Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Hamas ta yi barazanar ƙin sakin mutanen da take garkuwa da su

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba and A'isha Babangida

  1. PDP ta yi martanin bayan sauyin shekar 'yan majalisar dokokin jihar Rivers zuwa APC

    Babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya PDP ta nemi hukumar zaben kasar INEC ta gudanar da sabon zabe don cike gibin da ta ce an samu bayan sauyin sheka da wasu 'yan majalisar dokoki a jihar Ribas suka yi.

    Jam'iyyar ta dage a kan cewa lallai sai 'yan majalisar dokokin jihar 27 sun sauka daga kujerunsu.

    Da safiyar yau ne aka ba da rahotannin cewa 'yan majalisar dokokin jihar sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP wadda a doronta ne aka zabe su, zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

    Ana kallon matakin a matsayin wani sabon babi da rikici siyasa tsakanin tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja na yanzu, Nyesom Wike da gwamnan jihar mai ci, Siminalayi Fubara.

    Kwanan baya ne rahotanni suka ce, ana yunkurin tsige gwamnan daga kan kujerarsa.

    Nyesom Wike dan jam'iyyar PDP, wanda amma ya karbi mukami a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta APC, ya shiga takun-saka da jam'iyyar tasa tun kafin babban zaben kasar, lokacin da ya gaza samun tikitin takarar shugaban kasa.

    Wasu masu sharhi na cewa sauyin shekar da 'yan majalisar dokokin jihar Ribas suka yi a ranar Litinin din nan, mai yiwuwa sharar fage ce ga yunkurin komawar minista Wike zuwa jam'iyya mai mulki, amma dai ba ta taba ji ya ambata ba a bainar jama'a.

  2. Sai da safe

    Mun kawo ƙarshen rahotonni a wannan shafi.

    Za mu kawo sababbi idan Allah ya kai mu gobe da safe.

    Fatan za mu kwana lafiya.

  3. An nemi Kotun Kolin Amurka ta yanke hukunci kan ko Trump na da rigar kariya

    Wani lauya na musamman ya nemi Kotun Kolin Amurka ta yanke hukunci a kan ikirarin ko ana iya gurfanar da tsohon shugaban kasar Donald Trump a gaban kotu kan zargin shirya makarkashiya don tafka magudin zaben 2020.

    Lauya Jack Smith na son kotun kolin ta yanke hukuncin cikin sauri a kan ikirarin Donald Trump na cewa yana da rigar kariyar shugaban kasa.

    Rokon ya zo ne bayan Mista Trump ya nemi a jinkirta shari'arsa a daidai lokacin da kotunan daukaka kara ke sauraron kararrakin da aka gabatar.

    A yanzu haka dai an tsara cewa za a fara sauraron shari'ar ranar 4 ga watan Maris a Washington DC.

  4. Tarayyar Turai za ta sa takunkumai ga 'yan kama-wuri-zauna da ke far wa Falasdinawa

    Gwamnatin Birtaniya ta bayyana alamun cewa tana shirin kakaba takunkumai ga 'yan kama-wuri-zauna na Isra'ila da ke da alhalin haddasa tarzoma kan Falasdinawa a yankunan Gabar Yamma da Kogin Jordan.

    Yanzu ita ma Tarayyar Turai ta ce za ta gabatar wa kasashe wakilan kungiyar kudurin cewa ya kamata su sanya takunkumai ga 'yan kama-wuri-zauna masu tsattsauran ra'ayi da suka aikata kan Falasdinawa a Gabar Yamma.

    Babban jami'in harkokin wajen Tarayyar Turai Josep Borrel ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan wata ganawa da ministocin kungiyar a Brussels.

    Hare-hare sun karu a Gabar Yamma tun bayan fara yaki a Zirin Gaza, bayan harin da Hamas ta kai kudancin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.

    Miyagun hare-hare ciki har da harbe-harben bindiga kan Falasdinawa daga Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna a Gabar Yamma da Kogin Jordan sun yi matukar karuwa.

    Da yawan hare-haren na faruwa ne yayin da kawayen Isra'ila na mafi kusanci, ciki har da Amurka da Birtaniya suke alla-wadai da tarzomar 'yan kama-wuri-zauna masu tsattsauran ra'ayi kuma sun nemi a gurfanar da masu aikata irin wannan laifi a gaban kotu.

  5. Ɗaliban Jami'ar Lafiya da aka yi garkuwa da su sun kuɓuta

    An sako ɗalibai takwas na Jami’ar Tarayya ta Lafiya a jihar Nasarawa da aka sace a makon jiya.

    Hukumomin jami’ar sun ce ɗaliban sun dawo cikin ƙoshin lafiya kuma tuni aka mika su ga iyayensu.

    Sai dai jami'an tsaro da hukumar jami'ar ba su bayyana ko an biya kuɗin fansa kafin a sake su ba.

    Abubakar Ibrahim, shi ne daraktan sashen hulɗa da jama’a da yada labarai na jami‘ar, ya kuma yi wa Badamasi Abdulkadir Mukhtar ƙarin bayani.

  6. Labarai da dumi-dumi, Osimhen ne gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na 2023

    Hukumar ƙwallon Afirka ta Caf ta sanar da ɗan wasan gaba na Najeriya, Victor Osimhen, a mastayin gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na 2023.

    Caf ta sanar da Osimhen ne a taron karrama gwarazan 'yan ƙwallon nahiyar na 2023 da ke gudana yanzu haka a birnin Marrakesh na Moroko.

    Ɗan ƙwallon mai shekara 24 ya taimaka wa ƙungiyarsa Napoli ta Italiya wajen lashe kofin Serie A, da kuma cin ƙwallaye mafiya yawa a kakar 2022-23.

    Shi ne ɗan wasan Najeriya na farko da ya lashe kambin cikin shekara 24, bayan Nwankwo Kanu ya lashe ta a shekarar 1999.

    • Osimhen ya ce yana kaunar Napoli a zuciya ba iyaka
    • 'Osimhen zai iya kai ƙololuwar nasara'
  7. Gwamnatin Ghana ta dakatar da shugabannin sakandare kan zargin cin hanci

    Hukumar kula da ilimi a Ghana (GES) ta dakatar da wasu shugabannnin makarantun sakandare 11 sakamakon zargin su da karbar kudaden sababbin ɗalibai ba bisa ƙa'ida ba. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ofisoshin GES na yankuna suka fitar.

    GES ta ce ta fara gudanar da bincike mai zurfi kan yadda shugabannin suka gudanar da ayyukansu.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton Fahad Adam daga birnin Accra:

  8. Fitattun 'yan wasa biyar da ba su taba lashe gwarzon Afirka ba

  9. Matashiyar da ta katse taron COP28 ta ce an ƙwace takardun izininta

    Yar shekara 12 mai fafutukar kare muhalli da ta katse taron COP28 kan muhallli na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce an karbe izinin ta.

    Tun da farko Licypriya Kangujam ta yi kira ga MDD ta umarci wadanda suka shirya taron muhalli su mayar mata da takardun bayananta idan har da gaske suna son kawo karshen gurɓacewar muhalli.

    Yar fafutukar dauke da kwali ta ce "rayuwar yan' uwanta yara kanana na fuskantar kalubale sakamakon sakaci, ya kamata ku ceci duniya daga bala'in sauyin yanayi".

    Licypriya Kangujam ta jagoranci gangamin yaki da gurbata muhalli a harabar Taj Mahal da ke kasar Indiya.

    • Taron sauyin yanayi Najeriya ta je yi a Dubai ko sharholiya?
    • Me ke janyo matsanancin zafin da ake fama da shi a duniya?
  10. Ana amfani da abinci da ruwan sha a matsayin makaman yaƙi a Gaza - MDD

    Hukumar MDD mai tallafa wa 'yan gudun hijirar Falasɗinawa ta ce ana amfani da yunwa da ƙarancin ruwan sha a matsayin makaman yaƙi a Zirin Gaza.

    United Nations Relief and Works Agency for Palestine Refugees (UNRWA) ta bayyana hakan cikin wani saƙo da ta wallafa a dandalin X game da yaƙin da Isra'ila ke yi da Hamas a Gaza.

    Tun a farkon yaƙin da ya ɓarke ranar 7 ga watan Oktoba Isra'ila ta sanar da toshe Zirin Gaza, inda ta hana shigar da abinci, da ruwan sha, da katse lantarki, kodayake daga baya ta ce ta dawo da su.

    "Da yawan mutane kan shafe kwana biyu ko uku ba su ci abinci ba a Gaza," in ji UNRWA.

    Ta ƙara da cewa: "Abokan hulɗarmu na yin duk mai yiwuwa da ɗan abin da suke da shi - amma dai ana ci gaba da amfani da abinci, da ruwan sha, da man fetur a matsayin makaman yaƙi a Gaza."

    MDD ta ce fiye da rabin Falasɗinawa miliyan biyu a zirin na Gaza na fama da yunwa.

  11. 'Yan Zimbabwe sun kaɗu da bayyana ministan kuɗin kasar a matsayin gwarzon Afirka

    Al'ummar kasar Zimbabwe da yawa ne suka bayyana matukar mamaki bayan an bayyana sunan Mthuli Ncube a matsayin "Ministan Kudi mafi Fice a Afirka cikin Shekarar nan" duk da hargitsin da tattalin arzikin kasar yake ciki.

    Wani mai amfani da dandalin sada zumunta na X wanda a baya ake kira Tuwita, ya ce lambar karramawar "daidai take da jinjina wa shugaban jirgin ruwan da ya auka cikin wani rami".

    Wani mai amfani da shafin ya bayyana lamarin da cewa "barkwanci ne mafi girma a cikin shekara goma".

    Masana tattalin arziki sun ce alkaluman rashin aikin yi a Zimbabwe ya kai kashi 85.

    Fiye da kashi 80% na hada-hadar kudi ana yin su ne dalar Amurka saboda rashin gwiwar da ake da shi a kan kudin kasar, cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Wata cibiya mai suna Reputation Poll International - da ta ce tana "kula da harkokin fice da mutane suka yi" ce - ta bai wa Mthuli Ncube lambar karramawar a ranar Lahadi.

    Ministan wanda Shugaba Emmerson Mnangagwa ya nada a shekara ta 2018, ya fada wa jaridar Herald mallakar gwamnati cewa ya yi matukar farin ciki da samun wannan lambar girmamawa.

    Ya ce lambar wata martabawa ce ga aikin da shi da ayarin ma'aikatan Baitul Mali suka yi ne na "jagorantar sauye-sauyen tattalin arziki a kasar".

    Sai dai, wani dan fafutuka Hopewell Chin'ono ya fada a shafin X cewa lambar karramawar wani "cin fuska" ne ga al'ummar Zimbabwe.

    • Ko an samu ci gaba a Zimbabwe bayan rasuwar Mugabe?
  12. Tinubu ya ƙaddamar da motocin gwamnatin Borno masu amfani da gas da lantarki

    Gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ƙaddamar da motoci 107 masu amfani da gas da masu amfani da lantarki da za a yi sufurin da su a faɗin jihar.

    Shugban Ƙasa Bola Tinubu ne ya jagoranci ƙaddamar da motocin hayar, a wani mataki na rage raɗaɗin janye tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi a watan Mayu.

    An yi bikin ne a kusa da fadar Shehun Borno Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-kanemi.

    A watan Satumba ne, Gwamna Babagana Umara Zulum ya ƙaddamar da motocin bas 77, waɗanda suka fara ɗaukar fasinjoji a birnin Maiduguri da kuma ƙaramar hukumar Jere, a cewar gmamnatin jihar.

    • Fankon kundin kasafin kuɗi Tinubu ya ba mu — Ƴan Majalisa
    • Manyan shari'o'in zaɓen Najeriya mafi bazata ya zuwa yanzu
  13. 'Yan wasan Man United na goyon bayan Ten Hag - McTominay

  14. Abin da ya sa muka ƙi sakin Bazoum - Tchiani

  15. A cikin hotuna: Hayaki na ci gaba da tashi a Zirin Gaza

    Mun samu sabbin hotuna daga sassan Zirin Gaza, yayin da hayaki ke turnukewa sama sanadin jerin hare-haren Isra'ila ta sama.

    Lamarin na zuwa ne bayan Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi kira ga kungiyar 'yan gwagwarmaya da makamai ta Hamas "su mika wuya nan take".

    Dubi hotuna na baya-bayan nan, a nan kasa:

  16. Mun raba wa iyalai 68,000 fulawa a Zirin Gaza - UNRWA

    Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke tallafa wa 'yan gudun hijirar Falasɗinawa ta ce ita da abokan hulɗarta sun raba wa mazauna Gaza fiye da 68,000 tallafin fulawa.

    Sai dai ta yi gargaɗin cewa har yanzu akwai buƙata mai yawan gaske.

    "Duk da irin halin da ake ciki, abokan hulɗr UNRWA na ci gaba da tallafa wa mutane," in ji ta cikin wani saƙon X da ta yaɗa daga shafin abokan hulɗar nata.

    "Jimillar iyalai 68,650 ne suka samu tallafin fulawa zuwa yanzu [a Gaza] - amma muna buƙatar ƙari sosai da sosai don taimaka wa mutum miliyan 1.9 da ke gudun hijira a Gaza."

    Tun da farko, UNRWA ta ce sama da rabin mazauna Gaza na fama da yunwa sakamakon hare-haren Isra'ila da suka hana rarraba kayan agajin yadda ya kamata.

  17. An ajiye Bailly da wasu 'yan wasa hudu saboda rashin kokari a Besiktas

  18. Ma'aikatar lafiyar Gaza ta ce an kashe Falasɗinawa 18,205

    An samu ƙarin bayani game da adadin Falasɗinwan da aka kashe a Zirin Gaza daga ma'aikatar lafiya ta Gazan ƙarƙashin Hamas.

    Ta ce mutum 18,205 ne suka mutu tun bayan fara yaƙin a ranar 7 ga watan Oktoba, yayin da aka raunata wasu 49,645.

  19. Za mu nemi a tabbatar da adalci ga mutanen Tudun Biri - Sarkin Musulmi

    Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ce kungiyar da yake jagoranta - Jama'atu Nasril Islam - za ta nemi a tabbatar da adalci ga mutanen da harin jirgin sojojin Najeriya maras matuki ya aukawa bisa kuskure a cikin jihar Kaduna.

    Sarkin Musulmi ya ba da wannan tabbaci ne yayin babban taron kungiyar Jama'atu Nasril Islam na shekara-shekara a ranar Litinin din nan, daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta sake neman afuwa a kan abin da ya faru, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

    “A matsayinmu na cikakkun Musulmai, mun dauka cewa abin da ya faru kaddara ce daga Allah kuma za mu duba, mu ga abin da za mu iya yi ga wadanda wannan harin ya shafa, za mu tabbatar da mun yi ta bibiya don ganin an yi adalci.

    “Ba ma ganin kowa amma muna son ganin an yi wa kowa adalci. A matsayinmu na Musulmai dukkanmu mun ji takaici kan abin da ya faru,” a cewarsa.

    Game da taron na Jama'atu Nasril Islam, Sarkin Musulmi ya ce an tsara shi ne don tattaunawa kan batutuwan da ke faruwa a fadin duniya game da Musulmai da kuma addinin Musulunci.

    Ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta mayar da hankali wajen gyaran titunan kasar musamman titin Minna zuwa Suleja da Minna zuwa Bida wadanda ke cikin mummunan yanayi a jihar Neja.

    A jawabinsa, ministan yada labarai na Najeriya, Alhaji Mohammed Idris ya sake nanata neman afuwar Shugaba Bola Tinubu da kuma jajantawa kan mummunan harin jirgin sama maras matuki da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane da jikkata wasu da dama a garin Tudun Biri.

    Ya ce shugaban kasar ya amince da fara shirin FULAKO, wanda zai ba da damar gina gidaje da kananan asibitoci da makarantu da dakunan kula da lafiyar dabbobi a wani bangare na bin matakan da ba na soji ba, ga rikice-rikicen 'yan fashin daji da na satar mutane don kudin fansa a arewa.

    • Tarihin rayuwar Sultan na Sokoto, Sarkin Musulmin Najeriya
  20. 'Isra'ila ta ci gaba da luguden wuta a kudanci da tsakiyar Gaza'

    Kafofin yada labaran Falasdinawa sun ba da rahoto kai miyagun hare-hare da isra'ila ta kai Zirin Gaza ta sama a ranar Litinin.

    Kamfanin dillancin labaran Wafa na gwamnatin Falasdin ya ce mutum shida, akasarinsu kananan yara ne aka kashe lokacin da aka jefa bam a gidan iyalin Subh da ke unguwar Tal al-Sultan a birnin Rafah na kudanci da safe.

    Shi ma, kamfanin dillancin labaran Safa mai alaka da kungiyar Hamas, ya wallafa sunayen mutum goma da ya ce sun mutu, ya kara da cewa a cikinsu har da 'yan gudun hijira wadanda suka tsere wa hare-haren Isra'ila daga birnin Khan Younis mai makwabtaka.

    Kamfanin Wafa ya ce an kashe mutum biyar, ciki har da yara uku a wani hari kan wani gida a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat, sannan an kashe wata mata da yaro lokacin da aka kai hari gidan iyalin Mishari da ke garin Deir al-Balah mai makwabtaka.