Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Harin Isra'ila kan sansanin Jabalia ya kashe gomman Falasɗinawa

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa and Umar Mikail

  1. An jikkata mutum biyu a wani harbi a asibiti a Toda, Japan

    An jikkata wasu mutane biyu sakamakon harbin bindiga a wani asibit da ke birnin Toda da ke tsakiyar kasar Japan, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito.

    Wanda ake zargi yana da shekaru tsakanin 50 zuwa 70, ya gudu ne a kan babur, kuma a halin yanzu ana neman sa.

    A lokaci guda kuma rahotanni sun nuna cewa an yi garkuwa da mutum biyu a cikin wani gidan waya da ke garin Warabi da ke kusa.

    Babu tabbas idan waɗannan al'amuran biyu suna da alaƙa.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar Japan sun yaɗa hotunan wani mutum dauke da bindiga a ƙofar ofishin gidan waya da ke kusa da babban asibitin Toda Chuo, inda aka yi harbin.

    An bayyana waɗanda suka jikkata a matsayin likita da tsoffi majinyaci, yayin da kuma waɗanda akayi garkuwa da su wasu mata biyu ‘yan shekara 20 zuwa 30 ne.

    Ofishin gidan waya a Warabi yana da tazarar kilomita 2.5 daga asibitin.

    Jami’an tsaro sun kewaye yankin, kuma an aika da tawagogin bincike na musamman.

    Hukumomi sun shawarci mazauna yankin da ke da nisan mita 300 daga ofishin gidan waya na Warabi da su fice, tare da rufe gine-ginen da ke kusa da su.

    • An tsare dan shekara shida da zargin harbin malamarsa da bindiga a Amurka
    • 'Ba mu hana likitoci duba masu harbin bindiga ko hatsarin mota ba'
  2. Mutanen da aka kashe a Gaza sun ƙaru da sama da 200

    Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce adadin waɗanda suka mutu a Gaza ya kai 8,525 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

    Wannan ya haɗa da yara 3,542 da mata 2,187, da kuma ma'aikatan kiwon lafiya 130.

    Ya zuwa ranar Litinin, adadin wadanda suka mutu ya tsaya a 8,306

    • Bayani kan hanya ɗaya tilo da Falasɗinawa za su iya fita daga Gaza
    • Yaya mamayen ƙasa na sojojin Isra'ila zai kasance a Gaza?
  3. Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da zaɓen Sanata Natasha Akpoti

    Kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta tabbatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduagan ta jam'iyyar PDP, a matsayin wadda ta lashe zaɓen 'yar majalisar dattijai mai wakiltar Kogi ta Tsakiya.

    Hukunci da rukunin alƙalan kotun uku suka yanke ranar Talata, ya tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta jihar Kogi tare da korar ƙorafin Sanata Abubakar Ohere na APC.

    Kotun ta amince da bahasin Joshua Usman, lauyan Natasha wanda ta ce yana kan hujja.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa a ranar 6 ga watan Satumba ne Kotun Sauraron ƙararrakin Zaben 'Yan majalisa ta Jihar Kogi ta ayyana nasara ga Natasha, bayan ta rusa zaben Sanata Abubakar Ohere.

    • Shin 'yan siyasar Najeriya na ta'azzara labaran bogi?
    • Jihohin da ba za a yi zaɓen gwamna ba a ranar Asabar
  4. Saudiyya ta kusa samun damar daukar bakuncin gasar kofin duniya ta 2034

  5. Fitaccen malami Sheikh Zakir Naik zai gabatar da lakcoci a makon Danfodio na bana

    Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan ɗan ƙasar Indiya, Dr. Zakir Naik na ci gaba da ziyara a Najeriya, a wani ɓangare na taron gabatar da lakcoci a makon Danfodio da ake gudanarwa duk shekara a Sokoto.

    Malamin wanda ya isa Sokoto ranar Litinin tare da ɗansa Fariq Naik, ya ziyarci Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III a fadarsa.

    Ana sa rai, malamin zai gabatar da jerin lakcoci tsawon kwanakin da zai shafe yana wannan ziyarar.

  6. An kashe ma'aikacin MDD da iyalinsa, su goma a Gaza

    Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da 'yan gudun hijirar Falasɗinawa, UNRWA ta bayyana cikin baƙin ciki cewa ma'aikatanta 64 ne suka rasa rayukansu a Gaza a rikicin Isra'ila da Hamas.

    Hukumar ta ƙara da cewa wani abin takaicin shi ne, ɗaya daga cikin ma'aikatan da aka kashe harda daukacin iyalinsa da suka hada da ‘ya’ya takwas da matarsa ​​yayin da suke gida.

    Mai magana da yawun hukumar, Juliette Touma, ta bayyana damuwa game da cunkoso a matsuguni 450 da suke gudanarwa a fadin Gaza, inda jimillar mutane 670,000 suka nemi mafaka.

    Lamarin dai ya yi kamari, inda rahotanni ke cewa cututtuka kamar su zawo da gudawa suna yaduwa.

    Ana buƙatar tsagaita wuta na jin ƙai cikin gaggawa saboda hatta wuraren da ya kamata a kiyaye, da suka haɗa da majami'u da masallatai da wuraren Majalisar Ɗinkin Duniya, abin ya shafa.

    • Takaddamar Isra'ila da shugaban MDD saboda kalamansa kan harin Hamas
    • Taliban ta hana mata aiki a karkashin Majalisar Dinkin Duniya
  7. Isra'ila ta zargi Hamas da "ɓuya a bayan Falasɗinawa"

    Kakakin rundunar sojin Isra'ila Peter Lerner ya shaida wa BBC Breakfast cewa "Hamas na fakewa da Falasɗinawa, fararen hula."

    Ya kuma bayyana irin mummunan tasiri da rikicin Gaza da Isra'ila ya haifar a ɓangarorin biyu, inda ya jaddada buƙatar ganin ƙungiyar ta Hamas ta tafi domin ayyukan kungiyar na jawo wahala ga kowa da kowa.

    Lerner ya zargi Hamas da jibge kadarorinta a yankunan fararen hula, da suka haɗa da sanya jirage marasa matuka masu fashewa a saman rufin gidaje da harba rokoki daga wurare da ke kusa da cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya.

    Ya kuma ba da rahoton cewa, an harba rokoki sama da 7,000 daga Gaza zuwa cikin Isra'ila tun daga ranar 7 ga Oktoba.

    Bugu da kari, a baya Lerner ya yi iƙirarin cewa Hamas na amfani da asibitoci a Gaza a matsayin cibiyar gudanar da ayukan soji, da shirya hare-harensu da kuma garkuwa da fararen hula.

    • Me ya sa hankalin duniya ya karkata kan Zirin Gaza?
    • Fargaba na ƙaruwa yayin da Isra'ila ke jibge dakarunta a kan iyakar Gaza
  8. Hotunan jana'iza a Gaza yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare

    Isra'ila ta sanar da kai hare-hare kan jimillar wurare 300 a Zirin Gaza.

    A halin da ake ciki kuma, a cikin Gaza, ana ci gaba da gudanar da jana'izar mutane da dama da suka rasu tun ranar 7 ga watan Oktoba.

  9. Amurka za ta cire Nijar da wasu kasashen Afirka daga tsarin ciniki na AGOA

    Shugaban Amurka Joe Biden ya kaddamar da wani shiri na cire ƙasashen Uganda da Gabon da Nijar da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya daga cikin shirin bunƙasa kasuwanci na musamman tsakanin Amurka da Afirika da aka fi sani da 'African Growth and Opportunity Act (AGOA)'.

    Shugaban ya ce dalilin da ya sa aka yanke wannan shawarar shi ne, ko dai waɗannan ƙasashe sun shiga cikin jerin manyan kasashe da ke take haƙƙin ɗan'adam ko kuma ba su nuna ci gaba a mulkin dimokraɗiyya ba.

    AGOA, wani shiri ne da aka ƙaddamar a cikin 2000, da ke bai wa ƙasashen Afirka na kudu da hamadar Sahara damar shiga ba Amurka ba tare da biyan haraji ba, da kayayyaki sama da 1,800.

    Shugaba Biden ya ba da misali da rashin bin tsarin siyasa da bin doka da oda a matsayin dalilan rashin cancantar Nijar da Gabon, saboda juyin mulkin da sojoji suka yi a baya-bayan nan.

    Ya kuma yi nuni da gagarumin take hakkin ɗan'adam da gwamnatocin kasashen Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Uganda suka yi a matsayin hujjar cire su daga cikin shirin.

    Ya zuwa yanzu dai babu wani martani a hukumance daga ƙasashen hudu da abin ya shafa.

    Wannan matakin ya biyo bayan korar da aka yi wa Burkina Faso da Mali da kuma Guinea daga AGOA bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a waɗannan kasashe.

    • Amurka da Rwanda na fada kan kayan gwanjo
    • Rikicin Afghanistan: Yadda dangantakar Turai da Amurka ta yi tsami
  10. 'Sojojin Isra'ila sun zafafa hare-hare a kewayen asibitin Al-Quds da ke Gaza'

    Kungiyar agaji ta Falasɗinawa ta Red Crescent ta ce sojojin Isra'ila sun zafafa hare-hare a kewayen asibitin Al-Quds da ke birnin Gaza.

    Ƙungiyar ta wallafa sako a shafukan sada zumunta da ke cewa ana ci gaba da luguden wuta da harba makaman atilare a yankin.

    Isra'ila ta ce ta zafafa hare-harenta a yankin ne domin tarwatsa Hamas da ke iko da Zirin Gaza.

    Tana ci gaba da nanata gargaɗinta ga fararen hula, na su fice daga asibitin da sauran gine-gine.

    Sai dai ma'aikatan lafiya da na agaji na cewa ba su da mafita a yanzu.

    A wani hari na daban kuma sojojin Isra'ila sun lalata wani gini da suka ce na Hezbollah ne a cikin Lebanon.

    • Halin da aka shiga a Gaza ranar da aka katse hanyoyin sadarwa
    • Ana kwashe 'yan Isra'ila a ƙauyukan iyaka da Lebanon saboda barazanar hari
  11. Sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe wani rikakken ɗan bindiga a Kebbi

    Dakarun tsaron sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe wani rikakken ɗan bindiga da aka fi sani da suna Mai-Nasara a dajin Sangeko na jihar Kebbi.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito wata sanarwa da Alhaji Ahmed Idris, babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar Kebbi ya fitar na cewa jami'an tsaron sun kama mutum biyar da ake zargin 'yan fashin daji da ke cikin gungun masu aikata laifuka.

    Ya ambato gwamnatin Kebbi ta yaba da jajircewar jami’an tsaron wajen yaƙi da miyagun laifuka musamman a yankin kudancin jihar.

    “Goyon bayan jama'a da hadin kanku ya zama wajibi sosai domin jami’an tsaro su cimma burin da ake so na fatattakar masu aikata laifuka da kuma dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarmu."

    Ya ja hankalin jama'ar yankin su yi kokarin taimakawa jami’an tsaro ta kowanne fanni, musamman da sahihan bayanan sirri don samun nasarar fada.”

    • Fuskokin 'ƴan ta'addan' da sojojin Najeriya ke nema ruwa-a-jallo
    • 'Rashin haɗin kan gwamnatoci dama ce ga 'yan bindiga'
  12. Al'amura sun yi matukar muni a Gaza, yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hari

    Taron gaggawan kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya ji cewa yanayi ya yi matukar muni a Gaza, yayin da Isra'ila ke cigaba da jefa bama-bamai a yankin.

    Shugabar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya, Lisa Doughten, ta ce ba za a iya kwatanta yanayi na akubu da mutane suka shiga wajen neman abinci, da ruwan sha da matsuguni ba, wanda ya kai matakin kololuwa.

    Ta ce suna fargabar abubuwan da za su biyo baya nan gaba, saboda akwai hujojji masu karfi da ke nuna rikici na iya bazuwa cikin wasu yankunan.

    Asusun kula da Ƙananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ya ce sama da yara 420 ake kashewa ko jikkatasu a kullum a Gaza.

    • Yaya mamayen ƙasa na sojojin Isra'ila zai kasance a Gaza?
    • Mene ne hatsarin shiga yaƙi ta kasa a Zirin Gaza?
  13. An zabi sabon shugaban majalisar dokoki a jihar Rivers

    Majalisar dokokin jihar Rivers ta zaɓi Edison Ehie a matsayin kakakinta.

    Zaɓen nasa ya gudana ne a yayin zaman majalisar, inda 'yan majalisar 26 suka kada kuri'ar amincewa da shi.

    Wannan hukuncin ya biyo bayan dakatarwar da aka yi wa wasu manyan shugabannin majalisar.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa bayyanar Ehie a matsayin sabon shugaban majalisar ya biyo bayan da ‘yan majalisar guda 26 suka tsige magabacinsa, Martins Amaehule,

    Da yake zantawa da manema labarai bayan zaben sa, Ehie ya bayyana jin daɗinsa ga abokan aikinsa da suka ɗora masa alhakin jagorantar majalisar.

    “Alƙawarina ga mutanen Rivers shine zan kasance mai adalci ga kowa da kowa; Zan tabbatar da bin doka da oda.

    “Ba zan ci amanar abokan aikina ba. Ba zan ci amanar mutanen Rivers ba. Ba zan ci amanar mazaba ta ba."

    “Zan tabbatar da ‘yancin cin gashin kan Majalisar Dokokin Jihar Ribas, tare da mutunta juna ga bangaren shari’a da bangaren zartarwa na gwamnati,” inji shi.

    Bugu da kari, sabon kakakin ya bayyana cewa zai tabbatar da cewa ‘yan majalisar da aka dakatar sun samu sahihin saurare ta hanyar kwamitin koke.

    • Zaɓen Najeriya a Jihar Rivers: Jiha mai arzikin man fetur maras lantarki
    • Me zai faru a jihar Ribas bayan soke ‘yan takara ta APC
  14. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da safiyar Talata tare da fatan kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa lafiya.

    Aisha Babangida da Ibrahim Yusuf ne za su kawo muku rahotanni daga sassan duniya, musamman game da halin da ake ciki a hare-haren da Isra'la ke kai wa Zirin Gaza da kuma martanin mayaƙan Hamas a kan ƙasar.