Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An lalata wasu makarantun da Falasɗinawa ke samun mafaka - MDD
Wannan shafi ne da ke kawo mu ku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza, Mukhtar Adamu Bawa, Haruna Kakangi and Ahmad Tijjani Bawage
Masu raunuka fiye da 20,000 ne ke maƙale a Gaza - MSF
Ƙungiyar Likitoci ta 'Medecins sans frontieres' ta ce masu raunuka fiye da 20,000 ne ke maƙale a Gaza.
Jami'an Masar sun ce 'yan ƙasashen waje 335, da masu tsananin raunuka ko jinya 75 ne aka shigar ƙasar domin yi musu magani ta kan iyakar Rafah a ranar Laraba.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce an ga motocin ɗaukar marasa lafiya ɗauke da majinyata a harabar asibitocin Masar.
To sai dai ƙungiyar MSF ta yi kira da a ƙara adadin masu raunukan da ake kwashewa, da kuma kiran tsagaita wuta tare da shigar da ƙarin kayan agaji zuwa Gaza, inda ake cikin tsananin buƙatar tallafi.
"Na kaɗu da yadda kowa ke tambayar abinci, da ruwan sha," in ji Philippe Lazzarini, wani babban jami'an MDD da aka bari ya shiga Gaza tun bayan fara yaƙin.
Zan kori duk ministan da ya gaza taɓuka abin kirki - Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi barazanar korar duk ministan da bai taɓuka abin kirki a ma'aikatarsa ba.
Tinubu na wannan maganar ne a lokacin taron bitar kwana uku da aka shirya wa ministoci mataimaka na musamman ga shugaban ƙasar, da manyan sakatarorin gwamnati, da sauran manyan jami'an gwamnati .
Shugaban ƙasar ya ce ya zaɓo manyan jami'an gwamnatin nasa ne domin su taimaka a ci nasarar tafiyar da gwamnati tare.
Ya ƙara da cewa “a ƙarshen wannan bita, za mu sanya hannu a kan takardar yarjejeniyar fayyace ƙwazon aiki".
“Don haka ne ma muka ɓullo da sashen tantance ƙwazo, kuma a ƙarshen wannan bita za ku saka hannu kan yarjejeniyar fahimta tsakaninku (ministoci) da manyan sakatarorin gwamnati da kuma ni kaina", in ji Tinubu.
“Matuƙar ka yi ƙwazo, babu abin fargaba a ciki, idan kuwa ba ka yi komai ba, za mu duba, matuƙar babu abin da ka yi, za mu sauke ka, babu wanda zai iya rayuwa shi kaɗai".
Nijar ta ƙaddamar da bututun man fetur zuwa Jamhuriyar Benin
Shugabannin mulkin soja na Nijar sun ƙaddamar da wani babban batutun man fetur da zai riƙa tura ɗanyen mai daga ƙasar zuwa Jamhuriyar Benin, mai maƙwabtaka.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato gidan talbijin na ƙasar na cewa aikin - wanda ke da tsawon kusan kilimita 2,000 - zai bai wa Nijar damar sayar da ɗanyen man fetur da take haƙowa a kasuwannin duniya a karon farko, ta hanyar amfani da mashigar ruwan Seme da ke Benin.
An gudanar da bikin ƙaddamar da aikin cibiyar haƙo man fetur ta Agadem, mai nisan kilomita 1,700 daga Yamai baban birnin ƙasar.
Firaministan Nijar, Ali Mahaman Lamine, ya ce za a yi amfani da kuɗin da aka samu daga cinikin man fetur din "don tabbatar da tsaro da ci gaban ƙasarmu".
Kan iyakar Nijar da Jamhuriyar Benin ta kasance a rufe sakamakon jerin takunkuman da ƙungiyar Ecowas ta saka wa Nijar bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli.
Wakilai daga ma'aikatun makamashin ƙasashen Mali da Burkina Faso - waɗanda ke nuna goyon bayansu ga sabuwar gwamnatin sojin Nijar - sun halarcin bikin ƙaddamar da aikin.
An tsara kammala aikin a shakerar 2022, to amma annobar korona ta haddasa jinkirin aikin, kamar yadda masu gudanar da aikin suka shada wa AFP.
Kamfanin man Fetur na Ƙasar China, (CNPC) ne ke aikin haƙo man.
Gwamnatin Nijar ta ce aikin ya laƙume dala biliyan shida, ciki har da dala biliyan huɗu na gina wuraren man, da kuma dala biliyan 2.3 na aikin shimfiɗa bututun man.
Ta ƙara da cewa wannan aiki zai bai wa ƙasar damar ƙara yawan man da take haƙowa zuwa ganga 110,000 a kowace rana, da nufin ƙara shi zuwa 200,000 a kowace rana zuwa shekarar 2026.
Ƙasar Nijar - wadda sojoji suka kifar da gwamnatin farar hula cikin wata Yuli - ta fuskanci jerin zanga-zanga da kiraye-kirayen ficewar sojojin Faransa daga ƙasar.
Ga kuma jerin takunkumai daga ƙungiyar Ecowas, sannan ƙasashen Yamma da dama sun yanke tallafin da suke ba ta.
Bankin duniya ya yi gargaɗin cewa arzikin da ake samu a cikin ƙasar na iya raguwa da kashi 2.3 a wannan shekara matuƙar ba ɗage mata takunkuman ba.
Za a gudanar da taron bunkasa harkokin ciniki tsakanin Amurka da Afirka (AGOA)
A yau Alhamis ne ake sa ran fara taron shekara-shekara na shirin ci gaban Afirka da ake kira AGOA a birnin Johannesburg na Afirka Ta Kudu.
Shirin - wanda ake gudanarwa da zummar bunƙasa mu'amalar kasuwanci tsakanin Amurka da ƙasashen Afrika tun shekara ta 2000 - ya kunshi ƙasashen Afirka 35.
Wasu daga ciki irinsu Lesotho da Kenya da Madagascar, sun yi nasarar amfani da wannan shiri wajen bunƙasar tattalin arziki da samar da ayyukanyi a ƙasashensu.
Sai dai masu sharhi na cewa shirin da ake ganin zai taka rawa wajen ƙara danƙon zumunci tsakanin ƙasashen kudu da hamadar sahara da Amurka, ya gaza wajen cimma manufar Amurka da ke ƙoƙarin rage tasirin China a Afrika.
Amurka za ta daƙile ƙyamar da ake nuna wa Musulunci a ƙasar
Fadar gwamnatin Amurka ta ce za ta bijiro da wani tsari na ƙasa da zai daƙile tsanar da ake nunawa Musulunci.
Sanarwar na zuwa ne yayinda ake nuna tsananin damuwa a Amurka kan yaƙin Isra'ila da Hamas.
Kakakin gwamnatin Amurka, Karine Jean-Pierre, ta ba da misali da kisan da ta bayyana da 'rashin imani' da aka yi wa wani yaro Bafalasdine mazaunin Amurka mai shekara shida a Chicago, da 'yansanda suka alakanta da yaƙin da ake yi.
Shugaba Biden, da ke neman tazarce a zaɓen shekara mai zuwa, ya je Isra'ila domin nuna goyon-bayansa ga Firaminista Benjamin Netanyahu.
MDD ta ce hare-haren Isra'ila a Jabalia na iya zama laifukan yaƙi
Hukumar kare hakkin bil adama ta MDD ta ce hare-haren saman da Isra'ila ke kai wa a sansanin 'yan gudun hijirar Jabalia na iya zama laifukan yaƙi.
Ta ce adadin fararan-hula da ake kashewa da girma ɓarnar da ake aikatawa na nuna damuwa matuƙa da tabbatar da cewa da gangan ake haransu.
Ofishin yaɗa labaran Hamas da ke Gaza ya ce sama da mutum 195 aka kashe a hare-haren daga ranar Talata zuwa Laraba, sannan akwai sama da mutum 120 da har yanzu ba a gansu ba.
Tsohon ministan harkokin waje a Masar, Nabil Fahmy ya ce bai kamata Isra'ila ta riƙa fakewa da yaƙi tana kashe fararan-hular Falasdinawa, da ba su ji ba, ba su gani ba da sunan daƙile Hamas, wannan ba daidai ba ne.
Mutane da dama na sa ran ficewa daga Gaza ta mashigar Rafah
Mutane da dama na saran ficewa daga Gaza bayan ƙoƙarin diflmasiyya da ya ba da damar buɗe iyakar Rafah domin shiga Masar.
Jami'an kan iyaka a Gaza sun ce za a cigaba da barin mutane su riƙa ficewa.
Majiyoyi diflomasiyya na cewa akwai mutum 7,500 baƙi daga ƙasashen ƙetare da ake saran su fice birnin nan da mako biyu.
Suma Falasdinawa da aka jikkata na da damar ficewa domin samun kulawa a Masar.
Shugaban Amurka Joe Biden ya yaba da ƙoƙorin tattaunawar diflomasiyya da ta ba da damar buɗe iyakar Rafah.
Ya ce ya yi farin-cikin ganin daruruwan ɓaki daga ƙasashen ƙetare da gomman Falasɗinawan da aka jikkata sun samu damar tsallaka iyakar Rafah zuwa cikin Masar, da aka buɗe na ɗan lokaci a ranar Laraba.
Marabanku
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkan mu da safiya.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a wannan lokaci, don kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a fadin duniya.