Mazauna yankin arewa maso yammacin ƙasar Habasha mai fama da tashin hankali na Amhara sun ce suna zargin dakarun gwamnati da kai hare-hare da jiragen sama marasa matuka, yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin sojoji da mayakan sa-kai.
Mazauna yankin Gabas da Yammacin Gojjam da kuma tsakiyar birnin Gonder na yankin sun shaida wa sashen Amharic na BBC cewa sun ga faɗan da aka kwashe kwanaki ana gwabzawa.
Rikicin dai a cewar mazauna yankin ya haɗa da amfani da manyan makamai da jirage marasa matuka, lamarin da ke haifar da damuwa ga lafiyar fararen hula.
A wata gunduma kuma, mazauna garin sun ce an kai hari ta sama a wata makaranta.
A birnin Lalibela mai tarihi, limamai da wani fitaccen dan adawa sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "rashin kulawa da harba manyan makamai na iya jefa majami'u cikin hatsari, waɗanda Kungiyar Ilimi da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNECSCO ta amince da su a matsayin wuraren tarihi na duniya.
Tashe tashen hankula sun ɓarke a cikin watan Agusta bayan kwashe watanni ana takun saka dangane da umarnin da gwamnati ta bayar na rusa wata ƙungiyar sa kai ta yankin.
Mayakan sa kai na yankin da aka fi sani da Fano sun mamaye manyan garuruwan yankin inda suka mamaye filin tashi da saukar jiragen sama na takaitaccen lokaci a farkon rikicin amma tun daga lokacin sojojin gwamnati suka fatattake su.
Sojojin dai sun ci gaba da gudanar da ayyukansu a ƙananan garuruwa da kauyuka.
Yunkurin da BBC ta yi don jin ta bakin jami'an Amhara bai yi nasara ba kuma babu wani bayani a hukumance game da fadan da aka sake gwabzawa.
-
Yadda aka kassara rundunar sojin Habasha
-
Habasha: Mahara sun hallaka mutun 32 a jihar Oromo