Hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC ta tabbatar da ɓarkewar cutar zazzabin Dengue a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya.
Babban Daraktan hukumar ta NCDC, Dakta Ifedayo Adetifa wanda ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja, ya ce mutum 71 ake zargin sun kamu da cutar, an tabbatar da mutum 13 sun kamu sai dai babu rahoron asarar rai daga ƙananan hukumomin jihar uku da aka samu ɓullar cutar.
Adetifa ya bayyana cewa galibin mutanen da ake zargin sun kamu da cutar ƴan shekara tsakanin 21 da kuma 40 ne inda ya ce an gano hakan cikin watan Nuwambar 2023.
Babban daraktan hukumar ya ce ɓarkewar cutar a yanzu yana mataki na matsakaici la'akari da binciken da aka yi game da haɗarin cutar. Ya kuma ce akwai isassun kayan aiki da kuma ma'aikatan lafiyar da za su duƙufa ko da an samu ɓarkewar cutar a sauran jihohin ƙasar.
Zazzabin Dengue cuta ce da sauro ke yaɗa ta a yankuna masu zafi da wuraren da ke maƙwabtaka da su.
Alamominta sun hada da zazzabi da ciwon kai da tashin zuciya da amai da ciwon gaɓɓai, da fitowar ƙurji. A wasu lokuta kuma, tana iya janyo mutuwa.
Ɓarkewar dengue a Najeriya wani ɓangare ne na ɓullar cutar a watannin baya-bayan nan a wasu ƙasashen Afirka kamar Senegal da Burkina Faso da Cabo Verde da Chadi da Ethiopia da Mali da Togo.
A cewar wata ƙididdiga daga hukumar kare cututtuka masu yaɗuwa ta Afirka, Burkina Faso ce ƙasar da cutar ta fi ƙamari inda aka samu mutum fiye da 600.
A watan Oktoba kuma, hukumar lafiya ta duniya, WHO ta yi gargaɗin cutar na iya bulla a kudancin Amurka da kudancin Turai da wasu sassan Afirka.
Adetifa ya shawarci ƴan Najeriya musamman mazauna jihar Sokoto da su yi riƙo da dukkan matakan kariya kamar sanya kayan da za su rufe jikinsu domin kare kansu daga cizon sauro sannan su kwanta a gidan sauro mai magani.
Sannan a cewarsa, ya kamata mutane su riƙa amfani da maganin sauro a wuraren da suke kwana tare da tabbatar da tsaftar muhallansu domin kare bai wa sauro mafaka.
-
Hukumar Lafiya ta sa noma a jerin cutukan da aka yi watsi da su
-
Cikakken bayani kan cutar Noma