Kusan sojojin Sudan 250 ne suka fice daga gabashin Dr Kongo, kwanaki bayan sojojin Kenya sun fara ficewa daga yankin, bayan ƙarewar yarjejeniyar.
Sojojin na daga cikin dakarun gabashin Afirka da aka kai ƙasar shekarar da ta gabata domin aikin wanzar da zaman lafiya a rikici tsakanin dakarun sojin DR Kongo da 'yan tawayen ƙungiyar M23.
Rahotonni da dama na cewa ƙungiyar 'yan tawayen na samun goyon bayan ƙasar Rwanda, zargin da ƙasar ta sha musantawa.
Akwai fargabar ci gaba da rikicin a gabashin ƙasar, ka iya shafar zaɓen ƙasar da za a yi cikin wannan wata.
Suma sojojin Sudan ta Kudu sun fice daga birnin goma a jirgin sama a ranar da yarjejeniyar wanzar da zaman lafiyar soji a gabashin ƙasar ke ƙarewa.
Shugaban ƙasar DR Kongo Felix Tshisekedi ba ya son zaman dakarun a ƙasar, don haka ya ƙi amincewa da tsawaita wa'adin zaman nasu.
An dai kai sojojin ne da nufin kawo ƙarshen rikici da ƙungiyar 'yan tawayen M23.
Shugabannin ƙasashen yankin gabashin Afirka na buƙatar tattaunawa don kawo ƙarshen rikicin, yayin da shugaba Tshisekedi ke son amfani da ƙarfin soji.
A nan gaba kaɗan ne cikin wannan wata za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasar, Mista Tshisekedi na buƙatar ƙuri'un yankin gabashin ƙasar, wannan dalili ne watakila ya sa yake son murƙushe gomman ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.
Kusan shekara 20 da aka shafe ana yaƙarsu, bai samar da wani ingantaccen sakamako ba.