Al'ummar Ghana, musamman magoya jam'iyyar NPP mai mulki na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu, bayan tsayar da Mataimakin Shugaban Kasar, Alhaji Mahamudu Bawunia, a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar a zabe mai zuwa.
A karshen mako ne dai, aka kammala zaben fid da gwani na jam'iyyar NPP tsakanin masu neman takara hudu, wadanda aka tantance daga cikin kusan mutum goma.
Mataimakin Shugaban Kasa Mahamudu Bawumia, zai kasance dan arewa na farko kuma Musulmi da zai yi takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam'iyyar NPP tun bayan komawar Ghana kan tafarkin dimokradiyyar jam'iyyu da dama a 1992.
A jawabinsa bayan samun nasara, Mahamudu Bawumiya ya yi alkawarin jagorantar NPP "mai hadin kai da kuzari" zuwa nasara a zaben kasar na 2024.
Ya lashe zaben fitar da gwani ne da gagarumin rinjaye, inda ya samu kuri'u kashi 61.47%. Babban abokin karawar Bawumia a zaben fid da gwanin na karshen mako, Kennedy Ohene Agyapong, wanda ya samu kashi 37.4 na kuri'u da aka kada, ya karbi sakamakon zaben.
Shugaba Nana Akufo-Addo zai sauka daga kan mukamin shugaban kasa bayan zaben watan Disamban 2024, lokacin da zai kammala wa'adin mulkinsa na biyu.
Ana sa ran zaben zai fi zafi tsakanin 'yan takarar shugaban kasa biyu, Mahamudu Bawumia na jam'iyyar NPP da tsohon shugaban Ghana John Dramani Mahama na babbar jam'iyyar adawa ta NDC.
Tare da Mista Mahama wanda shi ma ya fito daga arewa, wannan ne karon farko da manyan jam'iyyun siyasar Ghana biyu suka tsayar da 'yan takarar shugaban kasarsu duka 'yan arewa.
Ana kallon kudancin Ghana, a matsayin inda jam'iyyar NPP ta fi karfi, yayin da NDC ke da da dumbin magoya baya a arewaci.
Dauko Mahamudu Bawumia, NPP na fatan cewa za ta samu karin karbuwa a yankin arewa, yayin da jam'iyyar ke sa ran ci gaba da rike martabarta a tsakanin magoya baya daga kudancin kasar.
Wani dan kasar da muka zanta da shi, ya ce zaben mataimakin shugaban Ghana a matsayin dan takarar NPP, wani babban kalubale ne ga jam'iyyar NDC mai adawa da kuma dan takararta John Mahama.
Ya ce tsohon shugaban kasar Mahama ya taba mulki, kuma sun ga kamun ludayinsa, ba sabon dan takara ba ne a wajensu.
Shi ma wani wanda ga alama mai goyon bayan jam'iyyar NDC ne ya ce, Lashe zaben da Bawumia ya yi, bai ba su wani tsoro ba.
Ya mayar da martani ga masu ikirarin za su rusa aniyar dan takarar NDC na cin zabe wa'adi na biyu.
Mahamudu Bawumia shi ne shugaban kwamitin kula da tattalin arziki na gwamnatin Ghana don haka zai fuskanci gagarumin aiki wajen shawo kan masu zabe su amince su kada masa kuri'u, don bai wa NPP karin damar mulki a wa'adi na uku.
-
Jama'iyar NPP a Ghana na duba halin zuwa kotu
-
Yadda Babban Bankin Ghana ya yi asarar dala biliyan 5 a shekara ɗaya