Sai da Safe
Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na kai-tsaye.
Ku tara gobe da safe don samun wasu sababbi.
Mu huta lafiya..
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Nabeela Mukhtar Uba and Haruna Kakangi
Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na kai-tsaye.
Ku tara gobe da safe don samun wasu sababbi.
Mu huta lafiya..
An sami sanarwan cewa an sake jinkirta kaɗa ƙuri’ar da Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi na dakatar da yaƙin Gaza.
Yanzu an shirya kaɗa ƙuri'ar da ƙarfe 22:00 GMT. An dai yi ta tataunawa sosai game da yadda aka tsara lafazin ƙudurin, kuma mambobin majalisar za su so su kaucewa duk wata dama ta kin amincewa da shi.
Amurka ta ki amincewa da daftarin ƙudurin na ƙarshe saboda lafazin da ya ƙunsa.
Ministan tsaron Isra'ila, Yoav Gallant, ya ce hare-haren ƙasa da sojojin Isra'ila za su "kara fadada" a yankin zirin Gaza, in ji kafofin yada labaran Isra'ila.
A lokacin da yake rangadi a kan iyakar Gaza, Gallant ya ce: "Khan Younis ya zama sabon babban birnin ta'addanci. Ba za mu bari a aiwatar da ayyukanmu a can ba har sai mun isa ga manyan jami'an Hamas", jaridar Times of Israel ta nakalto daga bayanan da ofishinsa ta wallafa.
Yayin da yakin Ukraine da Rasha ke gab da cika shekaru biyu, rundunar sojin Ukraine na buƙatar ƙarin sojoji 500,000, kamar yadda shugaban ƙasar Volodymyr Zelensky ya bayyana,
A wani taron manema labarai a Kyiv, ya ce kwamandojinsa na neman “mutane 450,000-500,000”, yana mai cewa wannan lamari da ke tattare da mautkar “damuwa” kuma mai tsadar gaske. Ya ce yana bukatar ƙarin bayani kafin ya goyi bayan matakin, yana mai nuni da cewa akwai sojoji 500,000 da ke bakin daga.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan koma bayan da aka samu na raguwar agaji daga Amurka da ƙungiyar tarayyar turai (EU).
'Yan jam'iyyar Republican a majalisar dokokin Amurka sun fara da daƙile wani shirin soji na dala biliyan 60 (£ 47bn) ga Ukraine a farkon wannan watan.
Hakan ya biyo bayan dakatarwar da kasar Hungary ta yi wa yarjejeniyar ba da tallafin kuɗi na Tarayyar Turai ta Yuro biliyan 50 a makon da ya gabata. Shugabannin EU sun ce ba za a bar Ukraine ba tare da goyon baya ba.
Ukraine na fuskantar ƙarancin harsasai yayin da take ci gaba da fafatawa da sojojin Rasha, biyo bayan mamayar da Moscow ta yi mata watan Fabrairun 2022.
Shugaban ƙungiyar Hamas Ismail Haniyeh zai yi balaguro zuwa Masar a gobe Laraba, kamar yadda wata majiya ta shaida wa BBC.
Za mu kawo muku ƙarin bayani da zarar mun samu.
Majalisar ƙoli ta jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta sha alwashin ɗaukar matakan ladabtarwa kan Miinistan Abuja Nyesom Wike, da wasu ‘yan jam’iyyar da suka yi mata zagon ƙasa, a lokacin da ya dace.
Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya faɗa yayin wani taron manema labarai ranar Talata cewa jam’iyyar ta sha bamban da matsayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka kan rikicin siyasar jihar Ribas.
Damagun ya dage cewa dole ne hukumar zaɓe ta ƙasa (Inec) ta gudanar da zaɓen cike gurbin kujerun ‘yan majalisar dokoki 27 da suka sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
"PDP ta buƙaci a yi amfani sashe na 109, da sashe na 84 (15) na dokar zaɓe ta 2022 don a tsayar da ranar gudanar da zaɓe a mazaɓu 25 na jihar Ribas da aka samu gurabe a dalilin sauya sheƙa daga jam’iyyar tun kafin kotu ta yanke hukunci," in ji shi.
'Mun san cewa ba Wike kaɗai ba ne; akwai wasu mutanen da su ma suka yi wa jam’iyyar zagon ƙasa...Za mu ladabtar da kowa. Idan Wike yana tunanin cewa ya fi ƙarfin wannan jam’iyyar, za mu nuna masa cewa ya yi kuskure."
Masana kimiyya sun shiga damuwa kan tasirin da 'yan'adam za su iya yi ga duniyar wata, kuma sun ce suna son hana ɗan'adam ɗin yin babbar illa ga watan.
Masu bincike na Jami'ar Kansas sun ce balaguron da ɗan'adam ke yi zuwa sararin samaniya ya mayar da duniyar wata ta zamo wata cibiya ta hada-hadar mutane.
Sama da kumbo 100 aka harba zuwa duniyar wata a cikin shekara 60 da suka gabata, kuma an yi ƙiyasin cewa ɗan'adam ya baro tarkacen shara kimanin kilogiram 226,800 a kan doron duniyar watan.
Hukumar yaki da cin hanci a Najeriya, EFCC, ta tabbatar da tsare tsohon ƙaramin ministan lantarki, Olu Agunloye, kwanaki bayan ta bayyana cewa tana neman sa.
Wata majiya a hukumar ta shaida wa gidan talabijin na Channels a ranar Talata cewa Agunloye yana tsare tun ranar 13 ga watan Disamba.
EFCC dai ta ce kimanin mako guda da ya gabata take neman Agulonye bisa zargin almundahanar dala biliyan shida da ke da alaƙa da aikin samar da wutar lantarki ta Mambilla da ake ta cecekuce a kan sa.
Agunloye ya kasance minista a gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo daga 1999 zuwa 2003.
Obasanjo ya zarge shi da bayar da kwangilar aikin ba tare da amincewar majalisar zartarwa ta tarayya ba a lokacin, zargin da tsohon ministan ya sha musantawa.
Kusan kashi biyu cikin uku na mutanen Sudan ba su samun kulawar likitoci yayin da yaƙi ke ci gaba da faɗaɗa a ƙasar, a cewar ƙungiyar ba da agaji ta Save the children.
Kusan jarirai 30,000 ake tsammanin za a haifa ba tare da taimakon asibiti ba cikin wata uku masu zuwa.
Wannan na zuwa ne bayan dakarun tawaye na RSF sun kutsa garin Wad Madani, birnin da ya kasance mafaka ga ɗaruruwan dubban mutane da suka guje wa tashin hankalin daga birnin Khartoum.
Ko kafin yaƙin ya ɓarke a watan Afrilu, Sudan na fama da yawaitar mutuwar mata masu ciki, yanzu ɗaruruwan dubban mata masu ciki na hanƙoron neman sauka lafiya, inda kashi ɗaya cikin uku ne kaɗai na matan ke samun damar kulawar likioci.
Save the Children ta yi gargaɗin cewa jarirai da iyayensu mata na iya samun matsalolin da za su kwashe tsawon rayuwarsu suna fuskanta, ko ma su yi ajalinsu.
Duk da matakan difilomasiyya da aka sha ɗauka don kawo zaman lafiya, yaƙin Sudan na ci gaba da ta'azzara da ƙara faɗaɗa zuwa wasu bangarorin ƙasar.
Wata wutar daji ta kama ganga-ganga a yankin Reykjanes da ke kudu maso yammacin ƙasar Iceland bayan makonni ana girgizar ƙasa.
An kwashe kusan mutum 4,000 daga Grindavik a watan da ya gabata, daga garin da akasarinsa na masunta ne mai nisan kilomita huɗu.
Wutar ta fara ci ne a arewacin garin da misalin ƙarfe 10:17 na dare ranar Litinin agogon yankin, in ji 'yan sandan Iceland.
Shugaba Vladimir Putin ya amince da cewa wasu ɓangarorin rundunar sojojin Rasha na bukatar garambawul saboda matsalolin da yakin Ukraine ya fallasa.
Cikin jawabin da ya yi a taron jami'an ma'aikatan gwamnati da aka yaɗa kai-tsaye ta gidan talabijin na Rasha, kalaman Putin sun ɗan bambanta da ministan tsaronsa game da halin da sojojin Rasha ke ciki.
Putin ya ce ya kamata a inganta hanyoyin sadarwa da na tsaron sama da kuma amfani da bayanan sirri, amma kuma ya dage cewa masana'antun Rasha sun yi saurin ɗaukar mataki kan rikicin fiye da ƙasashen Yammacin Turai.
Putin ya kuma yi tsokaci kan yarjejeniyar soji tsakanin Finland da Amurka da aka ƙulla a ranar Litinin, yana mai cewa Washington ta ƙara ƙaimi a kusa da kan iyakokin Rasha.
Matakin dai ya ƙara haifar da dambarwar diflomasiyya tsakanin Finland da Rasha, waɗanda alaƙarsu ta lalace sakamakon mamaye Ukraine da Rasha ta yi da kuma yunƙurin Finland na shiga ƙungiyar Nato.
Ya za ka ji idan ka yi bikin cika shekara 81 da yin aure?
Abin da ya faru ke nan ga waɗannan ma'auratan, wato Dorothy Walter, mai shekara 103 da Tim Walter mai shekara 102.
Sun hadu ne lokacin dukkanin su na da shekaru 18 da haihuwa a duniya, a yankin Southampton na ƙasar Ingila, lokacin yaƙin duniya na biyu, lokacin suna aiki a wani kamfanin haɗa jirage.
Ma'auratan waɗanda a yanzu suke rayuwa a wani gidan kula da gajiyayyu da ke Kent, sun yi aure ne lokacin suna da shekaru 21 da haihuwa.
Mista Walter: "Muna cikin farin ciki a tare, a kodayaushe."
Sun ce sirrin daɗewar su a tare shi ne "ba sa yin gardama da juna".
Masana sun yi gargaɗi cewa hare-haren da ake kaiwa kan jiragen ruwan ƴan kasuwa a tekun maliya na haifar da barazanar tayar da farashin man fetur da sauran kayayyaki.
Kamfanoni da dama sun dakatar da jigila ta hanyar bayan da ƴan tawayen Houthi suka kai hari kan jiragen ruwan a Yemen.
Babban kamfanin fiton kaya na Denmark, Maersk, a ranar Talata, ya ce zai sauya wa wasu daga jiragensa hanya.
Lamarin ya sa Amurka ƙaddamar da wani ƙawance na duniya domin kare jiragen ruwa a tekun na Maliya.
ƙasashen da suka shiga ƙawancen tsaron akwai Birtaniya da Canada da Faransa da Bahrain da Norway da Sifaniya.
Sakataren harkokin tsaron Amurka, Lloyd Austin ya gudanar da wani taro ta intanet da ministoci daga ƙasashe fiye da 40 inda ya nemi wasu ƙarin ƙasashe su bayar da gudumawa domin kare jiragen ruwa a tekun na Maliya.
Rahotanni sun ce ana samun ƙaruwar hare-hare daga ƴan tawayen Houthin tun watan Oktoba, abin da ya tursasa wa kamfanonin jiragen ruwan da dama neman mafita.
Ma'aikatar lafiya a Gaza arashin ikon Hamas ta ce Falasɗinawa 19,667 ne aka kashe a zirin tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.
Cikin wata sanarwa da ta sabunta a shafukanta na sada zumunta, ma'aikatar ta ce an jikkata wasu 52,586.
Sabbin alƙaluman na zuwa ne yayin da ƙasashen duniya ke ƙara matsa wa Isra'ila ta tsagaita wuta a Gazan don kare rayuka da kuma bari a shiga da kayan agaji.
Yaƙin ya ɓarke ne mako 10 da suka wuce bayan mummunan harin da mayaƙan Hamas suka kai cikin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, inda suka kashe aƙalla mutum 1,200 tare da yin garkuwa da kusan 240.
Mai kula da kai kawon likitoci masu ba da taimakon agaji, Ricardo Martinez, ya ce ya ga yadda mutane ke karɓar gawarwakin mutane daga titunan Gaza yayin da yake aiki a baya-bayan nan a Zirin.
Cikin wani rahoto da ya gabatar a kungiyar, Martinez ya ce: "Da yawa sun je ƙarɓar gawawwakin mutanen da ke yashe a kan tituna - wasu kusan wata biyu - sun ruɓe. Ta yaya za ku fasalta irin wannan raɗaɗin?"
Martinez ya ƙara da cewa "rayuwa a Gaza batu ne na sa'a kawai."
Ya bayyana cewa rashin ruwa da tsaftataccen muhalli na kisa fiye da bama-bamai," musamman a yanayin rashin mai ko wuta.
Ya ce cunkoson mutane a kudu har ya kai "kana ji kamar kana filin ƙwallon da ke cike maƙil da mutane, mutane masu yawa na amfani da banɗakuna kaɗan sannan kuma babu man da za a iya janyo ruwa".
Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce mutum 20 aka kashe wasu da dama kuma suka ji rauni bayan shafe dare Isra'ila na luguden wuta a Rafah da ke Kudancin Gaza.
Kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu, Wafa ya ce ɗan jarida Adel Zourub na cikin mutanen da suka mutu sai dai ba a kai ga sanin kafar yaɗa labaran da yake yi wa aiki ba.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hari ne a tsakiyar Rafah abin da ya halaka mai samar wa Hamas maƙudan kuɗi, Subhi Ferwana.
Bayanai daga Taraba a Najeriya na cewa an sace mutum 21 har da sarki mai daraja ta uku na al'ummar Pupule, Alhaji Umaru Nyala a ƙaramar hukumar Yorro da ke jihar.
Wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne suka yi awon gaba da su bayan da suka mamaye ƙauyen cikin dare inda suka riƙa harbin kan mai uwa da wabi a sassa daban-daban na ƙauyen.
Wani shaida da ya yi hira da gidan Talabijin na Channels ya ce cikin mutum 22 da aka sace, har da wata mai juna biyu, da wasu ƴan gida ɗaya da kuma ɗan sarkin da dogarin sarkin.
Wannan ne karo na uku da ake sace mutane don neman kuɗin fansa a ƙauyen cikin ƙasa da wata shida kuma ba a taɓa cafke waɗanda ake zargi ba.
Shaidu sun kuma ce a yanzu, mutanen ƙauyen na zama cikin zullumi yayin da wasu kuma ke tserewa.
Har yanzu ƴan sanda ba su tabbatar da faruwar lamarin ba inda suka ce sun aike tawagar jami'ansu zuwa wajen domin gudanar da bincike.
Ga wasu hotuna na ɓarnar da girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.2 ta yi a Lardin Gansu da ke arewa maso yammacin China.
Mutum sama da 120 ne aka tabbatar sun mutu sanadiyyar lamarin.
Rundunar ƴan sanda a jihar Jigawa ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai shekara 40 da wani mai shekara 30 dukkansu a ƙaramar hukumar Gumel ta jihar bisa zarginsu da bai wa wani da ta kira riƙaƙƙen ɗan fashi da makami kuma mai garkuwa da mutane kariya.
Ɗan fashin dai ya kasance kan gaba a jerin mutanen da rundunar take nema ruwa a jallo.
Rundunar ta bayyana haka ne cikin bayanin da ta wallafa a shafinta na Facebook inda ta ce ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya bayyana cewa shi ne yake tuka ɗan fashin a kan babur idan ya je ƙauyen yayin da ɗayan kuma ya ce mutumin da ake nema ruwa a jallo yana kai masa hulunansa domin ya wanke su kasancewar ita ce sana'arsa.
ASP Abubakar Isah, Kakakin rundunar ƴan sandan a Jigawa ya ce an ƙara ƙaimi domin kama mutumin da ake zargi ɗan fashi ne.
Ya kuma ce yayin samamen da ƴan sanda suka kai lunguna da saƙo, an kama mutum 25 da ake zargi da kasuwancin miyagun ƙwayoyi.
Kakakin rundunar ya ce da zarar an kammala bincike a sashen binciken manyan laifuka da ke Dutse, za a gurfanar da mutanen da aka kama a kotu domin su fuskanci tuhuma.