Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kungiyar NIPR ta damu kan matsayin Najeriya a idon duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najieriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Hamas ta sanar da mutuwar kwamandojinta huɗu

    Rundunar sojin Hamas, 'al Qassam Brigades', ta sanar da labarin kisan kwamandojinta huɗu.

    Cikin wata sanarwa da ta saki ta shafinta Telegram - da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato - ƙungiyar ta ce ɗaya daga cikin kwamandojin nata da aka kashe shi ne Ahmad Al Ghandour, da aka fi sani da Abu Anas, da aka bayyana da ''mamban majalisar ƙoli ta sojin ƙungiyar wanda kuma shi ne kwamandan yankin arewaci".

    Sai dai sanarwar ba ta yi ƙarin haske kan lokaci da wurin da ake kashe kwamandojin ba.

  2. Amsoshin Takardu

  3. 'Yara 'yan uwan juna da Hamas ta saki ba su san an kashe mahaifiyarsu ba'

    Kawun wasu yara wa da kanwa da Isra'ila ta sako jiya ya ce bai san yadda zai sanar musu da kisan mahaifiyarsu ba.

    An ɗauke 'yan uwan junan biyu - Noam Or, mai shekara 17, da ƙanwarsa Alma, mai shekara 13 - a gidansu da ke Kibbutz Be'eri ranar 7 ga watan Oktoba.

    Kawun yaran mai suna Ahal Besorai ya shaida wa BBC yadda 'jikinsa ya yi sanyi" bayan da ya yi magana da yaran ta hanyar kiran bidiyo a lokacin da suke asibiti bayan an sake su.

    “Labarin yadda aka kama su da yadda aka riƙe su na nuna cewa sun sha wahala, sannan kuma ba su san cewa an kashe mahaifiyarsu da 'yar uwarsu ba," in Berosai.

    "Dole ne mu gaya musu wannan baƙin labari. Yaran na cikin yanayi na razana da firgici, kasancewar ba a tsare su tare da mahaifisu ba wanda shi ma aka kama shi, an tsare su daban-daban".

    • Labarai da dumi-dumi, An fasa gidan yari tare da sakin fursunoni a Saliyo

      Rahotonni daga Saliyo na cewa an kai hari gidan yari tare da sakin fursunoni, jim-kaɗan bayan jin ƙarar harbe-harbe a Freetown babban birnin ƙasar da safiyar yau Lahadi.

      Wani jami'in da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce shaidun gani da ido sun tabbatar masa cewa wasu mahara ɗauke da makamai sun fasa gidan yarin 'Pademba Road' da ke tsakiyar birnin Freetown tare da sakin fursunoni.

      Kawo yanzu ba a sa adadin fursunonin da suka tsare ba.

      Da safiyar yau ne mazauna birnin suka ce sun ji ƙarar harbe-harben ne daga aƙalla barikokin soji biyu da ke birnin.

      Harin gidan yarin na zuwa ne bayan da hukumomin ƙasar, suka yi kira ga 'yan ƙasar da su kwantar da hankula, suna masu cewa sun shawo kan matsalar.

      Cikin sanarwar da shugaban ƙasar, Julius Maada Bio ya fitar daga fadarsa, ya ce an maido da zaman lafiya, tare da ƙaddamar da farautar maharan.

      Ƙungiyar Ecowas da Amurka sun yi Allah wadai da lamarin

      Tuni dai aka sanya dokar hana fita a faɗin ƙasar

    • Bafalasɗiniyar da ta kwashe shekara takwas a gidan yarin Isra'ila ta samu yanci

      Israa Jaabis na daga cikin Falasɗinawa mata da aka saki daga gidajen yarin Isra'ila ranar Asabar, a wani ɓangare na musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Hamas.

      An ɗaure ta a gidan yarin tun shekarar 2015, bayan da motarta ta lalace a kan wata babbar hanya, kilomita ɗaya da rabi daga wani shingen bincike a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

      An samu gardama kan dalilin lalacewar motar, Inda Isra'ila ta ce matar ta yi yunƙurin kai harin bom ne da motar.

      To amma a lokacin kafofin yaɗa labaran Larabawa sun ce motar ta lalace ne sakamakon samun matsalar inji, lamarin da ya sa motar ta kama da wuta.

      Jaabis ta samu raunukan ƙuna a lokacin aukuwar lamarin, inda har fuskarta ta ƙone.

      Daga nan ne aka yanke mata hukuncin ɗaurin shekara 11 a gidan yari, inda kawo yanzu ta shafe shekara takwas daga ciki, kafin a sake ta a jiya.

      A shekarar da ta gabata ne ta rubuta takardar buƙata da hukumomin gidajen yarin Isra'ila na ba ta damar, yi mata aiki a hancinta da kuma fuskarta, buƙatar da Isra'ila ta yi watsi da ita.

      Bayan da ta shaƙi iskar 'yanci, Jaabis, mai shekara 38 ta rungume ɗanta, Mua’tassim, mai shekara 15, da ta bari a lokacin yana ɗan shekara takwas a duniya.

    • Shugaban Saliyo ya yi kiran a kwantar da hankula

      Rahotonni daga Saliyo na nuna cewa har yanzu ƙura ba ta lafa ba, duk kuwa da dokar hana fita da hukumomin ƙasar suka sanya, bayan da wasu mahara suka yi yunkurin kutsawa cikin barikokin soji a birnin Freetown.

      Mazauna birnin sun ce sun jin ƙarar harbe-harbe manyan makamai daga ɓangaren barikin soji na Wilberforce da ke kusa da fadar shugaban ƙasa.

      Cikin sanarwar da shugaban ƙasar ya fitar daga fadarsa, ya ce tuni aka shawo kan matsalar, kuma an ƙaddamar da farautar maharan, to amma shaidu sun ce har yanzu tsugune- ba ta ƙare ba.

      Wakilin BBC da ke birnin ya ce har yanzu ƙurar ba ta lafa ba.

      Ya ce ya ga sojoji ɗauke da manyan makamai a birnin, sannan ya ga wasu da ke rera waƙoƙin cewa sun shirya ''Tsaftace Saliyo".

      A watan Yuni ne shugaba Julius Maada Bio ya sake lashe zaɓe da kankanin rinjaye, lamarin da ya kusa kaiwa ga zagaye na biyu.

      A watan Agusta kuma aka kama mutane masu yawa ciki har da manyan sojojin ƙasar bisa zargin shirya wa shugaban ƙasar juyin mulki.

      Cikin fiye da shekara uku da suka gabata ana samun yawaitar juyin mulki a Yammaci da yankin tsakiyar Afirka, ciki har da Guinea mai makwabtaka da har yanzu ke ƙarƙashin mulkin soji.

    • Masu ɗinka tufafin mata sun koka kan tilasta musu rufe shagunansu a Afghanistan

      Masu ɗinkin tufafin mata sun gudanar da zanga-zanga a Afghanistan musamman a birnin Herat bayan hukumomin Taliban sun tilasta masu rufe shagunansu.

      Daya daga cikin maɗinkan ya ce rayuwa ta yi tsanani a Afghanistan saboda ƙaruwar talauci da rashin ayyukan yi.

      Babu dai wata sanarwa daga shugabannin Taliban game da matakin.

      Hukumomin Taliban ɗin dai sun ɗauki matakin rufe makarantun mata da kuma hana matan zuwa jami'a tun bayan da suka ƙwaci mulki shekaru biyu da suka gabata

    • Labarai da dumi-dumi, Ana jin ƙarar harbe-harbe a birnin Freetown na Saliyo

      Ana jin ƙarar harbe-harbe a Freetwon babban birnin Saliyo da sanyin safiyar yau Lahadi.

      Mazauna birnin sun ce sun ji ƙarar harbe-harben ne daga aƙalla barikokin soji biyu.

      Tuni hukumomi suka sanya dokar hana fita a faɗin ƙasar baki ɗaya wadda ta fara aiki nan take.

      Cikin wata sanarwar da ma'aikatar yaɗa labaran ƙasar ta fitar, ta ce wasu mutanen ne da ba a son ko su wane ne ba, suka yi yunƙurin shiga barikokin sojin ƙasar na Wilberforce da ke birnin Freetown

      Sanarwar ta ce jami'an tsaro sun samu nasarar fatatakar 'yan bindigar.

      A baya-bayan nan ƙasashen yankin Yammacin Afirka na fuskantar barazanar juyin mulki, inda a cikin shekara uku aka samu juyin mulkin soji a wasu ƙasashen yankin, ciki har da Guinea mai makwabtaka da Saliyo.

    • Isra'ila ta ce ta karɓi jerin sunayen mutanen da za a saki a rukuni na uku

      Isra'ila ta ce ta karɓi jerin sunayen rukuni na uku na mutanen da aka yi garkuwa da su, waɗanda Hamas za ta saki ranar Lahadi.

      Ofishin firaministan Isra'ila ya ce tuni aka sanar da 'yan uwansu wannan mataki.

      A ranar Asabar ‘yan Isra’ila 13 da ‘yan ƙasar Thailand huɗu Hamas ta saki.

      Haka kuma Isra'ilar ta saki ƙarin falasdinawa 39 da take tsare da su - Shida daga cikinsu mata ne da yara - wasunsu sun shafe shekaru a tsare.

    • Assalamu alaikum

      Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barnku da hutun ƙarshen mako.

      Abdullahi Bello diginza ke fata sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

      Ku ziyarci shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.