Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Aisha Adam Hussaini ce ta lashe gasar Hikayata ta BBC Hausa, 2023

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa, Abdullahi Bello Diginza and Haruna Kakangi

  1. Sojojin Isra'ila sun ce za a ci gaba da tsagaita buɗe wuta a Gaza

    Sojin Isra'ila sun sanar da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Gaza da ƙarin kwana guda, daidai lokacin da masu shiga tsakani ke kokarin ganin an sako karin wadanda bangarorin biyu ke tsare da su.

    Isra'ilawa 12 da 'yan Thailand 4 da mayaƙan Hamas ke tsare da su a Zirin Gaza, da kuma suka samu 'yanci a jiya Laraba sun isa Isra'ila.

    Ita ma Isra'ila ta saki Falasdinawa mata da kananan yara 30 da ta ke tsare da su agidajen kasonta.

    Majiyar FalasƊinawa na cewa za a Ƙara tsawaita tsagaita wutar da kwanaki 4, yayin da majiyar Isra'ila ke cewa da kwanaki 2.

    Sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken na Tel Aviv domin bukatar kara wa'adin.

    • Yadda Hamas ta haɗa dakarun da suka kai wa Isra'ila harin 7 ga Oktoba
    • Abin da ya kamata ku sani kan yarjejeniyar Isra'ila da Hamas
  2. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da war haka.

    Barkan ku da sake kasancewa da mu a shafin kai tsaye na BBC Hausa

    Aisha Babangida ce za ta kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.