Gaba a yau Alhamis ne ake sa ran Kotun ƙolin ƙasar za ta fara sauraron ɗaukaka
ƙarar da gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf da jam'iyyarsa ta NNPP
suka shigar a gabanta.
Gwamnan na jam'iyyar NNPP na ƙalubalantar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ya
tabbatar da hukuncin kotun sauraran ƙararrakin zaɓe da ta soke nasararsa tare
da bayyana Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen
gwamnan jihar.
Wannan ne dai karon farko da kotun za ta fara zama kan ƙarar da gwamnan ya shigar.
Ɗaya daga cikin lauyoyin NNPP, Barista Bashir Muhammad Tudun Wuzirci ya ce sun gabatar da dukkan abubuwan da ya kamata su gabatar gaban kotu.
"Da yardar Allah kotu za ta tabbatar da zaɓn da mutanen Kano suka yi wa Abba Kabir Yusuf." kamar yadda Barista Bashir Tudun Wuzurci ya bayyana.
A nasa ɓangaren. lauyan APC, Barista Abdullahi Adamu Fagge ya ce "dukkan ɓangarorin biyu musamman su waɗanda suka ɗaukaka ƙara za su yi bayani na cewa kotun ƙasa ta yi kuskure ba ta yi daidai ba dangane da hukuncin da ta yi,"
"Daga ɓangarenmu mu da aka ɗaukaka ƙara a kan hukuncin da ya yi mana daɗi, za mu yi bayanai mu nuna cewa hukuncin nan an yi shi daidai, kotun ɗaukaka ƙara ta yi daidai, muma mu zo da hujjoji gamsassu na shari'a." in ji lauyan APC.
Suma masu ruwa da tsaki a jam'iyyun NNPP da APC suna ji gaba da yin tsokaci kan lamarin. Hisham Habib, ɗan jam'iyyar NNPP ya yi fatan kotun ta duba wahalar da mutanen Kano suka sha ta yi watsi da tsarin da aka zo da shi da ake ganin ba shi da tasiri.
Suma ƴan jam'iyyar APC kamar Aminu Mi Dawa Fagge ya ce suna ci gaba da addu'ar nasara kuma sun nemi jama'ar Kano su karɓi kowane hukunci kotu za ta yanke domin zaman lafiya da kuma ci gaban jihar.
-
Kotun ɗaukaka ƙara ta kammala sauraron shari'ar zaɓen gwamnan Kano
-
Siyasar Kano: APC da NNPP sun koma ga Allah kafin hukuncin kotu