Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ana ci gaba da gwabza faɗa a Gaza da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba and A'isha Babangida

  1. Mu kwana lafiya

    Mun kawo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na ranar Talata.

    Ku tara gobe da safe don kawo muku wasu sababbin rahotonnin.

    Mu kwana lafiya.

  2. Isra'ila na rasa goyon baya a duniya - Joe Biden, Daga Barbara Plett Usher, Wakliyar BBC a Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka

    Shugaban Amurka Joe Biden ya ce Isra'ila ta fara rasa goyon bayan da take samu a fadin duniya.

    Kalaman nasa sun dogara ne a kan bayanai daga harkokin wani gangami, kuma yana dangantaka batun ne a kan damuwar da kasashen duniya ke nuna da kaduwa game da luguden wutar da ake yi a Gaza.

    Sai dai, Biden bai bayar da wata alama da ke nuna cewa Isra'ila na rasa goyon bayan Amurka a kan matakin sojojin da take dauka a Gaza ba, duk da damuwar da ke karuwa ta gwamnatinsa game da dumbin asarar rayukan Falasdinawa da ruguje-ruguje kan cibiyoyin fararen hula.

    Ba shakka dai ya bayyana bambancin da suke da shi tsakaninsa da Isra'ila game da shirin da ke akwai kan makomar Gaza.

    Ya ce gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu na adawa da masalahar kafa kasa biyu tsakaninsu da Falasdinawa, wani abu da manyan jami'an gwamnatin Biden ke shelantawa bayan kawo karshen yakin da ake yi.

    Ya kuma neni Netanyahu ya "karfafa tare da sauya....gwamnati mafi ra'ayin 'yan mazan jiya a tarihin Isra'ila," don samo mafita ta dindindin ga rikicin Isra'ila da Falasdinawa.

  3. Tsawon ran 'yan Najeriya ya ƙaru

    Alkaluman tsawon rai a tsakanin 'yan Najeriya maza da mata sannu a hankali sun karu tun daga shekara ta 2015 zuwa 2022, a cewar hukumar kididdiga ta kasar.

    Wannan na kunshe ne a cikin wani rahoton kididdiga na hukumar don shekara ta 2022 da aka fitar ranar Talata a Abuja.

    Rahoton ya ce tsawon rai tun daga haihuwa ga 'ya'ya maza a Najeriya ya karu daga shekara 53.2 a 2015 zuwa shekara 55.1 a 2022, yayin da tsawon ran mata a Najeriya ya karu daga shekara 55.3 a 2015 zuwa shekara 57.2 a 2022.

    “Wannan karuwa na nuna cewa an samu ci gaba a tsawon wannan lokaci game da koshin lafiyar mata da kananan yara, kuma an samu bunkasar harkokin kula da lafiya," cewar rahoton.

    “Ya kuma nuna cewa an samu raguwar alkaluman mace-mace mai alaka da wani takamaiman sanadi.”

    Hukumar kididdiga ta Najeriya ta kuma ce don samun karin ingancin tsawon rayuwa a Najeriya, akwai bukatar gwamnati ta zuba kudi a shirye-shirye da manufofin bunkasa lafiya masu matukar tasiri.

  4. Ma'aikatar lafiya ta Falasɗinawa ta ce Isra'ila ta kashe mutum shida a Jenin

    Ma'aikatar lafiya ta Falasɗinawa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ta ce an kashe mutum shida sakamakon harin da jirgi maras matuƙi ya kai kan sansanin 'yan gudun hijira na Jenin.

    Ma'aikatar ta ce akwai yaro ɗan shekara 13 cikin Falasɗinawan da aka kashe a harin da Isra'ila ta kai.

    Tun da farko ta bayar da rahoton cewa mutum huɗu ne suka mutu kafin daga baya su zama shida.

  5. Lagos ta cika shekara hudu babu fashin banki ko daya - Sanwo-olu

    Gwamnatin Lagos ta bayyana samun gagarumin inganci na tsaron rayuka a fadin babban birnin harkokin kasuwancin na Najeriya, bayan an cika shekara hudu cur ba tare da an samu fashin banki ba.

    Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu ne ya bayyana haka yayin wani taron zauren jama'a kan batun inganta tsaro a Lagos ranar Talata.

    A ciki wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Babajide Sanwo-olu ya ce kokarin da suke yi ba tare da nuna gajiyawa ba, ya haifar da kyakkyawan sakamako.

    Gwamnan ya kuma bayyana samun gudunmawar naira biliyan biyu a asusun amintattu don tabbatar da tsaron jihar Lagos.

    Sai dai ya koka a kan karuwar tashe-tashen hankula masu alaka da bambancin jinsi a Lagos, inda ya ce an samu korafe-korafe fiye da 256, tare da kama mutum 333 da ake zargi.

    Babajide Sanwo-olu ya ce gwamnatinsa ta samar da sabbin motocin sintiri guda 300 don tallafa wa hukumomin tsaro a Lagos, da kuma karfafa tsarin tattara bayanan sirri da sake fasalin cibiyar karbar kiran gaggawa don kai dauki a fadin jihar.

  6. Kotu ta ce ɓangaren Fubara ya ci gaba da jagorancin majalisar jihar Ribas

    Wata babbar kotun jihar Ribas a kudancin Najeriya ta umarci kakakin majalisar dokokin jihar, Edison Ehie, ya ci gaba da jan ragama har sai lokacin da ta kammala sauraron ƙorafin da aka shigar gabanta.

    Kazalika, ta dakatar da 'yan majalisar da ke biyayya ga Ministan Abuja Nyesom Wike daga amfani da harabar majalisar bayan umarnin da gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, ya bayar na yi mata kwaskwarima.

    Mai Shari'a M.W Danagogo ne ya bayar da umarnin cikin wani hukunci kan ƙorafin da ya nemi kotun ta hana Amaewhule da wasu zuwa farfajiyar majalisar har sai an kammala gyaran ginin tsohuwar majalisar da aka ƙona.

    Edison Ehie, wanda ya shigar da ƙarar tare da majalisar dokokin jihar, ya kuma buƙaci a ba shi damar ci gaba da jagorantar majalisar har sai an kammala sauraron ƙarar.

    Haka nan, ya nemi kotu ta dakatar da Amaewhule daga bayyana kan sa a matsayin kakakin majalisar.

    • Yadda Wike ya tayar da ƙura bayan naɗa shi ministan Abuja
  7. Ana ci gaba da gwabza faɗa a Gaza da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

  8. An gano gawawwakin 'yan Isra'ila biyu da aka yi garkuwa da su

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta sun gano gawawwakin 'yan kasar biyu da Hamas ta yi garkuwa da su, a wani wuri da ake tsare da su a Gaza.

    Sun ce an shaida su a matsayin Eden Zecharya mai shekara 27, wadda aka sace daga bikin raye-raye na Nova da kuma Ziv Dado mai shekara 36 wadda tun tuni rundunar sojin ta Isra'ila ta bayyana mutuwarta.

    A cikin wata sanarwa, rundunar sojin Isra'ila ta ce an sanar da dangin mamatan game da wannan lamari.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa: "Rundunar Sojin Isra'ila na aika sakon ta'aziyya ga dangin wadanda suka mutu kuma za ta ci gaba da tallafa musu.

  9. Me ya faru yau a Falasdin?

    Idan yanzu kuka fara bibiyar mu, ga abitar abubuwan da suka faru zuwa yanzu a Gaza:

    • Isra'ila na ci gaba da luguden bam a Zirin Gaza, inda ta fi mayar da hankali kan birnin Khan Younis na kudanci.Tana kuma luguden wuta ta sama a can kudanci, inda a Rafah kusa da kan iyaka da Masar. Jami'an Hamas sun ce an kashe mutum 22 a can
    • Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kasa da kashi daya cikin uku na asibitocin Gaza ne ke ci gaba da aiki, kuma wadanda suke a buden, suna aiki ne rabi-da-rabi kawai. Jami'in Hukumar Lafiya Richard Peeperkorn ya ce "ba za mu sake yarda mu rasa karin wani asibiti ko cibiyar lafiya ba"
    • Ma'aikatar lafiya ta Falasdin a yankin Gabar Yamma da ke karkashin mamaya ya ce mutum shida aka kashe a Jenin, ciki har da wasu biyar a wani harin jirgi maras matuki. Ma'aikatar ta ce wani yaro dan shekara 13 na cikin Falasdinawan da aka kashe
    • Kungiyoyin ba da agaji na gargadin cewa bukatun ayyukan jin kan dan'adan a Zirin Gaza sun ta'azzara, don kuwa dan kankani ne daga cikin kayan tallafin da ake bukata ke iya shiga
    • Babban Zauran Majalisar Dinkin Duniya na gab da kada kuri'a kan wani kuduri wanda ba lallai ne a yi aiki da shi ba, da ke neman "tsagaita wuta don jin kan dan'adam cikin gaggawa” a Gaza
  10. Messi da Ronaldo za su fuskanci juna a Saudi Arabia

  11. Chiellini ya yi ritaya daga taka leda

  12. Kotu ta yanke wa sojoji maza hukunci kan cin zarafin sojoji mata ta hanyar lalata

    Wata Kotu a Japan ta samu wasu tsofaffin sojoji uku da laifin cin zarafin abokan aikinsu mata ta hanyar lalata.

    Wannan hukunci mai muhimmanci na zuwa ne bayan wata, mai suna Rina Gonoi ta haifar da muhawara tare da janyo hankalin duniya lokacin da ta bayyana labarinta a shafin YouTube a 2022.

    Daga nan ne masu gabatar da ƙara a birnin Fukushima suka sake gurfanar da mutanen uku a watan Maris.

    Yin magana kan cin zarafi ta hanyar lalata abu ne da mutane ke ƙyama a Japan, kuma ana kallon shi a matsayin abu maras kyawu.

    Sau da dama ba a cika jin rahoton irin wannan matsala ba, kuma batun ya janyo hankalin ƙasar ne kawai a shekarun baya-bayan nan, sa'ilin da aka samu rahotannin da suka girgiza al'umma, kamar na Ms Gonoi.

    Wannan ne hukunci mafi girma kan cin zarafi ta hanyar lalata da aka zartar a ƙasar, tun bayan da ƙasar ta yi yi gyaran-fuska ga dokokinta kan cin zarafi ta hanyar lalata, wanda ya hada da sake ma'anar abin da ake nufi da fyaɗe da kuma shekarun neman izini.

  13. Ana ci gaba da taƙaddama kan nuna wa dalibai zanen tsiraici a Faransa

    Ministan ilmi na Faransa ya kai ziyara wata makaranta, inda wasu dalibai suka ƙi kallon wani zane mai dauke da mata tsirara a lokacin darasi, lamarin da ya sanya malamarsu ficewa daga aji.

    Daliban sun kuma zargi malamarsu da furta kalaman wariyar launin fata da kuma ƙin jinin Musulunci, abin da makarantar ta musanta.

    Malamai a makarantar Jacques-Cartier da ke kusa da birnin Paris sun ƙauracewa aiki don mayar da martani.

    Tunzuri ga alama ya ƙaru tun lokacin da aka shiga sabon zangon karatu, inda jami'ai ke ba da misali da ƙorafe-ƙorafen iyaye game da samun matsala a manhajar karatu da kuma yadda ake hukunci.

    An fara rikici ne lokacin da wata malama ta nuna wa dalibai zanen mai suna Diana and Actaeon, wanda ke tsokaci gamre da wani bigire a labaran almara na sabon zamani daga littafin Metamorphoses na fitaccen marubucin waƙoƙin Romawa, wato Ovid.

    Daliban sakandire masu yawa ne 'yan aji daya, tsakanin shekara 11 zuwa 12, suka ce zanen na ƙarni na 17 daga gwanin zanen nan dan ƙasar Italiya, Giuseppe Cesari, ya bata musu rai, kamar yadda Sophie Venetitay daga wata kungiyar malamai ta shaida wa BBC.

    "Wasu dalibai sun kawar da kansu, kuma ransu ya baci, suka ce sun kadu," cewar Mis Venetitay, inda ta kara da cewa "wasu kuma sun zargi malamar da furta kalaman nuna wariyar launin fata" a lokacin darasi a aji.

    • Yadda aka yi wa wasu 'yan mata tsirara a hotunan da AI ya kirkira
  14. Sojojin Isra'ila sun yi karin haske kan silar mutuwar wasu dakarunsu a Gaza

    Sojojin isra'ila sun ce jimillar sojojin kasar 105 aka kashe tun farkon fara shirin mamaye ta kasa a Gaza.

    Yayin da 20 suka mutu a hare-hare bisa kuskure da suka ritsa da su, kamar yadda kafofin yada labaran isra'ila suka ruwaito.

    Wani mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila ya ce a cikin 20 din, soja 13 sun mutu ne sanadin harbi daga abokan aikinsu, wadanda suka yi kuskuren daukansu a matsayin abokan gaba.

    Sauran bakwai kuma sun mutu, a wasu al'amura masu alaka da sarrafa makamai da tartsatsin albarusai ko kuma aka tattake su da kuma "harbi ba tare da bin ka'ida ba".

  15. Peter Obi ya ziyarci mutanen da aka jefa wa bam a Kaduna

    Bayan harin bazata da sojoji suka kai a ƙauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da isassun kudade ga sojoji da sauran hukumomin tsaro domin inganta ayyukansu.

    Obi ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ziyarci waɗanda abin ya shafa a asibitin koyarwa na Barau Dikko da ke babban birnin jihar a ranar Talata.

    Gidan talabijin na Channels ya ruwaito Obi na koka wa da cewa kawo yanzu ƙasar nan ta samu tashin bama-bamai 16 da sojoji suka yi bisa kuskure da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 500, ba tare da wani abu da Gwamnatin Tarayya ta yi ba wajen ganin an daƙile aukuwar irin wannan bala’i.

    Sai dai Obi ya jaddada buƙatar gwamnati ta tallafa wa sojoji don ganin ba a sake samun tashin bama-bamai na bazata ba.

    Obi ya lura cewa isassun kudade ga sojoji shine mabuɗin wajen tinkarar matsalolin tsaro da ke addabar al'umma a wannan zamani.

    Ya goyi bayan kiraye-kirayen a binciki harin da sojoji suka kai ta sama, kamar dai yadda ya bayar da shawarar kafa wata gidauniya da za ta tallafawa waɗanda harin Tudun Biri ya rutsa da su, musamman wadanda lamarin mai da su marayu.

    • Harin sojoji a Kaduna: 'An ƙona mana yara an ƙona mana mazaje'
    • Hare-haren jiragen yaƙin Najeriya bisa kuskure takwas a kan fararen hula
  16. An kashe aƙalla fararen hula 30 a wani hari da aka kai a kauyen Burkina Faso

    Aƙalla fararen hula 30 ne wasu ‘yan bindiga sanye da kakin sojoji suka kashe a wani kauye da ke kudu maso gabashin Burkina Faso.

    An kashe mutanen ne a kauyen Dongounani da ke Fo commune ranar 8 ga watan Disamba, amma sai yau aka samu rahoton.

    “A ranar kasuwa, cewar wani shaida da ke wucewa, wasu mutane sanye da kakin sojoji sun zo a kan babura. An umurci wata mata ta bi su…Bayan ƴan mintuna kaɗan, sai mutanen sanye da riguna suka fitar da matar daga cikin taron, inda suka kashe ta a nan take. Daga nan ne mazauna garin suka yi ƙoƙarin guduwa, amma aka kama wasu kuma aka kashe su” in ji mai watsa labaran.

    Ya ƙara da cewa waɗanda abin ya shafa sun haɗa da ƙananan yara, mata masu juna biyu da kuma tsofaffi.

    Kawo yanzu dai babu wani ƙarin haske daga jami'an gwamnati ko rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na cikin gida.

    An zargi jami'an tsaron ƙasar ta yankin Sahel da aikata irin wannan ta'asa.

    A baya dai rundunar sojin ƙasar ta ɗora alhakin kai hare-hare kan fararen hula a kan ‘yan ta’addan da ta ce suna kama da jami’an tsaro.

  17. Kungiyar BudgIT ta yi ikirarin gano maimaicin ayyuka a kudurin kasafin kudin Najeriya

    Wata kungiya mai bibiyar harkokin kasafin kudi da ake kira BudgIT Nigeria ta nemi gwamnatin kasar ta sake nazarin kudurin kasafin kudin 2024 da Shugaba Bola Tinubu ya gabatarwa majalisa.

    A cikin wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafinta na X wanda a baya ake kira Tuwita, BudgIT Nigeria ta bayyana damuwar cewa bayan cikakken nazari kan abin da kudurin kasafin kudin ya kunsa, ta lura cewa gwamnatin Tinubu ta ci gaba da aiki da tsarin kasafin kudi mai cutarwa daga gwamnatin da ta gabata, da ke dabbaka cin hanci da rashawa da rashin aikin yi da kuma fatara.

    Sanarwar ta ce wani muhimmin abu da ta lura da shi, shi ne rashin sanya bayanan kasafin kudi dalla-dalla na wasu hukumomi da ma’aikatun gwamnati a cikin kudurin kasafin kudin.

    Ta ce ga misali babu bayanai dalla-dalla na kasafin kudin majalisar dokokin Najeriya da Hukumar raya yankin Neja Delta da hukumar raya yankin Arewa maso Gabas, sannan ba a ga kudurin kasafin kudin hukumomin kasar da dama ba.

    Kungiyar ta kuma ce nazarinta ya gano maimaicin ayyukan da aka warewa kudi a cikin kasafin daga ciki akwai kudin aikin gyara gidajen shugaban kasa da na mataimakinsa.

    Ta yi ikirarin cewa tun a baya cikin kwarya-kwayan kasafin kudin 2023, an ware naira biliyan takwas don gyara gidajen shugaban kasa da na mataimakinsa a fadar Aso Rock da kuma na Dodon Barrack da ke Lagos.

    Sai dai abin mamaki in ji kungiyar, an sake ware naira miliyan 500 don gyaran gidan shugaban kasa na Aso Rock, yayin da aka ware naira biliyan biyar don gyaran gidan Dodon Barrack a kwarya-kwaryan kasafin kudin 2023, sannan kuma aka sake gabatar da kudurin gyara gidajen a kan naira biliyan tara da miliyan 300 a kasafin 2024.

    • Fankon kundin kasafin kuɗi Tinubu ya ba mu — Ƴan Majalisa
    • ‘Majalisar dokoki ba ta bin diddigin yadda ake aiwatar da kasafin kudi'
  18. Gwamnati ta karya alƙawarin biyan ma'aikata tallafin naira 35,000 - NLC

    Ƙungiyoyin Ƙwadagon Najeriya sun bayyana damuwa kan yadda gwamnatin ƙasar ta kasa ci gaba da biyan ma’aikata naira dubu talatin da biyar a mastayin kuɗaɗen tallafi da ta yi alƙawarin biyan ma’aikata a kowane wata, sakamakon cire tallafin man fetur.

    Ma’akatan gwamnatin tarayyar da dama ne suka ce baya ga watan Satumba da aka biya su naira dubu talatin da biyar sau daya tak, har yanzu ba su sake samun wani ba.

    Ƙwamared Titus Amba, mataimakin shugaban ƙwadago na ƙasa ya ce musabbabin faruwan hakan ba inda ya ƙara da cewa ƙungiyar za ta yi tuntuɓa ta ji me ya sa aka fara biyan kuɗin tallafin kuma aka katse.

    Ga ƙarin bayani a rahoton da Zubairu Ahmad Kasarawa ya haɗa.

    • 'Yan sandan Bauchi na bincike kan magidancin da ake zargi da yi wa matarsa fashi da taɓarya
  19. Kyafyin din Chelsea James na yawan jin rauni

  20. Gwamnan Ondo Akeredolu zai fara hutun jinya gobe, Laraba

    Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, zai fara hutun jinya a yau Laraba, kamar yadda me magana da yawunsa, Richard Olatunde, ya bayyana.

    A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Olatunde ya ce yayin da Akeredolu ke hutun, mataimakin gwamnan, Lucky Aiyedatiwa, zai dauki tafiyar da lamurran jihar, a matsayin mukaddashinsa.

    Akeredolu, Babban Lauyan Najeriya (SAN), kuma tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), ya sake lashe zabensa a matsayin gwamnan jihar a watan Oktoban 2020 kuma an rantsar da shi a karo na biyu a watan Fabrairun 2021.

    Sai dai kuma, wa'adi na biyu na gwamnan, tun daga watan Janairun 2023, bai kasance cikin kwanciyar hankali ba, domin sai da aka kai shi ƙasar waje neman magani a watan Yuni.

    Dan siyasar mai shekaru 67 ya dawo Najeriya ne a watan Satumba bayan watanni da ya yi a ketare, inda ya ci gaba da zama a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

    Akeredolu dai na fuskantar matsin lamba daga jam'iyyun adawa kan ya yi murabus ko kuma ya miƙa mulki ga mataimakinsa, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya na shekara ta 1999 ya tanada.

    Haka kuma, masu biyayya ga gwamnan a majalisar dokokin jihar sun riƙa yin takun-saka da mataimakin gwamnan, lamarin da ya kai ga har sai da shugaba Bola Tinubu ya sanya baki.

    A cikin sanarwarsa, Olatunde ya ce gwamnan zai bayar da fifiko ga lafiyarsa tare da tabbatar da samun cikakkiyar lafiya kafin ya ci gaba da aikinsa.

    “Za a aika da wata takarda a hukumance ɗauke da bayani game da hutun jinyar da gwamnan zai yi da kuma sanarwar mika mulki ga mataimakin gwamnan ga majalisar dokokin jihar, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada." In ji sanarwar.

    Tun da farko dai, rahotanni a Najeriya sun ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci majalisar dokokin jihar Ondo ta tabbatar da miƙa harkokin mulki ga matamakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa ba tare da wani sharaɗi ba.