Sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijar sun soke dokar hana fasa-kwaurin 'yan ci-rani a ƙasar, da ta shafe tsawon shekara takwas.
Dokar ta bai wa hukumomi damar ɗaukar mataki a kan masu safarar ƴan ci-rani ta yankin babbar hamadar Nijar zuwa Libya kafin su dangana da Turai.
Amma an hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum - wanda ya yi aiki da Tarayyar Turai don dakile kwararar mutane ta Tekun Bahar Rum - daga kan mulki a watan Yuli.
Tuni dai Janar Abdourahmane Tchiani ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban ƙasa.
Gwamnatin soji da ke mulki ta sanar da soke dokar ne a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce dokar ba ta yi la'akari da muradun Nijar da 'yan ƙasar ba.
Haka kuma ta ce za a saki duk waɗanda aka samu da laifi a karkashin dokar ta 2015.
Matakin dai wata manuniya ce cewa gwamnatin mulkin soji a Yamai, babban birnin ƙasar na shirin tabbatar da ikonta kan 'yancin cin gashin kan ƙasar, duk da matsin lamba daga ƙasashen duniya.
Bayan juyin mulkin da aka yi, Tarayyar Turai ta dakatar da duk wasu ayyukan haɗin gwiwar tsaro da ƙasar da ke Afirka ta Yamma.
Babban jami'in harkokin waje na EU, Josep Borrell, ya bi sawun Amurka da Faransa a watan Yuli ta hanyar kin amincewa da Janar Tchiani a matsayin shugaba.
Ya kuma ce za a dakatar da tallafin kuɗi da ake bai wa Nijar, har sai baba-ta-gani.
Kawo yanzu dai ba a bayyana yadda ƙungiyar ta Turai za ta mayar da martani ga abin da ke zama babbar illa ga dabarunta na dakile kwararar ƴan ci-rani daga Afirka ba.
A shekara ta 2015, masu neman mafaka da ƴan ci-rani sama da miliyan daya ne suka yi ƙoƙarin shiga Turai, lamarin da ya sa Nijar ta matsa kaimi wajen zartar da dokar da aka soke yanzu.
An samuwar raguwa sakamakon haka - amma masu fataucin sun koka da aiwatar da ita a cikin shekarun da suka biyo baya.
A yanzu dai akwai fargabar cewa ƙungiyoyin masu safarar mutane na iya ganin soke dokar a matsayin wata dama ta sake tura ƴan ci-rani zuwa ƙasashen da ke kan iyaka da Nijar kamar Libya ko Aljeriya domin tafiya Turai.
-
Abin da ya hana sulhu tsakanin Ecowas da Nijar - Tuggar
-
Kawuna sun rabu kan korar da sojojin Nijar ke wa ƙasashen duniya