Sai da safenku
Masu bibiyarmu a wannan shafi, ƙarshen rahotonnin ke nan.
Za mu sake kasancewa da ku a wani shafin daban gobe da safe don kawo wasu labaran kai-tsaye.
Kafin lokacin,Umar Mikail ne ke fatan mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo labaran abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya daban-daban.
Mukhtar Adamu Bawa and Nabeela Mukhtar Uba
Masu bibiyarmu a wannan shafi, ƙarshen rahotonnin ke nan.
Za mu sake kasancewa da ku a wani shafin daban gobe da safe don kawo wasu labaran kai-tsaye.
Kafin lokacin,Umar Mikail ne ke fatan mu kwana lafiya.
Ƙungiyar agaji ta Palestine Red Crescent Society (PRCS) ta fitar da wani bidiyo da ke nuna Falasɗinawan da harin Isra'ila ya raunata cikinsu har da yara, lokacin da ake kai su Asibitin al-Amal a yankin Khan Younis.
Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce mutum 20 aka kashe a harin tare da jikkata wasu da yawa lokacin da Isra'ila ta kai harin kusa da asibitin na al-Amal.
Cikin wata sanarwa a dandalin X, PRCS ta ce wannan ne karo na uku da dakarun Isra'ila ke kai hari kusa da al-Amal a Khan Younis.
"Ya kamata asibitoci su zama mafaka, bai ababen kai wa hari ba," in ji ta PCRS.
Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Lebanon ta ruwaito cewa wani hari da Isra'ila ta kai ya kashe mayaƙin ƙungiyar Hezbollah tare da 'yan uwansa biyu.
An ce an kai harin ne kan wani gida a unguwar Bint Jbeil,da ke da nisan kilomita biyu daga iyakar ƙasar da Isra'ila.
Wata sanarwa da Hezbollah ta fitar ta ce ɗaya daga cikin mutanen ɗan ƙasar Austria ne da ke ziyartar 'yan uwansa a yankin.
Tun watan Oktoba ne aka fara ɓarin wuta tsakanin ƙungiyar daga Lebanon da kuma dakarun Isra'ila a kan iyakokin ƙasashen biyu.
Ministan Isra'ila Benny Gantz ya gargaɗi gwamnatin Lebanon cewa idan ba ta kori Hezbollah daga kan iyaka ba su za su yi hakan da kansu.
Majalisar Dinkin Duniya ta naɗa ministar kuɗi ta Holland mai barin gado Sigrid Kaag a matsayin babbar jami'iar kula da ayyukan jin ƙai da sake gina yankin Gaza.
Naɗin dai ya biyo bayan ƙudirin da Kwamitin Tsaro na MDD ya amince da shi ne a makon jiya na neman ƙara yawan kayan agaji ga al'ummar Zirin Gaza, waɗanda ke fuskantar mawuyacin hali na rayuwa.
Ms Kaag, wadda ƙwararriya ce a Gabas ta Tsakiya, tana jin Larabci sosai, kuma za ta fara aiki a ranar 8 ga watan Janairu.
Wakilin BBC ya ce Amurka ta yi maraba da naɗin nata, sai dai wani jami'in Isra'ila Ailon Lavy, ya yi gargadin cewa kasarsa ba za ta yi aiki da duk wani jami'in MDD da ke goyon bayan abin da ya kira "farfagandar Hamas" ba.
An kaddamar da katafaren butum-butumin Shakira An kaddamar da wani butum-butumin tagulla na shahararriyar mawakiya, Shakira, a kauyenta Barranquilla da ke kasar Kwalambiya (Colombia).
Mutum-mutumin mai tsawon mita 6.5 tamka ce ta Shakira lokacin da take lankwasa jikinta a lokacin da take cashewa a shahararriyar wakarta mai taken Hips Don’t Lie.
Kaddamarwar, wadda aka yi ranar Talata, ta samu halartar mahaifan mawakiyar, William Mebarak da Nidia Ripoll, da kuma magajin garin na Barranquilla.
Mawakiyar ta wallafa hotunan kaddamar da mutum-mutumin a shafinta na instagram tare da mahaifan nata a gaban gunkin.
Ko kafin kaddamar da shi, Shakira ta ja hankali a wannan shekarar mai karewa bayan da ta fitar da wata waka game da tsohon abokin zamanta kuma shahararren dan kwallon kafa na duniya Gerard Pique.
Shakira ta gode wa masassakin mutum-mutumin nata, Yino Márquez da dalibansa, bisa kwarewar da suka nuna.
Mawakiyar ta samu nasarori da dama a wannan shekara ta 2023, ciki har da lashe lambobin yabo uku a ‘Latin Grammy Awards’ na wakokin da aka yi cikin harsunan Sifaniya da Portugal.
Dubban mutane ne suka halarci jana'izar tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ta Najeriya Ghali Umar Na'Abba a fadar sarkin Kano.
Shugabanni da 'yan siyasar jihar da dama ne suka halarci Ƙofar Kudu da ke Masarautar Kano a yammacin yau Laraba.
Daga cikin waɗanda ake iya gani a waɗannan hotunan na ƙasa har da Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima, da Mataimakin Gwamnan Kano Aminu Abdussalam Gwarzo.
Kazalika, akwai jagoran jam'iyyar NNPP kuma tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso, da tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin.
Ghali Na'Abba ya rasu ranar Laraba a wani asibiti da ke Abuja babban birnin Najeriya bayan ya yi jinya.
Hukumomi a Kano sun gurfanar da matashiyar matar aure, Hafsat Surajo, wadda ake yi wa laƙabi da Chuchu, a gaban kotu, bisa zargin kashe matashi Nafi'u Hafiz da kuma yunƙurin kashe kanta.
Rundunar 'yan sandan jihar ta ce an gurfanar da Hafsat Surajo ne tare da ƙarin mutum biyu a gaban babbar kotun majistare da ke unguwar 'Yankaba a cikin ƙwaryar birnin.
Ɗaya daga cikin lauyoyin waɗanda ake tuhuma, Barrista Rabi'u Sidi, da yake jawabi ga manema labarai bayan fitowa daga kotun, ya ce takardun ƙara, sun nuna cewa ana kuma tuhumar mijin Hafsat da wani malami da kuma ƙarin wani mutum, a kan haɗa baki da ɓoye laifi da kuma bayar da bayanan ƙarya.
Sai dai, Barista Sidi ya ce da aka karanta mata tuhume-tuhumen guda biyu a gaban kotu, Hafsat Surajo ta amsa laifi kan tuhumar farko, amma ta musanta tuhuma ta biyu.
Shi ma wani, Barista I.S Abdullahi, lauyan malamin da 'yan sanda suka kama bisa zargin yi wa mamacin wanka, ya ce wanda yake karewa ya musanta tuhume-tuhumen da aka yi masa.
Ya ce sun nemi kotu ta bayar da belin waɗanda ake ƙara, amma masu gabatar da ƙara sun nemi kotu ta ba su dama su yi nazarin wannan buƙata, kafin bayar da matsayinsu.
To amma, mai magana da yawun 'yan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa, ya ce waɗanda ake zargin sun amsa dukkan tuhume-tuhumen da aka yi musu.
Kotun dai daga bisani, ta ɗage zamanta zuwa ranar 8 ga watan Janairu don yanke hukunci a kan buƙatar ba da belin.
Sanarwar da SP Abdullahi Haruna Kiyawa, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano ya fitar daga baya, na cewa a ranar Alhamis ne jami’ansu suka kama Hafsat Surajo ‘yar shekara 24 da ke Unguwa Uku bisa zargin kashe Nafi'u Hafiz, ɗan shekara 38 a gidanta na aure.
Haka zalika binciken ‘yan sandan a cewar sanarwar, ya kai su ga kama mijin matashiyar, Dayyabu Abdullahi mai shekara 38, sai kuma Mallam Adamu mai shekara 65.
An rantsar da gwamnan Ondo na riƙo, Lucky Aiyedatiwa a matsayin cikakken gwamnan jihar, sa'o'i bayan mutuwar Rotimi Akeredolu sanadin cutar kansa a ƙasar Jamus.
Alƙalin alƙalan jihar Mai shari'a Olusegun Odusola ne ya rantsar da shi a ofishin gwamnan Ondo ciki birnin Akure.
Mataimakin gwamnan, ya karɓi ragamar mulkin jihar a matakin riƙo, bayan Gwamna Rotimi Akeredolu ya aika wasiƙa ga majalisar dokokin jihar don sanar da ita game da ƙudurinsa na tafiya jinya da kuma miƙa ragamar mulkin jihar ga Lucky Aiyedatiwa.
Tun farko, an yi ta dambarwa a fagen siyasar jihar, lokacin da majalisar dokokin Ondo ta fara yunƙurin tsige Lucky Aiyetadiwa daga kan kujerar mataimakin gwamna.
Sakataren gwamnan jihar da kwamishinonin Ondo da shugaban jam'iyyar APC da alƙalan jihar na cikin manyan jami'an da suka halarci taron rantsuwar.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa yana cikin alhini tare da al’ummar jihar Ondo, bisa rasuwar gwamnansu, Rotimi Akeredolu.
A cikin wata wasiƙa da ya fitar, Tinubu ya ce “Ba za mu sake ganin mutum kamarsa ba”.
Ya ce gwamnatinsa za ta karrama Gwamna Rotimi don ganin ba a mance da hidimar da ya yi wa al’umma ba.
Tinubu ya ce tuni ya yi wayar tarho da uwargidan marigayin Betty da kuma mai riƙon muƙamin gwamnan jihar Lucky Aiyedatiwa inda ya miƙa ta’aziyyarsa gare su kan wannan rashi.
Ya bayyana Gwamna Akeredolu ba kawai a matsayin aboki ba, ɗan’uwansa ne kuma shaƙiƙi. Ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi ga jam’iyyarsu ta APC mai mulki da kuma iyalai ma’abota rajin ci gaba.
Gwamnatin jihar Ondo ta fitar da sanarwa a kan rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu, wanda ta ce ya tafi ya bar wagegen giɓi a zukata.
Sanarwar wadda kwamishiniyar yaɗa labaran jihar, Bamidele Ademola-Olateju ta fitar, ta tabbatar da cewa Aredolu ya mutu ne lokacin da yake jinya a ƙasar Jamus sanadin cutar kansar mafitsara da ya yi fama da ita tsawon lokaci.
“An aika wasiƙa ga Shugaba Bola Tinubu don sanar da shi a hukumance game da labari mai ɗaga hankali. Iyali da Gwamnatin Jihar Ondo na jinjinawa goyon bayansa ga Gwamna Akeredolu a lokacin rashin lafiyarsa.”
Sanarwar ta ce za a fitar da sanarwa nan gaba don jin ƙarin bayani game da shirye-shiryen yi masa jana'iza.
Gawawwakin Falasɗinawan da ba a shaida su ba, kimanin 80 aka binne a wani babban kabari a Rafah, kudancin Gaza.
Majiyoyi daga ma'aikatar lafiyar Gaza da ke ƙarƙashin ikon Hamas, sun faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an kwashe su ne "daga ɗakunan ajiye gawa da kaburbura" zuwa Isra'ila don hukumomi su tantance idan babu 'yan Isra'ilan da ake garkuwa da su a ciki.
Daga bisani kuma aka mayar da su ta mashigar Kerem Shalom a kudancin Gaza.
Rundunar sojojin Isra'ila ta ce tana tantance waɗannan bayanai.
Isra'ila ta ce akwai 129 a cikin mutum 240 waɗanda har yanzu ba a san inda suke ba, bayan an sace su sannan aka kwashe su zuwa cikin Gaza ranar 7 ga watan Oktoba. Hare-haren wannan rana da Hamas ta jagoranta sun yi sanadin mutuwar mutum 1,200.
Falasɗinawa sama da 20,600 aka kashe a luguden bama-baman da Isra'ila ke yi tun daga wancan lokacin, a cewar ma'aikatar lafiyar Gaza.
Aƙalla mutum 10, ciki har da yarinya ƴar shekara tara sun mutu a gabashin Australiya sakamakon mamakon ruwan saman da aka yi ranakun kirsimeti da kuma ranar raba kyautuka wato Boxing Day a turancin Ingilishi.
Akasarin mutanen da suka mutu a jihar Queensland inda har yanzu dubban mutane ba su da hasken wutar lantarki.
An samu iska mai ƙarfin gaske da ambaliyar ruwa a Victoria da New South Wales.
Hukumomi sun yi hasashen samun ƙarin ruwan sama kamar da bakin ƙwarya amma sana tunanin yanayin zai inganta.
"Wannan ne karon farko da aka taɓa samun iska mai ƙarfi ta lalata turakun wutar lantarki da aka dasa da daben siminti. Abu ne da ba mu yi hasashen sa ba." in ji Firimiyan Queensland Steven Miles.
Mazauna a yankunan New South Wales da South Australia sun shiga kaɗuwa ganin yadda ƙanƙara da dama da girmansu ya kai ƙwallon golf suka mamaye ƙasa.
Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya isa Filato -jihar da a baya-bayan nan ƴan bindiga suka kai wasu munanan hare-hare da ya halaka sama da mutum 140.
Gidan Talabijin na Channels ya wallafa wani bidiyo da ke nuna wasu manyan muƙarraban gwamnati da gwamnan jihar ta Filato zaune suna dakon isowar mataimakin shugaban Najeriyar a filin jirgin sama na Yakubu Gowon.
Kashim Shettima na ziyara a jihar ne domin duba irin ɓarnar da aka yi bayan hare-haren na jajiberin kirsimeti.
Daga cikin tawagar gwamnatin akwai mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu tare da Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa.
Ziyarar tasu na zuwa ne ƴan kwanaki da kai harin da ya girgiza al'ummar ƙasar.
Yau Najeriya ta shiga alhini sakamakon mutuwar wasu jiga-jigan ƴan siyasa biyu - gwamnan jihar Ondo mai ci, Rotimi Akeredolu da tsohon kakakin majalisar wakilai Ghali Umar Na'abba.
An fara samun labarin rasuwar tsohon Kakakin majalisar Najeriyar ne yana da shekara 65 yayin da gwamna Akeredolu ya mutu yana da shekara 67 da haihuwa.
Dukkansu, kamar yadda bayanai suka tabbatar sun yi fama da rashin lafiya inda kuma suka yi jinya a asibiti.
Tuni dai al'ummar Najeriya suka fara miƙa saƙon ta'aziyya bisa rashe-rashen na safiyar yau.
Shugaban bankin raya ƙasashen Afirka, Afdb Akinwunmi Adesina, a saƙon ta'aziyyarsa, a shafin X, ya bayyana kaɗuwarsa bisa rasuwar gwamna Akeredolu wanda ya ce ya sadaukar da kansa ga hidimtawa al'ummarsa. Ya kuma yi addu'ar Allah ya bai wa iyalansa da al'ummar jihar haƙurin rashi.
Shi ma gwamna Ahmadu Umar Finitiri na jihar Adamawa, a saƙon ta'aziyyarsa ya ce za a ci gaba da tuna wa da hidindimun da gwamna Akeredolu ya yi.
Game da rasuwar Ghali Na'abba kuwa, gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya ce marigayin ya yi aiki sosai wajen ciyar da kundin tsarin mulki da ƴancin al'umma da kuma dimokraɗiyya gaba. Ya kuma ce Najeriya ta yi babban rashi kasancewarsa dattijon ƙasa.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shi ma ya miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalansa da gwamnati da kuma al'ummar Kano.
Ya kuma bayyana yadda marigayin ya tsaya kai da fata kan ƙudirorinsa kuma mutum ne mai son ganin komai na tafiya bisa tsari, a cewar Kwankwaso.
Shi kuwa Dakta Abubakar Bukola Saraki, shugaban majalisar dattawa na 13, ya bayyana Ghali Na'abba a matsayin mutumin da tsarin shugabancinsa ke haska yadda ya jajirce kan tsare-tsaren dimokraɗiyya da shari'a.
Rundunar sojin Isra'ila na faɗaɗa hare-hare ta ƙasa a tsakiyar zirin Gaza, kusan wata uku bayan da aka soma yaƙin.
Wani jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana matuƙar damuwa game da yadda aka kai hari kan sansanonin ƴan gudun hijra da ya cika maƙil da mutanen da suka ɗaiɗaita.
Rundunar sojin ta Isra'ila ta ce ta kai hari kan wani hedikwatar Hamas na ƙarƙashin ƙasa a Jabalia da ke arewacin Gaza tare da kai hare-hare ta sama a Khan Younis a kudanci.
Kakakin hukumar lafiya ta duniya ya faɗa wa BBC cewa abokan aikinsa sun shiga tashin hankali a ko ina a Gaza.
Babban bankin Najeriya, CBN ya bai wa ƴan ƙasar tabbaci cewa kuɗaɗen ajiyarsu da ke asusun bankuna ba sa fuskantar wani haɗari inda ya jaddada samun daidaito a tsarin bankunan ƙasar.
Babban bankin ƙasar ya shawarci jama'a da su ci gaba da haulɗa da bankuna kamar yadda aka saba inda ya nemi ƴan ƙasar su yi watsi da rahotanni marasa tushe game da halin da bankunan ƙasar ke ciki.
CBN ya ce yana da dukkan kayan aikin da ake buƙata wajen gudanar da ayyukansa da suka shafi hada-hadar kuɗaɗe.
Wata sanarwa da mai riƙon muƙamin sashen yaɗa labarai na CBN, Hakama Sidi-Ali ta fitar, ta ce "Babban bankin CBN ya ga wasu rahotanni a wasu kafafen yaɗa labarai game da shawarar da aka bai wa gwamnatin tarayya na karɓe iko da wasu cibiyoyin kuɗi ƙarƙashin kulawarsa.
"Bankunan Najeriya suna harkokinsu yadda ya kamata. CBN na shawartar jama'a su ci gaba da tafiyar da harkokinsu ba tare da samun fargaba kan rahotannin da ake yaɗawa ba waɗanda ba daga CBN suka fito ba." kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Ƴan sanda sun kama wasu matasa biyu - ƴan uwan juna bayan da aka harbe babbar yarsu har lahira sakamakon wani rikici da ya taso yayin rabon kyautukan kirsimeti.
Ƙanin matashiyar mai shekara 23 ne ya harbe ta a ƙirji yayin da ɗanta - wata 10 da haihuwa ke cikin jakar goyon jarirai, kamar yadda shugaban ƴan sandan jihar Florida ya bayyana.
Ofishin shugaban ƴan sandan Gundumar Pinella ya ce daga baya babban wansa ya harbi ƙanin da bindiga.
Ofishin ya ƙara da cewa an yi harbin ne bayan wata jayayya game da wanda ya fi cancanta ya samu ƙarin kyaututtuka.
Jami'i Bob Gualtieri ya faɗa wa ƴan jarida cewa babban matashin, mai shekara 15, ya ruga daga inda lamarin ya faru tare da jefar da bindigarsa.
An kai ƙanin mai shekara 14 asibiti kuma yana samun lafiya kuma a cewar ƴan sanda za a sa shi a komarsu da zarar ya samu sauƙi.
Masu gabatar da ƙara a yankin za su yi nazari kan lamarin sannan su yanke shawarar ko za a tuhume shi da kisan ƴar uwarsa, in ji Gualtieri.
An kai matashiyar asibiti inda aka tabbatar da ta mutu, kamar yadda jami'in ya bayyana.
Ya ce matashiyar, mai yara biyu ta yi ta zub da jini har ya kai ba ta iya numfashi sai dai ya ƙara da cewa ba abin da ya samu jakar goyon jaririn.
An dai kama matashin ɗan shekara 15 tare da tuhumarsa da yunƙurin kisa da kuma ɓoye shaida.