Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Amurka ta ce har yanzu akwai mutum 400,000 a arewacin Gaza

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. MDD ta kaɗu da mummunan hari kan motocin majinya a Gaza

    Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya ce ya kaɗu matuka kan mummunan harin da aka kai wa motocin ɗaukar marassa lafiya a Gaza, inda ya bayyana hakan abu mafi muni a dan tsakanin nan.

    Sojojin Isra'ila sun kare matakin kai hari kan motocin babban asibitin Gaza a jiya Juma'a.

    Mai magana da yawun gwamnatin Isra'ila Evlyn Levy ya faɗa wa BBC cewa haƙika a ƙarƙashin dokokin duniya, motocin ɗaukar marasa lafiya na da kariya, amma da zarar an yi amfani da su wajen jigilar makaman yaƙi, to sun rasa wannan kariyar.

    Ya zargi ƙungiyar Hamas da amfani da motocin domin jigilar mayaƙanta.

    A ɓangare guda ƙungiyar agajin MDD da ke kula da 'yan gudun hijirar Falasɗinawa ta ce lamura sun fara fin ƙarfinta dangane da bai wa Falasɗinawa da ke fakewa a wurarenta kariya.

  2. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkan mu safiyar Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a wannan yini, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a fadin duniya.

    Sai ku biyo mu ta shafukanmu na Facebook da X, domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.

    Muna alfahari da ku!