Mu kwana lafiya
Ƙarshen rahotonnin ke nan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Ku biyo mu gobe da safe don samun wasu rahotonnin.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa and Umar Mikail
Ƙarshen rahotonnin ke nan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Ku biyo mu gobe da safe don samun wasu rahotonnin.
Ofishin ayyukan jin-ƙai na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya ce hare-haren da Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna ke kai wa Falasɗinawa ya ƙaru a Gabar Yamma da Kogin Jordan tun bayan harin da Hamas ta kai Isra'ila mako uku da suka gabata.
Ya zuwa yanzu 'yan kama-wuri-zaunan sun kai hare-hare sama da 170 cikin wannan lokacin.
Rikicin ya yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa 120.
An kuma kashe sojan Isra'ila ɗaya. Amurka ta yi kira ga Isra'ila da ta bai wa farar hula Falasdinawan da ke rayuwa a Gabar Yamma da Kogin Jordan daga hare-haren 'yan bindigar Yahudawa.
Ministan Harkokin Waje na Najeriya Yusuf Maitama Tuggar ya karɓi baƙuncin Jakadan Falasɗinawa a Najeriya Abdullah M. Abu Shawesh a yau Talata a Abuja.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ce sun tattauna game da yanayin da ake ciki a Zirin Gaza. yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a yaƙin da ta ce tana yi da mayaƙan Hamas.
Babban sakataren gidauniyar caca ta ƙasa a Najeriya, National Lottery Trust Fund (NLTF), ya ce 'yan Najeriya fiye da miliyan 65 ne ke kashe miliyoyin naira kan cacar duk da matsin tattalin arziki da ake ciki.
Bello Maigari ya ce kasuwar caca da ake yi ta intanet a duniya ta samu cigaba sosai, abin da ya sa darajarta ta kai dala biliyan 50.
Jami'in na NLTF ya bayyana haka ne a Legas yayin taron wasan "game" na ƙasa.
"Ya zuwa Satumban 2021, an yi ƙiyasin cewa kasuwar caca ta intanet ta kai darajar dala biliyan 50 kuma darajarta ta ci gaba da hauhawa tun daga lokacin," in ji shi.
A cewar wani rahoto da kamfanin caca na Orange Business Intelligence Technology (ORBIT) ya wallafa a watan Maris na 2023, kasuwar caca a Najeriya ta samar da kuɗin shiga sama da dala biliyan biyu a 2020, inda 'yan Najeriya fiye da miliyan 60 'yan shekara 18 zuwa 40 suka kashe dala miliyan 5.5.
Rundunar sojan Isra'ila ta tabbatar da harin da ta kai kan sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia, tana mai cewa ta kashe wani kwamandan Hamas da sauran mutanen "da ke tare da shi a ginin da kuma ƙarƙashin ƙasa".
Harin ya kashe aƙalla mutum 50, yayin da wasu rahotonni ke cewa adadin ya zarta haka. Mun kawo muku hotunan yadda Isra'ila ta ragargaza gine-gine a nan.
Mai magana da yawun rundunar, Daniel Hagari, ya ce harin ya jawo rushewar wasu gine-ginen da "ke da hanyoyi masu tsayi".
"Abin da ya sa aka gina waɗannan hanyoyi shi ne kai wa dakarunmu hari," in ji shi.
latsa hoton ƙasa ku kalli bidiyon ɓarnar da harin ya yi:
Mutum huɗu sun jikkata bayan wani hari roka da a kan yankin Ashdod da ke kudancin Isra'ila, a cewar hukumomin agaji.
Wani mutum mai shekara 50 ya ji mummunan rauni sannan wasu mazan uku suka ji ƙananan raunuka.
An kai dukkansu asibiti kuma jami'an agaji na ci gaba da duba yankin ko akwai ƙarin waɗanda suka ji rauni.
Masu zanga-zangar da ke kira a tsagaita wuta a yaƙin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza sun hana Sakataren Harkokin Wajen Amurka jawabi a taron Majalisar Dattawa ta ƙasar.
Mutane da dama ne suka miƙe a cikin jama'a kuma suka dinga ihun "a tsagaita wuta nan take!".
Rundunar sojan Isra'ila ta ce an kashe dakarunta biyu yayin harin da take kaiwa ta ƙasa a Zirin Gaza.
Wannan kisa ya kawo adadin mutanen da aka kashe a Isra'ila tun daga ranar 7 ga watan Oktoba zuwa 1,407.
Cikin waɗanda aka kashe akwai sojoji 317, da 'yan sanda 58.
Rundunar ta bayyana sunayen dakarun da aka kashe da Roei Wolf da Lavi Lipshitz, dukkansu 'yan shekara 20.
Kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ya isa sansanin Jabalia, inda hari ya kashe gomman Falasɗinawa.
Rahoton da yake bayarwa shi ne cewa an zaƙulo gawar mutum 47 zuwa yanzu.
Mazaunin wurin Ragheb Aqal ya ce sun ji wani abu mai kama da "girgizar ƙasa" ya afka wa sansanin.
Wani mummunan hari da aka kai kan sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia d arewacin Gaza ya kashe gomman Falasɗinawa.
Ƙungiyar Hamas ta zargi Isra'ila da kai harin, amma har yanzu rundunar sojin Isra'ila ba ta ce komai ba.
Masu zanga-zanga da ke kiran a tsagaita wuta a Gaza sun katse Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken a lokacin wani zaman sauraron jin bahasi na Majalisar Dattijai ranar Talata.
Mutane da yawa sun yi cincirindo suna ta kuwwar "A tsagaita wuta yanzu!"
Sakatare Blinken da Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin na gabatar da jawabi ne game da bukatar fadar White House ta neman amincewa da kudin tsaro dala biliyan 106.
Kudin ya kunshi dala biliyan 14.3 don tallafawa kokarin sojojin Isra'ila a kan kungiyar Hamas.
Suna tsaye daya bayan daya, masu zanga-zangar sun jira har lokacin da Mista Blinken ya fara bayar da bahasi kafin su fara yi masa ihu. Anthony Blinken dai ya dakata yayin da 'yan majalisar ala tilas suka jingine zaman a lokuta da dama.
'Yan sandan da ke kula da ginin majalisar dokokin sun yi hanzari suka rako masu zanga-zangar daga zauren a lokacin da suka fara ihu.
'Yan sanda sun ce an kama mutum 12 saboda yin zanga-zanga ba bisa ka'ida ba a cikin wani sashe na majalisar.
Wasu daga cikin wadanda suka katse zaman majalisar na da alaka da wata kungiya mai adawa da yaki wadda ake kira CODEPINK, ta kuma yi kira ga Amurka ta daina tura makamai Ukraine.
Masu zanga-zangar da dama sun daura kyalle mai rubutu "Ba mu yarda da yi wa Gaza kofar rago ba", daidai lokacin da suke kira ga Amurka ta dakatar da tura wa Isra'ila kudade.
Kungiyar CODEPINK ta tabbatar da cewa an kama wasu daga cikin wakilanta.
Ta ce wasu sun sanya jan fenti a hannuwansu "don nuna alamar jini". Mista Blinken ya yi nuni da masu zanga-zangar a karshen sanarwarsa da cewa, ga kuma "jijiyoyin wuyan da aka tayar a wannan daki".
"Dukkanmu mun dukufa wajen kare fararen hula. Dukkanmu mun san irin wahalhalun da ake ciki a daidai wannan lokaci da muke magana, dukkanmu mun dukufa wajen ganin karshen haka," a cewarsa.
Sai dai ya kara da cewa, abu ne mai muhimmanci ga Amurka ta mara baya ga abokan kawancenta.
Sansanin Jabalia yana arewacin Gaza ne kuma shi ne mafi girma daga cikin sansani takwas da ke Gaza.
MDD ta yi wa Falasɗinawa sama da 116,000 rajista a sansanin ya zuwa watan Yulin 2023.
'Yan gudun hijira sun fara zuwa sansanin ne bayan yaƙin 1948. Ƙaramin wuri ne amma mai jama'a da yawa. Girmansa bai wuce murabba'in kilomita 1.4 ba, kuma kusan dukkansa gidajen mutane ne.
Jabalia na da gine-ginen makarantu 26, wurin raba abinci, cibiyar lafiya biyu, ɗakin karatu, da kuma rijiyar ruwa bakwai.
Jabalia da sansanin Shati na cikin yankin da Isra'ila ta ce wurin ɓuya ne ga Falasɗinawa daga hare-harenta.
Cikin waɗannan hotunan da mai ɗaukar hoto na kamfanin Reuters ya tattaro, ana iya ganin yadda harin Isra'ila ya yi raga-raga da sansanin Jabalia na 'yan gudun hijira da ke Gaza.
Da yawa daga cikin hotunan sun yi munin da ba za mu iya wallafa su ba, amma ana iya ganin manyan ramuka da bama-bamai suka haƙa zagaye da kankare da ƙarafa na ɓaragauzai a ko'ina.
A ɗaya daga cikin gine-ginen, ana zaro wani yaro - wanda da alama ya tsira da ransa - daga wani bene. Benen ya kusa ruftawa a kansu.
Gomman mutane ne ke can suna ci gaba da neman waɗanda suka tsira da ransu da hannayensu.
Wani hoto daban ya nuna gawar wani da aka ɓoye fuskarsa ana zaro shi daga wani gini.
Rahotanni sun ce an samu dumbin mace-mace da jikkata a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza.
Ma'aikatar lafiya da ke karkashin jagorancin Hamas da kuma daraktan wani asibitin kasar Indonesiya da ke kusa sun ce an kashe akalla mutum.
Ma'aikatar ta ce fashewar ta faru ne sanadin wani harin Isra'ila ta sama.
Zuwa yanzu Isra'ila ba ta ce komai ba a kan rahoton fashewar da aka samu.
BBC na kokarin tantance bayanai a kan abin da ya faru.
Kamar yadda muke ci gaba da kawu muku rahotanni, tarzoma na karuwa a yankin Gabas ta Tsakiya - da Zirin Gaza da Gabar Yamma da Kogin Jordan da ke karkashin mamaya da kuma a iyakar Isra'ila da Lebanon har da ma can wani wuri daban.
A yanzu haka, mayakan Houthi a Yemen - daruruwan kilomitoci daga kudu maso gabashin Isra'ila - sun tabbatar da cewa tuni suka kaddamar da wani harin "dumbin" makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuka a kan Isra'ila.
Tun da farko, an ji karar jiniya a birnin Eilat na kudancin Isra'ila ranar Talata, bayan an samu wani "kutsen jirgi maras matuki na abokan gaba", da Isra'ila ta kakkabo shi a bahar maliya.
Mai magana da yawun rundunar sojin Houthis, Yahya Saree ya fada a wata sanarwar da ya gabatar a kafar talbijin na cewa karo na uku kenan suna kai hari Isra'ila - kuma za su ci gaba da yin haka.
Dakarun Houthi "za su ci gaba da kaddamar da hare-hare na musamman har sai Isra'ila ta kawo karshen kutsen da take yi a Isra'ila", Saree ya ce.
A makon jiya, Isra'ila ta zargi kungiyar 'yan tawayen Yemen din wadda Iran ke marawa baya da tura jirage marasa matuka tare da haddasa fashewar abubuwa a garuruwan Masar biyu - tana cewa burinsu su kai farmaki Isra'ila.
Babban Bankin Najeriya ya ce ba shi da wani shiri na sake kirkiro sabbin takardun naira a shekara mai zuwa.
Wata sanarwa da daraktan sadarwa na Bankin Najeriya, Isa Abdulmumin ya fitar ranar Talata, ta bukaci 'yan Najeriya su yi watsi da wani takaitaccen sakon waya da ake yadawa, wanda ke nuna cewa CBN na shirin sake bullo da sabbin takardun naira a shekara ta 2024.
Ya nunar cewa sakon ba haka yake ba.
“Mun shiga damuwa game da wannan batu, wanda muka musanta tun ba yanzu ba, amma ga alama yana samun karbuwa da muhawara masu yawa a kan illar irin wannan manufa ga tattalin arzikin Najeriya.
CBN ya ce “Muna son jaddada cewa bayanin da ke cikin wannan sako, ba haka yake ba". Ya kara da cewa masu wallafa sako a yunkurinsu na jamhuru, sun jirkita rubutun daga wata tsohuwar manufa ta gwamnan CBN na baya a shekara ta 2007, amma sai suke bayyana shi tamkar yanzu ya faru.
Ya dai nanata cewa a yanzu babu wani shiri na sake fasalin takardun kudin kasar.
Ministan harkokin cikin gida na Pakistan, Sarfraz Bugti ya ce hukumomin ƙasar za su fara tattarawa da korar ƴan gudun hijira da ba su da takardun izinin zama a ranar Alhamis ciki har da dubban daruruwan 'yan kasar Afghanistan.
Bugti ya ce waɗanda suka fita bisa raɗin kansu za su samu taimako a cibiyoyin wucin gadi da aka kafa domin tsugunar da su.
Dubban 'yan ƙasar Afganistan sun garzaya zuwa kan iyakar ƙasar kafin wa'adin da aka bayar na barin Pakistan ya ƙare.
Wani jami'in ya ce layukan motoci suna jira a kan iyakar Torkham da Afghanistan.
Akwai kimanin mutane miliyan ɗaya da rabi da ke fuskantar kora.
Majalisar Dinkin Duniya dai da sauran ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun buƙaci Pakistan da ta dakatar da aikin korar.
Firaministan Masar Mostafa Madbouly, ya yi watsi da duk wani shiri na mutanen da suka yi gudun hijira daga Gaza su koma zuwa yankin Sinai na Masar.
Wasu jami'an gwamnatin Isra'ila, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida na Isra'ila suka ruwaito, sun ba da shawarar mayar da fararen hular Gaza zuwa arewa maso gabashin Masar
Sai dai, a ziyarar da ya kai arewacin Sinai, Madbouly ya jaddada cewa, bai kamata a magance rikice-rikicen yankin ba, ta hanyar cin gajiyar kasar Masar.
Mashigar Rafah da ke karkashin ikon Masar dai ta kasance hanya daya tilo da fararen hular Falasɗinawa ke iya barin Gaza.
Muna ci gaba da kawo muku sabbin rahotanni a kan mamaye ta kasa da Isra'ila ke yi a Gaza - ta ce manufar hakan ita ce ta ruguza Hamas.Tashoshin shafin sada zumunta na Telegram wadanda Hamas da Islamic Jihad ke gudanarwa su ma suna ba da rahotanni kan abin da ke faruwa.
A cewar wadannan rahotanni, Reshen Hamas mai gwagwarmaya da makamai, na Al Qassam sun yi iƙirarin;
Har ila yau dakarun Quds, na Falasdinawa masu gwagwarmaya da makamai sun yi ikirarin kai hari kan wasu rukunin sojojin Isra'ila da wasu motoci dauke da harsasai a kusa da Erez da Al-Atatra a arewa maso yammacin Gaza.
Yana da muhimmanci a lura cewa BBC ba ta iya tabbatar da jerin ikirari nan take ba.
A farkon wannan watan dai kafin fara gagarumin farmaki ta kasa - Isra'ila ta tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikin sojojinta a wani samame da ta kai yankin Zirin Gaza.
Wani bidiyo da Rundunar Sojojin Isra'ila ta fitar a yau Talata, ya nuna dakarunta a kasa, suna kutsawa cikin Gaza.