Blinken ya mai da martani kan sukar da ake yi wa Amurka kan Isra'ila
A wani taron manema labarai na ƙarshen shekara, sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken mayar da martani kan sukar da ake yi wa Amurka yaƙin da Isra'ila ke gudanarwa a Gaza.
Yana magana ne a yayin da jami'an diflomasiyyar Majalisar Ɗinkin Duniya ke yunƙurin gujewa sake ƙin amincewa daga Amurka kan ƙudurin tsagaita wuta a Gaza.
"Ba na jin wani yana kira ga Hamas ta daina fakewa da fararen hula, ta ajiye makamanta, ta kuma mika wuya," in ji shi. "Komai zai ƙare gobe idan hakan ya faru."
Ya ƙara da cewa, "Yaya zai kasance ba a buƙatar komai daga maharin, sai gabatar da buƙatu ga wanda aka azabtar," in ji shi, yana mai jaddada cewa harin Hamas na ranar 7 ga Oktoba ne musababbin yaƙin.
Blinken ya ce Amurka ta kasance kan gaba wajen kai agajin jin ƙai a Gaza kuma tana son tabbatar da cewa ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya ya ci gaba da kokarin… ba tare da al'amura sun sake taɓarɓarewa ba.
Ya sake nanata matsayin gwamnatin na cewa dole ne Isra'ila ta ƙara yin ƙoƙarin kare fararen hula, amma tana da hakkin gudanar da wannan yaƙin.
Ofishin yaɗa labarai na gwamnatin Hamas ya sanar da cewa adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza a yanzu ya zarce 20,000.