Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Masana sun gano abin da ke sa masu juna biyu laulayi

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labaran abubuwan da ke faruwa sassan duniya daban-daban.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. 'Amurka na son kawo ƙarshen yaƙin Gaza ba tare da ɓata lokaci ba'

    Kakakin fadar gwamnatin Amurka ya ce gwamnatin ƙasar na buƙatar a kawo ƙarshen yaƙin Isra'ila da Hamas ba tare da 'ɓata lokaci ba'.

    Yayin da yake jawabi a taron manema labarai a birnin Washinton DC, John Kirby ya yi ƙarin haske kan ziyarar mai bai wa fadar shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro ya kai birnin Tel Aviv.

    Ya ƙara da cewa mista Sullivan ya tattauna da Isra'ila kan yadda za a rage hare-hare a Gaza ba ba da jimawa ba.

    Sai dai Mista Kirby ya ce "ba na son bayyana ainihin lokacin da hakan zai faru”.

  3. An gano yaron da ya ɓata tsawon shekara shida a wata ƙasa

    Hukumomi a Birtaniya sun ce wani yaro ɗan ƙasar mai shekara 17 da ya ɓace a Sifaniya a 2017, a yanzu an gano shi a Faransa.

    An gano Alex Batty a garin Revel da ke gabashin birnin Toulouse da safiyar ranar Laraba.

    Ofishin mai shigar da ƙara a birnin Toulouse ya shaida wa BBC cewa dangin yaron sun tabbatar da kamanninsa.

    Alex ya ɓace ne shekara shida da suka gabata bayan ya je hutu tare da mahaifiyarsa da kuma kakansa.

    Mahaifiyar da kuma kakansa nasa - waɗanda ba su ne ke da ikon kula da Alex ba - ba a sake ganinsu tun bayan ɓacewar tasa, amma an ci gaba da nemansu bisa alaƙa da ɓacewar tasa.

    A yanzu dai Alex na hannun hukumomi, yayin da ake jiran isowar 'yan sandan Birtaniya da ma'aikatan ofishin jakadancin ƙasar domin shirya yadda za a mayar da shi Ingila.

    'Yan sanda sun faɗa wa BBC cewa masu amfani da ababen hawa ne suka kai yaron ofishin 'yan sanda, bayan da suka kai gan shi yana gararamba a kan titi.

    Yaron ya ce ya shafe shekara biyu a Faransa, kamar yadda majiyar 'yan sandan ta bayyana.

  4. Ecowas ta tabbatar da dakatar da Nijar daga ƙungiyar

    Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas ta ce ta dakatar da Jamhuriyar Nijar daga dukkan harkokin ƙungiyar ƙasashen har sai ta mayar da mulkin dimokraɗiyya.

    Matakin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ecowas ta fitar da yammacin Alhamis, inda ta ce daga ranar 10 ga watan Disamba, ƙungiyar ƙasashen ta yarda cewa ba shakka, sojoji sun yi wa Shugaba Bazoum Mohamed juyin mulki.

    Ta ce kafin wannan lokaci, ƙungiyar na ɗaukar abin da ya faru a Nijar daga watan Yuli, a matsayin yunƙurin juyin mulki don haka, ba a dakatar da Nijar daga shiga harkokin mulki na Ecowas ba, abin da ke nufin jami'an gwamnatin Bazoum za su iya wakiltar Nijar a tarukan Ecowas.

    Ecowas ta ƙara da cewa har zuwa ranar da ta yi taronta na Abuja tsakanin shugabannin ƙungiyar ƙasashen, wanda shi ne karo na 64, Ecowas na ɗaukar Mohamed Bazoum a matsayin shugaban jamhuriyar Nijar.

    Sanarwar mai yiwuwa na martani ne ga wasu kalamai da jami'an gwamnatin mulkin sojan Nijar da suka hamɓarar da Bazoum Mohamed suka yi a ranar Laraba, suna zargin Ecowas da barin jami'an gwamnatin Bazoum na halartar tarukan ƙungiyar da sunan Nijar, Abin da suka ce ya ci karo da doka.

  5. 'Isra'ila za ta kawo ƙarshen hare-haren Gaza nan da mako uku'

    Wasu jami'an Amurka biyu sun shaida wa kafar yaɗa labarai a CBS - wadda abokiyar ƙawancen BBC ce - cewa Isra'ila ta shaida wa Amurka cewa za ta kawo ƙarshen hare-haren da take kai wa Hamas nan da mako biyu zuwa uku masu zuwa.

    Daya daga cikin jami'an ya ce hakan ba yana nufin kawo ƙarshen samamen soji a yankin ba, to amma ya ce hakan zai rage yawan hare-hare ta sama da na boma-bomaida Isra'ilar ke kai wa Gaza, kamar yadda kafar yaɗa labaran ta wallafa.

    Matakin na zuwa ne bayan da ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya shaida wa mai bai wa fadar shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan cewa ruguza Hamas zai iya ''ɗaukar watannai masu yawa''.

    "Amma za mu samu nasarar ruguza su," kamar yadda aka ambato shi yana cewa

  6. Shugaban Indonesia ya umarci sojoji su taimaki manoma a shuka shinkafa

    Shugaban Indonesia ya ba da umarni ga rundunar sojin ƙasar ta taimaka wa manoma wajen shuka shinkafa, yayin da tsananin fari da yanayin da ake kira El Nino ya ta'azzara, ke barazana ga yabanya.

    Shugaba Joko Widodo ya faɗa wa sojojin ƙasar su yi amfani da ruwan saman da aka samu a baya-bayan nan wajen taimaka wa ƙoƙarin noma a Indonesiya.

    Fari na tsawon lokaci ya rage yawan amfanin gona na abincin da aka fi ci a ƙasar mafi yawan jama'a a yankin Kudu maso Gabashin Asiya.

    Hauhawar farashi kuma ya ƙara yawan abincin da ake shigarwa, sannan yana barazana ga ƙoƙarin wadata ƙasar da abinci.

    Farin da aka samu tsawon watanni ya haddasa jinkirin fara girbin shinkafa - wanda galibi ake yi a watan Oktoba. Yawan shinkafar da ƙasar ta noma a bana ya ragu zuwa tan miliyan 30.9 daga tan miliyan 31.53 a bara.

    Yayin wata ziyara da ya kai yankin Pekalongan a tsakiyar Java ranar Laraba, Shugaba Joko Widodo ya wallafa wani bidiyo a tashar fadar shugaban ƙasar ta Youtube inda yake neman sojoji su fita su taimaka wa manoma da shuka.

  7. Isra'ila ta ce ruguza Hamas ka iya ɗaukar watanni masu yawa

    Isra'ila ta ce ruguza ƙungiyar Hamas ka iya ɗaukar ta zuwa watanni masu yawa.

    Ministan tsaron ƙasar Yoav Gallant ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan, a lokacin da ya ziyarci Isra'ila.

    Sanarwar bayan ganawar ta ambato Mista Gallant na cewa ''ruguza Hamas na buƙatar ƙarin watanni masu yawa''.

    Mista Gallant ya ce ba abu ne mai sauƙi ba ruguza gine-ginen da Hamas ta yi a Gaza.

    "Hakan na buƙatar lokaci - zai ɗauki watanni masu yawa, amma za mu samu nasarar lalata su," in ji shi.

    Ziyarar jami'in Amurkan na zuwa ne a yayin da ƙasashen duniya ke ci gaba da matsa lamba kan ƙaruwar kisa da taɓarɓarewar ayyukan tallafi a Gaza.

  8. Rebecca za ta zama mace ta farko da za ta yi alƙalancin wasa a Premier

  9. 'Yan Zamfara na kokawa da ƙona musu amfanin gona da 'yan bindiga ke yi

    Al’ummar ƙauyen Gwaram da ke karamar hukumar Talatar Mafara a jihar Zamfara, sun koka kan yadda ‘yan bindiga ke addabar su da hare-hare ba dare ba rana, inda har ta kai suna ƙona wa mutane amfanin gonar da suke nomawa.

    Mazauna garin sun ce ‘yan bindigar kan tattara abincin da suka noma ne su cinna masa wuta.

    Wannan lamari dai na barazanar haifar da yunwa a wasu sassan Najeriya sakamakon ƙalubalen tsaro da manoma ke fuskanta.

    Ga rahoton da Zubairu Ahmad Kasarawa ya haɗa muna.

  10. Kotun Ƙoli za ta yanke hukunci kan shari'ar neman sakin Nnamdi Kanu

    Jagoran ƙungiyar IPOB mai rajin ɓallewa don kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu, zai san matsayinsa a gobe Juma'a, ranar da kotun ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci a kan ƙarar da ya ɗaukaka don tursasa wa gwamnati ta sake shi.

    Gidan talbijin na Channels ya ruwaito cewa ayarin alƙalan kotun su biyar a ƙarƙshin jagorancin Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ne ya tsaida ranar yanke hukuncin bayan ya saurari bayanan ƙarshe daga lauyoyin gwamnati da kuma na jagoran 'yan a-waren.

    Lauyan Nnamdi Kanu ya roƙi kotun ba kawia ta bayar da umarnin gaggauta sakin shugaban IPOB ɗin ba, ta kuma ladabtar tare da cin tarar gwamnati wasu maƙudan kuɗaɗe saboda tsarewar da suke ci gaba da yi masa.

    Sai dai ɓangaren gwamnati, na neman kotun ƙolin ta jingine wani hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ya ba da umarnin a saki Nnamdi Kanu, kuma ta ba da damar ci gaba da yi masa shari'a a gaban babbar kotun tarayya kan tuhume-tuhume masu alaƙ da ta'addanci.

    Rahotanni sun ce a ranar 13 ga watan Oktoban 2022 ne, kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta ba da umarnin a saki Nnamdi Kanu daga inda ake tsare da shi, bisa hujjar cewa an sato shi kuma an ci mutuncinsa sannan "an ɗauko shi ta haramtacciyar hanya" daga Kenya zuwa Najeriya don ya fuskanci tuhume-tuhumen cin amanar ƙasa da ta'addanci.

  11. Yawan matalauta ya ƙaru zuwa miliyan 104 a Najeriya - Bankin Duniya

  12. An sake katse intanet da layukan sadarwa a Gaza

    Babban kamfanin sadarwa da ke Gaza ya ce an katse intanet da layukan sadarwa a yankin.

    Cikin wani saƙon X da kamfanin Paltel Ya wallafa ya ce an katse ''duka layukan sadarwa'' da ke Gaza sakamakon hare-haren da ake ci gaba da kai wa yankin.

    "Gaza ta sake shiga duhu," in ji kamfanin.

    A lokuta da dama an sha katse intanet da layukan sadarwa a Gaza, tun bayan fara yaƙin, ciki har da katsewar da aka yi a watan da ya gabata sakamakon rashin man fetur da za a saka wa injinan janaretocin kamfanonin sadarwar.

  13. An kori dukkan daraktocin hukumomi kula da sufurin jiragen sama na Najeriya

    Gwamnatin Najerya ta kori dukkan daraktocin hukumomin kula da sufurin jiragen sama a ƙasar sa'o'i bayan korar shugabannin hukumomin sashen.

    Cikin wata sanarwa da ministan sufuri, Festus Keyamo ya fitar ranar Alhamis, gwamnatin Najeriya ta ce ya kamata daraktocin da abin ya shafa, su miƙa ragamar aiki ga manyan jami'ai da ke hukumominsu nan take.

    Sanarwar ta samu sa hannun mai magana da yawun ministan sufurin jiragen sama, Odutayo Oluseyi.

    Hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya da hukumar kula da yanayin sararin samaniya ta Nimet da hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya da hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya da kuma hukumar bincike da tabbatar da tsaron lafiya ta ƙasa.

    Gwamnati ta ce mataki na da nufin sake fasalin harkar kula da sufurin jiragen sama da tabbatar da tsaron rayuka da inganci a fannin sufurin sama ga al'ummar Najeriya.

  14. Sojojin Nijar sun soki Ecowas kan yin taro da jami'an gwamnatin Bazoum

    Sojojin da ke mulki a Nijar sun bayyana halartar taron Ecowas da jami'an tsohuwar gwamnatin Mohammed Bazoum suka yi a matsayin wata takala kamar yadda kafar yaɗa labarai ta RTN ta bayyana.

    Tsohon Firaminista Mahamadou Ouhoumoudou da tsohon ministan harkokin waje Massoudou Hassoumi waɗanda dukkansu suka yi aiki ƙarƙashin hamɓararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum sun halarci taron Ecowas a Najeriya.

    A wata sanarwar bayan taro da Kanar Manjo Abdourahmane Amadou ya karanta, gwamnatin sojin ta ce Ecowas "tana son yi wa duk wani yunkuri na samar da maslaha ga yanayin siyasar ƙasar maƙarƙashiya".

    Ba zai yiwu Ecowas ta dakatar da Nijar daga ƙungiyarta ba sannan a ɗaya ɓangaren ta ƙyale wasu su wakilci ƙasarmu ba bisa tsari ba," in ji gwamnatin sojin.

    Da yiwuwar dangantaka tsakanin Nijar da Ecowas ta ƙara in tsami bayan da ƙungiyar ta ƙi amincewa da buƙatar Nijar ɗin na janye takunkuman da ta ƙaƙaba mata sakamakon juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli.

  15. 'An kashe mutum 179 cikin kwana guda a Gaza'

    Ma'aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce sojojin Isra'ila sun kashe mutum 179 a hare-haren da suka kai cikin kwana guda.

    Hakan ya sa adadin mutanen da suka mutu tun farkon yaƙin ya kai 18,787, yayin da kusan mutum 51,000 suka jikkata, kamar yadda ma'aikatar lafiyar ta bayyana.

    Isra'ila ta fara kai hare-hare cikin Gaza ne tun bayan da Hamas ta kai hare-haren 7 ga watan Oktoba, inda ta kashe mutum 1,200 tare da yin garkuwa da mutum 240.

    Sai dai an saki wasu daga cikinsu a lokacin yarjejeniyar musayar fursunoni cikin watan da ya gabata.

  16. 'Yan Najeriya na da 'yancin ɗaukar bidiyon 'yan sanda a bakin aiki'

    Hukumar 'yan sandan Najeriya ta ce \yan ƙasar a da damar ɗauar bidiyo da hotunan 'yan sanda a lokacin da suek bakin aiki.

    Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ƙasar, Muyiwa Adejobi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X ranar Alhamis.

    Adejobi na mayar da martani ne kan saƙon da wani mai amfani da shafin ya wallafa da ya ce 'yan sanda sun tatse shi naira 10,000 saboda bidiyon da ya ɗauke su a lokaci da suke binciken ababen hawa.

    Kakakin rundunar ya ce ba laifi ba ne ɗaukar hoto da bidiyon 'yan sanda a lokacin da suke bakin aiki.

    Ya ƙara da cewa rundunar ta sha gaya wa mutanen cewa babu laifi ɗaukar bidiyo da hotunan 'yan sandan da ke bakin aikin.

    Mista Adejobi ya ce duk wanda 'yan sanda suka ci zarafinsa saboda ɗaukarsu bidiyo ko hoto su kai rahoto ga hukumar 'yan sanda.

    Cikin sakonsa na X da ya wallafa, mista Adejobi ya ce ''ya kama kowane ɗan sanda ya sani cewa ba laifi ba ne ɗaukar bidiyo ko hotunansu a lokacin da suke bakin aiki''.

    Waɗanda ke cin zarafin masu ɗaukarsu hoto ko bidiyo saboda wannan, su daina.

  17. Fubara ya sa hannu kan kasafin kuɗin Rivers

    Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanya hannu kan kasafin kuɗin jihar na shekarar 2024 da ya kimanin naira biliyan 800.

    Hakan na zuwa ne kwana guda bayan gabatar da kasafin a zauren majalisar dokokin jihar mai mambobi biyar, ƙarƙashin jagorancin Edison Ehie.

    Nan take ne kuma 'yan majalisar suka gudanar da muhawara tare da amincewa da shi ba tare da ɓata lokaci ba, inda shi kuma gamnan ya sanya hannu a kansa yau Alhamis.

    An gudanar da bikin sanya hannu kan kasafin ne a babban ɗakin taro na ofishin gwaman da ke harabar gidan gwamnantin jihar.

    A ranar Talata ne dai wasu 'yan majalisar dokokin jihar 27 suka bayyana ficewa daga jam'iyyar PDP tare da komawa jam'iyyar APC.

    Lamarin da ya sa majalisar mai mabobi biyar ta ce ta kore su daga majalisar.

    A ranar Laraba ne kuma gwamnan jihar ya bayar da umarnin ruguza ginin majalisar dokokin jihar, yana mai cewa an ɗauki matakin ne bisa dalilan rashin ingancin ginin.

    To amma majalisar ta yi zamanta na ranar Laraba a gidan gwamnatin jihar, inda a nan ne aka gabatar mata da kasafin kuɗin jihar.

  18. An tuhumi wata mata da ta sace donot 10,000

    An tuhumi wata mata a Austrralia bisar zargin sace wata mota maƙare da donot da ya kai kimanin 10,000.

    Da safiyar ranar 29 ga watan Nuwamba ne motar ta ɓace daga wani gidan mai a Sydney babban birnin ƙasar.

    Mako guda bayan nan 'yan sanda suka gano motar, tare da dubban donot ɗin da suka lalace a wani wurin ajiye motoci, inda suka kama matar mai shekara 28 bisa zargin hannu.

    An dai zargi matar da laifin sace mota da yin tuƙi ba bisa ƙa'ida ba.

    Bidiyon da kyamarorin tsaro na CCTV suka ɗauka sun nuna matar na gararamba a harabar wani gidan mai tun da mairacen ranar 28 ga watan Nuwamba, kafin bidiyon ya nuna ta a lokacin da ta shiga cikin motar ɗaukar donot ɗin ta kuma tuƙa ta.

    Ba a dai sani ba, ko tana sane da cewa motar na ɗauke da donot 10,000.

  19. Kotu ta saki matar da aka ɗaure kan laifin kashe 'ya'yanta huɗu bayan gano kuskuren shari'a

    Wata mata da a baya aka yi wa laƙabi da ''mafi sharrin uwa'' ta samu 'yancin bayan da kotu ta gano cewa hukuncin ɗaurin da aka yi mata bisa laifin kisan 'ya'yan huɗu kuskure ne.

    A ranar Alhamis kotun ƙolin kudandin Wales ta ce hujjojin da aka yi amfani da ita wajen ɗaure Kathleen Folbigg ba su da ''tushe''.

    Gwamnati ta yafe wa matar mai shekara 56, tare da sakinta, bayan ta shafe shekara 20 a gidan yari.

    Misis Folbigg ta yi maraba da sabon hukuncin, tana mai cewa a baya an yi watsi da gaskiya da hujjojinta cikin gomman shekaru da suka gabata.

    "A baya kotu ta ɗora min laifi alhalin ta san cewa a wasu lokuta yara kan yi mutuwar fuju'a (Mutuwar da ba a tsammata ba)'', kamar yadda ta bayyana a wajen harabar kotun ranar Alhamis.

    An bayyana shari'arta a matsayin ɗaya daga cikin shari'u mafiya kuskure a Australia.

    An yanke mata hukunci ne kan mutuwar jariranta huɗu tsakanin shekarar 1989 zuwa 1999, 'yan tsakanin kwanaki 19 zuwa ata 18, inda masu shigar da ƙara a lokacin suka zarge ta da maƙure su.

    Inda a lokacin kotu ta yanke mata hukuncin ɗaurin shekara 40, kodayake daga baya an sassauta hukuncin zuwa shekara 30, sai dai ta ɗaukaka ƙara, amma ba ta yi nasara ba.

    A farkon wannan shekara ne kuma aka sabunta duba ƙarar tata, inda aka gano cewa akwai shakku game da hujjojin da aka yi amfani da su wajen kama ta da laifi.

    Sai aka ƙaddamar da sabon binciken kimiyya, wanda kuma ya gano cewa mutuwar jariran nata ta Allah da annabi ne, sakamon wata lalura da ta shafi ƙwayoyin halittarsu.

    Da wannan hujjar ne kuma kotun ta yi amfani wajen wanke ta daga laifin da aka tuhumeta da shi.

    Sai dai lauyoyinta sun ce za su buƙaci a biya ta diyyar ɓata mata lokaci da aka yi.

  20. Kwamishinan shari'a na jihar Rivers ya ajiye aiki

    Yayin da rikicin siyasa ke daɗa ƙamari a Jihar Rivers da ke Kudancin Najeriya, kwamishinan shar'a kuma babban atoni na jihar, Farfesa Zacchaeus Adangor ya ajiye aiki.

    Sai dai a wasikarsa ta ajiye aiki, Adangor ya faɗa wa Gwamna Similanayi Fubara cewa ya ɗauki matakin saboda wasu dalilai na ƙashin kai.

    Adangor wanda ya riƙe muƙami a gwamnatin baya ta Nyesom Wike, ya yaba wa gwamna Fubara saboda ba shi damar yin aiki a ƙarƙashinsa.

    Ƙurar rikicin siyasa ta turnuƙe a jihar ta Rivers tun bayan da aka fara samun saɓani tsakanin tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike da gwamnan jihar Similanyi Fubara.

    Lamarin da ya kai ga wakilan majalisar dokokin jihar, waɗanda ke biyayya ga Wike sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

    Baya ga haka nan an rushe ginin zauren majalisar, inda gwamnatin jihar ta kafa hujja da cewa ta yi ne a ƙoƙarin yin gyara.