Amurka ta ce har yanzu akwai mutum 400,000 a arewacin Gaza

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Yaƙin Gaza ya ɗauke hankalin duniya daga kan namu - Zelensky

    .

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce yaƙin da ake yi tsakanin Isra'ila da Gaza ya ''ɗauke hankali duniya" daga yaƙin da ake yi a ƙasarsa.

    Ya ce wannan na ''ɗaya daga cikin burin'' Rasha, wadda ta ƙaddamar da mamaya kan Ukraine a watan Fabrairun 2022.

    Mista Zelensky ya musanta batun cewa yaƙin Ukraine ya ƙi ci ya ki cinyewa, duk kuwa da iƙirarin hakan da babbar hafsan sojin ƙasar ya yi.

    Yayin da yake jawabi ga shugabar hukumar tarayyara Turai, Ursula von der Leyen da ta ziyarci birnin Kyiv, mista zelensky ya ce ''A bayyane take yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya ya ɗauke hankalin duniya" daga na Ukraine.

  2. Abin da ya kamata ku sani kan wasan Sociedad da Barca

  3. Babu ƙasar da za ta yadda a kashe mata fararen hula - Blinken

    Daya daga cikin manema labarai ya tambayi sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, me isra'ila ta cimma a hare-haren da take kai wa Gaza in ban da "kisan kusan mutum 10,000"

    Yayin da yake magana kan hare-haren 7 ga watan Oktoba da Hamas ta ƙaddamar, sai ya ce ''babu wata ƙasa da ake wakilta a nan, ko ma a duniya da za ta yadda a kashe mata fararen hula ba tare da ta ɗauki mataki ba".

    To sai dai ya dage cewa akwai buƙatar ɗaukar matakai domin kare fararen hula, ya ce a lokacin ganawarsa da gwamnatin Isra'ila "mun bayyana matakan da za a bi domin taƙaita cutarwar da ake yi wa fararen hula".

    Haka kuma Mista Blinken ya ce "babban kalubale ne" yadda Hamas _ mai tarin mayaƙa da makamai - ta cusa kanta tsakiyar fararen hula, inda take iko da makarantu da asibitoci da masallatai da sauran gine-gine.

  4. Labarai da dumi-dumi, Sojoji sun ce an mayar da Camara gidan yari

    Sojojin mulkin Guinea sun ce an mayar da tsohon shugaban ƙasar Moussa Dadis Camara gidan yari.

    Da asubahin yau ne wasu mutane ɗauke da makamai suka fasa gidan yarin da yake ciki a birnin conakry suka sace shi tare da wwasu mutum uku.

    Ana yi wa Mista Camara da sauran mutanen shari'a ne kan kisan magoya bayan jam'iyyar adawa 156 a wani gangami da aka gudanar a shekarar 2009.

  5. Tserewar Falasɗinawa zuwa Masar da gasar kamun Kifi cikin hotunan Afirka

  6. Masar ta jaddada kiran tsagaita wuta 'nan take' a Gaza

    Sameh Shoukry

    Firaministan Harkokin Waje na Masar Sameh Shoukry ya ce ƙasarsa na yin duk abin da za ta iya wajen kai kayan agaji Gaza da kuma kula da mutanen da aka jikkata.

    Ya ƙara jaddada ra'ayin ƙasashen Larabawa na "neman cikakkiya kuma babbar tsagaita wuta a Gazan "ba tare da wani sharaɗi ba".

    Yana magana ne a taron manema labarai da suka gudanar yanzun nan tare da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken a birnin Amman na Jordan.

  7. Mahara sun sace tsohon shugaban Guinea daga gidan yari

    .

    Asalin hoton, AFP

    Ministan shari'ar gwamnatin mulkin sojin Guinea, Charles Alphonse Wright, ya ce wasu mutane ɗauke da makamai sun kai hari gidan yarin Conakry babban birnin ƙasar da asubahin ranar Asabar.

    Inda suka sace tsohon shugaban ƙasar, Moussa Dadis Camara da wasu mutum uku da ke tsare a gidan yarin.

    Tuni aka rufe kan iyakokin ƙasar, sanna aka ƙaddamar da farautar maharan.

    An ta jin ƙarar harbe-harben bindiga a birnin Conakry, sannan an jibge tarin sojoji masu yawa, tare da taƙaita zirga-zirgar mutane a birnin.

    Rahotonni sun ce an samu ɗaya daga cikin mutanen maharan suka saki, to sai dai ba a gano Mista Camara da sauran mutum biy ba.

    Ana yi wa Mista Camara da sauran mutanen shari'a ne kan kisan magoya bayan jam'iyyar adawa 156 a wani gangami da aka gudanar a shekarar 2009.

    Hukumomin kasar sun ce suna yaƙinin gano mutanen da waɗanda suka kitsa sakin nasu.

    Ƙasar Giuinea - wadda ke ƙarƙashin mulkin soji - na ɗaya daga ciki ƙasashen yammacin Africa da suka fukanci juyin mulki cikin shekarun baya-bayan nan.

    Wani abu da ƙungiyar Ecowas ke alla-wadau da shi, tana mai cewa hakan na kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron yankin.

  8. Amurka ta gargaɗi 'yan ƙasarta kan zuwa manyan otal-otal a Najeriya

    m

    Asalin hoton, Reuters

    Amurka ta fitar da wani gargaɗi ga 'yan ƙasarta da ke zaune a Najeriya da su kauce wa zuwa manyal otal-otal a ƙasar.

    Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar gaggawa da ƙasar ta aike wa 'ya'yanta mazauna Najeriya ranar Juma'a 3 ga watan Nuwamba.

    Sanarwar gargaɗin ta ce ta an ɗauki matakin gargaɗin ne saboda samun bayanan sirri game da yiwuwar kai hari manyan otol-otal a faɗin ƙasar.

    Ta buƙaci Amurkawan da ke ƙasar su riƙa lura a manyan otal-otal, da wuraren da suke zaune, su kuma rage bayyana kansu a bainar jama'a, sannan su riƙa bin shawarwarin tafiye-tafiye zuwa Najeriya da Amurkan ke fitar wa kafin su shiga kowane Otal.

    Sanarwar ta ce, “Gwamnatin Amurka na sane da sahihan bayanai da ke nuna barazana a man'yan otal-otal a manyan biranen Najeriya".

    "Jami'an tsaron Najeriya na aiki tuƙuru, don magance barazanar", in ji sanarwar.

    haka kuma sanarwar ta fitar da wasu lambobin wayar ofisoshin jakadancinta da ke Abuja da Legas, ga duk Ba'amurken da ke buƙatar taimako.

  9. Lafiya Zinariya

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  10. 'Yan bindiga sun sace matan shugaban ƙaramar hukuma a Jigawa

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu ‘yan bindiga da a san ku su wane ne ba sun kai hari gidan shugaban ƙaramar hukumar Kiyawa da ke jihar Jigawa tare da sace matansa guda biyu.

    Shugaban ƙaramar hukumar Honarabul Nasiru Ahmed Kiyawa - wanda ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin - ya ce 'yan bindigar sun je gidan nasa ne bayan sallar Isha'i a ranar Juma'a daddare, inda suka kore mutanen da ke kofar gidan nasa kafin su shiga ciki.

    Ya ƙara da cewa "sau biyu suna harba bindiga a ƙofar gidana kafin su shigo ciki".

    Daga nan ne kuma suka tafi da matan nasa guda biyu, inda kuma har yanzu suke garkuwa da su, kamar yadda ya tabbatar wa BBC.

    Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar DSP Lawan Adam Shiisu ya tabbatar wa BBC faruwar lamarain, inda ya ce rundunar 'yan sandan jihar ta samu kiran gaggawa kan lamarin, inda kuma nan take suka tura jami'ansu domin kai ɗauki.

    Sai dai kafin zuwan jami'an na 'yan sanda tuni 'yan bindigar sun yi awon gaba da matan shugaban ƙaramar hukumar.

    DSP Shiisu ya ce tuni rundunar 'yan sanda jihar ta baza jami'an a lungu da saƙo na ƙaramar hukumar domin kuɓutar da matan.

    Ya kuma ce rundunar 'yan sandan na maraba da duk wasu bayanai da za su taimaka wajen kai ga gano masu garkuwan don kuɓutar da matan.

    Matsalar garkuwa da mutane dai wani baƙon al’amari ne a jihar ta Jigawa, to sai dai matsalar na neman kunno kai cikin jihar a baya-bayan nan.

  11. Real Madrid na atisayen tunkarar Rayo a La Liga

  12. Lafiya Zinariya kan matsanancin ciwon kai

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  13. Amurka ta ce har yanzu akwai mutum 400,000 a arewacin Gaza

    Wakilin AMurka na musamman David Satterfield ya ce har yanzu akwai kimanin mutum 400,000 a arewacin Gaza.

    Isra'ila ta shafe makonni tana kiran mazauna arewacin Gaza su koma kudancin yankin, wanda suke kallo a matsayin wuri mai tsaro ko aminci.

    Tun daga wanna lokaci ne suke ta kai hare-haren bom a yankin ta sama da ta ƙasa, duk da cewa an samu hare-hare ta sama a kudancin ƙasar.

    Yayin da yake magana da manema labarai a Amman, babban birnin Jordan, Mista Satterfield ya ce kimanin mutum 800,000 zuwa miliyan ɗaya ne suka koma kudancin Gaza, yayin da kimain 400,000 har yanzu ke yankin na arewaci.

  14. Gane Mini Hanya

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  15. Blinken ya gana da firaministocin Lebanon da Qatar

    Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken na ganawa da shugabani da ministocin harkokin wajen ƙasashen Gabas ta Tsakiya.

    Da farko an tsara ganawarsa da mai riƙon muƙamin Firaministan Lebanon Najib Mikati, wanda ofishinsa ya ce ya dage wajen nuna wa Blinken muhimmancin aiki tare don tsagaita wuta a Gaza.

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Blinken yayin da ya gana da faraministan Lebanon, Najib Mikati

    An kuma ɗauki hotonsa a lokaci da yake gaisawa da Firaministan Qatar, Mohammed bin Abdulrahman al-Thani.

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Blinken na gaisawa da firaministan Qatar
  16. 'An kashe mutum 15 a harin da aka kai wa motocin marasa lafiya'

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Agajin Falasɗinawa ta Red Crescent (PRCS), ta ce mutum 15 ne suka mutu sakamakon harin da Isra'ila ta kai wa motocin ɗaukar marasa lafiya a Gaza.

    Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, ƙungiyar ta ce sau biyu ana kai wa tawagar ayarin motocin hari a kan hanyarsu ta zuwa asibitin Al-Shifa, kilomita guda daga bakin kofar asibitin.

    Ƙungiyar ta ce motocin na cike da majinyata a lokacin da aka kai musu harin.

    PRCS ta ce motocin sun ɗauki marasa lafiyar ne daga asibitin domin fitar da su daga Gaza ta mashigar Rafah, to sai dai bayan tafiyar kilomita huɗu daga asibitin sai suka tarar hanya ta toshe, dole ta sa suka juya da nufin komawa asibitin.

    Tun da farko ma'aikatar lafiyar Hamas a Gaza ta ce aƙalla mutum 13 ne suka mutu sakamakon fashewa wani bom a wajen asibitin na Al-Shifa.

    Sashen bin diddigi na BBC ya tantance sahihancin bidiyo da hotunan da ke nuna yadda mutane suka jikkata da yiwuwar waɗanda suka mutu na kwance a wajen asibitin.

    A martanin da ta mayar, rundunar sojin Isra'ila ta ce mutanen da suka mutu a hari kan motocin ɗaukar marasa lafiyar, mayaƙan Hamas ne.

    Sojojin na Isra'ila sun zargi ƙungiyar da amfani da motocin majinyatan don yin jigilar mayaƙanta da makamai, duk da cewa har yanzu ba su bayyana hujjar hakan ba.

  17. Ra'ayi Riga: Ce-ce-ku-ce kan saya wa matar Tinubu motocin alfarma

    Fadar shugaban Najeriya za ta kashe kusan naira biliyan 4.4 don saya wa matar shugaban ƙasa da fadar shugaban ƙasa motoci da kuma wata fiye da naira biliyan 13 don gyaran gidajen shugaban ƙasa da na mataimakinsa a Abuja da Legas.

    Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan ƙasar ke kukan matsin rayuwa da suke ciki, inda gwamnati take ƙara kiraye-kirayen jama'a su ƙara haƙuri.

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  18. 'Isra'ila ta kashe gomma mayaƙan Hamas a cikin kwana guda'

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar sojin isra'ila (IDF), ta ce ta kashe "gomman'' mayaƙan Hamas tare da lalata abubuwan more rayuwa na ƙungiyar a cikin kwana guda.

    Ta ce Hamas ta ƙaddamar da "hare-hare masu yawa" kan sojojinta ta hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da sansanonin soji a arewacin Zirin Gaza.

    Sojojin na Isra'ila sun kum ce dakarunsu sun fafata da mayaƙan na Hamas, tare da "kashe da dama da cikinsu" da kuma lalata uku daga cikin wuraren da Hamas ke lura da zirga-zirgar abokan gaba.

    IDF ta kuma ce ta ƙaddamar da wani samame a kudancin Gaza, inda a nan ma suka ce sun kashe mayaƙan ƙungiyar masu yawa.

    A jiya ne Isra'ila ta ce dakarunta sun yi birnin Gaza ƙawanya tare da kashe manyan dakarun ƙungiyar 10, da suka shirya harin 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadiyyar kisan 'yan Isra'ila 1,400.

  19. Blinken ya isa Jordan a ƙoƙarin shiga tsakani kan rikicin Gaza

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa ƙasar Jordan, domin tattaunawa da wakilan ƙasashen Larabawa da sarki Abdallah na Jordan.

    Mista Blinken zai kuma gana da wakilan Larabawa da ke kiran a gaggauta dakatar da bude wuta a Gaza.

    Haka kuma sakataren harkokin wajen Amurkan, zai gana da ministocin harkokin ƙasashen wajen Jordan da Saudiyya da Qatar da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa, da kuma wakila hukumomin Falasɗinawa.

    Halin tagayyara da tsananin buƙatar taimako na ƙara yawa a Gaza, inda farar hula ke tsananin buƙatar taimakon abinci da ruwan sha da magani, yayin da asibitoci ke ci gaba da fuskantar hare-hare.

  20. Amurka na ƙoƙarin kuɓutar da mutanen da Hamas ke garkuwa da su

    Jami'an gwamnatin Amurka sun ce suna kokari don ganin an kuɓutar da waɗanda mayaƙan Hamas ke garkuwa da su a Gaza.

    Sai dai sun ce babu takamaimai lokacin da suke sa ran cimma nasarar kuɓutar da mutanen.

    Jami'an - waɗanda suka yi hira da manema labarai, kuma suka buƙaci a sakaya sunansu - sun ce tattaunawar ta shiga wani yanayi mai matuƙar wahala da suke buƙatar taka tsantsan musamman ganin yadda ake tsare da mutanen a tsakiyar fagen daga.

    A ziyarar da ya kai Tel Aviv a jiya Juma'a, sakataren harkokin wajen Amurka ya buƙaci a tsagaita wuta da kai agaji Gaza, amma firaminista Netanyahu ya kafe cewa luguden wuta yanzu sojin Isra'ila suka fara.