Sojojin Isra'ila sun kashe mutum ɗaya a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan
Ma'aikatar lafiya ta Falasɗinawa ta sanar da cewa sojojin Isra'ila sun kashe wani Bafalasdine guda daya tare da jikkata wasu hudu a wani samame da suka kai cikin dare a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan. .
Ɗaya daga cikin waɗanda suka jikkata yana cikin mawuyacin hali", in ji ma'aikatar.
A cikin kwanaki bakwai da suka gabata, an kashe aƙalla Falasdinawa takwas a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ciki har da yara biyu.
Bisa ƙididdigar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi, an kashe Falasɗinawa 246 da suka hada da yara 65 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordantun ranar 7 ga watan Oktoba.
Wannan adadi bai hada da ‘yan uwan Falasɗinawa biyu da aka kashe a harin da aka kai kan fararen hula a wata tashar bas a makon jiya.
- Daruruwan mutane na ci gaba da ficewa daga asibitin Al-Shifa na Gaza
- 'Na rasa kusan duk ƴan'uwana a rikicin Isra'ila da Gaza'