Fiye da mutum 20 sun mutu sakamakon fashewar bututun mai a Ribas
Wata fashewa da ta faru bayan fasa wani bututun ɗanyen mai da ke ƙarƙashin ƙasa a ƙaramar hukumar Ogba/Egebema/Ndoni da ke jihar Ribas ta halaka aƙalla mutum 20.
Lamarin ya faru ne a ƙarshen makon daya gabata a ƙaramar hukumar da ke zama ɗaya daga cikin cibiyoyi masu arzikin mai da iskar gas a jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Rahotanni na cewa an kwantar da mutanen da suka samu ƙuna a asibitoci da dama a garin.
Zuwa yanzu, babu tabbacin abin da ya jawo fashewar da ta haddasa gobara da kuma adadin mutanen da suka mutu.
Shugaban matasan yankin ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da matasan suke raba ɗanyen man da aka sato a jarkoki.
Wani ɗan jarida ya tabbatar cewa gobarar ta tashi lokacin da matasan suke rige-rigen kwasar ɗanyen man daga wani bututu da ke ƙarƙashin ƙasa a lokacin da gobarar ta tashi.
- 'Mutum 15 ne suka mutu a fashewar bututu a Lagos'