh Kiper ya ce hare-haren sun halaka mutum biyu a yankin.

    Ya ce Rasha ta kai hare-haren ne kan gidaje kuma mutane da dama sun ji rauni - harda yara biyu ƴan ƙasa da shekara 10.

    Biyu daga cikin waɗanda suka ji rauni a cewar rahotanni suna cikin mawuyacin hali.

    Magajin garin Lviv ya ce an halaka mutum ɗaya da raunata mutum takwas a yankin da ke yammacin ƙasar.

    Bayanai sun nuna an kashe mutum biyu a Kyiv sai mutum biyar a Dnipro yayin da mutum ɗaya ya rasa ransa a Kharkiv sai wani guda a Zaporizhzhia.

    Andriy Sadovy ya ba da rahoton yadda harin ya shafi wata makaranta inda ya wallafa hoton wani aji da yadda aka ruguza tagogi, sai kuma ɓuraguzan ginin da suka warwatsu a ko ina.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaba Zelensky, a saƙon da ya wallafa a shafin X ya ce hare-haren na Rasha sun shafi makarantu da ɗakin masu juna biyu da gidajen mutane.

    Ya ce "a yau, Rasha ta yi amfani da kusan kowane irin makami da take da shi."

    "Ta harba makamai masu linzami kusan 100 kan Ukraine, kuma galibinsu an daƙile su." kamar yadda ya ce.

    Zelensky ya ce suna ci gaba da ƙoƙari wajen samar da kayan agaji ga mutanen da abin ya shafa tare da alƙawarin mayar da martani ga hare-haren na Rasha.

  16. Muna aiki tuƙuru domin sake fasalin tattalin arzikin Najeriya – Tinubu

    ..

    Asalin hoton, @OfficialAPCNg/X

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa tana aiki tuƙuru domin sake gyara tattalin arzikin ƙasar ta yadda za a mayar da hankali kan samar da manyan ayyuka tare da sabunta ayyukan more rayuwa.

    Shugaba Tinubu ya bayyana haka jiya Alhamis lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin kwamitin gudanarwar jam'iyyar APC a jihar Legas.

    A cewarsa, "ina sa ran za a fitarda kasafin kuɗi kowane lokaci daga yanzu, za ku ga yadda aka karkata kan manyan ayyuka, dole ne sabunta lalacewar ayyukan more rayuwa, mu kuma gyara hakan tare."

    Ya kuma bayyana damuwa game da yawan yaran da basa zuwa makaranta a ƙasar bayan rahoton baya-bayan nan da aka fitar.

    "Ya zama dole mu magance wannan matsala ta hanyar samar da ƙarin makarantu da ɗiban malamai aiki da samar da tsarin ciyar da ɗalibai." kamar yadda Tinubu ya bayyana.

    Shugaba Tinubu ya ce dole ne dimokraɗiyya ta ci gaba kuma ta tafi da kowa da zummar magance talauci ta hanyar samar da damarmaki na aiki ga matasa da kuma inganta ilimin yaran Najeriya.

    Ya ce yin haɗin gwiwa da ɓangarorin gwamnati da dama abu ne mai muhimmanci wajen ci gaban gwamnatinsu da kuma Najeriya.

    A nasa ɓangaren, shugaban Jam'iyyar APC, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da Tinubu cewa kwamitin gudanarwar jam'iyyar ya yi tsare-tsaren tabbatar da nasarar APC a zaɓen cike gurbin da ke tafe a watan Fabarairun 2024.

  17. Rasha ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a sassan Ukraine

    ...

    Rasha ta ƙaddamar da harin makami mai linzami da na jirage marasa matuƙi a sassan Ukraine.

    Hukumomi sun ce jirage marasa matuƙi fiye da 10 ƙirar Iran suka afka Lviv da ke yammacin Rasha, sai yankin Sumy da ke arewa maso gabas da shi ma ya fuskanci luguden wutar daga tsallaken iyaka.

    Jami'ai a Odesa sun ce wani dogon gini ya kama da wuta bayan da jirgi maras matuƙi ya kai hari.

    An kuma ji ƙarar fashe-fashe da dama a Kharkiv da ke arewa maso gabashin Ukraine.

    Hukumomi sun kuma ba da rahoton mutane da suka jikkata sanadiyyar lamarin.

  18. Maine ta zama jiha ta biyu da ta hanaTrump tsayawa takara

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Jihar Maine ta zama jiha ta biyu a Amurka da ta hana Donald Trump tsayawa takara a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar Republican domin neman kujerar shugaban ƙasa.

    Babbar jami’ar zaɓen Jihar ta ce an dakatar da tsohon shugaban ƙasar ne a ƙarƙashin wata ƙa’idar tsarin mulki da ta haramta wa masu tayar da ƙayar baya rike muƙami, saboda abubuwan da ya gudanar gabannin tarzomar da aka yi a majalisar dokokin Amurka a shekarar 2021.

    Kwamitin yaƙin neman zaɓen Trump ya kira matakin a matsayin cin zarafi ga dimokraɗiyyar Amurka tare da cewa za a shigar da ƙara cikin gaggawa.

    A makon da ya gabata aka dakatar da Mista Trump shiga zaɓen fidda gwanin jam’iyyar a jihar Colorado saboda irin dalilan da Jihar Maine ta bayyana.

  19. MDD ta buƙaci hukumomin Najeriya su yi bincike kan hare-haren ƴan bindiga a Filato

    ..

    Hukumar kare haƙƙin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira ga hukumomin Najeriya su ƙaddamar da bincike ba tare da ɓata lokaci ba kan jerin hare-haren da ƴan bindiga suka kai jihar Filato lamarin da ya halaka mutum kusan 150.

    Shugaban hukumar, Volker Turk ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin X inda ya ce "na kaɗu sosai da yadda ƴan bindiga suka kai jerin hare-hare kan ƙauyuka da dama na jihar Filato."

    A cewarsa, ya kamata a gudanar da cikakken bincike da ya yi daidai da dokokin kare haƙƙin bil adama na ƙasa da ƙasa. Hukumar ta kuma ce ya kamata a hukunta waɗanda aka samu da hannu a kai hare-haren.

    Wasu ƴan bindiga ne suka kai hare-haren jihar ta Filato - yankin da ya shafe shekaru yana fama da tashin hankali mai nasaba da ƙabilanci da kuma addini.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    A cewarsa, akwai buƙatar gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakan da suka dace domin hana faruwar munanan hare-haren a gaba.

    Yankin arewa maso yamma da tsakiyar Najeriya dai sun daɗe suna fama da hare-haren ƴan bindiga inda suke kai samame kan ƙauyuka su sace musu kayayyaki tare da garkuwa da mutane don samun kuɗin fansa.

    • Jami'in diflomasiyyar da ya sauya al'amuran duniya
    • Ko kun san me ake tattaunawa a taron Majalisar Dinkin Duniya?
  20. Barka da Juma'a!

    Masu bibiyarmu a wannan shafi na Kai Tsaye, assalamu alaikum. Da fatan kun wayi gari cikin ƙoshin lafiya.

    Kamar yadda aka saba, za mu kawo muku labarai da rahotanni na wainar da ake toyawa a Najeriya da Nijar da ma sauran ƙasashen duniya.

    Akwai kuma wasu ƙarin labaran a shafukanmu na sada zumunta kamar Fesbuk da X da kuma Instagram inda a nan ma za ku kalli bidiyo.